“Ba Ya Faɗa Musu Kome Ba Sai Game Da Misali”
“Yesu ya faɗa ma taron da misalai; ba ya faɗa musu kome ba sai game da misali.”—MATTA 13:34.
1, 2. (a) Me ya sa ba shi da sauƙi a manta da misalai masu ci? (b) Waɗanne irin misalai ne Yesu ya yi amfani da su, waɗanne tambayoyi suka taso game da yadda yake amfani da misalai? (Dubi hasiya.)
ZA KA iya tuna wani misali da ka ji, ƙila a wani jawabi da ka saurara shekaru da yawa da suka shige? Misalai masu ci da ƙyar a manta da su. Wani mawallafi ya lura cewa misalai “sukan sa kunnuwa su zama idanu su sa masu sauraro su ga hoton abin da suke ji.” Domin ya fi mana sauƙi mu fahimci abubuwa tare da ƙaga yadda suke a azanci, misalai sukan sa ya zama da sauƙi a fahimci ra’ayoyi. Misalai sukan ƙara ma’ana ga kalmomi, suna koyar da darussa da zai yi wuya mu manta.
2 Babu wani malami a duniya da ya taɓa kasancewa da gwaninta a yin amfani da misalai fiye da Yesu Kristi. Yana da sauƙi a tuna da almarar Yesu da sun kusan kai shekaru dubu biyu tun da ya faɗe su.a Me ya sa Yesu ya dogara sosai a kan irin wannan hanyar koyarwa? Kuma me ya sa misalansa suke ci haka?
Dalilin da Ya Sa Yesu Ya Koyar ta Misalai
3. (a) Daidai da Matta 13:34, 35, wane dalili ɗaya ne ya sa Yesu ya yi amfani da misalai? (b) Menene ya nuna cewa lallai Jehovah ya daraja wannan hanyar koyarwa?
3 Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai biyu da suka sa Yesu ya yi amfani da misalai. Na farko, yin haka ya cika annabci. Manzo Matta ya rubuta: “Yesu ya faɗa ma taron da misalai; ba ya faɗa musu kome ba sai game da misali: domin abin da aka faɗi ta bakin annabi ya cika, cewa, in buɗe bakina da misalai.” (Matta 13:34, 35) “Annabi” wanda Matta ya yi ƙaulinsa wanda ya rubuta Zabura 78:2 ne. Mai zaburar ya rubuta ta wurin hurewar ruhun Allah ƙarnuka kafin haihuwar Yesu. Ba abin mamaki ba ne cewa shekaru ɗarurruwa Jehovah ya ƙudura cewa Ɗansa zai koyar ta wurin misalai? Lallai Jehovah ya daraja wannan hanyar koyarwa!
4. Yaya Yesu ya bayyana dalilin da ya sa ya yi amfani da misalai?
4 Na biyu, Yesu kansa ya bayyana cewa ya yi amfani da misalai saboda ya ware waɗanda zukatansu sun taurara. Bayan da ya gaya wa “taro mai-girma” almarar mai shuki, almajiransa suka yi tambaya: “Don me ka ke yi musu zance da misalai?” Yesu ya amsa: “Ku aka ba da za ku san asiran mulkin sama, amma a garesu ba a bayar ba. Domin wannan ni ke yi musu zance da misalai; domin cikin dubawa ba su gani ba, cikin ji ba su ji ba, ba su kuwa fahimta ba. A garesu kuma an cika annabcin Ishaya, da ya ce, Cikin ji za ku ji, amma ba za ku fahimta ba ko kaɗan; cikin dubawa za ku gani, ba za ku gane ba ko kaɗan: Gama zuciyar al’umman nan ta yi taiɓa.”—Matta 13:2, 10, 11, 13-15; Ishaya 6:9, 10.
5. Ta yaya misalan Yesu ya ware masu sauraro masu tawali’u daga waɗanda suke da zukata ta fahariya?
5 Me ke cikin misalan Yesu da ya ware mutane? A wasu lokatai, masu sauraronsa sai sun yi bincike da kyau don su fahimci ma’anar furcinsa. An aririci mutane masu tawali’u su yi tambaya don su samu ƙarin bayani. (Matta 13:36; Markus 4:34) Ta haka, misalan Yesu sun bayyana gaskiya ga waɗanda suke da yunwarta; kuma misalansa sun rufe gaskiya daga waɗanda suke da zukata ta fahariya. Lallai Yesu malami ne mai girma! Yanzu sai mu bincika wasu abubuwa da suka sa misalansa suke da kaifi.
Zaɓen Bayani
6-8. (a) Wane zarafi ne masu sauraron Yesu na ƙarni na farko ba su da shi lokacin? (b) Waɗanne misalai suka nuna cewa Yesu ya yi zaɓe a yadda yake ba da bayani?
6 Ka taɓa tunanin yadda yake ga waɗancan almajirai na ƙarni na farko da suka saurari Yesu yana koyarwa? Sun sami gata su ji muryar Yesu, amma ba su da zarafin buɗe littattafai don su tuna abin da ya faɗa. Maimakon haka, suna bukatar su kasance da kalmomin Yesu a azantai da kuma zukatansu. Ta wurin yin amfani mai kyau da misalai, Yesu ya sa ya zama da sauƙi su tuna abin da ya koyar. Ta yaya?
7 Yesu yana zaɓe a batun bayani. Idan ana bukatar ambata ainihin abu ko kuma a yi wani nanatawa, yana mai da hankali sosai ya yi hakan. Shi ya sa ya ambata adadin tumaki da mai su ya bari don ya je ya nemi wanda ya ɓata, yawan sa’o’in aiki da masu aiki suka yi cikin gonar anab, da kuma talinti nawa aka ba da jingina.—Matta 18:12-14; 20:1-16; 25:14-30.
8 Har ila, Yesu ya bar wasu bayani da ba a bukata don mu iya fahimtar ma’anar misalan. Ga misali, cikin almarar bawa marar tausayi, bai ba da bayanin dalilin da ya sa bawan ya ci bashi har ya kai dinari 60,000,000 ba. Abin da Yesu yake nanatawa bukatar yin gafara ne. Muhimmin abu shi ne, ba yadda bawan ya ci bashin ba ne, amma yadda aka gafarta masa bashin da kuma yadda shi ya bi da ɗan’uwansa bawa da ya ci ɗan bashinsa. (Matta 18:23-35) Haka kuma, cikin almarar ɗa mubazzari, Yesu bai ba da bayanin abin da ya sa ƙaramin ɗan ya biɗi gadōnsa da abin da ya sa ya lalata shi ba. Amma Yesu ya ba da bayanin yadda uban ya ji da kuma yadda ya aikata sa’ad da ɗansa ya yi gyara kuma ya dawo gida. Ana bukatar bayani game da yadda uban ya aikata domin darasi da Yesu yake so ya koyar, cewa Jehovah yana gafartawa a “yalwace.”—Ishaya 55:7; Luka 15:11-32.
9, 10. (a) Da yake ambata waɗanda suke cikin almararsa, a kan menene Yesu ya mai da hankali? (b) Yaya Yesu ya sa ya zama da sauƙi ga masu sauraronsa da kuma wasu su tuna da almararsa?
9 Yesu kuma yana da hikima a yadda yake nuna waɗanda ke cikin almararsa. Maimakon ba da bayani na dalla-dalla a kwatanta mutanen, sau da yawa Yesu yana mai da hankali ga abin da suka yi ko kuma yadda suka aikata cikin labarin da yake bayarwa. Shi ya sa, maimakon ya kwatanta yadda mutumin Basamariyen yake, Yesu ya yi zancen abin da ya fi muhimmanci—yadda Basamariyen ya taimaki Bayahude da aka ji wa rauni yana kwance a kan hanya. Yesu ya tanadar da bayanin da ake bukata don ya koyar da ƙaunar maƙwabci da ya kamata a nuna wa mutane ban da yarenmu ko kuma ga waɗanda ba mu fito daga ƙasa ɗaya ba.—Luka 10:29, 33-37.
10 Yadda Yesu ya mai da hankali a yin amfani da bayanin cikin almararsa ya sa ta zama gajeruwa kuma a ƙa’ide. Ya sa ya zama da sauƙi ga masu sauraronsa na ƙarni na farko—da kuma wasu da yawa da za su karanta shi cikin Lingilar—su tuna da su da kuma darussa masu muhimmanci da suke koyarwa.
Daga Abubuwa na Yau da Kullum
11. Ka ba da misalan yadda almarar Yesu ya nuna abubuwa da babu shakka ya lura da su yayin da yake girma a Galili.
11 Yesu gwani ne a yin amfani da almara da ke game da rayuwar mutane. Da yawa cikin almararsa suna ɗauke da abubuwa da babu shakka ya lura da su yayin da yake girma ne a Galili. Ka ɗan dakanta, ka yi tunani game da rayuwarsa da farko. Sau nawa ya lura da mamarsa tana curin gurasa da yisti da ta ɗiba kaɗan daga tsohon curi ya zama yisti na sabon curi? (Matta 13:33) Sau nawa yake ganin masunta suna jefa taru cikin ruwayen Tekun Galili? (Matta 13:47) Sau nawa yake ganin yara suna wasa a kasuwa? (Matta 11:16) Mai yiwuwa ne Yesu ya lura da wasu abubuwa na yau da kullum da suke cikin almararsa—irin da ake shukawa, bikin aure na farin ciki, da kuma gonar alkama da ke nuna a cikin rana.—Matta 13:3-8; 25:1-12; Markus 4:26-29.
12, 13. Yaya almarar Yesu ta alkama da zawa ta nuna yadda ya saba da yanayin yankin?
12 Ba abin mamaki ba fa da yanayi na kowacce rana suke cikin almara da yawa na Yesu. Don a ƙara fahimtar gwanintarsa a yin amfani da wannan hanyar koyarwar, zai yi kyau a bincika abin da kalmominsa suke nufi ga Yahudawa da suke sauraronsa. Bari mu ɗauki misalai biyu.
13 Na farko, a cikin almararsa na alkama da zawa, Yesu ya faɗi game da wani mutumin da ya shuka alkama a gonarsa amma ‘maƙiyi’ ya shigo gonar ya shuka masa zawa. Me ya sa Yesu ya zaɓi wannan misali na mugun hali? To, ka tuna cewa ya ba da almarar nan a kusa da Tekun Galili ne, kuma sana’ar mutanen Galili noma ce. Me ya kai wannan muni da maƙiyi ya shiga a ɓoye ya shuka mugun zawa a gonar manomi? Cikin dokoki na ƙasarsu a lokacin, ya nuna cewa irin wannan abin ya faru. Ba a bayyane yake cewa Yesu ya yi amfani da yanayi da masu sauraronsa suka saba da shi ba?—Matta 13:1, 2, 24-30.
14. A cikin almarar Basamariye mai maƙwabtaka, me ya sa yake da muhimmanci cewa Yesu ya yi amfani da hanyar da take “daga Urushalima zuwa Jericho” don ya koyar da darasinsa?
14 Na biyu, ka tuna da almarar Basamariye mai maƙwabtaka. Yesu ya fara da cewa: “Wani mutum yana tafiya daga Urushalima zuwa Jericho; ya gamu da mafasa, suka yi masa tsiraici, suka dudduke shi, suka tashi, suka bar shi tsakanin rai da mutuwa.” (Luka 10:30) Mafi muhimmanci, Yesu ya yi amfani da hanyar da take “daga Urushalima zuwa Jericho” don ya koyar da darasin. Lokacin da yake faɗin almarar, yana Yahudiya ne, kusa da Urushalima; saboda haka masu sauraronsa sun san hanyar. An san wannan hanyar da haɗari, musamman idan mutum shi kaɗai ke tafiya. Hanyar tana da kwāna-kwāna da mafasa suke samun wajen ɓuya.
15. Me ya sa babu wanda zai ba da hujjar rashin tausayin firist da Balawi na cikin almarar da ta ƙunshi Basamariye mai maƙwabtaka?
15 Da akwai abin lura a yadda Yesu ya ambaci hanyar da take “daga Urushalima zuwa Jericho.” Bisa ga labarin, na farko firist ne sai kuma Balawi suke tafiya a kan wannan hanyar—amma babu wani cikinsu da ya tsaya ya taimaki mai raunin. (Luka 10:31, 32) Firistoci suna hidima a haikali a Urushalima, kuma Lawiyawa suna taimakonsu. Firistoci da yawa da kuma Lawiyawa suna zama a Jericho yayin da ba sa aiki a haikali, domin Jericho mil 14 ne kawai daga Urushalima. Saboda haka, lallai suna da dalilin yin tafiya a kan wannan hanyar. Ka kuma lura cewa, firist da Balawi suna tafiya a kan hanyar da ke “daga Urushalima,” suna dawowa daga haikali. Saboda haka, babu wani da zai ba da hujjar rashin tausayin mutanen nan, ‘Sun guji mutumi mai raunin ne domin kamar ya riga ya mutu, kuma taɓa gawa zai ƙazantar da su na ɗan lokaci da ba za su iya yin hidima ba a haikalin.’ (Leviticus 21:1; Litafin Lissafi 19:11, 16) Ba a bayyane yake cewa almarar Yesu a kan abubuwan da masu sauraronsa suka saba da su ba ne?
Da Aka Ɗauko Daga Halitta
16. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa Yesu ya sarƙu da halitta?
16 Da yawa cikin misalai da almarar Yesu sun nuna yadda ya sarƙu da shuke-shuke, dabbobi, da kuma wasu abubuwa. (Matta 6:26, 28-30; 16:2, 3) Ina ya sami irin ilimin nan? Yayin da yake girma a Galili, yana da zarafi da yawa na lura da halittar Jehovah. Fiye da haka, Yesu “ɗan fari ne gaban dukan halitta,” kuma Jehovah ya yi amfani da shi “gwanin mai-aiki” a halittar dukan abubuwa. (Kolossiyawa 1:15, 16; Misalai 8:30, 31) Abin mamaki ne da Yesu ya sarƙu da halitta haka? Bari mu ga yadda ya yi amfani mai kyau da wannan ilimin a koyarwarsa.
17, 18. (a) Ta yaya kalmomin Yesu da ke a Yohanna sura 10 ya bayyana cewa ya sarƙu da halayen tumaki? (b) Menene baƙi da suke zuwan ƙasashen Littafi Mai Tsarki suka lura game da gamin makiyaya da tumakinsu?
17 Cikin misalan Yesu mafi ban motsawa shi ne wanda ke a Yohanna sura 10, inda ya kamanta dangantakarsa ta kusa da mabiyansa da na makiyayi da tumakinsa. Kalmomin Yesu ya nuna cewa ya san halayen tumaki sosai. Ya nuna cewa tumaki suna yarda a yi musu ja-gora, kuma cewa suna bin makiyayin cikin aminci. (Yohanna 10:2-4) Baƙi da suke zuwa ƙasashen Littafi Mai Tsarki sun lura da gamin da ke tsakanin makiyaya da tumaki. Masanin halitta H. B. Tristram na ƙarni na 19 ya lura: “Na taɓa ganin makiyayi yana wasa da garkensa. Yana musu wasan gudu; tumakin suka bi shi suka kewaye shi. . . . A ƙarshe suka gewaye shi suna wasan tsalle-tsalle a jikinsa.”
18 Me ya sa tumaki suke bin makiyayinsu? “Gama sun san muryatasa,” in ji Yesu. (Yohanna 10:4) Shin, tumaki sun san muryar makiyayinsu da gaske? Daga abin da ya lura, George A. Smith ya rubuta cikin littafinsa The Historical Geography of the Holy Land: “Wani lokaci muna shan iska da rana a kusa da wata rijiyar Yahudawa, sai makiyaya uku ko kuma huɗu suka taho da garkensu. Garken suka gauraya da juna, muna mamaki yadda kowanne makiyayi zai iya sanin nasa. Amma bayan da suka gama shan ruwa da kuma wasa, sai makiyaya bi-da-bi suka kama hanyarsu dabam dabam zuwa kwarin, kuma kowanne ya yi kirar da yake yi wa nasa; kuma kowanne cikin tumakin suka bi nasu makiyayi daga cikin garken yadda suka taho.” Hakika babu wata hanya da ta fi kyau da Yesu zai kwatanta wannan darasin. Idan muka gane kuma yi biyayya da koyarwarsa kuma muka bi ja-gorarsa, za mu iya kasance ƙarƙashin kulawa mai kyau na ƙauna na “makiyayi mai-kyau.”—Yohanna 10:11.
Ya Ɗauko Daga Aukuwa da Masu Sauraronsa Suka Sani
19. Don ya huɗubantar da koyarwar ƙarya, yaya Yesu ya yi amfani da abin da ya faru a yankin?
19 Ana iya ɗauko almara masu ci daga labarai ko kuma misalai da za a iya samun darasi ciki. A wani lokaci, Yesu ya yi amfani da wani abin da ya faru domin ya ƙi wani ra’ayin cewa masu-alhaki ne bala’i ke faɗa musu. Ya ce: “Ko kuwa waɗannan ashirin biyu babu, da soro ya auko musu cikin Silwami, ya kashe su, kuna tsammani su masu-alhaki [masu zunubi] ne gaba da dukan mazauna cikin Urushalima?” (Luka 13:4) Yesu ya yi bayani sarai gaba da irin wannan ra’ayin ƙaddara. Waɗannan mutane 18 ba su mutu ba domin wani zunubi da Allah ya hore su. Maimako, mutuwarsu domin sa’a ne da tsautsayi. (Mai-Wa’azi 9:11) Ta haka ya huɗubantar da koyarwar ƙarya ta yin nuni ga wani aukuwa da masu sauraronsa suka sani.
20, 21. (a) Me ya sa Farisawa suka hukunta almajiran Yesu? (b) Wane labari ne na Nassi Yesu ya yi amfani da shi ya kwatanta cewa Jehovah bai nufi tilasta dokar Asabarci ba? (c) Me za a tattauna cikin talifi na gaba?
20 A cikin koyarwarsa, Yesu kuma ya yi amfani da misalai na Nassi. Ka tuna da lokacin da Farisawa suka hukunta almajiransa domin sun tsinka kuma ci hatsi a ranar Asabarci. A gaskiya kam, almajiran sun karya mugun bayanin dokar Farisawan ne na abin da wai aiki ne a ranar Asabarci ba Dokar Allah ba. Don ya bayyana cewa Allah ba ya tilastawa a zancen dokarsa ta Asabarci, Yesu ya ambaci abin da ya faru da ke a 1 Samu’ila 21:3-6. Da suke jin yunwa, Dauda da mutanensa suka tsaya a mazauni kuma suka ci gurasa na nuni, da ta tsufa. Da ma tsofaffin gurasar domin firistoci ne su ci. Duk da haka, domin yanayin da ake ciki, ba a hukunta Dauda da mutanensa don sun ci ba. Alhali, wannan ne kaɗai inda Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da tsohon gurasa da waɗanda ba firistoci ba suka ci. Yesu ya san Nassin da ya yi daidai da zai yi amfani da shi, kuma masu sauraronsa Yahudawa sun san wannan.—Matta 12:1-8.
21 Hakika, Yesu Babban Malami ne! Babu shakka, sai mu yi mamaki kawai game da iyawarsa da babu na biyunsa a idar da muhimman gaskiya a hanyar da masu sauraronsa suka fahimta. To, ta yaya za mu iya yin koyi da shi a koyarwarmu? Za a tattauna wannan cikin talifi na gaba.
[Hasiya]
a Misalan Yesu sun fito daga fannoni dabam dabam, sun haɗa da almara, kwatanci, da kuma kamanci. An san shi da yin amfani da almara, da aka ba da ma’anarsa cewa “gajeruwar tatsuniya ce, labari da a cikinta ake fahimtar gaskiya ta ɗabi’a ko kuma ta ruhaniya.”
Ka Tuna?
• Me ya sa Yesu ya koyar da misalai?
• Waɗanne misalai suka nuna cewa Yesu ya yi amfani da misalai da masu sauraronsa na ƙarni na farko suka sani?
• Ta yaya Yesu ya yi amfani da iliminsa na halitta cikin gwanintarsa a yin amfani da misalai?
• A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya yi amfani da aukuwa da masu sauraronsa suka sani?
[Hotuna a shafi na 22]
Yesu ya yi zancen bawa da ya ƙi ya gafarta bashi kalilan kawai da kuma uban da ya gafarta wa ɗan da ya kwashi dukan gadōnsa ya lalatar
[Hoto a shafi na 23]
Menene manufar almarar Yesu na Basamariye mai maƙwabtaka?
[Hoto a shafi na 24]
Shin tumaki da gaske sun san muryar makiyayinsu?