Ka Motsu Ka Yi Yadda Yesu Ya yi?
“Ya ga taro mai-yawa, ya ji juyayinsu, gama kamar tumaki su ke waɗanda ba su da makiyayi: ya fara koya masu.”—MARKUS 6:34.
1. Me ya sa za a fahimci abin da ya sa wasu mutane suke nuna kyawawan halaye?
ACIKIN dukan tarihi, mutane da yawa sun nuna kyawawan halaye. Za ka iya fahimtar abin da ya sa. Jehovah Allah yana da, kuma yana nuna ƙauna, kirki, yana yin kyauta, da kuma wasu halaye da muke so. An halicci mutane a kamanin Allah. Saboda haka za mu iya fahimtar abin da ya sa mutane da yawa suna iya nuna ɗan ƙauna, kirki, tausayi, da kuma wasu halaye irin na Allah, kamar yadda yawanci suke nuna suna da lamiri. (Farawa 1:26; Romawa 2:14, 15) Ko da yake, za ka iya gane cewa wasu suna nuna waɗannan halaye da sauƙi fiye da wasu.
2. Waɗanne nagargarun ayyuka ne mutane sukan yi da jin cewa suna kwaikwayon Kristi?
2 Wataƙila ka san maza da mata waɗanda sau da yawa sukan ziyarci ko kuma taimaka ma majiyata, sukan ji tausayin naƙasassu, ko kuma sukan bada kyauta ga matsiyata. Ka tuna kuma da wasu mutane waɗanda tausayinsu ya motsa su bada rayuwansu ga aiki a mazaunan kutare ko kuma gidan marayu, waɗanda suka bada kansu ga yin aiki a asibiti ko kuma wajen kula da masu rashin lafiya mai tsanani, ko mutane waɗanda suke ƙoƙari su taimaki marasa gidaje ko ’yan gudun hijira. Mai yiwuwa wasunsu suna jin suna kwaikwayon Yesu, wanda ya kafa tafarki wa Kiristoci. A cikin Lingila mun karanta cewa Kristi ya warkar da masu rashin lafiya kuma ya ciyar da mayunwata. (Markus 1:34; 8:1-9; Luka 4:40) Ƙauna, kulawa, da juyayin da Yesu ya nuna, bayyana ne na “nufin Kristi,” wanda shi ma kwaikwayon Ubansa na sama ya yi.—1 Korinthiyawa 2:16.
3. Don mu fahimci daidai nagargarun ayyukan Yesu, me ya kamata mu bincika?
3 Ka lura cewa mutane da yawa a yau da ƙauna da kuma juyayin Yesu ya motsa su, sun ƙyale wani muhimmin sashi na nufin Kristi? Za mu sami fahimi cikin wannan ta bincika Markus sura 6 a hankali. A wurin mun karanta cewa mutane sun kawo marasa lafiya wa Yesu ya warkar da su. A cikin mahallin, mun gane cewa da ya ga dubbai da suka zo wurinsa suna jin yunwa, Yesu ya ciyar da su ta hanyar al’ajibi. (Markus 6:35-44, 54-56) Warkar da marasa lafiya da kuma ciyar da mayunwata muhimmiyar hanya ce ta nuna ƙauna da kuma juyayi, amma sune hanyoyi mafi muhimmanci da Yesu ya taimaki wasu? Kuma ta yaya za mu iya yin kwaikwayon misalinsa mafi kyau na ƙauna, kirki, da kuma juyayi, kamar yadda ma ya yi kwaikwayon Jehovah?
