Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 4/1 pp. 5-7
  • Menene Zai Taimake ka Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Zai Taimake ka Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kafa Zuciyarka da Hankalinka
  • Ƙalubalen Kasancewa da Halin da ya Dace
  • Ƙalubalen Mu Yarda a Koyar da Mu
  • Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Yara da Suka Faranta wa Allah Rai
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Ta So Ta Yi Taimako
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 4/1 pp. 5-7

Menene Zai Taimake ka Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?

“KA ƁOYE ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Luka 10:21) Waɗannan kalaman da Yesu ya gaya wa Ubansa na sama sun nuna cewa, muna bukatar mu kasance da hali mai kyau idan muna son mu fahimci Littafi Mai Tsarki. Jehobah ya bayyana hikimarsa domin ya yi tanadin littafin da mutane masu tawali’u da kuma masu son su koya ne kawai za su iya fahimta.

Nuna tawali’u yana da wuya ga yawancinmu. Dukanmu mun gaji fahariya. Bugu da ƙari, muna zaune ne a “kwanaki na ƙarshe,” a cikin mutane “masu-son kansu, . . . masu-ruba, masu-girman kai.” (2 Timothawus 3:1-4) Waɗannan sune halayen da suke hana mu fahimtar Kalmar Allah. Abin baƙin ciki, yanayin wurin da muke zaune na shafan dukanmu. Ta yaya za ka iya nuna halin da ya dace don fahimtar Littafi Mai Tsarki?

Ka Kafa Zuciyarka da Hankalinka

Ezra wanda shi ne shugaban mutanen Allah a dā, “ya kafa zuciyatasa ga biɗar shari’ar Ubangiji.” (Ezra 7:10) Da yadda za mu iya kafa zuciyarmu? Hakika. Muna iya somawa ta wajen kasancewa da ra’ayin da ya dace game da Nassosi. Ga ’yan’uwa Kiristoci, manzo Bulus ya rubuta: “Sa’anda kuka karɓi maganar jawabi daga garemu, watau maganar Allah ke nan, kuka karɓe ta, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah.” (1 Tassalunikawa 2:13) Ko da yake an yi amfani ne da mutane su rubuta Nassosi, abin da suka rubuta daga Jehobah ne. Fahimtar wannan gaskiyar zai sa mu ƙara gaskata da abin da muka karanta.—2 Timothawus 3:16.

Wata hanya kuma da za mu iya kafa zuciyarmu ita ce ta yin addu’a. Tun da yake ruhu mai tsarki ne ya hure Littafi Mai Tsarki, za mu fahimci saƙon da ke cikinsa da taimakon wannan ruhun. Muna bukatar mu yi addu’a don samun wannan taimakon. Ka lura da yadda hakan ya zama damuwar mai zabura wanda ya rubuta: “Ka fahimtadda ni, ni kuma zan maida hankali ga shari’arka; hakika zan kiyaye ta da dukan zuciyata.” (Zabura 119:34) Muna bukatar mu yi addu’ar samun hankalin da zai sa mu fahimci abin da aka rubuta da kuma zuciyar kirki da za ta sa mu karɓi abin da aka rubuta. Idan muna son mu fahimci Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu yarda da abin da ke gaskiya.

Yayin da kake yin bimbini don kasancewa da hali mai kyau, ka yi la’akari da yadda yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimake ka. Muna da dalilai masu kyau na karanta Kalmar Allah, amma abu mafi muhimmanci shi ne cewa, tana taimaka mana mu kusaci Allah. (Yaƙub 4:8) Mun fahimci Jehobah yayin da muka karanta game da yadda ya ɗauki mataki a kan yanayi dabam dabam, yadda yake ɗaukan waɗanda suke ƙaunarsa da tamani, da kuma yadda yake bi da mutanen da suka ƙyale shi. Ya kamata ainihin manufarmu na karanta Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci ya zama, na sanin Allah sosai da kuma ƙarfafa dangantakarmu da shi.

Ƙalubalen Kasancewa da Halin da ya Dace

Menene zai iya hana mu mu fahimci Kalmar Allah? Ƙalubale guda shi ne, manne wa imanin mutanen da muke yi wa biyayya. Alal misali, kana iya manne wa imani da kuma ra’ayoyin waɗanda ake ɗauka da daraja. Amma, idan waɗannan mutanen ba sa ɗaukaka ko kuwa daraja gaskiyar Kalmar Allah fa? A irin wannan yanayin, zai iya zama ƙalubale a fahimci ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu bincika abubuwan da aka koya mana sosai.—1 Tassalunikawa 5:21.

Mahaifiyar Yesu, Maryamu ta fuskanci irin wannan ƙalubalen. An yi renonta bisa al’adar Yahudawa. Tana bin Dokar Yahudawa kuma tana zuwa majami’a. Daga baya ta fahimci cewa hanyar bautar da iyayenta suka koya mata ba karɓaɓɓiya ba ce a wajen Allah. Saboda haka, Maryamu ta karɓi koyarwar Yesu, kuma tana cikin mutanen ikilisiyar Kirista ta farko. (Ayukan Manzanni 1:13, 14) Ba wai ta nuna rashin daraja ba ne ga iyayenta ko al’adarsu; akasin haka, ta nuna ƙaunarta ce ga Allah. Idan muna son mu amfana daga Littafi Mai Tsarki, kamar Maryamu dole ne mu nuna aminci ga Allah fiye da kome.

Abin baƙin ciki, yawancin mutane ba sa daraja gaskiyar Littafi Mai Tsarki sosai. Wasu sun fi son su bi al’adun ƙarya na addinai. Wasu kuma suna nuna rashin daraja ga gaskiya ta wajen furcinsu da kuma hanyar rayuwarsu. Hakika, amincewa da gaskiyar Littafi Mai Tsarki na bukatar sadaukarwa: Yana iya jawo rashin jituwa tsakaninka da abokanka, maƙwabtanka, abokan aikinka, har ma iyalinka. (Yohanna 17:14) Duk da haka, mutumin nan mai hikima ya rubuta: “Ka sayi gaskiya kada ka sayar.” (Misalai 23:23) Idan ka ɗauki gaskiya da muhimmanci sosai, Jehobah zai taimake ka ka fahimci Littafi Mai Tsarki.

Wani ƙalubale na ƙin fahimtar saƙon Littafi Mai Tsarki shi ne ƙin yin amfani da abin da ya ce. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku aka ba da za ku san asiran mulkin sama, amma a garesu ba a bayar ba. Gama zuciyar al’umman nan ta yi taiɓa, kunnuwansu kuwa suna da nauyin ji.” (Matta 13:11, 15) Yawancin mutanen da Yesu ya yi wa wa’azi sun ƙi su saurare shi, kuma sun ƙi su canja rayuwarsu. Waɗannan sun bambanta da attajirin da Yesu ya yi maganarsa a cikin kwatancinsa! Sa’ad da ya sami lu’u lu’u mai tamanin gaske, attajirin ya sayar da dukan abin da yake da shi domin ya saye shi! Hakazalika, ya kamata mu ɗauki fahimtar gaskiyar Littafi Mai Tsarki abu mai tamani.—Matta 13:45, 46.

Ƙalubalen Mu Yarda a Koyar da Mu

Babban ƙalubalen fahimtar Littafi Mai Tsarki shi ne kasancewa da halin koyo. Wani na iya iske shi da wuya ya amince da sababbin ra’ayoyi daga wurin talaka. Duk da haka, manzannin Yesu Kristi “mutane marasa-karatu ne.” (Ayukan Manzanni 4:13) Sa’ad da yake bayyana dalilin haka, Bulus ya rubuta: “Duba fa irin kiranku, ’yan’uwa, ba a kira masu-hikima dayawa ga zancen jiki ba, ba masu-iko dayawa ba, ba masu-daraja dayawa ba: amma Allah ya zaɓi abubuwa marasa-hikima na duniya, domin shi kumyatadda waɗanda suke masu-hikima.” (1 Korinthiyawa 1:26, 27) Idan yana maka wuya ka nuna sauƙin kai sa’ad da mutum marar ilimi ke koyar da kai, ka tuna cewa Allah yana amfani da shi ko ita ne ya ko ta koyar da kai. Da gatan da ya fi na samun koyarwa daga Jehobah, “Mai-Koya” mana?—Ishaya 30:20; 54:13.

Shugaban sojoji na Siriya, Na’aman ya iske shi da wuya ya karɓi umurni daga wani talaka. Ya je wajen annabin Jehobah, Elisha, domin samun warkarwa daga kuturta. Amma, Allah ya ba Na’aman umurnin abin da zai yi ya warke ta bakin wani bawa. Saƙon da kuma yadda aka isar da ita sun gwada tawali’un Na’aman, har hakan ya sa da farko ya ƙi yin biyayya da maganar annabin Allah. Daga baya, ya canja halinsa kuma ya sami warkarwa. (2 Sarakuna 5:9-14) Muna fuskantar irin wannan ƙalubalen sa’ad da muke son mu karanta Littafi Mai Tsarki. Muna iya koyan cewa idan muna son mu sami warkarwa na ruhaniya da kuma halinmu, muna bukatar mu bi wata sabuwar hanyar rayuwa. Za mu iya nuna tawali’u kuwa kuma mu ƙyale wani ya zo ya koya mana abin da muke bukatar mu yi? Waɗanda suke son a koyar da su ne kawai za su iya fahimtar Littafi Mai Tsarki.

Wani mutum mai iko da ke ƙarƙashin Kandakatu, sarauniyar Habasha, ya nuna hali mai kyau. A kan hanyarsa ta komawa Afirka a cikin karusarsa, almajiri Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa. Filibus ya tambayi mutumin ko ya fahimci abin da yake karantawa. Cikin tawali’u mutumin ya ce: “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni?” Mutumin ya yi baftisma sa’ad da ya fahimci Kalmar Allah. Bayan haka, “ya kama tafiyassa yana murna.”—Ayukan Manzanni 8:27-39.

Shaidun Jehobah galibi talakawa ne. A kowane mako suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki a gidajen mutane fiye da miliyan shida. Tun da yake Littafi Mai Tsarki yana koyar da hanyar rayuwa mafi kyau, yana bayyana bege mafi kyau ga mutane, kuma yana sa mu san Allah sosai, miliyoyin mutane sun ga cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma fahimtar abin da yake cewa jin daɗi ne mai girma. Jin daɗi ne da za ka iya samu.

[Hoto a shafi na 7]

Ya yi wa Na’aman wuya ya yarda da umurnin da wani talaka ya ba shi

[Hoto a shafi na 7]

Fahimtar Littafi Mai Tsarki na daɗaɗa mana zuciya

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba