Tambayoyi Daga Masu Karatu
Sa’anda Yesu Kristi ya tura manzanni goma sha biyu yin wa’azi, shin ya gaya musu ne su ɗauki sanduna kuma su sa takalma?
Wasu mutane suna musu cewa labarai uku na Linjila da suka bayyana yadda Yesu ya tura manzanninsa ba su jitu ba. Ta wurin gwada waɗannan labarai, za mu zo ga kammalawa mai kyau. Da farko, ku gwada abin da Markus da Luka suka rubuta. Labarin Markus ya ce: “[Yesu] ya dokace su kada su ɗauki guzuri, sai sanda kaɗai; banda gurasa, banda jika, banda kuɗi a cikin ɗamarassu; sai a tafi da takalma a ƙafa: kada a sa riga biyu kuma.” (Mar. 6:7-9) Luka ya rubuta: “Kada ku ɗauki kome domin tafiya, ko sanda, ko zabira, ko gurasa, ko kuɗi; kada ku yi riga biyu.” (Luk 9:1-3) Mun lura da abin da ake gani kamar ba su jitu ba a waɗannan ayoyin. Bisa ga rubutun Markus, an gaya wa manzannin su ɗauki sanda kuma su saka takalma, amma rubutun Luka ya ce kada su ɗauki kome, ko ma sanda. Luka bai ambata takalma ba kamar Markus.
Don fahimtar abin da Yesu yake neman ya bayyana a wannan lokacin, ka lura da kalmomi da suke cikin duka Linjila ukun. A labaran da aka yi ƙaulinsu da kuma a littafin Matta 10:5-10, an gaya wa manzannin cewa kada su saka ko kuma riƙe “riguna biyu.” Wataƙila, kowanne cikin manzannin yana saka riga ’yar ciki guda. Saboda haka, ba sa bukatar tafiya da wata riga. Hakazalika, sun saka takalma. Markus ya nanata bukatar sa “takalma a ƙafa,” wato, takalman da sun riga sun saka. Sanduna kuma fa? Littafin nan The Jewish Encyclopedia ya ce: “Wataƙila yin tafiya da sanda al’adar Ibraniyawa ce a dā.” (Far. 32:10) Markus ya ambata cewa manzannin ba sa bukatar su “ɗauki guzuri don tafiyar” sai dai sanda da suke riƙe da shi sa’ad da Yesu yake ba da umurnin. Saboda haka, marubutan Linjilar suna nanata umurnin Yesu na cewa kada su makara garin neman ƙarin abubuwa don tafiyar.
Matta ya sake nanata wannan batun, da yake ya ji sa’ad da Yesu ya ba da umurnin kuma shi ya rubuta shi. Yesu ya ce: ‘Kada ku yi tanajin zinariya, ko azurfa, ko jan ƙarfe cikin ɗamararku; ko jakka domin hanya, ko riguna biyu, ko takalma, ko sanda: gama ma’aikaci ya isa abincinsa.’ (Mat. 10:9, 10) Takalman da manzannin suka saka da kuma sandunan da suke riƙe da su a hannayensu kuma fa? Yesu yana gaya musu kada su yi tanadin waɗannan abubuwan, amma bai ce musu su jefar da abin da suke da shi ba. Don me ya ba da irin wannan umurnin? Domin “ma’aikaci ya isa abincinsa.” Ma’anar umurnin Yesu ke nan, wanda ya jitu da gargaɗinsa a Huɗuba a kan dutse cewa kada su yi alhinin abin da za su ci, sha, ko kuma abin da za su yafa.—Mat. 6:25-32.
Ko da yake labaran Linjila da farko za su iya zama kamar ba su jitu ba, amma dukansu suna magana a kan batu ɗaya. An bukaci manzannin su je daidai yadda suka saba kuma kada neman ƙarin abubuwa ya janye hankalinsu. Me ya sa? Domin Jehobah zai yi musu tanadi.
A littafin Mai-Wa’azi 2:8 na fassarar New World Translation da wasu fassarorin Littafi Mai Tsarki, Sulemanu ya yi maganar “mace, har ma ’yan mata” su wane ne Sulemanu yake zancen su?
Ba za mu iya kasance da tabbaci ba, amma abu ɗaya mai yiwuwa shi ne su sanannun mata ne da Sulemanu ya gamu da su a fada.
A littafin Mai-Wa’azi sura 2, Sulemanu ya ambata abubuwa dabam dabam da ya cim ma, haɗe da tsarin gine-gine masu girma. Ya daɗa: “Na tattaro azurfa da zinariya da taskokin sarakuna, da na ƙasashe; na samo mawaƙa maza da mata, da abin marmari ga ’yan Adam, da mace, har ma ’yan mata.”—M. Wa. 2:8, NW.
’Yan sharhi da yawa suna ganin cewa “mace, har ma ’yan mata” da Sulemanu yake zancen su su ne mata baƙi da kuma ƙwaraƙwarai da ya kawo daga baya, mata da suka sa shi yin bautar ƙarya. (1 Sar. 11:1-4) Saboda haka, akwai matsala da wannan bayanin. Lokacin da Sulemanu ya rubuta waɗannan kalmomin, ya riga ya sarƙu da “mace, har ma ’yan mata.” Kuma a wannan lokacin yana da dangantaka mai kyau da Jehobah, domin Allah yana hure shi ya rubuta littattafan Littafi Mai Tsarki. Wannan shekarun rayuwarsa ba sa’ad da ya auri mata ɗarurruwa daga wasu al’ummai da kuma ƙwaraƙwarai kuma ya soma bauta ta ƙarya ba.
A littafin Mai-Wa’azi, Sulemanu ya ce ya nemi “ya sami magana masu-daɗin ji, da abin da aka rubuta daidai, kalmomin gaskiya ke nan.” (M. Wa. 12:10) Alhali ya san da kalmomin nan na “mata,” “sarauniya,” da kuma “ƙwaraƙwarai,” domin ya yi amfani da waɗannan kalmomin a hurarun rubuce-rubucensa. (Mis. 5:18; 12:4; 18:22; M. Wa. 9:9; W. Waƙ. 6:8, 9) Amma a littafin Mai-Wa’azi 2:8, ba a yi amfani da waɗannan sanannun kalmomin ba.
A cikin waɗannan kalmomi na “mace, har ma ’yan mata,” mun samu wuri ɗaya kawai da aka yi amfani da (tilo da kuma jam’i) a cikin Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba a saba ba a yaren Ibrananiyawa. Masana sun yarda cewa ba a san ma’anarta ba. Masu fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa sun ɗauki wannan furcin da yake Mai-Wa’azi 2:8 cewa yana magana ne ga mata, da aka ambata tilo da sa’annan kuma jam’i wanda babu kamarsa. Juyin nan “mace, har ma ’yan mata” ya nuna abin da wannan azancin yake nufi.
Sulemanu sananne ne sosai, har ya sa sarauniyar Sheba daga mulki mai wadata ta ji labarin shi, ta ziyarce shi, kuma ya burge ta. (1 Sar. 10:1, 2) Wannan ya nuna ainihin ma’anar furcin Sulemanu na “mace, har ma ’yan mata.” Mai yiwuwa yana nuni ne ga fitattun mata da ya gamu da su a fadarsa a shekaru da yawa da yake da dangantaka mai kyau da Allah.