Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
“Ɗana, ka san Allah na ubanka, ka bauta masa da sahihiyar zuciya.”—1 LABA. 28:9.
KA NEMI AMSOSHIN WAƊANNAN TAMBAYOYI:
․․․․․
Mece ce zuciya ta alama?
․․․․․
A wace hanya ce za mu bincika zuciyarmu?
․․․․․
Ta yaya za mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya?
1, 2. (a) Wace gaɓa ta jiki ce ake yawan amfani da ita a alamance a cikin Kalmar Allah? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci abin da zuciya ta alama take nufi?
SAU da yawa, Kalmar Allah tana yin amfani da gaɓoɓi dabam-dabam na jikin ’yan Adam wajen yin kwatance. Alal misali, Ayuba ya ce: ‘Ba aikin zilama a hannuwana ba.’ Sarki Sulemanu ya ce: ‘Bishara kuma tana sa ƙasussuwa su yi ƙiba.’ Jehobah ya tabbatar wa Ezekiel: ‘Na sa kanka ya yi ƙarfi kamar dutse.’ Kuma wasu mutane sun gaya wa manzo Bulus: ‘Kana kawo waɗansu baƙin al’amura ga kunnuwanmu.’—Ayu. 16:17; Mis. 15:30; Ezek. 3:9; A. M. 17:20.
2 Amma, an fi yin amfani da wata gaɓa ta jiki a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan gaɓa ita ce wadda Hannatu mai aminci ta ambata sa’ad da take addu’a: ‘Zuciyata tana kirari cikin Ubangiji.’ (1 Sam. 2:1) Marubutan Littafi Mai Tsarki sun ambata zuciya kusan sau dubu. A yawancin lokaci sun yi hakan a alamance. Yana da muhimmanci mu fahimci abin da zuciya take wakilta, domin Littafi Mai Tsarki ya ce muna bukatar mu kiyaye ta.—Karanta Misalai 4:23.
MECE CE ZUCIYA TA ALAMA?
3. Ta yaya za mu fahimci abin da “zuciya” take nufi a cikin Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.
3 Ko da yake Kalmar Allah ba ta ba da ma’anar zuciya ta alama ba, amma mun san abin da take nufi. Ta yaya ta yi hakan? Alal misali, ka yi tunanin itacen da ke da ƙananan ganyaye da yawa. Idan ka tsaya kusa da shi, ba za ka ga ganyayen da yawa ba, kuma ba za ka san yadda itacen baki ɗaya yake ba. Amma idan ka ja da baya kuma ka kalli itacen za ka ga fasalin itacen gabaki ɗaya. Hakazalika, muna bukatar mu bincika wurare da yawa da aka yi amfani da kalmar nan “zuciya” a cikin Littafi Mai Tsarki domin mu fahimci abin da take nufi. Mece ce zuciya ta alama?
4. (a) Mece ce “zuciya” take wakilta? (b) Mene ne abin da Yesu ya faɗa a Matta 22:37 yake nufi?
4 Marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da “zuciya” don su kwatanta halinmu. Hakan ya ƙunshi sha’awarmu da tunaninmu da mutuntakarmu da iyawarmu da muradinmu da kuma maƙasudanmu. (Karanta Kubawar Shari’a 15:7; Misalai 16:9; Ayyukan Manzanni 2:26.) Amma, da akwai lokatai da kalmar nan “zuciya” take da wata ma’ana dabam. Alal misali, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Mat. 22:37) A wannan misalin, kalmar nan “zuciya” tana nufin motsin rai da sha’awa da kuma yadda mutum yake ji. Yesu bai ambata zuciya da rai da azanci tare ba domin yana son ya nanata cewa muna bukatar mu nuna muna ƙaunar Allah ta yadda muke ji da yadda muke rayuwa da kuma yadda muke amfani da azancinmu. (Yoh. 17:3; Afis. 6:6) Amma sa’ad da aka ambata “zuciya” kaɗai, hakan yana nufin ainihin halinmu.
DALILIN DA YA SA MUKE BUKATAR MU KIYAYE ZUCIYARMU
5. Me ya sa za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya?
5 Sarki Dauda ya tuna wa Sulemanu: “Ɗana, ka san Allah na ubanka, ka bauta masa da sahihiyar zuciya da yardan rai kuma: gama Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan sifofin tunani.” (1 Laba. 28:9) Hakika, Jehobah yana bincika dukan zukata, har da namu. (Mis. 17:3; 21:2) Za mu iya zama aminan Jehobah kuma mu yi farin ciki nan gaba idan abin da yake a cikin zuciyarmu ya faranta wa Jehobah rai. Saboda haka, muna da dalili mai kyau na bin hurarriyar shawarar Dauda ta wajen yin iya ƙoƙarinmu don mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.
6. Mene ne ya kamata mu yi don kada mu yi sanyi a bautarmu ga Jehobah?
6 Ta aikin da muke yi da ƙwazo a matsayin Shaidun Jehobah, muna nuna cewa muna son mu bauta wa Allah da zuciya ɗaya. Duk da haka, mun fahimci cewa muguwar duniya ta Shaiɗan da zuciyarmu da ke yawan sa mu zunubi suna iya shafanmu kuma su raunana ƙuduri da muka yi cewa za mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. (Irm. 17:9; Afis. 2:2) Don mu tabbata cewa hakan bai faru ba, muna bukatar mu riƙa bincika zuciyarmu a kai a kai. Ta yaya za mu iya yin hakan?
7. Mene ne yake nuna yanayin zuciyarmu?
7 Hakika, ba wanda yake ganin abin da yake cikin zuciyarmu, kamar yadda ba wanda zai iya ganin abin da ke cikin itace. Duk da haka, a cikin Huɗuba da Yesu ya yi a kan Dutse, ya ambata cewa kamar yadda ’ya’yan itatuwa suke bayyana yanayin itace, hakan ne ayyukanmu suke nuna ainihin yanayin zuciyarmu. (Mat. 7:17-20) Bari mu tattauna ɗaya cikin waɗannan ayyukan.
HANYA ƊAYA DA ZA MU BINCIKA ZUCIYARMU
8. Yaya abin da Yesu ya faɗa a Matta 6:33 ya nuna abin da yake cikin zuciyarmu?
8 A cikin wannan huɗuba da ya yi a kan dutse, Yesu ya gaya wa masu sauraronsa ainihin abin da za su yi don su nuna cewa suna son su bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Ya ce: ‘Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.’ (Mat. 6:33) Hakika abin da muka saka farko a rayuwarmu yana nuna sha’awarmu da tunaninmu da kuma shirye-shiryenmu. Hanya ɗaya da za mu san ko muna bauta wa Allah da zuciya ɗaya ita ce ta yin tunani sosai game da abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu.
9. Mene ne Yesu ya gayyaci wasu mazaje su yi, kuma mene ne yadda suka aikata ya nuna?
9 Wani abin da ya faru ba da daɗewa ba bayan Yesu ya umurci almajiransa su “fara biɗan mulkin,” ya nuna cewa abin da mutum ya sa kan gaba a rayuwa zai iya sa a san abin da ke cikin zuciyarsa. Luka marubucin Linjila ya soma ba da labarin ta wajen cewa Yesu ‘ya shirya sosai garin ya tafi Urushalima,’ ko da yake ya san abin da zai same shi a wurin. Sa’ad da Yesu da manzanninsa suke “cikin tafiya,” Yesu ya haɗu da wasu maza kuma ya gayyace su ku “biyo ni.” Waɗannan maza suna a shirye su karɓi gayyatar Yesu, amma suna son su yi wasu abubuwa tukuna. Ɗaya cikinsu ya amsa: ‘Ka yarda mini in tafi tukuna in binne ubana.’ Wani ya ce: ‘Zan bi ka, Ubangiji; amma ka yarda mani in yi sallama tukuna da waɗanda su ke cikin gidana.’ (Luk 9:51, 57-61) Babu shakka da akwai bambanci tsakanin yadda Yesu ya nace a yin nufin Allah da zuciya ɗaya da kuma yadda mazajen nan suka amsa gayyatar Yesu! Ta wajen saka damuwarsu a kan gaba da ayyukan Mulki, sun nuna cewa ba sa son su bauta wa Allah da zuciya ɗaya.
10. (a) Ta yaya mabiyan Kristi suka aikata ga gayyatar Yesu? (b) Wane kwatanci ne Yesu ya ba da?
10 Yadda muka amsa gayyatar Yesu dabam ne. Mun amince da gayyatar sa na mu zama mabiyansa kuma muna bauta wa Jehobah a kowace rana. Ta hakan muna nuna yadda muke ji game da Jehobah. Duk da haka, ko da mun shagala a bautarmu ga Jehobah, muna bukatar mu tuna cewa zuciyarmu tana iya kasancewa cikin haɗari. Mene ne haɗarin? Mun san hakan daga abin da Yesu ya gaya wa waɗanda ya gayyata su zama almajiransa, ya ce: “Kowane mutum wanda ya sa hannunsa ga keken noma, idan ya duba baya, ba ya cancanci mulkin Allah ba.” (Luk 9:62) Wane darassi ne za mu iya koya daga wannan kwatancin?
SHIN MUNA NACE GA YIN “ABIN DA KE NAGARI”?
11. A kwatancin Yesu, mene ne ya faru da aikin da wani manomi yake yi kuma me ya sa?
11 Bari mu ƙara bayyana kwatancin Yesu dalla-dalla domin mu fahimci darassin sosai. Wani manomi ya shagala da aiki. Amma, sa’ad da yake aiki, yana ta tunani game da iyalinsa da abokansa da abinci da kaɗe-kaɗe da shaƙatawa da kuma wuri mai laima da zai je ya huta. Sai ya soma marmarin waɗannan abubuwan. Bayan ya yi noma na ɗan lokaci, wannan manomin ya daɗa sha’awar waɗannan abubuwa sosai da har ya daina aikinsa kuma “ya duba baya.” Ko da yake yana da sauran aiki da yawa, wannan sha’awar ta janye hankalin manomin kuma bai yi aikinsa da kyau ba. Babu shakka, shugabansa ya yi baƙin ciki domin manomin bai jimre ba.
12. Ta yaya Kirista a yau zai iya kasancewa cikin irin yanayin da manomi na kwatancin Yesu yake ciki?
12 Yanzu ka yi la’akari da yadda irin wannan yanayin zai iya faruwa a yau. Manomin yana iya zama kowane Kirista da yake bauta wa Allah da kyau amma zuciyarsa tana cikin haɗari. Alal misali, a ce wani ɗan’uwa yana da ƙwazo a wa’azi sosai. Amma, ko da yana halartan tarurruka kuma yana yin wa’azi, ya ci gaba da yin sha’awar wasu fannoni na rayuwa da ake yi a duniya. A cikin zuciyarsa, yana sha’awarsu sosai. Bayan ɗan’uwan ya bauta wa Allah shekaru da yawa, sha’awar abin duniya ta nauyaya shi da har ya daina bauta wa Allah kuma “ya duba baya.” Ko da yake yana da aiki da yawa da zai yi a hidimarsa, bai ‘riƙe maganar rai gam-gam’ ba kuma ayyukan da yake yi a bautarsa ga Allah yana cikin haɗari. (Filib. 2:16, Littafi Mai Tsarki) Jehobah “Ubangijin girbi” yana baƙin ciki idan mai bauta masa ya daina jimrewa.—Luk 10:2.
13. Mene ne yake nufi a bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya?
13 Darassin a bayane yake. Bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya ya ƙunshi halartan tarurrukan ikilisiya da kuma yin wa’azi, amma ba shi ke nan ba. (2 Laba. 25:1, 2, 27) Idan Kirista ya ci gaba da son abubuwan da ke “baya,” wato, abin duniya, abotarsa da Jehobah za ta kasance cikin haɗari. (Luk 17:32) Sai idan mun “yi ƙyamar abin da ke mugu” kuma muka “rungumi abin da ke nagari” ne za mu “cancanci mulkin Allah.” (Rom. 12:9; Luk 9:62) Saboda haka, muna bukatar mu tabbata cewa babu kome a cikin duniyar Shaiɗan, ko idan muna ganin yana da amfani ko kuma kyau da zai hana mu yin ayyukan Mulki da zuciya ɗaya.—2 Kor. 11:14; karanta Filibiyawa 3:13, 14.
KA KASANCE A FAƊAKE!
14, 15. (a) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya sa mu rage ƙwazonmu a hidimar Jehobah? (b) Ka ba da misalin yadda Shaiɗan yake ƙoƙari ya yaudare mu.
14 Mun keɓe kanmu ga Jehobah don muna ƙaunarsa. Kuma da yawa cikinmu mun ƙuduri aniya cewa za mu ci gaba da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya tun daga lokacin. Amma har ila, Shaiɗan yana ƙoƙari ya rinjaye mu. Yana son ya ɓata zuciyarmu. (Afis. 6:12) Hakika, ya san cewa ba za mu daina bauta wa Jehobah farat ɗaya ba. Saboda haka, yana amfani da wannan ‘duniyar’ don ya raunana ƙwazonmu ga Allah a hankali. (Karanta Markus 4:18, 19.) Me ya sa Shaiɗan yake yin nasara sosai ta wajen yin amfani da wannan dabara?
15 A ce kana sauraron labarai na ƙarfe shida na safe da ƙaramin rediyo da aka sa sababbin batura. Da ƙarfe takwas na safe kana sauraron labarai da wannan rediyo amma ba ka sani ba cewa wani ya cire sabon batir guda kuma ya sauya shi da wanda aka yi amfani da shi kwana guda. Shin za ka san an canja batir ɗin? Da kyar. Amma idan kafin ƙarfe huɗu na yamma, wani ya sauya ɗayan sabon batir da wanda aka yi amfani da shi kwana biyu? Wataƙila har ila ba za ka san cewa wani ya canja batir ɗin ba. Me ya sa? Domin ƙarar tana ragewa a hankali. Hakazalika, abubuwan da ke cikin duniyar Shaiɗan suna iya sa ƙwazonmu ya riƙa ragewa a hankali. Idan hakan ya faru, yana kamar Shaiɗan yana yin nasara wajen rage sababbin batura na ƙwazonmu a hidimar Jehobah. Idan Kirista bai kasance a faɗake ba, ba zai lura ba cewa ƙwazonsa yana ragewa a hankali.—Mat. 24:42; 1 Bit. 5:8.
ADDU’A TANA DA MUHIMMANCI
16. Ta yaya za mu kāre kanmu daga dabarun Shaiɗan?
16 Ta yaya za mu iya kāre kanmu daga dabarun Shaiɗan kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. (2 Kor. 2:11) Addu’a tana da muhimmanci. Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa su “yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.” Sai ya aririce su: “Kuna addu’a kowane loto . . . da kowace irin addu’a da roƙo.”—Afis. 6:11, 18; 1 Bit. 4:7.
17. Wane darassi ne za mu koya daga addu’o’in da Yesu ya yi?
17 Don mu kasance da aminci, muna bukatar mu yi koyi da Yesu da kuma ƙwazonsa na bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Luka ya rubuta yadda Yesu ya yi addu’a a daren da ya rasu: “Domin kuma yana cikin raɗaɗi ya ƙara naciyar addu’a.” (Luk 22:44) Wannan ba shi ne lokaci na farko da Yesu ya yi addu’a sosai ba, amma a wannan lokacin zai jimre gwaji mafi wuya a rayuwarsa a duniya. Saboda haka, ya ‘ƙara nacewa’ a yin addu’a, kuma Jehobah ya amsa addu’ar. Misalin Yesu ya nuna cewa a wasu lokatai za a iya yin addu’a sosai. Idan muna fuskantar gwaji masu wuya sosai kuma Shaiɗan ya daɗa rinjayarmu, hakan zai sa mu yi addu’a sosai don Jehobah ya kāre mu.
18. (a) Mene ne ya kamata mu tambayi kanmu game da addu’o’inmu, kuma me ya sa? (b) Waɗanne abubuwa ne suke shafan zuciyarmu kuma a waɗanne hanyoyi ne suke yin hakan? (Duba akwati da ke shafi na 16.)
18 Ta yaya irin waɗannan addu’o’in za su shafe mu? Bulus ya ce: ‘Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku.’ (Filib. 4:6, 7) Idan muna son mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya, wajibi ne mu nace da yin addu’a kuma mu yi hakan a kai a kai. (Luk 6:12) Saboda haka, ka tambayi kanka, ‘Shin ina yin addu’a sosai da kuma a kai a kai?’ (Mat. 7:7; Rom. 12:12) Amsarka tana bayyana yawan yadda kake son ka bauta wa Allah da zuciya ɗaya.
19. Mene ne za ka yi don ka ci gaba da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya?
19 Kamar yadda muka tattauna, abubuwa da muka saka kan gaba a rayuwa suna nuna abin da ke cikin zuciyarmu. Yana da kyau mu tabbata cewa abubuwa da muka bar a baya ko kuma dabarun Shaiɗan ba su hana mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya ba. (Karanta Luka 21:19, 34-36.) Saboda haka, kamar Dauda muna roƙon Jehobah: “Ka daidaita zuciyata.”—Zab. 86:11.
[Akwati a shafi na 16]
ABUBUWA UKU DA SUKE SHAFAR ZUCIYARMU
Za mu iya ɗaukan matakai don mu kula da zuciyarmu ta alama kamar yadda za mu yi abubuwa don mu samu lafiyayyar zuciya ta zahiri. Bari mu tattauna abubuwa uku da za su shafi zuciyarmu:
1 Abinci: Muna bukatar mu ci abinci mai lafiya don zuciyarmu ta zama lafiyayya. Hakazalika, ya kamata mu tabbata cewa mun samun abinci mai kyau na Kalmar Allah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki mu kaɗai da yin bimbini da kuma halartar tarurruka.—Zab. 1:1, 2; Mis. 15:28; Ibran. 10:24, 25.
2 Motsa jiki: Don mu samu lafiya, zuciyarmu ta zahiri tana bukatar wasan motsa jiki da zai sa tana bugawa da sauri. Hakan nan ma, muna bukatar mu riƙa motsa zuciyarmu ta alama ta wajen kasancewa da ƙwazo a hidima da kuma ƙara lokacin da muke hidima idan zai yiwu.—Luk 13:24; Filib. 3:12.
3 Mahalli: Wurin da muke zama da kuma wurin da muke yin aiki suna iya shafar zuciyarmu ta zahiri da kuma ta alama. Amma muna samun kwanciyar hankali sa’ad da muke tare da ’yan’uwanmu da suka damu da mu kuma suna bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.—Zab. 119:63; Mis. 13:20.