Ya Motsu Ya Biya Bukatu na Ruhaniya
4. Me ya faru a labarin da yake cikin Markus 6:30-34?
4 Yesu ya ji tausayin waɗanda suke wurinsa musamman domin bukatunsu na ruhaniya. Waɗannan bukatu sun fi muhimmanci fiye da bukatu na jiki. Ka yi la’akari da labarin Markus 6:30-34. Abin da ya auku da aka rubuta ya auku ne a gaɓar Tekun Galili, kusa da lokacin Faska ta shekara ta 32 A.Z. Manzanni suna murna, da kyakkyawan dalili. Bayan sun gama tafiye-tafiyensu mai yawa, sun zo wurin Yesu, babu shakka suna zumamin ba shi labarin abin da suka gani. Duk da haka, jama’a sun taru. Taron ya yi yawa sosai da har Yesu da manzanninsa ba su sami damar hutu ba balle su ci abinci. Yesu ya gaya wa manzannin: “Ku zo da kanku waje ɗaya inda ba kowa, ku huta kaɗan.” (Markus 6:31) Suka shiga jirgin ruwa, wataƙila kusa da Kafarnahum, suka haye zuwa ƙetaren Tekun Galili wajen da babu kowa. Amma jama’an suka ruga ta gabar tekun suka riga jirgin zuwa. Yaya Yesu zai yi? Ya yi fushi ne cewa ba a bar shi ya huta ba? Ko kaɗan!
5. Yaya Yesu ya ji game da jama’a da suka zo wurinsa, kuma me ya yi masu?
5 Ganin waɗannan dubban jama’a haɗe da marasa lafiya, waɗanda suke jiransa da marmari, ya sa Yesu ya ji juyayi. (Matta 14:14; Markus 6:44) Da Markus yake ambata abin da ya sa Yesu ya ji juyayi, ya rubuta: “Ya ga taro mai-yawa, ya ji juyayinsu, gama kamar tumaki su ke waɗanda ba su da makiyayi: ya fara koya masu abu dayawa.” (Markus 6:34) Yesu ya ga mutane babu iyaka. Ya ga mutane da suke da bukatu na ruhaniya. Suna kama da tumaki da suka ɓata, ba su da makiyayi da zai kai su kiwo ko kuma ya tsare su. Yesu ya san cewa shugabanan addinai marasa tausayi, waɗanda ya kamata su zama makiyaya masu kula, sun la’anci talakawan kuma ba sa biya masu bukatunsu na ruhaniya. (Ezekiel 34:2-4; Yohanna 7:47-49) Yesu ya yi niyyar kula da su, yin abin da ya fi kyau garesu. Ya fara koya masu game da Mulkin Allah.
6, 7. (a) Menene Linjila ta bayyana ya fi muhimmanci a yadda Yesu ya biya bukatun mutanen? (b) Menene ya motsa Yesu ya yi wa’azi da kuma koyarwa?
6 Ka lura da jeri da kuma abin da ya fi muhimmanci a cikin labarin da ke hannun riga da shi. Luka ne ya rubuta wannan, shi likita ne wanda ya damu da lafiyar wasu. “Taron . . . suka bi bayansa [Yesu]: ya karɓe su, ya yi masu zance a kan mulkin Allah; waɗanda su ke bukatar warkaswa kuma, ya warkadda su.” (Luka 9:11, tafiyar tsutsa tamu ce; Kolossiyawa 4:14) Ko da ba haka yake ba a dukan labarin mu’ujiza, a cikin wannan, menene hurarren labarin Luka ya faɗa da fari? Zancen nan cewa Yesu ya koyar da mutanen.
7 Wannan babu shakka ya jitu da nanaci da muka samu daga cikin Markus 6:34. Wannan ayar ta nuna sarai abin da musamman ya motsa Yesu ya ji tausayi. Ya koya wa mutanen, wajen biya masu bukatunsu na ruhaniya. Da farko a cikin hidimarsa, Yesu ya ce: “Dole sai in yi Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Amma dai, ba zai zama daidai ba idan muka yi tunanin cewa Yesu ya sanar da saƙon Mulkin kawai domin aikinsa ne, kamar dai ya yi aikin wa’azin don dole ne. A’a, juyayinsa mai kyau ga mutanen shine muhimmin dalilin sanar masu bishara. Taimako mafi girma da Yesu ya yi—har wa marasa lafiya, masu aljanu, matsiyata, ko kuma mayunwata—shine ya taimake su su san, su karɓa, kuma su so gaskiya game da Mulkin Allah. Wannan gaskiyar tana da muhimmanci domin matsayin Mulkin a kunita ikon mallaka na Jehovah da kuma tanadar da albarka na dindindin wa ’yan Adam.
8. Yaya Yesu ya ji game da wa’azi da kuma koyarwarsa?
8 Wa’azin Yesu da ƙwazo game da Mulkin shine muhimmiyar dalilin da ya sa Yesu ya zo duniya. A kusan ƙarshen hidimarsa a duniya, Yesu ya gaya wa Bilatus: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin im bada shaida ga gaskiya. Kowanene da ke na gaskiya ya kan ji muryata.” (Yohanna 18:37) A cikin talifai biyu da suka gabata, mun lura cewa Yesu mutum ne mai juyayi—mai kula, mai sauƙin kai, mai la’akari, mai amincewa, fiye da duka kuma, mai ƙauna. Idan muna so mu gane nufin Kristi da gaske muna bukatar mu fahimci waɗannan ɓangaren mutumtakarsa. Yana da muhimmanci kuma mu san cewa nufin Kristi ta haɗa da yadda ya sa aikin wa’azi da kuma koyarwarsa a farko.
Ya Aririce Wasu Su Bada Shaida
9. Ga su wanene wa’azi da kuma koyarwa ya fi fifiko?
9 Fifita da aka ba wa’azi da kuma koyarwa—don nuna ƙauna da juyayi—ba don Yesu ne kaɗai ba. Ya aririce mabiyansa su yi kwaikwayon abin da ya motsa shi, abin da ya fi muhimmanci gareshi, da kuma ayyukansa. Alal misali, bayan Yesu ya zaɓi manzanninsa 12, me za su yi? Markus 3:14, 15 ya gaya mana: “Ya sanya goma sha biyu, [waɗanda ya kira ‘manzanni,’ NW ] domin su zauna tare da shi, domin kuma shi aike su garin su yi wa’azi, su kuma sami ikon da za su fitarda aljanu.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Ka ga abin da ya fi fifiko ga manzannin?
10, 11. (a) Lokacin da zai aike manzannin, menene Yesu ya gaya masu su yi? (b) A lokacin da ya aike manzannin, menene muhimmin abu da za su yi?
10 Daga baya, Yesu ya sa 12 ɗin su warkar da wasu kuma su fitar da aljanu. (Matta 10:1; Luka 9:1) Sai ya aike su ziyara wajen “ɓattatun tumaki na gidan Isra’ila.” Su yi menene? Yesu ya umurce su: “A cikin tafiyarku kuma ku yi wa’azi, ku ce, Mulkin sama ya kusa. Ku warkadda marasa-lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku fitar da aljanu.” (Matta 10:5-8; Luka 9:2) To, menene suka yi da gaske? “Suka fita, suka [1] yi wa’azi mutane su tuba. [2] Suka fitarda aljanu dayawa, suka shashafe marasa-lafiya kuma dayawa da mai, suka warkadda su.”—Markus 6:12, 13.
11 Tun da ba a kowane misali ba ne aka ambaci koyarwa da farko, jeri na saman nan yana yawan sa muhimmanci akan batun abin da ya fi fifiko ko kuma muradin yin hakan? (Luka 10:1-9) To dai, kada mu rage muhimmancin yawan yadda aka ambaci koyarwa kafin warkarwa. Ka yi la’akari da mahallin a zancen nan. Jim kaɗan kafin ya aiki manzanni 12 ɗin, yanayin taron ya ba Yesu tausayi. Mun karanta cewa: “Yesu ya yi yawo cikin dukan birane da ƙauyuka, yana koyaswa cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin, yana warkadda kowace irin ciwuta da kowane irin rashin lafiya. Amma sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Sa’annan ya ce ma almajiransa, Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa.”—Matta 9:35-38.
12. Mu’ujiza ta Yesu da manzanninsa tana da wane ƙarin manufa?
12 Ta wurin kasancewa tare da shi, manzannin sun koyi kaɗan daga nufin Kristi. Sun gano cewa kasancewarsu da ƙauna da kuma juyayi da gaske wajen mutane ya ƙunshi yin wa’azi da kuma koyarwa game da Mulkin—wannan shine muhimmiyar sashe na nagargarun ayyukansu. Game da wannan, nagargarun ayyuka irin ta zahiri, kamar su warkar da marasa lafiya, ya yi fiye da taimaka wa mabukata kawai. Kamar dai yadda ka sani, warkarwa da kuma ciyar da mutane ta hanyar al’ajabi ya jawo wasu mutane. (Matta 4:24, 25; 8:16; 9:32, 33; 14:35, 36; Yohanna 6:26) Amma dai, fiye da taimako na zahiri, waɗannan ayyuka hakika sun motsa masu lura su gane cewa Yesu Ɗan Allah ne “annabin” da Musa ya annabta.—Yohanna 6:14; Kubawar Shari’a 18:15.
13. Annabci da ke cikin Kubawar Shari’a 18:18 ya nuna wane aiki ne na “annabin” da zai zo?
13 Me ya sa yake da muhimmanci cewa Yesu shine “annabin”? Wane ayyuka ne na musamman aka faɗa game da wannan? An ce wannan “annabin” zai zama mashahuri ne wajen warkarwa da mu’ujiza ko kuma bada abinci wa mayunwata don juyayi? Kubawar Shari’a 18:18 ta annabta: “Ni tayar masu da annabi daga cikin yan’uwansu, kamarka [Musa]; in kuma sa zantattukana cikin bakinsa, za ya kuwa faɗa masu dukan abin da na umurce shi da shi.” Saboda haka har lokacin da manzannin suke koyon yin juyayi da kuma nuna shi, sun kammala cewa nufin Kristi ya kamata ya bayyana cikin ayyukansu na wa’azin da kuma koyarwa. Wannan shine abu mafi kyau da za su yi wa mutane. Ta haka, marasa lafiya da masiyata za su amfana na dindindin, ba kawai amfani na ɗan lokaci na gajeren rayuwan ’yan Adam ba ko ɗan kalaci da za su ci sau ɗaya ko biyu ba.—Yohanna 6:26-30.
Ka Gina Nufin Kristi a Yau
14. Yaya yin wa’azinmu ya ƙunshi kasance da nufin Kristi?
14 Babu waninmu da zai ga nufin Kristi kamar aba ce musamman don ƙarni na farko—don Yesu da kuma almajiransa na farko waɗanda manzo Bulus ya rubuta game da su: “Nufin Kristi yana wurinmu.” (1 Korinthiyawa 2:16) Babu ɓata lokaci, za mu yarda cewa tilas ne mu yi wa’azin bishara kuma mu almajirantar da mutane. (Matta 24:14; 28:19, 20) Duk da haka, yana da amfani mu bincika muradinmu na yin aikin. Kada ya zama kawai muna yi don an ce mu yi ne. Ƙauna ga Allah ita ce muhimmiyar dalilin da ya sa muke haɗa hannu a yin hidima, kuma zama kamar Yesu da gaske ya ƙunshi zama wanda juyayi ke motsa mu mu yi wa’azi kuma mu koyar.—Matta 22:37-39.
15. Me ya sa juyayi sashen da ya dace ne a cikin hidimarmu ga jama’a?
15 Gaskiya, yana da wuya wasu lokutta a yi juyayin waɗanda ba su yarda da abin da muka yarda da su ba, musamman ma lokacin da muka fuskanci rashin marmari, ƙi, ko kuma hamayya. Duk da haka, idan muka ƙi mu so mutane ko mu yi juyayinsu, za mu yi rashin muhimmin abin da ke motsa mu mu yi aikin hidima ta Kirista. To, ta yaya za mu gina yin juyayi? Za mu yi ƙoƙarin gane mutane kamar yadda Yesu ya gane su, kamar “tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Wannan bai kwatanta wasu da yawa da suke haka ba? Maƙiyayan addinin ƙarya sun yashe kuma sun makantar da su a ruhaniya. Saboda wannan, ba su san lafiyayyar ja-gora ba da ke cikin Littafi Mai-Tsarki, ko kuma yanayin Aljanna wanda Mulkin Allah zai kawo nan gaba kaɗan bisa duniyarmu. Suna fuskantar matsalolin rayuwa na yau da kullum—haɗe da talauci, hargitsin iyali, ciwo, da kuma mutuwa—ba tare da bege na Mulki ba. Muna da abin da suke bukata: bisharar mai ceton rai ta Mulkin Allah wanda yanzu ya kafu a cikin sama!
16. Me ya sa ya kamata mu so gaya ma wasu bisharar?
16 Lokacin da ka yi bimbinin bukatu na ruhaniya na waɗanda suka kewaye ka, zuciyarka ba ta motsa ka ka yi iyaka ƙoƙarinka ka gaya masu game da nufin Allah na ƙauna? Babu shakka, aikinmu na nuna juyayi ne. Idan muka ji tausayin mutane kamar yadda Yesu ya yi, zai bayyana cikin muryoyinmu, a fuskokinmu, a yadda muke koyarwa. Dukan wannan za su sa saƙonmu ya zama da daɗi ga “dukan waɗanda suke da zuciyar kirki don rai na har abada.”—Ayukan Manzanni 13:48, NW.
17. (a) Waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙauna da kuma juyayi ga wasu? (b) Me ya sa ba batun yin nagargarun ayyuka ko kuma yin hidima ga jama’a kawai ba ne?
17 Ya kamata ƙaunarmu da juyayi, su bayyana a dukan tafarkin rayuwarmu. Wannan ya ƙunshi muna yin kirki wa miskinai, marasa lafiya, da kuma matsiyata—muna yin abin da za mu iya yi don mu sauƙaƙa masu wahalarsu. Ya ƙunshi ƙoƙarinmu ta furci da kuma ayyuka wajen huce baƙin cikin waɗanda suka yi rashin wanda suke ƙauna. (Luka 7:11-15; Yohanna 11:33-35) Duk da haka, irin nuna ƙaunar nan, kirki, da kuma juyayi kada ya zama ainihin muhimmancin nagargarun ayyukanmu, kamar yadda yake ga wasu masu bada taimako. Ƙoƙari da irin ingancin nan na Allah ke motsa mu mu yi sun fi jimawa amma kuma da wanda muke nuna wajen yin aikin wa’azi da koyarwa na Kirista. Ka tuna da abin da Yesu ya ce game da shugabannan addinin Yahudawa: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, masu-riya! gama kuna karɓan ushira ga ɗanɗoya da anise da algaru, amma kun ƙyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinƙai da bangaskiya: waɗannan fa wajib ne a gareku ku aika, ba kuwa a fasa waɗancan ba.” (Matta 23:23) Ga Yesu ba kawai batun ka zaɓi wannan ko wancan ba ne—ko taimakon mutane wajen bukatunsu na jiki ko kuma koya masu batun ruhaniya mai bada rai. Yesu ya yi duka biyun. Duk da haka, a bayyane yake sarai cewa aikin koyarwarsa ya fi muhimmanci domin taimakon da ya yi zai zama na har abada.—Yohanna 20:16.
18. Ga menene ya kamata bincikenmu na “nufin Kristi” zai motsa mu mu yi?
18 Ya kamata mu yi godiya wa Jehovah da ya bayyana mana nufin Kristi! Ta wurin Linjila, za mu iya samun sani sosai na tunani, juyayi, inganci, ayyuka, da kuma abin da ke fifiko na mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa. Ya rage a garemu mu karanta, mu yi bimbini akansa, kuma mu yi abin da Littafi Mai-Tsarki ya bayyana game da Yesu. Ka tuna, idan da gaske za mu yi kamar yadda Yesu ya yi, da farko sai mun koyi mu yi tunani, juyayi, kuma mu bincika al’amura yadda ya yi, ga iyakar gwargwadon iyawarmu na mutane ajizai. Bari mu ɗaura aniyar gina da kuma nuna nufin Kristi. Babu wata hanyar rayuwa da ta fi, babu hanyar da ta fi kyau a kula da mutane, kuma babu wata hanyar da ta fi mana kyau da kuma wasu don mu matso kusa ga wanda ya yi kwaikwayonsa daidai, Allahnmu mai ƙauna, Jehovah.—2 Korinthiyawa 1:3; Ibraniyawa 1:3.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane fahimi ne Littafi Mai-Tsarki ya bayar game da yadda sau da yawa Yesu yake biyan bukatun mutane da suke cikin bukata?
• Menene Yesu ya nanata a umurci mabiyansa?
• Ta yaya za mu nuna “nufin Kristi” a cikin ayyukanmu?
[Hoto a shafi na 17]
Menene nagarta mafi kyau da Kiristoci za su iya yi ma wasu?