Ka Ci Gaba Da Yin Godiya
“Ina misalin darajar tunaninka . . . ya Allah! Ina misalin yawan jimlassu!”—ZABURA 139:17.
1, 2. Me ya sa ya kamata mu yi godiya don Kalmar Allah, kuma yaya ne mai zabura ya furta godiyarsa?
AN GANO wani abu mai kyau. Sa’ad da ake gyara haikalin Jehobah a Urushalima, Babban Firist Hilkiya ya gano “litafin shari’ar Ubangiji, wanda Musa ya bayas,” littafi ne na asali da aka gama shekaru 800 da suka shige! Ka yi tunanin yadda Sarki Josiah mai jin tsoron Allah ya ji sa’ad da aka kai masa littafin! Hakika, ya ɗauke shi da tamani kuma ya sa Shaphan, sakatarensa ya karanta masa da babban murya.—2 Labarbaru 34:14-18.
2 A yau, mutane da yawa suna iya karanta Kalmar Allah gabaki ɗayanta ko rabinta. Amma hakan na nufin Nassosi ba shi da muhimmanci ne? A’a! Hakika, yana ɗauke da maganar Maɗaukaki, da aka rubuta don amfaninmu. (2 Timothawus 3:16) Da yake furta yadda ya ji game da Kalmar Allah, Dauda mai zabura ya rubuta: “Ina misalin darajar tunaninka zuwa gareni, ya Allah! Ina misalin yawan jimlassu!”—Zabura 139:17.
3. Menene ya nuna cewa Dauda mutumi ne mai ruhaniya?
3 Dauda bai taɓa daina daraja Jehobah, da Kalmarsa da tsarinsa na bauta ta gaskiya ba. Waƙoƙi masu daɗi da Dauda ya rera sun nuna yadda ya ji. Alal misali a Zabura 27:4 ya rubuta: “Abu guda ɗaya na yi roƙo ga Ubangiji, shi zan nema; in zauna cikin gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, domin in dubi jamalin Ubangiji, in yi ta tunani cikin haikalinsa.” A Ibrananci na asali, wannan furci “yi ta tunani” yana nufin “ka daɗe kana bimbini, ka bincika kanka, ka ji daɗin wani abu, ka yi farin ciki da abin, kuma ka so shi.” Hakika, Dauda mutumi ne mai ruhaniya wanda yake godiya don tanadi na ruhaniya da Jehobah yake yi kuma ya ji daɗin kowace gaskiya ta ruhaniya da Allah ya bayyana. Ya dace mu yi koyi da misalinsa na yin godiya.—Zabura 19:7-11.
Ka Yi Godiya Don Gatar Sanin Gaskiyar Littafi Mai Tsarki
4. Menene ya sa Yesu “ya yi murna ta wurin Ruhu Mai-tsarki”?
4 Fahimtar Kalmar Allah bai dangana ba da iliminmu ko kuma hikima ta duniya, da suke sa mutane fahariya. Maimakon haka, ya dangana ne da alherin Jehobah, wanda yake ba wa mutane masu tawali’u kuma masu zuciyar kirki da suka san bukatunsu na ruhaniya. (Matta 5:3; 1 Yohanna 5:20) Sa’ad da Yesu ya yi bimbini cewa da akwai wasu mutane ajizai da ake rubuta sunayensu a sama “ya yi murna ta wurin Ruhu Mai-tsarki, ya ce, Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.”—Luka 10:17-21.
5. Me ya sa bai kamata almajiran Yesu su yi wasa da gaskiyar Mulki da aka bayyana musu ba?
5 Bayan ya yi wannan addu’ar da zuciya ɗaya, Yesu ya juya wajen almajiransa ya ce: “Idanun da ke duban abin da ku ke duba masu albarka ne: gama ina ce maku, annabawa da sarakuna dayawa suka yi bege su duba abin da ku ke duba, ba su gani ba; su ji abin da ku ke ji, ba su kuwa ji ba.” Hakika, Yesu ya ƙarfafa mabiyansa masu aminci kada su yi wasa da gaskiyar Mulki mai tamani da aka bayyana musu. Ba a bayyana wa tsara na farko na bayin Allah waɗannan gaskiyar ba, kuma ba a bayyana wa “masu-hikima da masu-fahimi” na zamanin Yesu ba!—Luka 10:23, 24.
6, 7. (a) Waɗanne dalilai muke da shi na yin godiya don gaskiya? (b) Wane bambanci ake gani a yau tsakanin addini na gaskiya da na ƙarya?
6 A zamaninmu, muna da ƙarin dalilai na yin godiya don gaskiyar Allah, domin ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” Jehobah har ila yana ba mutanensa ƙarin fahimi game da Kalmarsa. (Matta 24:45; Daniel 12:10) Game da kwanaki na ƙarshe, annabi Daniel ya rubuta: “Mutane dayawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru.” (Daniel 12:4) Ba ka yarda ba cewa ilimin Allah a yau ya “ƙaru” kuma ana ciyar da bayin Jehobah da kyau a ruhaniya?
7 Mun ga bambancin da ke tsakanin ilimi na ruhaniya na mutanen Allah da rikicewa na addinin Babila Babba! Saboda haka, mutane da yawa da suka yi sanyin gwiwa ko kuma ba sa son addinin ƙarya sun koma bin bauta ta gaskiya. Waɗannan masu kama da tumaki ne da ba sa son su “yi tarayya da zunubanta [Babila Babba]” ko kuma su “sha rabon annobanta.” Jehobah da bayinsa suna gayyatar irin waɗannan zuwa ikilisiyar Kirista ta gaskiya.—Ru’ya ta Yohanna 18:2-4; 22:17.
Masu Godiya Suna Jerin Gwano Zuwa Wurin Allah
8, 9. Yaya kalmomin Haggai 2:7 suke cika a yau?
8 Game da gidansa na bauta na ruhaniya, Jehobah ya annabta: “Zan raurawarda dukan dangogi; kuma muradin dukan dangogi za ya zo; zan cika wannan gida da ɗaukaka.” (Haggai 2:7) Wannan annabci mai ban mamaki ya cika a zamanin Haggai sa’ad da sauran mutanen Allah da suka koma ƙasarsu suka sake gina haikali a Urushalima. A yau, kalmomin Haggai suna samun ƙarin cikawa game da haikali na ruhaniya mai girma na Jehobah.
9 Miliyoyi mutane sun riga sun yi jerin gwano zuwa haikali na alama domin su bauta wa Allah “cikin Ruhu da cikin gaskiya kuma,” kuma kowace shekara dubbai na “muradin dukan dangogi” sun ci gaba da shigowa. (Yohanna 4:23, 24) Alal misali, rahoto na shekarar hidima ta 2006 ya nuna cewa mutane 248,327 ne suka yi baftisma don su nuna cewa sun keɓe kansu ga Jehobah. Wannan ya nuna avirejin sababbi 680 kowace rana! Da yake suna ƙaunar gaskiya kuma suna son su yi wa Jehobah hidima a matsayin masu shelar Mulki, wannan ya nuna cewa Allah ne ya jawo su da gaske.—Yohanna 6:44, 65.
10, 11. Ka ba da labarin da ya nuna yadda mutane suke daraja gaskiyar Littafi Mai Tsarki.
10 Mutane da yawa cikin waɗannan masu zuciyar kirki sun soma bin gaskiya domin sun fahimci bambanci da ke “tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Malachi 3:18) Ka yi la’akari da labarin Wayne da Virginia, ma’aurata da suke zuwa cocin Farostatan, amma suna da tambayoyi da yawa da ba amsa ba. Ba sa son yaƙi kuma dukansu sun rikice kuma sun damu sa’ad da suka ga limamai suna sa wa sojoji da makamai albarka. Yayin da ma’auratan suka tsufa, sun ga cewa mutanen cocin ba sa kula da su, kuma ko da yake shekaru da yawa Virginia tana koyar da yara a ranar Lahadi a cocin, “ba wanda yake ziyararmu ko kuma ya nuna ya damu da yanayinmu ta ruhaniya,” in ji su. “Abin da cocin yake so shi ne kuɗinmu. Mun rikice ƙwarai.” Sun fi ma sanyin gwiwa sa’ad da cocinsu ya aminci da luwaɗi.
11 Yayin nan kuma, jikan Wayne da Virginia da kuma ’yarsu suka zama Shaidun Jehobah. Ko da yake Wayne da Virginia sun yi fushi da farko, daga baya suka canja ra’ayinsu kuma suka yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Wayne ya ce, “cikin wata uku kawai mun koyi abubuwa masu yawa a cikin Littafi Mai Tsarki fiye da abin da muka koya shekaru 70 da suka shige! Ba mu taɓa sanin cewa Jehobah ne sunan Allah ba, ba mu san kome ba game da Mulki da kuma Aljanna ta duniya ba.” Ba da daɗewa ba waɗannan ma’aurata suka soma halartar taron Kirista da yin wa’azin Mulki. “Muna son mu gaya wa kowa game da gaskiya,” in ji Virginia. Sun yi baftisma a shekara ta 2005 suna shekarunsu na 80. Sun ce: “Mun sami rukunin Kiristoci na gaskiya.”
Ka Yi Godiya don Kai ‘Shiryayye Ne Sarai Domin Kowane Managarcin Aiki’
12. Menene Jehobah koyaushe yake tanadinsa don bayinsa, kuma menene dole mu yi don mu amfana?
12 Koyaushe Jehobah yana taimakon bayinsa su yi nufinsa. Alal misali, Nuhu ya sami umurni game da yadda zai gina jirgi, wato, aikin da za a yi daidai a lokaci na farko! Kuma hakan ya kasance. Me ya sa? Domin Nuhu “ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.” (Farawa 6:14-22) A yau ma, Jehobah na shirya bayinsa su yi nufinsa. Hakika, aikinmu na musamman shi ne wa’azin bishara na Mulkin Allah da aka kafa da kuma taimakon waɗanda suka cancanta su zama almajiran Yesu Kristi. Kamar Nuhu, za mu yi nasara idan muka yi biyayya. Dole ne mu yi biyayya mu bi umurnin da Jehobah yake ba da wa ta Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa.—Matta 24:14; 28:19, 20.
13. Ta yaya Jehobah yake koyar da mu?
13 Don mu cika wannan aikin, dole ne mu koyi yadda ake ‘rarrabe’ kayan aikinmu na musamman, wato, Kalmar Allah, wadda “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 2:15; 3:16, 17) Kamar yadda yake a ƙarni na farko, Jehobah yana koyar da mu da kyau ta ikilisiyar Kirista. A yau, a cikin ikilisiyoyi 99,770 a dukan duniya, ana yin Makarantar Hidima ta Allah da Taron Hidima kowane mako don mu sami taimako a hidima. Kana godiya don waɗannan taro masu muhimmanci ta halartansu a kai a kai da kuma yin amfani da abubuwa da ka koya?—Ibraniyawa 10:24, 25.
14. Ta yaya bayin Jehobah suka nuna godiyarsu don gatar bauta wa Allah? (Ka haɗa da bayanin da ke cikin taswira a shafuffuka na 27 zuwa 30.)
14 Mutanen Allah da yawa a dukan duniya suna nuna godiyarsu don koyarwa da suke samu ta wajen yin ƙwazo sosai a hidima. Alal misali, a shekarar hidima ta 2006, masu shelar Mulki 6,741,444 sun ba da sa’o’i 1,333,966,199 a dukan fannoni na hidimar, waɗanda suka haɗa da gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida 6,286,618. Waɗannan wasu ne kawai cikin abubuwa masu ban ƙarfafa da ke cikin rahoto na dukan duniya. Don Allah ka bincika wannan rahoto sosai kuma ka sami ƙarfafa daga ciki, yadda ’yan’uwanmu na ƙarni na farko suka ƙarfafa daga rahoton yaɗa aikin wa’azi a lokacinsu.—Ayukan Manzanni 1:15; 2:5-11, 41, 47; 4:4; 6:7.
15. Me ya sa bai kamata mutum ya yi sanyin gwiwa ba game da hidima da yake yi wa Jehobah da dukan zuciya?
15 Yabon Allah da ake yi a kowace shekara yana nuna godiya da bayin Jehobah suke yi don gatar da suke da shi na sanin Jehobah da kuma ba da shaida game da shi. (Ishaya 43:10) Hakika, za a iya gwada yabon da wasu cikin ’yan’uwanmu da suka tsufa, masu rashin lafiya, ko waɗanda suka naƙasa suke yi da abin da gwauruwa ta ba da. Amma kada mu manta cewa Jehobah da Ɗansa suna godiya ga dukan waɗanda suke bauta wa Allah da dukan zuciyarsu, yayin da suke iyakacin ƙoƙarinsu.—Luka 21:1-4; Galatiyawa 6:4.
16. Waɗanne kayan koyarwa ne Allah ya yi tanadinsu a shekarun baya bayan nan?
16 Ban da koyarwa da ake mana don hidima, Jehobah ta ƙungiyarsa, ya ba mu kayan aiki mafi kyau. A shekarun baya, waɗannan kayan aiki sun ƙunshi littattafai kamar su Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami, Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya, Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, kuma kwanan nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Waɗanda suke godiya don waɗannan tanadi suna amfani da su da kyau a hidima.
Ka Yi Amfani da Kyau da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
17, 18. (a) Waɗanne sashe na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kake son ka nanata a hidimarka? (b) Menene wani mai kula da da’ira ya ce game da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
17 Da yake yana da babi 19, da kuma fihirisa da ya bayana abubuwa dalla-dalla da sauƙi, littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ya zama abin taimako sosai a hidima. Alal misali, babi na 12 ya tattauna batu mai jigo “Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai.” Wannan darasin ya bayyana wa ɗalibin yadda zai zama abokin Allah, abin da mutane da yawa ba su yi tunaninsa ba ko kuma suna ganin ba zai yiwu ba. (Yaƙub 2:23) Menene mutane suka ce game da wannan littafi na nazarin Littafi Mai Tsarki?
18 Wani mai kula da da’ira a Australiya ya ce littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? yana da “abin da ke motsa mutane nan da nan su soma tattaunawa.” Ya daɗa cewa littafin yana da sauƙi, hakan ya sa “masu shelar Mulki su kasance da tabbaci kuma su yi farin ciki a hidima. Shi ya sa wasu suke kiransa littafi mai tamani kamar zinariya!”
19-21. Ka ba da wasu labarai da suka nuna amfanin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
19 Wata mata a ƙasar Guyana ta gaya wa wani majagaba da ya zo gidanta, “Allah ne ya aiko ka.” Ba da daɗewa ba, mutumin da ke zama tare da matar ya bar ta da yaransu ƙanana biyu. Majagaban ya buɗe littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwar? zuwa babi na 1 kuma ya karanta sakin layi na 11 da babban murya, a ƙarƙashin ƙaramin jigo “Yaya Allah Yake Ji Game da Rashin Gaskiya da Muke Fuskanta?” “Darussan sun motsa ta sosai” in ji majagaban. “Sai ta tashi ta je bayan kantinta, ta yi kuka sosai.” Wannan matar ta yarda wata ’yar’uwa ta riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da ita a kai a kai kuma tana ci gaba sosai.
20 José, da yake da zama a Spain ya yi rashin matarsa a hatsarin mota. Ya nemi ta’aziyya ta wajen shan ƙwaya kuma ya nemi taimakon masanin halin ’yan adam. Amma masanan halin ’yan adam ba su iya amsa tambayar da ta fi damun José ba: “Me ya sa Allah ya ƙyale matata ta mutu?” Wata rana José ya yi magana da Francesc da suke aiki tare a kamfani ɗaya. Francesc ya ce su tattauna babi na 11 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, mai jigo “Me Ya Sa Allah ya Ƙyale Wahala?” Bayani na Nassi da aka bayar da kwatanci na malami da ɗalibi ya burge José sosai. Ya soma nazari sosai, ya halarci taron da’ira, kuma yanzu yana halartan taro a Majami’ar Mulki.
21 Roman, wani ɗan kasuwanci ɗan shekara 40 a Poland, yana daraja Kalmar Allah. Amma domin ya shagala da aikinsa, ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki kaɗan kuma ya daina. Duk da haka, ya halarci taron gunduma kuma ya karɓi littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Bayan haka, halinsa ya canja. Ya ce: “Da wannan littafin dukan koyarwa na musamman na Littafi Mai Tsarki ya zama cikakke.” Yanzu Roman yana nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuma yana ci gaba da kyau.
Ka Ci Gaba da Yin Godiya
22, 23. Yaya za mu ci gaba da nuna godiyarmu don bege da aka kafa a gabanmu?
22 Kamar yadda aka bayyana a Taron Gunduma na “Ceto Ya Kusa!” Kiristoci na gaskiya suna marmarin “ceto na har abada” da Allah ya yi alkawarinsa wanda ya yiwu ta jinin da Yesu Kristi ya zubar. Hanyar da ta fi da za mu nuna godiyarmu don wannan bege mai tamani ita ce ta wurin ci gaba da tsarkake kanmu “daga matattun ayyuka da za ku bauta ma Allah mai-rai.”—Ibraniyawa 9:12, 14.
23 Hakika, abin ban mamaki ne cewa masu shelar Mulki fiye da miliyan shida sun jimre a hidimar Allah cikin aminci duk da matsi na son kai da ya zama ruwan dare. Kuma hakan ya nuna cewa bayin Jehobah suna godiya sosai don gatarsu na bauta wa Allah, sun sani cewa wahalarsu “ba banza ta ke ba cikin Ubangiji.” Bari mu ci gaba da nuna irin wannan godiyar!—1 Korinthiyawa 15:58; Zabura 110:3.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene mai zabura ya koya mana game da nuna godiya ga Allah da tanadinsa na ruhaniya?
• Yaya kalmomin Haggai 2:7 suke cika a yau?
• Yaya Jehobah ya shirya bayinsa su bauta masa da kyau?
• Menene za ka yi don ka nuna godiyarka don alherin Jehobah?
[Hotuna a shafi na 25]
Jehobah ya shirya mu da kyau mu yi nufinsa