Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Luka
AN RUBUTA Linjilar Matta ne ainihi domin Yahudawa, ita kuwa Linjilar Markus, an rubutata ne domin waɗanda ba Yahudawa ba ne. Amma, ita kuwa Linjilar Luka an rubutata ne domin mutanen dukan al’ummai. An rubuta shi ne a wajen shekara ta 56 zuwa 58 A.Z., kuma littafin Luka yana ɗauke ne da cikakken labarin rayuwar Yesu da hidimarsa.
Da halin likita mai kula da tausayi, Luka ya bincika tun daga fari “abu duka daidai” kuma hakan ya ɗauki shekaru 35, daga shekara ta 3 K.Z. zuwa 33 A.Z. (Luka 1:3) Kusan kashi 60 na abubuwan da ke Linjilar Luka ba sa cikin sauran Linjilolin.
HIDIMARSA TA FARKO
Bayan ya ba da bayanai game da haihuwar Yohanna mai Baftisma da kuma Yesu, Luka ya gaya mana cewa Yohanna ya soma hidimarsa a shekara ta 15 ta sarautar Tibariyus Kaisar, wato a farkon shekara ta 29 A.Z. (Luka 3:1, 2) Yohanna ya yi wa Yesu baftisma a kusan ƙarshen wannan shekarar. (Luka 3:21, 22) A shekara ta 30 A.Z., ‘Yesu ya komo cikin Galili kuma ya soma koyarwa a cikin majami’unsu.’—Luka 4:14, 15.
Yesu ya soma wa’azinsa na farko a Galili. Ya gaya wa taron cewa: “Dole sai in yi Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma.” (Luka 4:43) Ya tafi tare da Siman mai kamun kifi da kuma wasu. Sai ya ce: “Daga nan gaba za [ku] kama mutane.” (Luka 5:1-11) Manzanninsa 12 suna tare da Yesu sa’ad da ya sake kewaye Galili a karo na biyu yana wa’azi. (Luka 8:1; Mat. 4:18, 19) A fitarsa ta uku, ya tura su sha biyun su “yi wa’azin mulkin Allah, su warkadda marasa lafiya.”—Luka 9:1, 2.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:35—Ƙwan cikin Maryamu ya cika gurbi a cikin da ta ɗauka? Idan ana son ɗan da Maryamu ta haifa ya zama jikan kakanninsa Ibrahim, Yahuda, da Dauda, kamar yadda Allah ya yi alkawari, dole ne a yi amfani da ƙwanta a halicci ɗan da za ta haifa. (Far. 22:15, 18; 49:10; 2 Sam. 7:8, 16) Amma fa, an yi amfani ne da ruhu mai tsarki na Jehobah wajen mai da kamiltaccen ran Ɗan Allah a cikin mahaifar Maryamu kuma ya sa ta ɗauki ciki. (Mat. 1:18) Hakan ya kawar da duk wani ajizancin da ke cikin ƙwan Maryamu kuma ruhun ya kāre ɗan tayin daga samun duk wata irin nakasa.
1:62—Zakariya ya zama kurma ne? A’a. Abin ya shafi muryarsa ce kawai. Mutane sun yi amfani ne da “nuni” don su tambaye shi sunan da yake son ya raɗa wa yaron amma hakan ba ya nufin cewa Zakariya ya kurmance. Wataƙila ya ji abin da matarsa ta ce game da sa wa yaron suna. Wataƙila wasu sun tambayi Zakariya ne game da wannan ta wajen yin amfani da alama. Domin muryarsa ce kawai ake bukatar a buɗe, hakan ya nuna cewa Zakariya yana jin magana.—Luk 1:13, 18-20, 60-64.
2:1, 2—Ta yaya ne bayanin nan “rubutu na fari” ya taimaka wajen sanin lokacin da aka haifi Yesu? A lokacin sarautar Kaisar Augustus, an yi ƙidaya fiye da guda, an yi na farkon ne a shekara ta 2 K.Z. don cikar Daniel 11:20 kuma an yi na biyun ne a shekara ta 6 ko 7 A.Z. (A. M. 5:37) Kiriniyus ne gwamnar Suriya a waɗannan lokuttan da aka yi ƙidayar, hakan na nufin cewa ya riƙe wannan maƙamin sau biyu. Ƙidaya na farko da Luka ya ambata ya nuna cewa an haifi Yesu ne a shekara ta 2 K.Z.
2:35—Mecece ma’anar ‘takobin’ nan da zai tsaga ran Maryamu? Wannan yana nuni ne ga baƙin cikin da Maryamu za ta yi sa’ad da ta ga mutane sun ƙi Yesu a matsayin Almasihu da kuma baƙin cikin da za ta yi saboda mutuwarsa.—Yoh. 19:25.
9:27, 28—Me ya sa Luka ya ce sake kamani ya faru ne “kwana wajen takwas” bayan da Yesu ya yi wa almajiransa alkawari cewa wasu a cikinsu “ba za su ɗanɗana mutuwa ba daɗai” har sai sun gan shi yana dawowa a cikin Mulkinsa, kuma Matta da Markus suka ce “bayan kwana shida”? (Mat. 17:1; Mar. 9:2) Luka ya daɗa kwana biyu ne, wato, ranar da aka yi alkawarin da kuma ranar da ya cika.
9:49, 50—Me ya sa Yesu bai hana wani mutumin da ke fitar da aljanu ba, duk da cewa mutumin ba mabiyinsa ba ne? Yesu bai hana mutumin ba domin a wannan lokacin ba a kafa ikilisiyar Kirista ba. Saboda haka, mutumin ba ya bukatar ya yi ta bin Yesu kafin ya ba da gaskiya ga sunan Yesu kuma ya fitar da aljanu.—Mar. 9:38-40.
Darussa Dominmu:
1:32, 33; 2:19, 51. Maryamu ba ta mance dukan abubuwan da suka faru da kuma waɗanda aka gaya mata da suka cika annabce-annabcen da aka yi ba. Muna tuna abubuwan da Yesu ya annabta game da “cikar zamani,” kuma muna haɗa abubuwan da ya ce da abubuwan da ke faruwa a yau kuwa?—Mat. 24:3.
2:37. Misalin Hannatu ya koya mana cewa muna bukatar mu bauta wa Jehobah a kullum, mu “lizima cikin addu’a,” kuma kada mu fasa “tattaruwanmu” a taron Kirista.—Rom. 12:12; Ibran. 10:24, 25.
2:41-50. Yusufu ya mai da abubuwa na ruhaniya abin farko a rayuwarsa kuma ya biya bukatu na zahiri da ruhaniya na iyalinsa. A waɗannan batutuwan, ya kafa wa shugabannin iyalai misali mai kyau.
4:4. Kada mu ƙyale rana ɗaya ta wuce ba tare da mun tattauna abubuwa na ruhaniya ba.
6:40. Ya kamata malamin Kalmar Allah ya kafa misali mai kyau ga ɗalibansa. Dole ne ya yi abubuwan da yake koyarwa.
8:15. Don mu ‘riƙe [kalmar] da haƙuri kuma mu bada amfani,’ muna bukatar mu fahimci Kalmar Allah, mu ɗauke ta da tamani, kuma mu karantata sosai. Muna bukatar mu yi addu’a kuma mu yi bimbini sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki.
HIDIMAR YESU TA ƘARSHE
Yesu ya tura mutane saba’in zuwa cikin birane da wurare a Yahudiya. (Luka 10:1) Ya yi tafiye-tafiye “yana ratsa birane da ƙauyuka, yana koyaswa.”—Luka 13:22.
Kwanaki biyar kafin Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z., Yesu ya shiga cikin Urushalima a kan jaki. Lokaci ya yi da kalmominsa ga almajiransa za su cika: “Ya ce, Dole sai Ɗan mutum ya sha wahalar abu dayawa; datiɓai da manyan malamai da marubuta su ƙi shi, a kashe shi, rana ta uku kuma a tashe shi.”—Luka 9:22, 44.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
10:18—Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa almajiransa guda saba’in cewa: “Na ga Shaiɗan faɗaɗe kamar walƙiya daga sama”? Yesu ba ya nufin cewa an riga an kori Shaiɗan daga sama. An kori Shaiɗan ne bayan da aka naɗa Kristi Sarki a sama a shekara ta 1914. (R. Yoh. 12:1-10) Wataƙila Yesu ya yi amfani ne da shuɗaɗɗen lokaci wajen nuna abin da zai faru a nan gaba don ya tabbatar da cewa hakan zai faru.
14:26—Ta yaya ne mabiyan Kristi za su “ƙi” danginsu? A cikin Littafi Mai Tsarki, “ƙi” yana iya nufin nuna ƙauna ga wani fiye da wani ko kuwa wani abu dabam. (Far. 29:30, 31) Kiristoci za su “ƙi” danginsu ne ta wajen ƙaunar Yesu fiye da danginsu.—Mat. 10:37.
17:34-37—Su wanene “angulai,” kuma wanene ‘gawar’ da suka taru a kai? An kwatanta waɗanda aka “ɗauka,” ko cece su, da angulai masu hangen nesa. ‘Gawar’ da suka taru a kai shi ne Kristi na gaskiya a bayyanuwarsa wanda ba a gani da ido, da kuma abinci na ruhaniya wanda Jehobah yake yi musu tanadi.—Mat. 24:28.
22:44—Me ya sa Yesu ya sha wahala sosai? Hakan ya faru ne don dalilai masu yawa. Yesu ya damu ne da yadda mutuwarsa a matsayin mai laifi za ta shafi Jehobah Allah da sunansa. Ƙari ga haka, Yesu ya sani sosai cewa rayuwarsa ta har abada da kuma rayuwar dukan mutane ta dangana ne a kan riƙe amincinsa.
23:44—Husufin rana ne ya jawo duhu na awa ukun da aka yi? A’a. Ana husufin rana ne kawai a lokacin da sabon wata ya fito, ba sa’ad da wata ya fita ba sosai, kamar lokacin Idin Ƙetarewa. Duhun da aka yi a ranar mutuwar Yesu mu’ujiza ce daga Allah.
Darussa Dominmu:
11:1-4. Idan muka gwada waɗannan umurnin da kalaman da ke cikin addu’ar Ubangiji wadda ta ɗan bambanta da wannan, wadda aka yi a Huɗuba Bisa Dutse watanni 18 kafin wannan lokacin, za mu ga cewa bai kamata addu’armu ta zama maimaita wasu kalmomi ba kawai.—Matt. 6:9-13.
11:5, 13. Ko da yake Jehobah yana shirye ya amsa addu’o’inmu, muna bukatar mu dage sa’ad da muke addu’a.—Luk 11:5, 13.
11:27, 28. Ana samun cikakken farin ciki ne kawai ta wajen yin nufin Allah da aminci ba dangantaka da iyali ba ko kuwa dukiyar da aka tara.
11:41. Ya kamata kyautar da za mu ba da ta fito ne daga cikin zuciyarmu.
12:47, 48. Wanda yake da hakki mai yawa amma ya ƙi kula da su laifinsa ya fi na wanda bai san ayyukansa ko kuwa bai fahimce su ba sosai.
14:28, 29. Yana da kyau mu yi rayuwa daidai ƙarfinmu.
22:36-38. Yesu bai gaya wa almajiransa su ɗauki makami don su kāre kansu ba. Maimakon haka, takobin da suka riƙe a daren da aka ci amanarsa ya sa Yesu ya koya musu darassi mai muhimmanci: “Duk wanda ya zari takobi, takobi ne ajalinsa.”—Mat. 26:52, Littafi Mai Tsarki.
[Hoto a shafi na 31]
Yusufu ya kafa misali mai kyau a matsayin maigida
[Hoto a shafi na 32]
Luka ya rubuta cikakken labarin rayuwar Yesu da hidimarsa