Babi Na Goma Sha Ɗaya
‘Ka Ci Gaba da Biɗan Mulkin da Farko’
1. (a) Me ya sa Yesu ya aririce masu sauraronsa su biɗi Mulkin da farko? (b) Wace tambaya ce za mu yi wa kanmu?
SAMA da shekaru 1,900 cikin wani jawabi a Galili, Yesu ya aririce masu sauraronsa: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcin [Allah].” Amma me ya jawo irin gaggawar nan? Ba lokacin da Kristi zai karɓi ikon Mulki yana can gaba ƙarnuka da yawa masu zuwa ba? Haka, amma Mulki na Almasihu abin da Jehovah zai yi amfani da shi ne a kunita ikonsa na mallaka kuma ya cika babban nufinsa wa duniya. Duk wanda ya fahimci muhimmancin waɗannan abubuwa zai saka Mulkin da farko a rayuwarsa. Idan haka wannan yake a ƙarni na farko, lallai haka zai zama a yau ma, da an riga an ɗora Kristi a kan gadon sarauta! Saboda haka, tambayar ita ce, Rayuwata tana nuna cewa ina biɗan Mulkin Allah ne da farko?—Matta 6:33.
2. Menene galibin mutane suke biɗa da ƙwazo?
2 A yau, miliyoyin mutane a dukan duniya, hakika, suna biɗan Mulkin da farko. Suna nuna goyon bayansu ga Mulkin ta sa rayuwarsu a yin nufin Jehovah, da yake sun keɓe kansu gare shi. A wata sassa kuma, yawancin mutane suna biɗan abubuwa ne na yau da kullum. Mutane suna biɗan kuɗi da kuma dukiya da annashuwa da kuɗi ke kawowa. Ko kuma su saka dukan ƙoƙarinsu a ci gaba da burinsu. Hanyar rayuwarsu na nuna sun damu da kansu, abin duniya, da kuma annashuwa. Suna sa Allah a wuri na biyu, idan fa sun gaskata da shi ke nan.—Matta 6:31, 32.
3. (a) Waɗanne irin dukiya ne Yesu ya ƙarfafa almajiransa su biɗa, kuma me ya sa? (b) Me ya sa ba ma bukatar mu dame kanmu ainu game da abin duniya?
3 Amma, ga almajiransa, Yesu ya ba da wannan gargaɗi: “Kada ku ajiye wa kanku dukiya a duniya,” da yake babu wani cikinsu da zai kasance har abada. “Amma,” in ji shi, “ku ajiye wa kanku dukiya cikin sama” ta wajen bauta wa Jehovah. Yesu ya aririci mabiyansa su sa idonsu ya zama “sosai” ta wajen mai da hankali da sa ƙarfinsu a yin nufin Allah. Ya gaya musu: “Ba ku da iko ku bauta wa Allah da [arziki] ba.” Amma game da abubuwan biyar bukata fa—abinci, sitira, da kuma mafaka? “Kada ku yi alhini,” Yesu ya yi gargaɗi. Ya jawo hankalinsu wajen tsuntsaye—Allah yana ciyar da su. Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su koyi darasi daga furanni—Allah ne ke sitirar da su. Bayin Jehovah masu basira ba su fi waɗannan duka daraja ba ne? “Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa,” in ji Yesu, “waɗannan abu [bukatu] duka fa za a ƙara muku.” (Matta 6:19-34) Ayyukanka suna nuna ka gaskata da haka?
Kada Ka Yarda a Shaƙe Gaskiyar Mulki
4. Idan mutum ya damu ainu game da abin duniya, me zai iya zama sakamakon haka?
4 Daidai ne mutum ya damu domin samun isashen abin da zai biya bukatar kansa da na iyalinsa. Amma idan mutum na damuwa ainu game da abin duniya zai jawo bala’i. Ko idan yana da’awar ya gaskata da Mulkin, a zuciyarsa kuwa ya sa wasu abubuwa farko, zai shaƙe gaskiyar Mulkin. (Matta 13:18-22) Alal misali, a wani lokaci wani mawadaci mai sarauta matashi ya tambayi Yesu: “Me zan yi domin in gāji rai na har abada?” Yana rayuwa ta ɗabi’a kuma yana bi da wasu da kyau, amma ya shaƙu da dukiyarsa. Ba zai iya barin dukiyar nan ya zama mabiyin Kristi ba. Saboda haka ya ƙi zarafi da zai sa ya kasance tare da Kristi cikin Mulki na samaniya. Sai Yesu ya ce a lokacin: “Da ƙyar kamar me masu-dukiya za su shiga cikin mulkin Allah!”—Markus 10:17-23.
5. (a) Da waɗanne abubuwa ne Bulus ya ƙarfafa Timothawus ya gamsu, kuma me ya sa? (b) Ta yaya Shaiɗan yake amfani da “son kuɗi” wajen kafa tarko mai halakarwa?
5 Bayan wasu shekaru, manzo Bulus ya rubuta wa Timothawus, wanda yake Afisas a lokacin, cibiyar kasuwanci. Bulus ya tuna masa: “Ba mu shigo da kome cikin duniya ba, ba kuwa za mu iya fita cikinta da kome ba; amma da shi ke muna da abinci da sitira, da su za mu yi wadar zuci.” Yin aiki don tanadar da “abinci da sitira” wa mutum da iyalinsa ya dace. Amma Bulus ya yi gargaɗi: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin halaka da lalacewa.” Shaiɗan yana da kissa. Da farko zai jarabi mutum a ƙananan hanyoyi. Ƙila babban matsi ya biyo bayan haka, yana buɗe zarafi a ci gaba ko kuma a samu wani aiki mafi kyau da ke kawo albashi mai yawa amma da ke bukatar ba da lokaci da dama, da an kayade shi ga al’amura na ruhaniya. Idan ba mu tsare kanmu ba, “son kuɗi” zai iya shaƙe abubuwa mafi muhimmanci na Mulkin. Bulus ya ce: “Waɗansu kuwa garin begen samu sun ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.”—1 Timothawus 6:7-10.
6. (a) Don kada tarkon son abin duniya ya kama mu, me dole mu yi? (b) Wane tabbaci za mu kasance da shi duk da yanayin tattalin arziki na duniyar yau?
6 Da ƙauna ta gaske ga ɗan’uwansa Kirista, Bulus ya aririci Timothawus: “Ka guje ma waɗannan abu” kuma, “ka yi yaƙin kirki na imani.” (1 Timothawus 6:11, 12) Muna bukatar ƙoƙari na gaske idan za mu guje wa hanyar rayuwa na son abin duniya na duniyar da ta kewaye mu. Amma idan muka yi fama cikin jituwa da bangaskiyarmu, Jehovah ba zai yasar da mu ba. Duk da tsadar kaya da rashin aiki da ya cika ko’ina, zai tabbatar da cewa muna da abin da muke bukata da gaske. Bulus ya rubuta: “Ku kawarda hankalinku daga ƙaunar kuɗi; ku haƙura da abin da ku ke da shi: gama shi [Allah] da kansa ya ce, Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba. Domin wannan fa gaba gaɗi muna cewa, Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum za ya yi mini?” (Ibraniyawa 13:5, 6) Kuma Sarki Dauda ya rubuta: “Dā yaro ni ke, yanzu kuwa na tsufa: amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.”—Zabura 37:25.
Almajirai na Farko Sun Kafa Misali
7. Menene Yesu ya faɗa wa almajiransa game da yin wa’azi, kuma me ya sa hakan ya dace?
7 Bayan da Yesu ya koyar da manzanninsa da kyau, ya aike su zuwa cikin Isra’ila su yi wa’azin bishara kuma su yi shela cewa: “Mulkin sama ya kusa.” Saƙo ne na farin ciki! Sarki Almasihu, Yesu Kristi, yana tsakaninsu. Tun da manzannin suna ba da kansu ga hidimar Allah, Yesu ya aririce su su yi gaba gaɗi cewa Allah zai lura da su. Saboda haka ya ce: “Kada ku ɗauki kome domin tafiya, ko sanda, ko zabira, ko gurasa, ko kuɗi; kada ku yi riga biyu. Kowane gidan da kuka shiga, ku zauna ciki, daganan kuma ku tashi.” (Matta 10:5-10; Luka 9:1-6) Jehovah zai tabbata ’yan’uwansu Isra’ilawa sun biya musu bukatunsu, waɗanda dama suna da halin marhabin.
8. (a) Ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa, me ya sa Yesu ya ba da sabon umurni game da yin wa’azi? (b) Me har ila mabiyan Yesu suke bukatar su saka farko a rayuwarsu?
8 Daga baya, kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa manzanninsa gaskiyar cewa za su yi aiki cikin yanayi da ya canja. Saboda hamayya da aikinsu, ba za a yi musu maraba ba da sauƙi a Isra’ila. Kuma, ba da daɗewa ba, za su fara kai saƙon Mulkin zuwa ƙasashe na Al’ummai. Yanzu suna bukatar su tafi da “zabira” da “gurasa.” Duk da haka, suna bukatar su ci gaba da biɗan Mulkin Jehovah da farko da kuma adalcinsa, da gaba gaɗi cewa Allah zai albarkaci ƙoƙarinsu su samu abinci da sitira.—Luka 22:35-37.
9. Ta yaya Bulus ya sa Mulkin da farko a rayuwarsa yayin da yake lura da bukatunsa na jiki, kuma wane gargaɗi ya bayar a kan wannan al’amarin?
9 Manzo Bulus misali ne mai kyau na wanda ya bi gargaɗin Yesu. Bulus ya yi rayuwarsa cikin hidima. (Ayukan Manzanni 20:24, 25) Da ya je wani waje don ya yi wa’azi, ya biya bukatunsa na jiki da kansa, har ma ya yi aikin gina tanti. Bai jira wasu su kula da shi ba. (Ayukan Manzanni 18:1-4; 1 Tassalunikawa 2:9) Duk da haka, yana karɓan kyauta yana godiya ga wasu da suke nuna ƙaunarsu ta wannan hanyar. (Ayukan Manzanni 16:15, 34; Filibbiyawa 4:15-17) Bulus ya ƙarfafa Kiristoci, kada su yi banza da hakkinsu na iyali don su yi wa’azi, amma maimako suna daidaita hakkokinsu masu yawa. Ya yi musu gargaɗi cewa su yi aiki, su yi ƙaunar iyalansu, kuma su raba abin da suke da shi da wasu. (Afisawa 4:28; 2 Tassalunikawa 3:7-12) Ya aririce su su dogara ga Allah, ba ga abin da suka mallaka ba, kuma su yi amfani da rayukansu a hanyar da ta nuna da gaske sun fahimci abin da ya fi muhimmanci. Cikin jituwa da koyarwar Yesu, wannan yana nufin biɗan Mulkin Allah da kuma adalcinsa da farko.—Filibbiyawa 1:9-11.
Ka Saka Mulkin da Farko a Rayuwarka
10. Menene yake nufi a biɗi Mulkin da farko?
10 Yaya yawan yadda mu muke saka hannu wajen gaya wa wasu bisharar Mulkin? A taƙaice, wannan ya dangana ga yanayinmu da kuma yadda muke nuna godiyarmu. Ka tuna cewa Yesu bai ce, ‘Ka biɗi Mulkin idan ba ka da wani abin yi ba.’ Sanin muhimmancin Mulkin, ya furta nufin Ubansa, yana cewa: “Ku biɗi mulkinsa.” (Luka 12:31) Ko da yake yawancinmu muna bukatar mu yi aiki don mu kula da kanmu da kuma iyalanmu, idan muna da bangaskiya, za mu sa rayuwarmu cikin aikin Mulki da Allah ya ba mu. Har ila kuma, za mu lura da hakki na iyalinmu.—1 Timothawus 5:8.
11. (a) Ta yaya ne misalin Yesu ya nuna cewa ba duka ne za su iya sa daidai yawan lokaci ɗaya cikin shelar saƙon Mulkin ba? (b) Waɗanne abubuwa ne suke shafan abin da za mu iya yi?
11 Wasunmu muna iya ba da lokaci mai yawa fiye da wasu a wa’azin bisharar Mulkin. Amma a cikin almararsa game da ƙasa iri iri, Yesu ya nuna cewa dukan waɗanda zuciyarsu take kamar ƙasa mai kyau za ta ba da ’ya’ya. To, yaya yawan yadda suke samun ’ya’ya yake? Yanayin mutane ya bambanta. Tsufa, lafiyar jiki, da kuma hakki na iyali duk abubuwa ne da suke shafansa. Amma idan akwai godiya ta ƙwarai, za a iya cim ma abubuwa da yawa.—Matta 13:23.
12. Wane makasudi na ruhaniya ne musamman aka ƙarfafa matasa su yi tunaninsa?
12 Yana da kyau mu kasance da makasudi da zai taimake mu mu faɗaɗa hidimarmu ta Mulkin. Ya kamata matasa su yi tunani sosai bisa misali mai kyau na matashi Kirista mai ƙwazo Timothawus. (Filibbiyawa 2:19-22) Menene zai fi musu kyau fiye da su shiga hidima ta cikakken lokaci yayin da sun gama makarantarsu? Tsofaffi ma za su amfana ta sa makasudi mai kyau na abubuwa na ruhaniya.
13. (a) Waye ke tsara abin da mu kanmu za mu iya yi cikin hidimar Mulki? (b) Idan muna biɗan Mulkin da farko da gaske, me za mu tabbatar?
13 Maimakon mu zargi waɗanda za su iya sa ƙarin lokaci, ya kamata bangaskiya ta motsa mu mu yi gyara don mu bauta wa Allah sosai yadda yanayinmu ya yarda. (Romawa 14:10-12; Galatiyawa 6:4, 5) Yadda aka nuna a yanayin Ayuba, Shaiɗan ya nace cewa abin da muka fi so, dukiyarmu ne, jin daɗinmu, da kuma lafiyar jikinmu kuma wai muradinmu na bauta wa Allah na son kai ne. Amma idan muna biɗan Mulkin da farko, muna sa hannu a tabbatar da cewa Iblis mugun maƙaryaci ne. Muna ba da tabbacin cewa abu na farko cikin rayuwarmu bauta wa Allah ne. A magana da ayyuka, muna tabbatar da ƙaunarmu mai zurfi ga Jehovah, goyon bayanmu na aminci ga ikonsa na mallaka, da kuma ƙaunarmu ga ’yan’uwa bil Adam.—Ayuba 1:9-11; 2:4, 5; Misalai 27:11.
14. (a) Me ya sa kasancewa da tsari na hidimar fage yake da amfani? (b) Yaya yawan yadda da yawa cikin Shaidu suke saka hannu cikin hidimar fage?
14 Tsari zai iya taimaka mana mu cim ma abu da yawa fiye da yadda muke yi. Jehovah kansa yana ‘da lotonsa’ na cika nufinsa. (Fitowa 9:5; Markus 1:15) Idan ya yiwu, yana da kyau mu saka hannu cikin hidimar fage sau ɗaya ko fiye da haka a mako. Shaidun Jehovah dubbai a dukan duniya suna aikin majagaba na ɗan lokaci, suna ba da misalin sa’o’i biyu kowacce rana wajen wa’azin bishara. Wasu dubbai suna aikin majagaba na kullum, suna amfani da sa’o’i biyu da rabi kowacce rana a shelar saƙon Mulkin. Majagaba na musamman da masu wa’azi a ƙasashen waje suna amfani da lokaci da ya fi haka a hidimar Mulkin. Za mu iya gaya wa wasu ma ba tare da shiri ba game da begen Mulkin, duk wanda zai saurara. (Yohanna 4:7-15) Ya kamata muradinmu ya zama na saka hannu da kyau cikin aikin yadda yanayinmu zai ƙyale, domin Yesu ya annabta: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14; Afisawa 5:15-17.
15. Game da hidimarmu, me ya sa kake jin gargaɗi da ke a 1 Korinthiyawa 15:58 na kan lokaci ne?
15 Shaidun Jehovah a duk ɓangarorin duniya, cikin haɗin kai, ko da daga wace al’umma suke, suna saka hannu cikin wannan gata ta hidima. Suna amfani da gargaɗi da aka hure na Littafi Mai Tsarki: “Ku kafu yadda ba ku kawuwa, kullum kuna yawaita cikin aikin Ubangiji, da shi ke kun sani wahalarku ba banza ta ke ba cikin Ubangiji.”—1 Korinthiyawa 15:58.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Da Yesu ya ce a ‘ci gaba da biɗan Mulkin da farko,’ me yake nuna ya kamata ya zama a wuri na biyu?
• Wane ra’ayi ya kamata mu kasance da shi game da biyan bukatunmu na jiki da kuma na iyalai? Wane taimako Allah zai yi mana?
• A waɗanne fasalolin hidima na Mulkin ne za mu iya saka hannu?
[Hoto a shafi na 107]
A kowacce ƙasa, Shaidun Jehovah a yau suna yin wa’azin bishara kafin ƙarshen ya zo