Ka Fahimci Alamar Dawowar Yesu?
BABU wanda yake so ya yi rashin lafiya mai tsanani ko kuwa ya sami kansa cikin haɗari. Domin ya kauce wa irin wannan bala’in, mutum mai hikima yana fahimtar alamun da suke nuni ga haɗari kuma sai ya ɗauki mataki nan da nan. Yesu Kristi ya ba da wata muhimmiyar alama da ya kamata mu fahimta. Abin da yake magana a kai zai shafi dukan ’yan adam. Wannan ya haɗa da kai da iyalinka.
Yesu ya yi magana game da Mulkin Allah, wanda zai kawar da mugunta kuma ya mai da duniya aljanna. Almajiransa suka soma ɗokin sanin lokacin da wannan Mulkin zai zo. Suka yi tambaya: “Mecece kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”—Matiyu 24:3.
Yesu ya sani cewa bayan mutuwarsa da kuma tashinsa daga matattu, shekaru masu yawa za su wuce kafin a naɗa shi Sarki Almasihu a sama kuma ya yi sarauta bisa ’yan adam. Tun da yake mutane ba za su san lokacin da aka naɗa shi ba, Yesu ya ba da alamar da za ta sa mabiyansa su gane ‘dawowarsa’ da kuma “ƙarewar zamani.” Waɗannan alamun sun ƙunshi fasaloli masu yawa da suka sa aka fahimci alamar, wato, alamar dawowar Kristi.
Marubutan Linjila, Matiyu, Markus, Luka, duk sun rubuta amsar Yesu. (Matiyu sura 24 da 25; Markus sura 13; Luka sura 21) Wasu marubutan Littafi Mai Tsarki sun ƙara ba da haske a kan alamar. (2 Timoti 3:1-5; 2 Bitrus 3:3, 4; Wahayin Yahaya 6:1-8; 11:18) Babu isashen wuri a wannan talifin da zai sa mu tattauna dukan batun, amma za mu tattauna abubuwa biyar da suke ƙunshe cikin wannan alamar da Yesu ya bayar. Za ka ga cewa wannan abu ne mai ma’ana kuma yana da muhimmanci a gare ka.—Dubi akwati a shafi na 5.
“Canjin da Ya Kawo Sabon Zamani”
“Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.” (Matiyu 24:7) Jaridar Jamus Der Spiegel ta ba da rahoton cewa, kafin shekara ta 1914, mutane “sun sa rai za a sami ƙarin ’yancin kai, ci gaba, da kuma ni’imar rayuwa mai kyau a gaba.” Sai komi ya canja farat ɗaya. “Yaƙin da ya soma a watan Agusta shekara ta 1914 kuma ya ƙare a watan Nuwamba shekara ta 1918 abu ne na ban mamaki. Ya canja tarihin ’yan adam, ya raba tsoho daga sabo,” in ji mujallar nan GEO. Fiye da sojoji miliyan 60 daga nahiyoyi biyar ne suka yi yaƙin. Matsakaicin sojoji 6,000 ne ake kashewa a kowace rana. Tun daga lokacin, ’yan tarihi na kowace tsara da kuma masu ra’ayin siyasa sun ɗauki shekaru na 1914 zuwa 1918 shekarun canji da suka kawo sabon zamani.”
Yaƙin Duniya na farko ya tilasta canji na dindindin ga ’yan adam kuma ya sa mutane cikin zamani na ƙarshe na wannan duniya. Wannan ƙarnin ya cika da yaƙe-yaƙe, faɗa da makami, da ta’addanci. Abubuwa ba su yi kyau a wannan ƙarnin ba. Ban da yaƙe-yaƙe, da wasu fasaloli na wannan alamar da suka bayyana.
Yunwa, Annoba, da Girgizar Ƙasa
“Za a kuma yi yunwa.” (Matiyu 24:7) Yunwa ta mamaye Turai a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, tun daga lokacin yunwa ta dami ’yan adam. Ɗan tarihi Alan Bullock ya rubuta cewa a shekara ta 1933 a Rasha da Ukraine, “mutane masu yawa da yunwa ke damu suna ta yawo a cikin ƙauyuka . . . An tara gawawwaki a bakin hanya.” A shekara ta 1943, ɗan jarida T. H. White, ya ga yadda aka yi yunwa a ƙasar Sin a yankin Henan. Ya rubuta: “A lokacin yunwa, kusan komi yana iya zama abinci, a daka a ci kuma jiki ya karɓa. Amma sai mutum ya ga cewa zai mutu ne zai ci abin da ba shi ciwuwa.” Abin baƙin ciki, yunwa a ’yan shekarun nan ta zama ruwan dare a Afirka. Ko da yake ana shuka abincin da zai ishe kowa, Ƙungiyar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa mutane miliyan 840 ne a duniya ba su da isashen abinci.
“Annoba a wurare dabam dabam.” (Luka 21:11) Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ba da rahoto cewa “an ƙiyasta cewa Cutar massassara ta Spain ta kashe tsakanin mutane miliyan 20 zuwa 50 a shekara ta 1918, fiye da annoba ko kuwa yaƙin duniya na ɗaya.” Tun daga lokacin, cututtuka kamar su zazzaɓi cizon sauro, zanzana, cutar fuka, shan inna, da kuma kwalera sun dami mutane da yawa. Kuma mutanen duniya sun razana game da yadda Cutar Kanjamau ke yaɗuwa. Yanayi a yanzu yana da ban mamaki domin duk da ci gaba da aka samu na magani, cututtuka na ci gaba da wanzuwa. Wannan saɓani, wanda har yanzu ’yan adam ba su fahimta ba, ya nuna sarai cewa muna raye ne a lokaci mai ban al’ajabi.
“Raurawar ƙasa.” (Matiyu 24:7) A shekara 100 da ta wuce, girgizar ƙasa ta kashe dubban mutane. In ji wata majiya, girgizar ƙasa da ke da ƙarfin rushe gine-gine kuma wadda za ta iya buɗe ƙasa ta ƙaru da kashi 18 kowace shekara tun shekara ta 1914. Muguwar girgizar ƙasa da ke da ƙarfin rushe gine-gine, tana aukuwa kusan sau ɗaya a shekara. Duk da ci gaban da aka samu a fasaha, adadin mutuwa sai ƙaruwa yake yi domin yawancin biranen da ke samun ƙaruwar mutane suna inda ake girgizar ƙasa.
Labari Mai Daɗi!
Yawancin fasalolin alamun wannan zamani na ƙarshe suna da ban wahala. Amma Yesu ya ambata wani labari mai daɗi.
“Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai.” (Matiyu 24:14) Aikin da Yesu da kansa ya soma, wato, wa’azin bishara ta Mulki, za ta ƙare a wannan zamani na ƙarshe. Wannan batu gaskiya ne. Shaidun Jehobah suna wa’azin saƙon Littafi Mai Tsarki kuma suna koya wa mutane su yi amfani da abin da suke koya a rayuwarsu. A yanzu, Shaidu fiye da miliyan shida ne suke wa’azi a ƙasashe 235 kuma a fiye da harsuna 400.
Ka lura cewa Yesu bai ce rayuwa za ta tsaya ba domin yanayi mai tsanani na wannan duniyar. Kuma bai ce dukan duniya za ta cika da fasali guda na alamar ba. Amma ya ambata aukuwa masu yawa da za su nuna alamar da za a fahimta daga ko’ina a duniya.
Maimakon a mai da hankali a kan aukuwa guda ko kuwa wani aukuwa dabam na musamman, ka ga alamar mai muhimmanci a dukan duniya? Abubuwan da suke faruwa suna shafan ka da iyalinka. Muna iya tambaya cewa, Amma me ya sa mutane kaɗan ne suka lura?
Bukatunmu Sune Na Farko
“Hankali da Wutan Lantarki!,” “Ka Rage Gudu.” Waɗannan sune alamu da gargaɗin da muke gani amma a yawancin lokaci mukan yi watsi da su. Me ya sa? Domin muna barin ra’ayinmu ya rinjaye mu. Alal misali, muna iya ganin cewa ya kyautu mu yi gudu da mota fiye da yadda doka ta ce, ko mu kasance da muradi mai ƙarfi na yin fitsari a inda aka hana. Amma rashin hikima ne yin watsi da waɗannan alamun.
Alal misali, hatsarin mota na kashe mutane dubbai a Nijeriya kowace shekara. Mutane da yawa kuma sun naƙasa. Kundin Dokar Hanya na Nijeriya ya nuna cewa yawancin hatsarin mota domin direbobi da yawa suna ƙyaliya ko kuma ba sa bin alamu na kan hanya ne. In ji mujallar Süddeutsche Zeitung, yawancin masu zuwa yawon shakatawa da suke yin watsi da waɗannan umurnin suna rayuwa ne bisa wannan kalamin, Jin daɗi ta dangana ne bisa kasada. Abin baƙin ciki, yin watsi da gargaɗi na iya kawo sakamako marar kyau.
Waɗanne dalilai ne mutane suke da shi na yin watsi da alamar da Yesu ya bayar? Wataƙila son zama mai kuɗi ya makantar da su, ko ƙiyayya ta tsoratar da su, ko sun kasa yanke shawara, ko tsarinsu ta sha kansu, ko kuwa tsoron rasa matsayinsu. Akwai ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa da zai sa ka yi watsi da alamun dawowar Yesu? Ba hikima ba ce idan ka fahimci wannan alamar kuma ka ɗauki matakin da ya dace?
Rayuwa Cikin Aljanna a Duniya
Mutane masu yawa suna yin biyayya da alamar dawowar Yesu. Kristian, wani matashi ma’auraci a Jamus, ya rubuta: “Waɗannan lokatai ne na baƙin ciki. Babu shakka, muna raye ne a zamanin ƙarshe.’ ” Shi da matarsa sun ba da lokaci mai yawa suna tattaunawa da mutane game da Mulkin Almasihu. Frank shi ma yana zaune ne a wannan ƙasar. Shi da matarsa sun ƙarfafa mutane da bisharar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Frank ya ce: “Domin yanayin duniya, yawancin mutane a yau suna alhini ainun game da rayuwa ta nan gaba. Muna ƙoƙarin ƙarfafa su da annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki na aljanna a duniya.” Kristian da Frank sun cika fasali ɗaya na alamar Yesu, wato, yin wa’azin bisharar Mulki.—Matiyu 24:14.
Yayin da wannan zamanin ƙarshe ya ƙare, Yesu zai kawar da wannan tsohon zamanin da mutanensa. Sa’annan Mulkin Almasihu zai kula da al’amura ta duniya, wadda za ta zama Aljannar da aka annabta. Za a ’yantar da ’yan adam daga rashin lafiya da mutuwa, kuma za a ta da matattu zuwa rai a duniya. Waɗannan sune bege masu kyau da ke jiran waɗanda suka fahimci alamar lokacin da muke ciki. Ba hikima ba ce mu ƙara koyo game da alamar, da kuma abin da ya kamata mu yi idan muna so mu tsira daga ƙarshen wannan zamanin? Hakika, ya kamata wannan ya zama batu na gaggawa ga kowa.—Yahaya 17:3.
[Bayanin da ke shafi na 3]
Yesu ya annabta aukuwa masu yawa da za su nuna alamar da za a gani a dukan duniya
[Bayanin da ke shafi na 5]
Ka ga alama mai muhimmanci kuwa?
[Box/Hotuna a shafi na 5]
FAHIMTAR ALAMUN ZAMANIN ƘARSHE
Yaƙe-yaƙen da babu irinsu.—Matiyu 24:7; Wahayin Yahaya 6:4
Yunwa.—Matiyu 24:7; Wahayin Yahaya 6:5, 6, 8
Annoba.—Luka 21:11; Wahayin Yahaya 6:8
Ƙaruwar taka doka —Matiyu 24:12
Girgizar ƙasa.—Matiyu 24:7
Lokacin wahala.—2 Timoti 3:1
Mugun son kuɗi.—2 Timoti 3:2
Rashin biyayya ga iyaye. —2 Timoti 3:2
Rashin ƙauna.—2 Timoti 3:3
Son annashuwa fiye da son Allah.—2 Timoti 3:4
Fajirai.—2 Timoti 3:3
Maƙiya nagarta.—2 Timoti 3:3
Rashin kula da haɗarin da ke gaba.—Matiyu 24:39
Masu ba’a da suka ƙi alamar zamanin ƙarshe.—2 Bitrus 3:3, 4
Yin wa’azin Mulkin Allah a dukan duniya.—Matiyu 24:14
[Wuraren da Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 4]
WWI soldiers: Daga littafin nan The World War—A Pictorial History, 1919; poor family: AP Photo/Aijaz Rahi; Polio victim: © WHO/P. Virot