Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 24 pp. 240-249
  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kana da Tamani ga Jehobah
  • Mene ne Jehobah Ya Gani a Cikinmu?
  • Jehobah Yana Tace Nagari Daga Mugu
  • Jehobah Yana Nuna Ƙaunarsa Sosai
  • “Allah Ƙauna Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Jehobah Ya Ƙidaye “Gashin Kanku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Mai Lura da Ya San Tamaninmu Luka 12:6, 7
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Jehobah Yana Kaunarka Sosai!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 24 pp. 240-249
Wata mata tana bakin ciki kuma tana zub da hawaye.

BABI NA 24

Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”

1. Wane tunani ne mai kasalarwa yake damun mutane da yawa, har ma da wasu Kiristoci na gaskiya?

JEHOBAH Allah yana ƙaunarka kuwa? Wasu sun yarda cewa Allah yana ƙaunar dukan mutane, kamar yadda Yohanna 3:16 ta ce. Amma suna jin cewa: ‘Allah ba zai taɓa ƙaunarsu ba.’ Har Kiristoci na gaskiya ma wani lokaci suna yin shakkar wannan. Da ya kasala, wani mutum ya ce: “Yana da wuya ƙwarai in yarda cewa Allah ya damu da ni.” Irin wannan shakkar tana damunka wani lokaci?

2, 3. Wa yake so mu gaskata cewa ba mu da amfani ko kuma ba mu dace da ƙauna ba a idanun Jehobah, kuma ta yaya za mu yaƙi wannan ra’ayin?

2 Shaiɗan yana ɗokin ya sa mu yarda cewa Jehobah Allah ba ya ƙaunarmu ko ma cewa ba ya ɗaukanmu da tamani. Hakika, sau da yawa Shaiɗan yana rinjayar mutane ta wajen sha’awar siffarsu da kuma fahariyarsu. (2 Korintiyawa 11:3) Har ma yana ƙoƙarin ya ci mutuncin raunannu. (Yohanna 7:47-49; 8:13, 44) Wannan haka yake musamman a waɗannan “kwanakin ƙarshe.” Mutane da yawa a yau sun yi girma a iyalai da babu “ƙauna.” Wasu kullayaumi suna tare da mutane masu zafin hali, masu son kansu, da kuma masu taurin kai. (2 Timoti 3:1-5) Lokaci mai tsawo na irin wannan tsanantawa, wariyar launin fata, ko kuma ƙiyayya zai iya sa irin waɗannan su tabbata cewa ba su da amfani ko kuma ba su dace a ƙaunace su ba.

3 Idan ka lura da irin wannan game da kanka, kada ka fid da rai. Da yawa cikinmu muna hukunta kanmu lokaci lokaci. Amma ka tuna, Kalmar Allah an shirya ta domin “gyaran hali” da “rushe wurare masu ƙarfi.” (2 Timoti 3:16; 2 Korintiyawa 10:4) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyarmu za ta kasance da tabbaci cewa za mu iya tsayawa a gaban Allah. Duk sa’ad da zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun sani cewa Allah ya fi zuciyarmu ya kuma san dukan kome.” (1 Yohanna 3:19, 20) Bari mu bincika wurare huɗu inda Nassosi suke taimaka mana mu sa zuciyarmu ta kasance da “tabbata” ga ƙaunar Jehobah.

Kana da Tamani ga Jehobah

4, 5. Ta yaya misalin Yesu na gwarare ya nuna cewa muna da tamani a idanun Jehobah?

4 Na farko, Littafi Mai Tsarki ya koyar kai tsaye cewa Allah yana ganin tamanin kowanne bawansa. Alal misali, Yesu ya ce: “Ba ana sayar da ɗan tsuntsu guda biyu kobo ɗaya ba? To, ba ɗayansu wanda zai fāɗi a ƙasa ba tare da sanin Ubanku ba. Ai, ko gashin kanku ma an ƙirga su. Saboda haka, kada ku ji tsoro. Ai, kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai.” (Matiyu 10:29-31) Ka yi la’akari da yadda waɗannan kalmomi suka kasance ga masu sauraron Yesu a ƙarni na farko.

Gwara tana ba jaririnta abinci.

“Ai, kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai”

5 Za mu yi mamaki, me ya sa wani zai sayi gwarare. To, a zamanin Yesu, gwarare su ne tsuntsaye mafi araha da ake sayarwa domin abinci. Ka lura cewa da kwabo guda marar amfani, mai saye zai samu gwarare guda biyu. Amma Yesu daga baya ya ce idan mutum yana shirye ya ɓad da kwabo biyu, zai samu, ba gwarare huɗu ba, amma biyar. Gyara da aka ƙara kamar dai ba ta da tamani ko kaɗan. Wataƙila waɗannan halittu ba su da amfani a idanun mutane, amma yaya Mahalicci yake ɗaukansu? Yesu ya ce: “Allah bai manta da ko ɗayansu ba [har wadda aka ba da ita gyara].” (Luka 12:6, 7) A yanzu za mu fara fahimtar abin da Yesu yake nufi. Idan Jehobah ya ɗauki irin wannan gwara da tamani, yaya yawan tamani da yake ɗaukan mutum da shi! Kamar yadda Yesu ya yi bayani, Jehobah ya san kome da kome game da mu. Gashin kanmu ma a ƙirge suke!

6. Me ya sa muka tabbata cewa Yesu ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce gashin kanmu a ƙirge suke?

6 Gashinmu a ƙirge suke? Wasu za su yi tsammanin cewa a nan Yesu bai yi gaskiya ba. Amma, ka yi tunani game da tashin matattu. Dole ne Jehobah ya san mu sosai domin ya sake halittarmu! Yana ɗaukanmu da tamani ƙwarai shi ya sa zai tuna kome game da mu, har da abin da muka gadā daga iyaye da abin da ke ƙwaƙwalwarmu da fahiminmu.a Ƙirga gashinmu—wanda matsakaicin kai yana ɗauke da gashi ƙwaya 100,000—zai kasance abu mai sauƙi ne idan aka gwada da wannan.

Mene ne Jehobah Ya Gani a Cikinmu?

7, 8. (a) Waɗanne halaye Jehobah yake farin cikin samu sa’ad da ya bincike zukatan ’yan Adam? (b) Waɗanne ayyuka ne da muke yi Jehobah yake ɗauka da tamani?

7 Na biyu, Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa Jehobah yana ɗaukan bayinsa da tamani. Wato, yana farin ciki domin halayensu masu kyau da kuma ƙoƙari da suke yi. Sarki Dauda ya gaya wa ɗansa Sulemanu: “Yahweh yana bincike kowace zuciya kuma yana gane niyyar kowace zuciya.” (1 Tarihi 28:9) Yayin da Allah yake bincike biliyoyin zukata na ’yan Adam a wannan duniya ta fin ƙarfi, da ƙiyayya, lalle dole ne ya yi farin ciki sa’ad da ya samu zuciya da take ƙaunar salama, gaskiya, da kuma adalci! Mene ne yake faruwa sa’ad da Allah ya samu zuciya da take cike da ƙaunarsa, da take neman ta san shi kuma ta gaya wa wasu game da wannan sanin? Jehobah ya gaya mana cewa yana lura da waɗanda suke gaya wa wasu game da shi. Yana ma da “littafin tunawa” domin dukan “waɗanda suke tsoron Yahweh, suna kuma yin tunanin sunansa.” (Malakai 3:16) Irin waɗannan halaye suna da tamani a gare shi.

8 Waɗanne nagargarun ayyuka ne Jehobah yake ɗauka da tamani? Hakika ƙoƙarinmu mu yi koyi da Ɗansa, Yesu Kristi. (1 Bitrus 2:21) Wani aiki guda mai muhimmanci da Allah yake ɗauka da tamani shi ne yaɗa bishara ta Mulkinsa. Mun karanta a Romawa 10:15: “Ina misalin ban sha’awar masu kawo labari mai daɗi!” Ba za mu yi tunanin ƙafafunmu suna da ban shaꞌawa ba, ko kuma kyawawa. Amma a nan suna wakiltan ƙoƙarce-ƙoƙarcen da bayin Jehobah suke yi wajen wa’azin bishara. Dukan irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce suna da tamani a idanunsa.—Matiyu 24:14; 28:19, 20.

9, 10. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana ɗaukan jimirinmu a lokacin wahala dabam dabam da tamani? (b) Yaya ne Jehobah ba ya ɗaukan bayinsa masu aminci?

9 Jehobah yana ɗaukar jimirinmu da tamani. (Matiyu 24:13) Ka tuna, Shaiɗan yana so ka ƙi Jehobah. Kowacce rana da ka kasance da aminci ga Jehobah rana ce da ka taimaka wajen mai da amsa ga zolayar Shaiɗan. (Karin Magana 27:11) Wani lokaci jimiri ba abu ba ne mai sauƙi. Matsalolin rashin lafiya, rashin kuɗi, baƙin ciki, da wasu tangarɗa za su iya sa kowacce rana ta kasance gwaji. Rashin biyan muradi zai iya kasancewa abin sa kasala. (Karin Magana 13:12) Jimiri daga dukan waɗannan ƙalubale yana sa ya ƙara tamani ga Jehobah. Abin da ya sa ke nan Sarki Dauda ya roƙi Jehobah ya tara hawayensa cikin ‘gorarsa,’ ya daɗa da tabbaci cewa: “Ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?” (Zabura 56:8) Hakika, Jehobah yana ɗaukan dukan hawaye da kuma wahalar da muka jimre wa sa’ad da muke riƙe amincinmu da tamani kuma yana tunawa da su. Irin wannan hawaye da wahala su ma suna da tamani a idanunsa.

Jehobah yana ɗaukan jimirinmu a lokacin gwaji da tamani

10 Duk da haka, zuciya da take hukunta kanta za ta iya ƙin wannan tabbacin na tamaninmu a idanun Allah. Za ta nace tana raɗawa: ‘Amma da akwai wasu da yawa da suka kasance abin koyi fiye da ni. Lalle Jehobah ba zai ji daɗi ba idan ya gwada ni da su!’ Jehobah ba ya gwada mutane da juna; ko kuma cewa marar la’akari ne mai tsanantawa a tunaninsa. (Galatiyawa 6:4) Yana binciken zukatanmu sosai, yana ɗaukan nagarta—ko kaɗan ce da tamani.

Jehobah Yana Tace Nagari Daga Mugu

11. Mene ne za mu koya game da Jehobah daga yadda ya bi da batun Abijah?

11 Na uku, sa’ad da Jehobah yake bincike mu, yana tace mu a hankali, yana neman abin da yake da kyau. Alal misali, sa’ad da Jehobah ya ba da umurni cewa a halaka dukan daular Sarki Jeroboam mai ridda, ya ba da umurni cewa a yi wa Abijah, ɗaya daga cikin ’ya’yan sarkin kyakkyawar jana’iza. Me ya sa? ‘Yahweh Allahn Isra’ila ya sami ɗan abu mai kyau.’ (1 Sarakuna 14:1, 10-13) Wato, Jehobah ya tace zuciyar saurayin kuma ya samu “nufin kirki” a wurin. Ko yaya ƙanƙantar wannan kirkin da aka gani, Jehobah ya ga ya dace a rubuta a Kalmarsa. Har ya ba shi lada, ya nuna jinƙai yadda ya dace ga ɗan wannan iyali mai ridda.

12, 13. (a) Ta yaya batun Jehoshaphat ya nuna cewa Jehobah yana neman kirki ne a cikinmu har ma a lokacin da muka yi zunubi? (b) Game da ayyukanmu masu kyau da halaye, ta yaya Jehobah yake nuna shi Uba ne mai ƙauna sosai?

12 Za a iya ganin misali musamman ma dangane da Sarki Jehoshaphat. Sa’ad da sarkin ya yi wauta, annabin Jehobah ya gaya masa: “Da yake ka yi haka, fushin Yahweh yana a kanka.” Lalle wannan batun natsuwa ne! Ba a nan saƙon Jehobah ya ƙare ba. Ya ci gaba: “Duk da haka, an sami wani abu mai kyau a cikinka.” (2 Tarihi 19:1-3) Nagarin fushi na Jehobah bai rufe masa ido ba daga abin kirki na Jehoshaphat. Lalle ba kamar mutane ba ne ajizai! Sa’ad da muka yi fushi da wasu, sai mu rufe idanunmu daga abin kirki da suke yi. Kuma sa’ad da muka yi zunubi, kasawa, kunya da kuma laifi da muke ji sai su rufe mana ido daga abin kirki da muke da shi. Ka tuna cewa, idan muka tuba daga zunubanmu muka yi ƙoƙari kada mu sake yinsu, Jehobah zai gafarta mana.

13 Yayin da Jehobah yake bincika zuciyarka, yana zubar da zunubi kamar yadda mai neman zinariya yake kawar da duwatsu marasa amfani. To, halayenka da ayyukanka na kirki fa? I, waɗannan ai sune “abin nema” yana ajiye su! Ka taɓa lura da yadda wasu iyaye masu ƙauna suke ajiye zane-zane da ’ya’yansu suka yi a makaranta, wani lokaci na shekaru da yawa bayan yaran sun manta da su? Jehobah Uba ne mai ƙaunar ’ya’yansa sosai. Muddin mun ci gaba da aminci gare shi, ba zai taɓa manta ba da nagargarun ayyuka da halayenmu. A hakikanin gaskiya, za a yi tsammanin zai manta da waɗannan rashin adalci ne, shi ba mai rashin adalci ba. (Ibraniyawa 6:10) Yana kuma tace mu a wata hanya.

14, 15. (a) Me ya sa ajizancinmu ba zai taɓa rufe wa Jehobah idanu ba ga nagarta da ke a gare mu? Ka ba da misali. (b) Mene ne Jehobah zai yi da abubuwa masu kyau da ya samu a gare mu, kuma yaya yake ɗaukan mutanensa masu aminci?

14 Jehobah yana hangar gaba da ajizancinmu kuma ya ga abin kirki da za mu iya. Alal misali: Mutane da suke son aikin zane za su yi ƙoƙari sosai su gyara zane da ya lalace. Ga misali, a Hukumar Hotuna na Ƙasar London, a Ingila, lokacin da wani mutum da ƙaramar bindiga ya lalata zanen Leonardo da Vinci zanen da ya kai dalla miliyan 30, babu wanda ya ba da shawarar cewa tun da zanen yanzu ba shi da kyau a jefar da shi. Nan da nan aka fara aikin gyara wannan kyakkyawan zane mai kusan shekara 500. Me ya sa? Domin yana da kyau a idanun masu son zane. Ba ka fi zane na alli da kuma gawayi ba? A idanun Allah hakika ka fi—ko yaya ajizanci da ka gada ya lalata ka. (Zabura 72:12-14) Jehobah Allah, ƙwararren Mahalicci na iyalin ɗan Adam, zai yi abin da ya dace ya mai da kamilcin waɗanda suka amsa ƙaunarsa.—Ayyukan Manzanni 3:21; Romawa 8:20-22.

15 Hakika, Jehobah yana ganin nagarta da muke da shi da ba za mu gani ga kanmu ba. Kuma kamar yadda muke bauta masa, zai sa wannan nagarta ta yi girma har sai mun kamilta. Ko yaya duniyar Shaiɗan ta bi da mu, Jehobah yana ɗaukan bayinsa a matsayin arziki.—Haggai 2:7.

Jehobah Yana Nuna Ƙaunarsa Sosai

16. Mene ne tabbaci mafi girma na ƙaunar Jehobah a gare mu, kuma ta yaya muka sani cewa wannan kyauta dominmu ne?

16 Na huɗu, Jehobah yana abubuwa da yawa ya nuna ƙaunarsa a gare mu. Hakika, hadayar fansa ta Kristi ita ce amsa mafi kyau ga ƙaryar Shaiɗan cewa ba mu da amfani ko kuma ba a ƙaunarmu. Kada mu manta cewa mutuwar azaba da Yesu ya sha a kan gungume da kuma azaba mai yawa da Jehobah ya jimre wajen kallon Ɗan da yake ƙauna ya mutu cewa tabbaci ne na ƙaunarsu a gare mu. Abin baƙin ciki, yana yi wa mutane da yawa wuya su gaskata cewa wannan kyautar an yi ta dominsu ne. Suna ganin ba su cancanta ba. Ka tuna cewa manzo Bulus ya kasance mai tsananta wa mabiyan Kristi. Duk da haka, ya rubuta: “Ɗan Allah, . . . ya ƙaunace ni, ya bada kansa kuma domina.”—Galatiyawa 1:13; 2:20.

17. Ta wace hanya ce Jehobah yake jawo mu gare sa kuma ga Ɗansa?

17 Jehobah yana tabbatar da ƙaunarsa wajen taimakonmu mu ci amfanin hadayar Kristi. Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Hakika, Jehobah da kansa yake jawo mu wurin Ɗansa da kuma begen rai madawwami. Ta yaya? Ta wajen aikin wa’azi, da yake zuwa wajenmu, da kuma ta wajen ruhu mai tsarki, da Jehobah yake amfani da shi ya taimake mu fahimtar da kuma yin amfani da gaskiya ta ruhaniya duk da kasawarmu da kuma ajizancinmu. Saboda haka, Jehobah zai iya cewa game da mu kamar yadda yake game da Isra’ila: “Hakika, na ƙaunace ki da ƙauna marar ƙārewa, na jawo ki wurina da ƙauna marar canjawa.”—Irmiya 31:3.

18, 19. (a) Wace hanya mafi kusa ne Jehobah yake nuna ƙaunarsa a gare mu, kuma mene ne ya nuna cewa yana damuwa da waɗannan? (b) Ta yaya Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa Jehobah mai sauraro ne da juyayi?

18 Wataƙila ta wajen gata ta addu’a ce muke fahimtar ƙauna ta Jehobah a hanya mafi zurfi. Littafi Mai Tsarki ya gayyaci kowannenmu ya yi “addu’a babu fasawa” ga Allah. (1 Tasalonikawa 5:17) Yana saurara. Har an kira shi “mai-jin addu’a.” (Zabura 65:2) Bai ba da wannan matsayin ga kowa ba, har Ɗansa ma. Ka yi tunani: Mahaliccin dukan halitta ya aririce mu mu zo gare shi cikin addu’a, da sakakken jiki. Wane irin mai sauraro ne shi? Marar tausayi, marar juyayi, ko kuma marar damuwa ne? A’a.

19 Jehobah yana da juyayi. Mene ne juyayi? Wani Kirista tsoho mai aminci ya ce: “Juyayi azabarka ce a zuciya ta.” Azabarmu da gaske tana shafar Jehobah? Mun karanta game da wahalar mutanensa Isra’ilawa: “Cikin dukan ƙuncinsu ya ƙuntata.” (Ishaya 63:9) Ba kawai Jehobah yana ganin masifarsu ba; ya yi juyayin mutanen. Zurfin yadda ya ji, kalmar Jehobah ga bayinsa sun kwatanta: “Duk wanda ya taɓa mutanena ya taɓa ƙwayar idona ne.”b (Zakariya 2:8) Lalle wannan zai yi zafi! Hakika, Jehobah yana juyayinmu. Sa’ad da muka wahala, shi ma ya wahala.

20. Wane irin tunani ne marar kyau da ya kamata mu guje shi, idan za mu yi biyayya ga gargaɗin da yake Romawa 12:3?

20 Babu wani Kirista mai hankali da zai yi amfani da wannan tabbacin na ƙaunar Allah da kuma daraja ga bayinsa ya kasance dalilin fahariya da kuma kumbura. Manzo Bulus ya rubuta: “Bisa ga alherin nan da aka yi mini, ina yi wa kowane ɗayanku gargaɗi cewa kada kowa ya ɗauki kansa da girma fiye da yadda ya kamata ya yi. A maimakon haka kowa ya mai da hankali game da yadda yake ganin kansa, wato ya dinga ganin kansa daidai gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.” (Romawa 12:3) Wata fassarar a nan ta ce: “Zan gaya wa kowannenku kada ya kimanta kansa fiye da matsayinsa, amma ya kimanta kansa daidai wa daida.” (A Translation in the Language of the People, na Charles B. Williams) Saboda haka yayin da muke bambaro cikin ƙaunar Ubanmu na samaniya, bari mu kasance da azanci mai kyau kuma mu tuna cewa ba lada ba ce kuma ba mu cancanci ƙaunar Allah ba.—Luka 17:10.

21. Waɗanne ƙaryace-ƙaryace na Shaiɗan dole mu ci gaba da ƙi, kuma wace gaskiya ce ta Allah ya kamata mu ci gaba da tabbatar wa zukatanmu?

21 Bari dukanmu mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu ƙi ƙaryar Shaiɗan, haɗe da ƙaryar da wai ba mu da amfani ko kuma cewa ba mu dace da ƙauna ba. Idan abin da ka fuskanta a rayuwa ya sa ka ɗauki kanka cewa kai matsala ne ga ƙauna mai zurfi na Allah, ko kuma ayyukanka nagargaru kamar ba su kai abin da idanunsa za su gani ba, ko kuma cewa zunubanka sun yi yawa ainun har da ya fi ƙarfin mutuwar Ɗansa mai tamani ya gafarta, to, an koya maka ƙarya. Ka ƙi waɗannan ƙaryace-ƙaryace da dukan zuciyarka! Bari mu cika da tabbatar wa zuciyarmu da gaskiyar da aka furta a kalmomin Bulus da aka hure: “Na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko halin yanzu ko na nan gaba, ko ikoki iri-iri, ko tsawo ko zurfi, ko wani abu dabam a dukan halitta, duk ba su isa ba sam su raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.”—Romawa 8:38, 39.

a Littafi Mai Tsarki a kai a kai ya danganta begen tashin matattu da tunanin Jehobah. Mutum mai aminci Ayuba ya gaya wa Jehobah: “Ya Allah, da ma ka . . . sa ranar da za ka tuna da ni!” (Ayuba 14:13) Yesu ya yi magana game da “waɗanda suke cikin kaburbura na [tuni].” Hakan daidai ne domin Jehobah yana tuna matacce da yake so ya ta da shi.—Yohanna 5:28, 29.

b Wasu fassara a nan suna nuna cewa wanda yake taɓa mutanen Allah yana taɓa ƙwayar idanunsa ne ko kuma na Isra’ila, ba na Allah ba. Wasu marubuta ne suke saka wannan kuskuren suna ganin wannan matanin ba shi da amfani saboda haka suka yi masa ɗan gyara. Wannan ƙoƙarinsu ya ɓoye zurfin juyayin Jehobah.

Tambayoyi don Bimbini

  • Zabura 139:1-24 Ta yaya kalmomin Sarki Dauda da aka hure suka nuna cewa Jehobah yana damuwa da kowannenmu?

  • Ishaya 43:3, 4, 10-13 Yaya Jehobah yake ji game da waɗanda suke yi masa Shaida, kuma yaya wannan ya bayyana cikin ayyuka?

  • Romawa 5:6-8 Me ya sa za mu tabbata cewa yanayinmu na zunubi ba ya hana ƙaunar Jehobah ta isa wurinmu kuma ta amfane mu?

  • Yahuda 17-25 Ta yaya za mu kasance cikin ƙaunar Allah, kuma waɗanne abubuwa ne suke hamayya da wannan?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba