Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 166
  • Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?
  • Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi game da son kudi?
  • Ta yaya za mu amfana daga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?
  • Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aiki da Kudi
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 166
Wani mutum yana mika hannu zai kwashi makudan kudi.

Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A’a. Littafi Mai Tsarki bai ce kudi mugun abu ba ne, kuma bai ce kudi ne ke jawo munana ayyuka ba. Furucin nan “kudi shi ne tushen mugunta” ba ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba ne. Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar shi ne cewa: “Kaunar kudi ita ce tushen kowace irin mugunta.”a​—1 Timoti 6:10.

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?

  • Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi game da son kudi?

  • Ta yaya za mu amfana daga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?

  • Ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da kudi

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?

Littafi Mai Tsarki ya amince cewa kudi yana da amfani. Idan ana yin amfani da kudi a hanyar da ta dace yana ma iya “tsare mutum.” (Mai-Wa’azi 7:12) Bugu da kari, Littafi Mai Tsarki ya yaba wa masu taimaka wa wasu, har da bayar da kyautar kudi.​—Karin Magana 11:25.

Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi cewa kada mu sa kudi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Ya ce: “Ku yi nesa da halin son kudi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi.” (Ibraniyawa 13:5) Darasin shi ne mu rika yin amfani da kudi yadda ya dace kuma mu guji neman arziki ruwa-a-jallo. A maimakon haka, mu gamsu da abin da muke da shi wato abinci da sutura da kuma wurin kwana.​—1 Timoti 6:8.

Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi game da son kudi?

Masu hadama ba za su sami rai na har abada. (Afisawa 5:5) Domin hadama kamar bauta wa gumaka ne ko bauta ta karya. (Kolosiyawa 3:5) Wani dalili kuma shi ne, masu hadama sukan ki bin ka’idodi masu kyau don su sami abin da suke sha’awa. Littafin Karin Magana 28:20 ya ce: “Mai neman samun arziki da sauri, ba zai kubuta daga hukunci ba.” Za su iya fada cikin jarraba na aikata laifuffuka kamar kwace, zamba, shari, sace mutum don fansa da kuma kisan kai.

Ko da son kudi bai sa mu kasance da halaye marasa kyau ba, yana iya jawo munanan sakamako. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma wadanda suke marmarin yin arziki sukan fādi cikin jarraba, cikin tarko na mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na banza.”​—1 Timoti 6:9.

Ta yaya za mu amfana daga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?

Idan muka ci gaba da yin abubuwan da Allah yake so kuma muka bi ka’idodinsa, hakan zai sa a rika daraja mu kuma Allah zai yi mana albarka da kuma goyi bayanmu. Allah ya yi wa wadanda suka faranta masa rai alkawari cewa: “Har abada ba zan bar ka ba, sam-sam ba zan yar da kai ba.” (Ibraniyawa 13:​5, 6) Ban da haka, ya tabbatar mana cewa “mai aminci zai cika da albarku.”​—Karin Magana 28:20.

Ayoyin Littafi Mai Tsarki da Suka Yi Magana Game da Kudi

Mai-Wa’azi 7:12: Kudi yakan “tsare mutum.”

Ma’ana: Idan aka yi amfani da shi da hikima, kudi yana da amfani domin zai iya tsare mutum.

Luka 12:15: “Ku lura fa, ku yi nesa da kowane irin kwadayi, don yawan kaya ba shi ne samun rai ba.”

Ma’ana: Kudi ba shi ne abu mafi muhimmancin a rayuwa ba, kuma ba zai sa mu sami rai na har abada ba.

1 Timoti 6:10: “Gama kaunar kudi ita ce tushen kowace irin mugunta. A cikin marmarin yin arziki da sauri, wadansu sun rabu da bangaskiyarsu har suka jawo wa kansu bakin ciki iri-iri masu zafi.”

Ma’ana: Kudi da kanta ba ta da laifi. Amma mutane da ke son kudi da kuma sa kudi ya fi muhimmanci a rayuwarsu, suna jawo wa kansu matsaloli kamar kashe aure da rashin lafiya domin yawan yin aiki.

Ibraniyawa 13:5: “Ku yi nesa da halin son kudi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi.”

Ma’ana: Maimakon mu rika neman kudi ruwa-a-jallo, zai fi dacewa mu gode wa Allah domin abin da muke da shi.

Matiyu 19:24: “Zai fi wa rakumi sauki ya bi ta ramin allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”

Ma’ana: Yesu ya gayyaci wani matashi mai arziki ya zama mabiyinsa. Mutumin ya ki domin ya fi mai da hankali ga dukiyarsa. Abin da ya sa Yesu ya yi gargadi nan ke nan. Mutumin da ya fi son kudi fiye da Allah, ba zai samu rai na har abada ba.

a Ana iya fassara wannan ayar haka: “Son kudi shi ne tushen mugayen ayyuka.”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba