Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Mu ‘Yi Tsaro’?
“ME NE kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Mat. 24:3) Muna iya karanta amsar da Yesu ya ba almajiransa a Matta sura 24 da Markus sura 13 da kuma Luka sura 21. Bayani da ya yi musu game da alamar ya fita sarai kuma ya yi hakan dalla-dalla yadda almajiransa za su fahimci abubuwa da ke cikin alamar da sauƙi. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku yi tsaro fa.”—Mat. 24:42.
Amma idan alamar za ta fita sarai, me ya sa ya ba da wannan ƙarin gargaɗin? Wataƙila domin waɗannan dalilai biyu ne. Na farko, abubuwan raba hankali suna iya sa wasu su ƙi lura da alamar, kuma hakan zai sa su yi rashin ruhaniya kuma su daina yin tsaro. Dalili na biyu shi ne cewa idan wani sashe na alamar ba ya faruwa inda Kirista yake da zama, zai ji cewa hakan bai shafe shi ba. Saboda haka, zai yi tunani cewa “ƙunci mai-girma” wato, sashe na ƙarshe na annabcin Yesu yana da nisa kuma ba ya bukatar ya “yi tsaro.”—Mat. 24:21.
“Ba Su Farga Ba”
Yesu ya tuna wa mabiyansa game da mutane da suka rayu a zamanin Nuhu. Babu shakka mutanen sun lura da wa’azin da Nuhu ya yi da jirgi mai girma da ya gina da kuma mugunta na wannan zamanin. Duk da haka, yawancinsu “ba su farga ba.” (Mat. 24:37-39, Littafi Mai Tsarki) Mutane da yawa a yau suna da irin wannan halin. Alal misali, mutane da yawa ba sa biyayya da ƙayyadadden yawan gudu sa’ad da suke tuƙi. Sau da yawa hukumomi suna saka galan a tituna na birane don su tilasta wa mutane su rage gudu sa’ad da suke tuƙi. Hakan nan ma, Kirista yana iya ganin alama cewa muna zama a kwanaki na ƙarshe amma ya ƙi mai da hankali da waɗannan alamun. Hakan ya faru wa Arielle, wata matashiya a Afirka ta Yamma.
Arielle tana jin daɗin kallon ƙwallon hannu da mata suke bugawa a talabijin. Sa’ad da makarantarsu ta kafa rukunin ’yan wasan ƙwallon hannu, son ta yi wasa ya sa ta manta cewa hakan zai iya zama haɗari ga abutarta da Allah. Ta shiga rukunin a matsayin gola. Mene ne ya faru? Ta bayyana: “Wasu cikin abokan wasa na suna da samari da suke shan ƙwayoyi da kuma taba sigari. Sun yi mini ba’a don na kasance dabam, amma ina ganin cewa kasancewa da waɗannan mutane ba zai shafe ni ba. Bayan ɗan lokaci, wasan ya soma shafan ruhaniyata. Ina yawan tunani game da wasan ƙwallon hannu. Sa’ad da nake wurin tarurrukan Kirista, sau da yawa hankalina sai ya koma filin wasan ƙwallon hannu. Hakan ma ya shafi halayena na Kirista. Sai cin wasan ya fi kasancewa da muhimmanci a gare ni, maimakon na riƙa yin wasan kawai. Na yi ta horon kaina sosai domin ina son na ci wasan. Hakan ya sa ni alhini sosai. Na yi hasarar abokai na domin wasan ƙwallon hannu.”
“Amma wani abu ya faru sa’ad da muke wani wasa da ya sa na yi tunani game da yanayi na. An ba rukunin da muke wasa da su fanareti. Ina a shirye na kama ƙwallon, amma kafin na sani, na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini na kama ƙwallon! Wannan ya sa na fahimci cewa na ɓata dangantaka ta da Jehobah. Mene ne na yi don na daidaita yanayin?”
“Na kalli faifan DVD na Young People Ask—What Will I Do With My Life?a Sai na tsai da shawara na sake kallonsa don na amfana. Bayan na kalla bidiyon, na san cewa ina da damuwa iri ɗaya da André, matashi da ke cikin wasan kwaikwayon. Musamman ma na lura da shawarar da dattijon ya ba André cewa ya karanta kuma ya yi tunani a kan Filibiyawa 3:8. Ni ma sai na yi hakan, kuma na daina ƙwallon.”
“Hakan ya shafi rayuwata sosai! Halin gasa da nake da shi da kuma alhinin suka ƙare. Na yi farin ciki matuƙa kuma na kasance kusa da abokaina Kiristoci. Abubuwa na ruhaniya sun kasance da muhimmanci a gare ni. Na mai da hankali a tarurruka kuma na soma more su kuma. Na kyautata aikin da nake yi a hidima. Yanzu ina hidimar majagaba na ɗan lokaci a kai a kai.”
Kana bukatar ka ɗauki mataki kamar yadda Arielle ta yi idan abubuwan raba hankali suna sa ka ƙyale alamar da Yesu ya ba mu. Za ka iya bin waɗannan shawarwarin. Ka bincika littafin nan Watch Tower Publications Index, wanda yake makamancin taswira da zai kai ga samun ɓoyayyen dukiya. Littafin ya nuna inda za ka samu shawara mai kyau da kuma labarai na mutane da suka fuskanci yanayi irin naka. Za ka fi amfana a tarurruka idan ka shirya da kyau kuma ka rubuta muhimman bayanai. Kuma idan ka zauna a gaba, za ka fi mai da hankali. Idan ana gabatar da sashe na tattaunawa da masu sauraro, ka yi ƙoƙari ka ba da amsa da wuri. Kuma ka yi lura ta wurin gwada abubuwan da suke faruwa a duniya a yau da kuma alamar da Yesu ya ba da tare da wasu annabce-annabcen da suka yi magana game da “kwanaki na ƙarshe.”—2 Tim. 3:1-5; 2 Bit. 3:3, 4; R. Yoh. 6:1-8.
Ku Kasance da “Shiri”
Alamar kwanaki na ƙarshe tana faruwa a dukan “iyakar duniya.” (Mat. 24:7, 14) Miliyoyin mutane suna zama a wuraren da cututtuka da karancin abinci da girgizar ƙasa da kuma wasu annabce-annabce da aka yi cikin Littafi Mai Tsarki suke tsanani sosai. Akasin haka, wasu mutane suna zama ne a wuraren da akwai ɗan salama da kwanciyar hankali. Idan wasu cikin alamun ba su taɓa shafanka ba, ya kamata ne ka ce ƙarshen har ila yana da nisa? Hakan ba zai kasance da hikima ba.
Ka yi tunani a kan annabcin da Yesu ya yi game da “yunwa da aloba.” (Luk 21:11) Ka tuna cewa Yesu bai ce hakan zai shafi dukan wurare kuma a lokaci ɗaya ba. Maimakon haka, ya ce hakan zai faru a “wurare dabam dabam.” Saboda haka ba za mu yi zaton abubuwa iri ɗaya su faru a ko’ina kuma a lokaci ɗaya ba. Kuma bayan da Yesu ya ambata cewa wasu za su sha wahala don yunwa, ya yi kashedi cewa mutane suna bukata su mai da hankali game da yawan cin abinci: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci.” (Luk 21:34) Saboda haka, bai kamata dukan Kiristoci su yi zaton shaida dukan alamun ba. Maimako, Yesu ya ce: “Lokacinda kun ga waɗannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.” (Luk 21:31) Ta wurin fasaha na zamani kamar su talabijin da kuma intane muna ganin alamun ko da ba ma shaida su a wurin da muke da zama ba.
Ka tuna kuma cewa Jehobah ya riga ya zaɓi “ranan nan da sa’an” da ƙunci mai girma zai soma. (Mat. 24:36) Babu abin da ke faruwa a duniya da zai iya canja “ranan nan da sa’an” da Jehobah ya ƙayyade.
Yesu ya gargaɗi dukan Kiristoci: “Ku zama da shiri.” (Mat. 24:44) Ya kamata mu kasance da shiri kullayaumin. Hakika, ba za mu riƙa yin ayyuka na ruhaniya a dukan lokaci ba. Kuma, babu ɗaya cikinmu da ya san abin da za mu riƙa yi sa’ad da ƙunci mai girma ya soma. Wasu za su kasance suna aiki a gona ko kuwa yin wasu ayyuka na gida. (Mat. 24:40, 41) Saboda haka, mene ne ya kamata mu riƙa yi don mu kasance da shiri?
Emmanuel da Victorine da yaransu mata shida suna zama ne a wani wuri a Afirka da alamun kwanaki na ƙarshe ba sa shafan su sosai. Sai suka tsai da shawara su riƙa tattaunawa game da abubuwa na ruhaniya kowace rana don ya taimaka musu su kasance da shiri. Emmanuel ya ce: “Ya yi wuya mu zaɓi lokacin da kowa zai so. A ƙarshe muka zaɓi rabin sa’a tsakanin ƙarfe shida da kuma shida da rabi da safe. Bayan mun bincika nassin yini, sai mu ɗan bincika sakin layi na littattafan da ake nazarinsu a ikilisiya a makon.” Hakan ya taimake su su kasance da shiri ne? Hakika, ya yi hakan! Emmanuel mai tsara ayyukan rukunin dattawa ne a ikilisiyarsu. Matarsa Victorine takan yi hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma ta taimaka wa mutane da yawa su san gaskiya. Yaransu suna samun ci gaba sosai a ruhaniya.
Yesu ya faɗakar da mu: “Ku yi lura, ku yi tsaro.” (Mar. 13:33) Kada ka ƙyale abubuwan raba hankali ya rage yin tsaron da kake yi. Maimako haka, kamar yadda Arielle ta yi, ka bi shawara mai kyau da ke cikin littattafanmu da kuma waɗanda muke samu daga tarurrukan ikilisiya. Kamar iyalin Emmanuel, ka yi ƙoƙari ka riƙa yin bincike kowace rana don ka nuna kana kasancewa da shiri kuma ka “yi tsaro.”
[Hasiya]
a Wasan kwaikwayo na zamani game da matashi Kirista da ya yi gwagwarmaya don yin abin da ya dace a gaban Jehobah.
[Hoto a shafi na 4]
Tattaunawa game da abubuwa na ruhaniya kowace rana ne ya taimaka wa Emmanuel da iyalinsa su “zama da shiri”