Jehovah Yana Biyan Bukatunmu Na Kullum
“Kada kuwa ku yi zuciya biyu. Gama . . . Ubanku ya sani kuna bukatar waɗannan abu.”—LUKA 12:29, 30.
1. Ta yaya Jehovah yake ciyar da dabbobi?
KA TAƁA kallon gwara ko wata tsuntsuwa tana saran abin da kamar datti ne? Wataƙila ka yi mamaki abin da za ta samu ta ci ta wurin saran ƙasa. A cikin Huɗubarsa Bisa Dutse, Yesu ya nuna cewa za mu iya koyan darasi daga yadda Jehovah yake ciyar da tsuntsaye. Ya ce: “Ku duba tsuntsaye na sama, ba su kan yi shuka ba, ba su kan yi girbi ba, ba su kan tattara cikin rumbuna ba; amma Ubanku na sama yana ciyarda su. Ku ba ku fi su daraja dayawa ba?” (Matta 6:26) Jehovah yana ciyar da dukan halittunsa a hanya ta ban al’ajabi.—Zabura 104:14, 21; 147:9.
2, 3. Waɗanne darussa na ruhaniya za mu iya koya da yake Yesu ya koya mana mu yi addu’a don abincin yini?
2 To, me ya sa Yesu ya haɗa cikin roƙonsa a addu’ar misali cewa: “Ka ba mu yau abincin yini”? (Matta 6:11) Za a iya koyan darrusa na ruhaniya masu ma’ana daga wannan roƙo mai sauƙi. Na farko, ya tuna mana cewa Jehovah ne Mai Tanadi Mai Girma. (Zabura 145:15, 16) ’Yan Adam za su iya shuki kuma su yi noma, amma Allah ne kaɗai zai iya sa abubuwa su yi girma a ruhaniya da kuma a zahiri. (1 Korinthiyawa 3:7) Abin da muke ci da kuma sha kyauta ce daga Allah. (Ayukan Manzanni 14:17) Roƙonsa ya ba mu bukatunmu na kullum yana nuna masa cewa muna godiya ga waɗannan tanadi. Hakika, irin wannan roƙo ba ya cire mana hakkinmu mu yi aiki idan za mu iya yin hakan ba.—Afisawa 4:28; 2 Tassalunikawa 3:10.
3 Na biyu, roƙon “abincin yini” ya nuna cewa bai kamata muna alhini ainun game da nan gaba ba. Yesu ya daɗa cewa: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da menene za mu yi sutura? Gama waɗannan abu duka Al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abu duka. Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abu duka fa za a ƙara muku su. Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama gobe za ya yi alhini don kansa.” (Matta 6:31-34) Addu’ar “abincin yini” ya kafa gurbin yin rayuwa mai sauƙi ta “ibada tare da wadar zuci.”—1 Timothawus 6:6-8.
Abincin Ruhaniya na Kullum
4. Waɗanne abubuwa da suka faru a rayuwar Yesu da na Isra’ilawa suka nanata muhimmancin cin abinci na ruhaniya?
4 Addu’armu don abincin yini ya kamata ta tuna mana bukatarmu ta abincin ruhaniya na kullum. Ko da yana jin yunwa sosai bayan ya yi azumi na dogon lokaci, Yesu ya tsayayya wa jarabar Shaiɗan cewa ya mai da duwatsu zuwa abinci, da ya ce: “An rubuta, ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowacce magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) A nan, Yesu ya maimaita abin da annabi Musa ya ce, wanda ya gaya wa Isra’ilawa: “[Jehovah] ya kuwa sauke girman kanka, ya bar ka ka ji yunwa, ya kuma ciyarda kai da manna, abin da ba ka san shi ba, ubanninka kuma ba su san shi ba; domin ya sa ka ka sani mutum ba da abinci kaɗai ya ke rayuwa ba, amma da kowane abin da ke fitowa daga bakin Ubangiji mutum ke rayuwa.” (Kubawar Shari’a 8:3) Yadda Jehovah ya yi tanadin manna ya ba Isra’ilawa ba kawai abinci na zahiri ba amma ya kuma koya musu darussa ta ruhaniya. Darasi na ɗaya shi ne cewa “kowacce rana su tattara bukatar yini.” Idan suka tattara fiye da abin da suke bukata a rana, sauran za su yi ɗoyi su kuma soma tsutsa. (Fitowa 16:4, 20) Amma, hakan bai faru ba a rana ta shida da za su tattara na kwana biyu ya ƙosar da bukatunsu don Asabarci. (Fitowa 16:5, 23, 24) Saboda haka, manna ta tuna musu cewa ya kamata su yi biyayya kuma cewa rayuwarsu ta dangana ba kawai a kan abinci ba amma a kan “kowane abin da ke fitowa daga bakin Ubangiji.”
5. Ta yaya Jehovah yake mana tanadin abincin ruhaniya na kullum?
5 Haka nan ma muna bukatar mu ci abincin ruhaniya na kullum da Jehovah yake tanadinsa ta wurin Ɗansa. Shi ya sa Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadin “abinci . . . a lotonsa” wa iyalin imani. (Matta 24:45) Ajin bawan nan mai aminci ba kawai yana ba da abincin ruhaniya a yalwace ta littattafan nazarin Littafi Mai Tsarki ba amma kuma yana ƙarfafa mu mu karanta Littafi Mai Tsarki kullum. (Joshua 1:8; Zabura 1:1-3) Kamar Yesu, mu ma za a ciyar da mu a ruhaniya idan muka yi ƙoƙari kullum mu koya game da Jehovah kuma mu yi nufinsa.—Yohanna 4:34.
Gafartawan Zunubai
6. A kan waɗanne basusuka za mu nemi gafara, a kan waɗanne yanayi Jehovah yake a shirye ya yafe su?
6 Roƙo na gaba cikin addu’ar misali shi ne: “Ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.” (Matta 6:12) Yesu ba ya maganar bashin kuɗi a nan. Yana nufin gafarta zunubanmu. Yadda Luka ya rubuta wannan roƙon a addu’ar misali shi ne: “Ka gafarta mana zunubanmu; gama mu da kanmu kuma muna gafarta ma dukan wanda ya ke mabarcinmu.” (Luka 11:4) Domin haka, sa’ad da muka yi zunubi, kamar Jehovah yana binmu bashi ne. Amma Ubanmu mai ƙauna yana shirye ya “shafe” ko kuma ya yafe wannan bashin idan muka tuba da gaske, muka “juyo” kuma muka nemi gafara ta bangaskiya a hadayar fansa ta Kristi.—Ayukan Manzanni 3:19; 10:43; 1 Timothawus 2:5, 6.
7. Me ya sa ya kamata kullum mu yi addu’a a gafarta mana?
7 A wata sassa, mun yi zunubi sa’ad da muka kasa cika mizanan adalci na Jehovah. Domin zunubi da muka gada, dukanmu muna zunubi ta abin da muke faɗa, muke yi, da kuma tunanin munanan abubuwa ko kuma mu kasa yin abubuwa da ya kamata mu yi. (Mai-Wa’azi 7:20; Romawa 3:23; Yaƙub 3:2; 4:17) Saboda haka, ko mun sani cewa mun yi zunubi a rana ko ba mu sani ba, a cikin addu’o’inmu na kullum muna bukatar mu roƙi a gafarta mana zunubanmu.—Zabura 19:12; 40:12.
8. Me ya kamata addu’ar neman gafara ta sa mu yi, da wane sakamako mai kyau?
8 Ya kamata mu yi addu’ar gafara bayan mun bincika kanmu sosai, mun tuba, kuma yi ikirari bisa ga imanin ikon fansa na jinin da Kristi ya zubar. (1 Yohanna 1:7-9) Don mu nuna cewa addu’armu ta gaske ce, dole mu goyi bayan roƙon gafara ta wurin ‘ayyuka waɗanda sun cancanci tuba.’ (Ayukan Manzanni 26:20) Ta haka, za mu kasance da bangaskiya cewa Jehovah yana shirye ya gafarta mana zunubanmu. (Zabura 86:5; 103:8-14) Sakamakon shi ne kwanciyar rai da babu na biyunta, “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka,” da “za ta tsare zukatan[mu] da tunanin[mu] cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 4:7) Amma addu’ar misali na Yesu ya ƙara koya mana game da abin da dole mu yi a gafarta mana zunubanmu.
Domin a Gafarta Mana, Dole Mu Gafarta wa Mutane
9, 10. (a) Wane bayani Yesu ya daɗa ga addu’ar misali, menene wannan ya nanata? (b) Yaya Yesu ya ƙara kwatanta bukatar mu gafarta?
9 Roƙon cewa “Ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu,” shi ne sashen addu’ar misali da Yesu ya yi bayani a kai. Bayan ya kammala addu’ar, ya daɗa: “Gama idan kuna gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku na sama kuma za ya gafarta muku. Amma idan ba ku gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofi ba.” (Matta 6:14, 15) A ta haka, Yesu ya bayyana sarai cewa Jehovah zai gafarta mana idan muna a shirye mu gafarta wa wasu.—Markus 11:25.
10 Wani lokaci, Yesu ya ba da misali da ya nuna cewa muna bukatar gafartawa idan muna son Jehovah ya gafarta mana. Ya ba da labarin wani sarki da ya yafe bashi mai yawa da wani bawa ya ci. Daga baya wannan sarkin ya hori wannan mutumin da ya ƙi ya yafe ɗan bashin da ɗan’uwansa bawa ya ci da bai kusan nasa ba ma. Yesu ya kammala wannan misalin da cewa: “Hakanan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta ma ’yan’uwanku.” (Matta 18:23-35) Darasin a bayyane yake: Yawan zunubi da Jehovah yake gafarta wa kowannenmu ya fi kowanne laifi da wani yake mana. Ballantana ma, Jehovah yana gafarta mana kullum. Saboda haka, za mu yafe laifi na wani lokaci da wasu suke mana.
11. Wane gargaɗi da manzo Bulus ya ba da za mu bi idan muna son Jehovah ya gafarta mana, da wane sakamako mai kyau?
11 Manzo Bulus ya rubuta: “Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta muku.” (Afisawa 4:32) Gafartawa na sa salama ta kasance tsakanin Kiristoci. Bulus ya daɗa ariritawa: “Domin ku zaɓaɓu na Allah ne, masu-tsarki, ƙaunatattu kuma, ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kolossiyawa 3:12-14) Dukan waɗannan suna cikin addu’ar misali da Yesu ya koya mana: “Ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.”
Kāriya Sa’ad da Ake Fuskantar Jaraba
12, 13. (a) Menene wannan roƙo cikin addu’ar misali ba ya nufi? (b) Wanene Mai Jaraba mai girma, mecece addu’a kada a kai mu cikin jaraba take nufi?
12 Yesu ya yi roƙo kuma cikin addu’ar misali cewa: “Kada ka kai mu cikin jaraba.” (Matta 6:13) Yesu cewa yake mu gaya wa Jehovah kada ya jarabe mu ne? Ba haka ba, domin an hure almajiri Yaƙub ya rubuta: “Kada kowa sa’anda ya jarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” (Yaƙub 1:13) Ƙari ga haka, mai Zabura ya rubuta: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Jehovah ba ya jiran mu yi kuskure, kuma ba ya jarabarmu mu yi kuskure. To, menene wannan sashe na addu’ar misali yake nufi?
13 Wanda yake ƙoƙari ya jarabce mu, ya sa mu fāɗi ta wurin dabaru, har ma ya cinye mu shi ne Shaiɗan Iblis. (Afisawa 6:11) Shi ne Mai Jaraba mai girma. (1 Tassalunikawa 3:5) Ta yin addu’a kada a kai mu cikin jaraba, muna gaya wa Jehovah kada ya ƙyale mu mu fāɗi sa’ad da muke fuskantar jaraba. Muna gaya masa ya taimake mu “kada Shaiɗan ya ci ribar kome a bisanmu,” kada mu fāɗa wa jaraba. (2 Korinthiyawa 2:11) Muna addu’a mu kasance cikin “sitirar Maɗaukaki,” muna samun kāriya ta ruhaniya da aka yi alkawarinsa wa waɗanda suke amince da ikon mallakar Jehovah a dukan abubuwa da suke yi.—Zabura 91:1-3.
14. Ta yaya manzo Bulus ya tabbatar mana cewa Jehovah ba zai yasar da mu ba idan muka biɗe shi sa’ad da muke fuskantar jaraba?
14 Idan wannan ne sha’awarmu ta gaske, kuma muna yi cikin addu’o’inmu da ayyukanmu, muna tabbata cewa Jehovah ba zai taɓa yasar da mu ba. Manzo Bulus ya tabbatar mana: “Babu wata jaraba [da za] ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa: amma Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1 Korinthiyawa 10:13.
“Ka Cece Mu Daga Mugun”
15. Me ya sa ya fi muhimmanci yanzu mu yi addu’a a cece mu daga mugun?
15 Bisa ga rubutun hannu na Nassosin Kirista na Helenanci da aka fi tabbata da shi, addu’ar misali na Yesu ya ƙare da kalmomin nan: “Ka cece mu daga Mugun.”a (Matta 6:13) Kāriya daga Iblis ta fi muhimmanci a wannan lokaci na ƙarshe. Shaiɗan da aljannunsa suna yaƙi da raguwar shafaffu, “waɗanda su ke kiyaye da dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu,” da abokan tarayyarsu “taro mai-girma.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9; 12:9, 17) Manzo Bitrus ya yi wa Kiristoci gargaɗi: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye: ku tsaya masa fa, kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku.” (1 Bitrus 5:8, 9) Shaiɗan zai so ya daina aikinmu na wa’azi, kuma ta mabiyansa a duniya—ko na addini, ’yan kasuwanci, ko ’yan siyasa—yana ƙoƙari ya tsoratar da mu. Amma, idan mun dage, Jehovah zai cece mu. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ku zama fa masu-biyayya ga Allah amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—Yaƙub 4:7.
16. Menene Jehovah yake amfani da shi ya taimake bayinsa da suke fuskantar gwaji?
16 Jehovah ya yarda a jarabci Ɗansa. Amma bayan Yesu ya yi tsayayya da Iblis, ya yi amfani da Kalmar Allah ya kāre kansa, Jehovah ya aika mala’iku su ƙarfafa shi. (Matta 4:1-11) Haka nan ma, Jehovah yana amfani da mala’ikunsa su taimake mu idan muka yi addu’a da bangaskiya kuma muka sa shi ya zama mafakarmu. (Zabura 34:7; 91:9-11) Manzo Bitrus ya rubuta: “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba, ya tsare marasa-adalci kuma ƙarƙashin hukunci har zuwa ranar shari’a.”—2 Bitrus 2:9.
Ceto na Dindindin Ya Kusa
17. Ta wurin koya mana addu’ar misali, ta yaya Yesu ya tsara abubuwa yadda suka dace?
17 A cikin addu’ar misali, Yesu ya tsara abubuwa yadda suka dace. Damuwarmu ta musamman ya kamata ya zama tsarkake suna mai girma kuma mai tsarki na Jehovah. Tun da abin da za a yi amfani da shi a cim ma wannan shi ne Mulkin Almasihu, muna addu’a Mulkin ya zo ya halaka dukan mulkoki ko kuma gwamnatoci na ’yan Adam ajizai, kuma a tabbata cewa ana nufin Allah sosai a duniya yadda ake yi a sama. Begenmu na rai har abada cikin aljanna a duniya ya dangana ga tsarkake sunan Jehovah kuma amince da ikon mallakarsa na adalci a dukan sararin samaniya. Bayan mun yi roƙo don waɗannan abubuwa da suka fi muhimmanci, za mu iya roƙon bukatunmu na kullum, gafarta zunubanmu, kuma a cece mu daga jaraba da kuma ruɗun mugun, Shaiɗan Iblis.
18, 19. Ta yaya addu’ar misali ta Yesu ta taimake mu mu kasance a faɗake kuma ta sa begenmu ta kasance “da ƙarfi har matuƙa”?
18 Lokaci da za a cece mu gabaki ɗaya daga mugun da kuma lalatacen zamaninsa yana kurkusa. Shaiɗan ya sani sarai cewa “sauran zarafinsa kaɗan ne,” da zai yi “hasala mai-girma” a duniya, musamman a kan bayin Jehovah masu aminci. (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) A cikin haɗaɗiyar “alamar zuwan[sa] da cikar zamani,” Yesu ya annabta aukuwa na musamman, wasu har ila suna gaba. (Matta 24:3, 29-31) Yayin da muke ganin waɗannan suna faruwa, begenmu na ceto zai zama da gaske. Yesu ya ce: “Sa’anda waɗannan al’amura sun soma faruwa, ku duba bisa, ku tada kanku; gama fansarku ta kusa.”—Luka 21:25-28.
19 Gajeriyar addu’ar misali da Yesu ya koya wa almajiransa ta yi mana ja-gora ga abin da za mu yi roƙonsa cikin addu’o’inmu yayin da ƙarshen yana kurkusa. Bari mu kasance da gaba gaɗi cewa har zuwa ƙarshe, Jehovah zai ci gaba da yi mana tanadin bukatunmu na kullum, na ruhaniya da na jiki. Kasance a faɗake ta yin addu’a zai taimake mu mu “riƙe mafarin sakankancewarmu da ƙarfi har matuƙa.”—Ibraniyawa 3:14; 1 Bitrus 4:7.
[Hasiya]
a Wasu Littafi Mai Tsarki na dā, kamar King James Version na Turanci, sun kammala Addu’ar Ubangiji da yabo ga Allah: “Mulkin naka ne, da iko, da ɗaukaka, har abada. Amin.” Littafin nan The Jerome Biblical Commentary ya ce: “Yabo ga Allah . . . ba ya cikin yawancin tabbataccen [rubutun hannu].”
A Maimaitawa
• Menene yake nufi sa’ad da muke roƙo a ba mu “abincin yini”?
• Ka bayyana addu’ar “ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.”
• Menene yake nufi sa’ad da muke cewa Jehovah kada ya kai mu cikin jaraba?
• Me ya sa muke bukatar mu yi addu’a a “cece mu daga Mugun”?
[Hotuna a shafi na 21]
Idan za a gafarta mana dole muna gafarta wa mutane
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 19]
Daga Lydekker