Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 8/1 pp. 19-23
  • “Ku Tsare Kanku Daga Dukan Ƙyashi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Tsare Kanku Daga Dukan Ƙyashi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Roƙon da Bai Dace Ba
  • Ka Guji Yin Ƙyashi
  • Yawan Dukiya
  • Rayuwa Mai Kyau a Nan Gaba
  • Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yaya Ƙarfin Dogararka Ga Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Bidi Mulkin Allah, Ba Abin Duniya Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 8/1 pp. 19-23

“Ku Tsare Kanku Daga Dukan Ƙyashi”

“Ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.”—LUKA 12:15.

1, 2. (a) Menene ka lura game da abubuwa da mutane suke so kuma suke biɗa a yau? (b) Ta yaya irin waɗannan halayen za su shafe mu?

KUƊI, dukiya, matsayi, da aikin da ake samun kuɗi sosai, da kuma iyali suna cikin abubuwa da yawancin mutane suke ganin cewa za sa su yi nasara ko kuma su sami kwanciyar rai a nan gaba. A bayyane yake cewa a ƙasashe masu arziki da marasa arziki, mutane da yawa suna mai da hankali ne ga biɗan abubuwa na duniya da yin nasara. A wani ɓangare kuma, sha’awar da suke yi wa abubuwa na ruhaniya sai ƙara raguwa take a kullum.

2 Wannan shi ne ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta. Ya ce: “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi . . . ma-fiya son annishuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta.” (2 Timothawus 3:1-5) Da yake suna zaune ne a cikin irin waɗannan mutanen a kullum, Kiristoci na gaskiya suna cikin matsi su bi irin wannan ra’ayi da salon rayuwa. Menene zai taimake mu mu yi tsayayya da ƙoƙarin da duniyar nan take yi don “ta mulmula mu yadda take so”?—Romawa 12:2, The New Testament in Modern English na J. B. Phillips.

3. Wane gargaɗi ne da Yesu ya ba da za mu bincika yanzu?

3 Tun da yake Yesu Kristi ne “shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta,” ya koya mana darussa masu muhimmanci game da wannan. (Ibraniyawa 12:2) Akwai lokacin da Yesu yake magana da jama’a a kan wasu al’amura game da bauta ta gaskiya, wani mutum ya katse masa magana ta wajen yin wani roƙo: “Malam, ka ce ma ɗan’uwana shi raba gadō da ni.” Yesu ya yi wa mutumin da duka mutanen da suke sauraransa gargaɗi mai muhimmanci. Ya yi musu gargaɗi sosai a kan ƙyashi kuma ya nanata wannan gargaɗin ta wajen yin wani kwatanci mai sa mutum tunani. Yana da kyau mu mai da hankali sosai ga abin da Yesu ya faɗa a wannan lokacin kuma mu ga yadda za mu amfana ta wajen yin amfani da shi a rayuwarmu.—Luka 12:13-21.

Roƙon da Bai Dace Ba

4. Me ya sa yadda mutumin ya katse wa Yesu magana bai dace ba?

4 Kafin mutumin ya katse masa magana, Yesu yana wa almajiransa da wasu magana ne a kan mai da hankali da yin riya, game da kasancewa da gaba gaɗin shaida Ɗan Allah, da kuma samun taimako daga ruhu mai tsarki. (Luka 12:1-12) Hakika, waɗannan darussa ne masu muhimmanci da almajiran suke bukatar su tuna. Yana cikin ba da wannan jawabin ne mai sa tunani, mutumin ya katse maganar da Yesu yake yi kuma ya roƙe shi ya magance jayayyar da iyalinsa ke yi a kan abin duniya. Duk da haka, akwai darassi mai muhimmanci da za mu iya koya daga abin da ya faru.

5. Menene roƙon da mutumin ya yi ya bayyana game da shi?

5 An rubuta cewa “ana sanin halin mutum a yawancin lokaci ta inda yake mai da hankalinsa sa’ad da yake sauraron gargaɗi na addini.” Yayin da Yesu yake magana game da al’amura na ruhaniya masu muhimmanci, wataƙila mutumin yana tunani ne game da abin da zai iya yi don ya samu kuɗi. Ba a faɗa ba ko yana da dalili mai kyau na yin ƙara game da gadon. Wataƙila yana ƙoƙarin ya yi amfani da ikon Yesu da kuma sunansa ne domin Yesu mai shari’a ne mai kyau a kan harkokin ’yan adam. (Ishaya 11:3, 4; Matta 22:16) Ko menene dalilinsa, tambayarsa ta nuna cewa yana da matsala, wato, rashin daraja abubuwa na ruhaniya. Wannan ba dalili mai kyau ba ne na bincika kanmu? Alal misali, a taron Kirista, yana da sauƙi mu dinga tunanin wasu abubuwa ko kuma mu riƙa tunanin abin da za mu yi a nan gaba. Maimakon haka, ya kamata mu saurari abin da ake faɗa kuma mu yi tunanin hanyoyi da za mu iya yin amfani da abin da muka ji don mu kyautata dangantakarmu da Ubanmu na samaniya, Jehobah Allah, da ’yan’uwanmu Kiristoci.—Zabura 22:22; Markus 4:24.

6. Me ya sa Yesu ya ƙi yin abin da mutumin ya roƙa?

6 Ko da menene ya motsa mutumin ya yi wannan roƙon, Yesu ya ƙi yin abin da mutumin ya roƙa. Maimakon haka, Yesu ya ce masa: “Mutum, wanne ya sanya ni alƙali ko mai-raba musu a bisanku?” (Luka 12:14) Sa’ad da ya faɗi haka, Yesu yana nuni ne ga wani abin da sananne ne ga mutanen, domin bisa Dokar Musa, ana naɗa alƙalai cikin birane su yi shari’a a kan irin waɗannan batutuwa. (Kubawar Shari’a 16:18-20; 21:15-17; Ruth 4:1, 2) A wani ɓangare kuma, Yesu ya damu ne da abubuwan da suka fi muhimmanci, wato, ya ba da shaida game da gaskiyar Mulki kuma ya koya wa mutane nufin Allah. (Yohanna 18:37) Maimakon mu bar abin duniya ta janye mana hankali, muna bin misalin Yesu ta wajen yin amfani da lokacinmu da kuzari mu yi wa’azin bishara kuma mu “almajirtadda dukan al’ummai.”—Matta 24:14; 28:19.

Ka Guji Yin Ƙyashi

7. Wane bincike ne Yesu ya yi?

7 Da yake yana iya sanin abin da ke cikin zuciya, Yesu ya sani cewa roƙon da wannan mutum ya yi ya ƙunshi wani abu mai tsanani shi ya sa ya roƙi Yesu ya sa hannu cikin al’amurar iyalinsu. Maimakon ya ƙi sa baki a roƙon, Yesu ya faɗi ainihin matsalar kuma ya ce: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.”—Luka 12:15.

8. Menene ƙyashi, kuma menene zai sa mutum ya yi?

8 “Ƙyashi” ba kawai sha’awa ba ce ta samun kuɗi ko wasu abubuwa, waɗanda suke da amfaninsu da aikinsu. “Mugun son arziki ne ko dukiya, ko kuwa son dukiyoyin wani” in ji wani ƙamus. Ya ƙunshi rashin gamsuwa da abubuwa, haɗamar samun abubuwa, wataƙila kayan wasu, don kawai a ce mutumin yana da su, ba tare da tunanin ko yana bukatar abin ba ko kuma yadda zai shafi wasu. Mutum mai ƙyashi yana barin abin da yake so ya sha kan tunaninsa da ayyukansa har abin ya zama allansa. Ka tuna cewa manzo Bulus ya kamanta mutum mai haɗama da mai bauta wa gunki, wanda ba zai gaji Mulkin Allah ba.—Afisawa 5:5; Kolossiyawa 3:5.

9. A waɗanne hanyoyi ne za a iya nuna ƙyashi? Ka ba da wasu misalai.

9 Shi ya sa Yesu ya yi gargaɗi a kan “dukan ƙyashi.” Ana iya yin ƙyashi a hanyoyi dabam dabam. Na ƙarshe cikin Dokoki Goma ta ambata wasu cikinsu, tana cewa: “Ba za ka yi ƙyashin gidan makusancinka ba, ba za ka yi ƙyashin matar makusancinka ba, ko bawansa, ko baiwassa, ko sansa, ko jākinsa, ko kowane abin da ke na makusancinka.” (Fitowa 20:17) Littafi Mai Tsarki yana cike da misalan waɗanda suka faɗa ciki mugun zunubi domin ƙyashi. Shaiɗan ne na farko da ya yi ƙyashin abin wani, wato ɗaukaka, daraja da iko da Jehobah kaɗai ne yake da su. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Hauwa’u ta yi ƙyashin samun ’yancin kai, kuma da yake an ruɗe ta a kan wannan batun ne ya sa ’yan adam suka soma zunubi da mutuwa. (Farawa 3:4-7) Aljanu, mala’iku ne da ba su gamsu da “riƙe matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama” don abin da ba nasu ba. (Yahuda 6; Farawa 6:2) Ka tuna da Balaam, Achan, Gehazi, da Yahuda Iskariyoti. Maimakon su yi haƙuri da abin da suke da shi a rayuwa, sun ƙyale sha’awar abin duniya ta sa su yi rashin matsayinsu, kuma hakan ya jawo musu halaka.

10. Ta yaya ya kamata ‘mu lura,’ kamar yadda Yesu ya ba da gargaɗi?

10 Ya dace da Yesu ya soma kashedi game da ƙyashi da waɗannan kalmomin “ku yi lura”! Me ya sa? Domin yana da sauƙi mutane su ga cewa wani mai haɗama ne ko mai ƙyashi ne amma da kyar ne su yarda cewa su ma suna yin hakan. Duk da haka, manzo Bulus ya nuna cewa “son kuɗi asalin kowace irin mugunta ne.” (1 Timothawus 6:9, 10) Almajiri Yaƙub ya bayyana cewa sa’ad da mugun sha’awa, “ta habala, ta kan haifi zunubi.” (Yaƙub 1:15) Daidai da gargaɗin Yesu, ya kamata ‘mu lura’ kada mu dinga kallon wasu da idon cewa su masu ƙyashi ne, amma mu bincika kanmu mu ga inda muka sa zuciyarmu, don mu ‘tsare kanmu daga dukan ƙyashi.’

Yawan Dukiya

11, 12. (a) Wane gargaɗi ne Yesu ya yi game da ƙyashi? (b) Me ya sa muke bukatar mu saurari gargaɗin da Yesu ya yi?

11 Da akwai wani dalilin da ya sa za mu mai da hankali da ƙyashi. Ka lura da abin da Yesu ya faɗa a gaba: “Ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luka 12:15) Ya kamata mu yi tunanin wannan sosai a zamaninmu na son abin duniya, inda mutane suke ganin cewa za ka yi farin ciki da nasara idan ka yi arziki. Da waɗannan kalmomi, Yesu ya nuna cewa ba a samun rayuwa mai ma’ana da gamsarwa ta yawan dukiya.

12 Amma wasu ba za su yarda ba. Suna iya tunanin cewa dukiya na sa a ji daɗin rayuwa kuma shi ya sa yake da kyau a nemi abin duniya. Shi ya sa suke ba da kansu ga biɗan ayyukan da zai sa su samu dukan abubuwan da suke so har da kayayyakin daki masu amfani da lantarki. Suna tunanin cewa wannan zai sa su more rayuwa. Ta yin irin wannan tunanin, ba su fahimci abin da Yesu yake nufi ba.

13. Wane ra’ayi ne ya dace mu kasance da shi game da rayuwa da dukiya?

13 Maimakon ya mai da hankali a kan ko ya dace ko bai dace ba a samu dukiya mai yawa, Yesu ya nanata cewa ba ‘yawan dukiya’ ba, wato, ba yawan abubuwan da mutum yake da su ba ne za su tsawonta ransa. Saboda haka, dukanmu mun sani cewa ba a bukatar abubuwa masu yawa don mu kasance da rai, ko kuma mu kiyaye ranmu. Abubuwan da kawai muke bukata su ne abinci, kayan sakawa, da wurin kwanciya. Mawadata suna da waɗannan abubuwan da yawa, kuma matalauta suna fama su sami abin da suke bukata. Amma, mawadata da matalauta suna zama ɗaya a lokacin da suka mutu, domin duk abin da suke da shi a wannan lokacin ya ƙare. (Mai-Wa’azi 9:5, 6) Saboda haka, idan rayuwa za ta kasance da ma’ana bai kamata ta dangana a kan abubuwan da mutum zai iya samu ko kuma abubuwan da yake da su ba. Hakan zai zama gaskiya sa’ad da muka bincika irin rayuwar da Yesu yake maganar ta.

14. Menene za mu iya koya daga kalmar nan ‘rai’ da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

14 Sa’ad da Yesu ya ce, “Ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba,” kalmar nan ‘rai’ da aka yi amfani da ita a Lingilar Luka (a Helenanci zo·eʹ) ba ta nufin salon rayuwa, amma cikakkiyar rayuwa.a Yesu yana cewa ko mu masu arziki ne ko matalauta, ko muna da kayan alatu ko kuma da kyar muke samun na ci, ba mu da cikakken ikon tsawonta ranmu ko kuma sanin ko za mu kasance da rai gobe. Yesu ya ce a Huɗubarsa Bisa Dutse: “Wanene a cikinku, don damuwa tasa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwa tasa?” (Matta 6:27) Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa Jehobah ne kaɗai “maɓulɓular rai” kuma shi kaɗai ne zai iya ba amintattu “hakikanin rai” ko kuma rai na “har abada,” a sama ko kuma a duniya.—Zabura 36:9; 1 Timothawus 6:12, 19.

15. Me ya sa mutane da yawa suke dogara ga abin duniya?

15 Kalmomin Yesu sun nuna cewa yana da sauƙi mutane su kasance da ra’ayin rayuwa da bai dace ba. Dukan ’yan adam ajizai ne duk da mawadata da matalauta, kuma abu ɗaya ne ke samunsu. Musa na dā ya ce: “Kwanukan shekarunmu shekara hauya uku ce da goma, idan kuwa domin ƙarfi sun kai hauya huɗu; fahariyarsu wahala ce da baƙin ciki: gama da sauri ya kan wuce, mu kan tashi.” (Zabura 90:10; Ayuba 14:1, 2; 1 Bitrus 1:24) Domin wannan, mutanen da ba su ƙulla dangantaka mai kyau da Allah ba sau da yawa suna amincewa da ra’ayin “bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu” da manzo Bulus ya yi maganarsa. (1 Korinthiyawa 15:32) Wasu, da yake sun san cewa rayuwa tana saurin wucewa suna ƙoƙari su sami kwanciyar rai da tallafawa na abin duniya. Wataƙila suna jin cewa samun abin duniya na zahiri masu yawa zai sa su sami kwanciyar rai. Da haka, suna aiki tuƙuru don su tara arziki da dukiya, suna kuskuren cewa irin waɗannan abubuwa ne za su kawo musu kwanciyar rai da farin ciki.—Zabura 49:6, 11, 12.

Rayuwa Mai Kyau a Nan Gaba

16. Rayuwa mafi ma’ana ta dangana ne a kan menene?

16 Wataƙila gaskiya ne cewa idan muna da abinci mai yawa, tufafi, da wurin kwanciya, da wasu kayan alatu ko kuma zuwa asibiti mai kyau za su iya sa mu ji daɗin rayuwa kuma su daɗa wasu shekaru ga rayuwarmu. Amma, ainihin irin wannan rayuwar ce mafi ma’ana kuma mai ba da kwanciyar hankali kuwa? Ba a gwada rayuwa mafi ma’ana ta shekarun mutum ko kuma ta yawan abin duniya da mutum yake da shi ko kuma yake morewa. Manzo Bulus ya nuna haɗarin sa rai a irin waɗannan abubuwa. Ya rubuta wa Timothawus: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu.”—1 Timothawus 6:17.

17, 18. (a) Waɗanne misalai na musamman game da dukiya ne ya dace mu yi koyi da su? (b) Waɗanne ƙarin kalmomin Yesu ne za mu bincika a talifi na gaba?

17 Ba shi da kyau mutum ya sa rai a dukiya domin ba ta “tsayawa.” Ayuba uban iyali mai arziki ne sosai, amma sa’ad da bala’i ta faɗa masa, dukiyarsa ba ta taimake shi ba; duk ɓacewa suka yi farat ɗaya. Dangantakarsa ce da Allah ta kiyaye shi a lokacin gwaji da jarabobbin da suka faɗa masa. (Ayuba 1:1, 3, 20-22) Ibrahim bai ƙyale yawan dukiyarsa ta hana shi karɓan aiki mai wuya daga Jehobah ba, kuma an albarkace shi da zama “uba na jama’ar al’ummai.” (Farawa 12:1, 4; 17:4-6) Ya kamata mu yi koyi da waɗannan da wasu misalai. Ko mu manya ne ko yara, muna bukatar mu bincika kanmu mu ga abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu da kuma inda muka sa ranmu.—Afisawa 5:10; Filibbiyawa 1:10.

18 Kalmomi kalilan da Yesu ya faɗa a kan ƙyashi da kuma ra’ayin da ya dace game da rayuwa suna da ma’ana kuma suna taimakawa. Amma, Yesu yana da ƙarin gargaɗi da zai yi, kuma ya ba da almara ko kwatanci mai sa tunani game da wani mawadaci wawa. Ta yaya wannan kwatanci ya dace da zamaninmu a yau, kuma menene za mu iya koya daga ciki? Talifi na gaba zai ba da amsoshin.

[Hasiya]

a Wata kalmar Helenanci da aka fassara ‘rai’ ita ce biʹ·os. In ji ƙamus na Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words, biʹ·os tana nufin “tsawon rayuwa,” “yadda ake rayuwa,” da kuma “abin biyan bukatar rayuwa.”

Mecece Amsarka?

• Menene za mu iya koya daga yadda Yesu ya ƙi ya aikata bisa roƙon da wani mutum da ke cikin jama’a ya yi?

• Me ya sa za mu mai da hankali da yin ƙyashi, ta yaya za mu yi hakan?

• Me ya sa abin da mutum yake da shi ba zai iya tsawonta rayuwarsa ba?

• Menene zai sa rai ya kasance da daraja kuma a sami kwanciyar rai?

[Hoto a shafi na 21]

Me ya sa Yesu ya ƙi roƙon wani mutum?

[Hoto a shafi na 21]

Ƙyashi yana iya jawo mummunan sakamako

[Hotuna a shafi na 23]

Ta yaya Ibrahim ya nuna ra’ayin da ya dace game da dukiya?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba