Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 55 sakin layi na 1-5
  • Ka Taimaka a Ikilisiyarku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaka a Ikilisiyarku
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Muna Gode wa Jehobah don Ƙaunarku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • “Ba da Kyauta ga Jehobah”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aiki da Kudi
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Za Mu Iya Ba Wanda Yake da Kome?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 55 sakin layi na 1-5
Darasi na 55. ’Yan’uwa suna gyara Majami’ar Mulkinsu.

DARASI NA 55

Ka Taimaka a Ikilisiyarku

Hoto
Hoto
Hoto

A faɗin duniya, miliyoyin mutane suna bauta wa Jehobah a ikilisiyoyi da yawa. Suna farin ciki don umurni da ja-gorancin da ake musu, kuma suna taimakawa a ikilisiya a hanyoyi da yawa. Haka ne kake ji game da ikilisiyarku?

1. A waɗanne hanyoyi ne za ka yi amfani da lokacinka da kuzarinka don ka taimaka a ikilisiyarku?

Dukanmu za mu iya taimakawa a ikilisiya. Alal misali, akwai wasu a ikilisiyarku da suka tsufa ko suke rashin lafiya? Za ka iya taimaka musu su halarci taro? Ko za ka iya taimaka musu yin wasu abubuwa, kamar yin cefane ko kuma aikace-aikacen gida? (Karanta Yakub 1:27.) Za mu kuma iya taimakawa wajen share Majami’ar Mulki da kuma yin gyare-gyare. Ba wanda yake tilasta mana yin waɗannan abubuwa. Amma ƙaunarmu ga Jehobah da ’yan’uwanmu ne take sa mu yi waɗannan abubuwan da “yardan rai.”​—Zabura 110:3.

Shaidu da suka yi baftisma suna iya taimakawa a ikilisiya a wasu hanyoyi kuma. ’Yan’uwa maza da suka cancanta za su iya zama bayi masu hidima kuma da shigewar lokaci, su zama dattawa. ’Yan’uwa maza da mata za su iya yin wa’azi a matsayin majagaba. Wasu Shaidu suna iya taimaka wajen gina wuraren ibada ko kuma su ƙaura zuwa wata ikilisiya da ke bukatar taimako.

2. Ta yaya za mu yi amfani da dukiyarmu don mu taimaka wa ’yan’uwa?

Za mu iya “girmama Yahweh da abin da” muke da shi. (Karin Magana 3:9) Muna farin cikin ba da gudummawar kuɗi ko wasu abubuwa don mu taimaka wa ikilisiyoyinmu da kuma wa’azin da ake yi a faɗin duniya. (Karanta 2 Korintiyawa 9:7.) Ana amfani da gudummawarmu wajen taimaka wa ’yan’uwanmu da bala’i ya shafa. Mutane da yawa sun tsai da shawarar “ajiye wani abu” a kai a kai don su yi gudummawa da shi. (Karanta 1 Korintiyawa 16:2.) Za mu iya saka gudummawarmu a akwati da ke wurin ibadarmu ko kuma mu bayar ta intane a donate.jw.org. Jehobah yana ba mu dama mu nuna ƙaunarmu gare shi ta yadda muke amfani da abubuwan da muke da su.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga hanyoyin da mutum zai iya taimakawa a ikilisiya.

3. Za mu iya amfani da dukiyarmu

Jehobah da Yesu suna ƙaunar waɗanda suke bayarwa da farin ciki. Alal misali, Yesu ya yaba wa wata gwauruwa da ta ba da gudummawa duk da cewa abin da take da shi bai da yawa. Ku karanta Luka 21:​1-4, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Sai mun yi gudummawa da kuɗi da yawa ne za mu faranta wa Jehobah rai?

  • Yaya Jehobah da Yesu suke ji idan muka ba da gudummawa da son rai?

Don ka san yadda ake amfani da gudummawarmu, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: ‘Kyauta ga Jehobah’ (4:​47)

  • Ta yaya ikilisiyoyi a faɗin duniya suke amfana don gudummawar da muke yi?

Wata ’yar’uwa tsohuwa tana saka gudummawarta a cikin akwati.

4. Za mu iya taimakawa

A zamanin dā, bayin Jehobah sun yi aiki tuƙuru don su kula da wuraren ibadarsu. Don a cim ma wannan aikin, ba kawai gudummawar kuɗi ake bukata ba. Ku karanta 2 Tarihi 34:​9-11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya kowane Ba’isra’ile ya taimaka wajen kula da wurin ibada?

Don ka ga yadda Shaidun Jehobah suke bin misalin bayin Allah na dā, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Ku Riƙa Kula da Wuraren Ibadarmu (3:​31)

Wani hoto daga bidiyon ‘Ku Rika Kula da Wuraren Ibadarmu.’ Maza da mata da kuma yara suna share cikin Majami’ar Mulkinsu.
  • Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tsabtace Majami’ar Mulkinmu kuma mu kula da ita?

  • A waɗanne hanyoyi ne za ka iya taimakawa?

Wasu Shaidu suna taimakawa wajen gina wata Majami’ar Mulki.

5. ’Yan’uwa maza za su iya biɗan ƙarin aiki a ikilisiya

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ’yan’uwa maza su yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka a ikilisiya. Don ku ga misalin yadda za su iya yin hakan, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku amsa tambayar da ke gaba.

BIDIYO: ’Yan’uwa Maza​—Ku Yi Ƙoƙari Ku Cancanci Yin Hidima (5:​19)

  • A bidiyon, ta yaya Ryan ya nuna himma wajen taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya?

Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ’yan’uwa maza za su iya yi don su zama bayi masu hidima da kuma dattawa. Ku karanta 1 Timoti 3:​1-13, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ake so ’yan’uwa maza su yi idan suna so su zama bayi masu hidima da kuma dattawa?

  • Mene ne ake so iyalansu su yi?​—Ka duba ayoyi na 4 da 11.

  • Idan ’yan’uwa maza suka yi ƙoƙari su cancanci yin hidimar nan, ta yaya kowa a ikilisiya zai amfana?

Wani dan’uwa matashi yana tura wani dan’uwa da ya tsufa keken guragu sa’ad da suke wa’azi gida-gida.

WANI YANA IYA CEWA: “Daga ina ne Shaidun Jehobah suke samun kuɗin gudanar da ayyukansu?”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Jehobah yana farin ciki sosai a duk lokacin da muka yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu da kuma dukiyarmu don mu taimaka a ikilisiya.

Bita

  • Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu don mu taimaka a ikilisiya?

  • Ta yaya za mu yi amfani da dukiyarmu don mu taimaka a ikilisiya?

  • A waɗanne hanyoyi ne za ka so ka taimaka a ikilisiya?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku san dalilin da ya sa Allah ya ce bayinsa su daina biyan zakka.

“Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Biyan Zakka?” (Talifin jw.org)

An ambata wasu ayyuka a Baibul da aka ba maza da suka yi baftisma. Amma me mace za ta yi idan tana so ta kula da ayyukan nan?

Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya (Hasumiyar Tsaro, Fabrairu 2021)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wasu Shaidun Jehobah masu ƙarfin zuciya suke yin sadaukarwa sosai don su kai wa ’yan’uwansu da ke wasu wurare littattafai.

Yadda Ake Rarraba Littattafai da ke Bayyana Littafi Mai Tsarki a Kwango (4:25)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda muke samun kuɗin gudanar da ayyukanmu da ya bambanta da yadda sauran addinai suke yi.

“A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kuɗin Yin Ayyukansu?” (Talifin jw.org)

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba