‘Ka gwada Mafifitan Al’amura’
‘Ka gwada mafifitan al’amura.’—FILIB. 1:10.
1, 2. Wane annabci game da kwanaki na ƙarshe ne wataƙila ya sa almajiran Yesu mamaki, kuma me ya sa?
YESU ya gaya wa almajiransa cewa za a halaka haikalin da ke Urushalima. Jim kaɗan bayan haka, sai waɗannan kalmomin suka dami Bitrus da Yaƙub da Yohanna da kuma Andarawus. (Mar. 13:1-4) A sakamako, suka tambaye shi: “Ka faɗa mana, yaushe waɗannan abubuwa za su zama? me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Mat. 24:1-3) Sai Yesu ya soma bayyana musu abubuwan da za su faru kafin a halaka Urushalima da kuma kafin a halaka wannan mugun zamani na Shaiɗan. Amma babu shakka, wata alama da Yesu ya ambata ya ba su mamaki sosai. Bayan ya gaya musu game da abubuwa kamar su yaƙe-yaƙe da yunwa da yawaitar mugunta, sai ya annabta cewa wani abu mai kyau ma zai faru a kwanaki na ƙarshe. Ka san wannan abin? Ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Mat. 24:7-14.
2 Almajiran Yesu sun ji daɗin yin wa’azin bishara tare da shi. (Luk 8:1; 9:1, 2) Kuma wataƙila sun tuna cewa ya ce: “Girbi dayawa ya ke, amma ma’aikata kadan suke: ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi shi aiki ma’aikata cikin girbinsa.” (Luk 10:2) Amma, ta yaya za su yi wa’azi a “cikin iyakar duniya” kuma su ba da “shaida ga dukan al’ummai”? Daga ina ne ma’aikatan za su fito? Almajiran ba su taɓa sanin yadda wannan annabcin da ke Matta 24:14 zai cika ba.
3. Ta yaya kalmomin da ke Luka 21:34 suke cika a yau, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?
3 Muna rayuwa a zamanin da annabcin Yesu yake cika. Miliyoyin mutane suna wa’azin bishara na Mulkin Allah a dukan faɗin duniya. (Isha. 60:22) Amma, Yesu ya ce zai yi wa wasu wuya ainun su sa wannan aikin ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarsu a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Hankalinsu zai kasu biyu kuma za su nauyaya. (Karanta Luka 21:34.) Muna ganin cikawar waɗannan kalmomin ma. Wasu bayin Jehobah sun fi mai da hankali ga wasu abubuwa dabam. Muna iya ganin hakan a zaɓin da suke yi a batutuwa kamar su aiki da makarantar gaba da sakandare da tara kayan mallaka da kuma yawan lokacin da suke yi suna wasanni da nishaɗi. Wasu suna rage ƙwazonsu a hidima sanadin matsi da kuma kai-da-kawowa na rayuwa. Zai dace ka tambayi kanka: ‘Yaya nake yi a wannan fannin? Ina saka nufin Allah farko a rayuwata kuwa?’
4. (a) Wace addu’a ce Bulus ya yi wa Kiristoci da ke Filibi, kuma me ya sa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da na gaba, kuma me ya sa?
4 Kiristoci a ƙarni na farko sun yi aiki tuƙuru don su saka hidimar Allah farko a rayuwarsu. Shi ya sa manzo Bulus ya yi addu’a cewa waɗanda suke Filibi su “gwada mafifitan al’amura.” (Karanta Filibiyawa 1:9-11.) Manzo Bulus da kuma yawancin Kiristoci a lokacin sun “ƙara ƙarfin hali ƙwarai garin faɗin maganar Allah ban da tsoro.” (Filib. 1:12-14) Hakazalika, yawancinmu a yau muna wa’azin Kalmar Allah da gaba gaɗi. Duk da haka, tattauna abin da ake cim ma a ƙungiyar Jehobah yanzu zai taimaka mana mu fi mai da hankali ga wa’azi. A wannan talifin, za mu tattauna shirye-shiryen da Jehobah ya yi don ya hanzarta cikawar kalmomin da ke Matta 24:14. Mene ne ƙungiyar Jehobah take yi, kuma ta yaya hakan yake shafarmu da iyalinmu? A talifi na gaba, za mu tattauna abin da zai taimaka mana mu jimre kuma mu bi ƙungiyar Jehobah sawu da kafa.
SASHEN ƘUNGIYAR JEHOBAH DA KE SAMA
5, 6. (a) Me ya sa Jehobah ya saukar wa bawansa da wahayi game da sashen ƙungiyarsa da ke sama? (b) Mene ne Ezekiyel ya gani a wahayi?
5 Akwai abubuwa da yawa da Jehobah bai sa a rubuta cikin Littafi Mai Tsarki ba. Alal misali, bai bayyana dalla-dalla yadda ƙwaƙwalwarmu ko sararin sama yake aiki ba, ko da hakan zai burge mutane sosai. Maimakon haka, Jehobah ya tanadar mana da bayanan da muke bukata don mu fahimci nufe-nufensa kuma mu yi su. (2 Tim. 3:16, 17) Yadda Jehobah ya yarda ya ba mu bayani game da sashen ƙungiyarsa da ke sama ya dace. Muna jin daɗin karanta su a littafin Ishaya da Ezekiyel da Daniyel da kuma Ru’ya ta Yohanna. (Isha. 6:1-4; Ezek. 1:4-14, 22-24; Dan. 7:9-14; R. Yoh. 4:1-11) Me ya sa Jehobah ya ƙyale mu mu san abubuwan da suke faruwa a sama?
6 Jehobah yana son mu riƙa tuna cewa muna sashen ƙungiyarsa na sararin sama. Sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama yana aiki tuƙuru don yin nufin sa. Alal misali, Ezekiyel ya ga wahayin sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama da wani babban karusa yake wakiltar ta. Wannan karusan yana gudu ainun kuma yana iya canja inda za shi nan take. (Ezek. 1:15-21) Ya kuma ga mutumin da ke tuƙa wannan karusan. Ezekiyel ya ce: “Na ga kuma kamar amber, sai ka ce wuta a cikinsa koina . . . Wannan kamanin surar darajar Ubangiji ne.” (Ezek. 1:25-28) Babu shakka, wannan wahayin ya sa Ezekiyel mamaki. Ya ga cewa Jehobah ne yake da cikakken iko bisa ƙungiyarsa kuma yana yin amfani da ruhunsa don yi mata ja-gora. Karusan da ke tafiya kwatanci ne mai kyau na yadda ake tafiyar da sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama.
7. Ta yaya wahayin Daniyel ya sa mu kasance da gaba gaɗi?
7 Daniyel ma ya ga wahayin da ya sa mu gaba gaɗi. Ya ga Jehobah wanda shi ne “mai-zamanin dā,” yana zaune a kursiyin da ke da taya. (Dan. 7:9) Jehobah yana son Daniyel ya ga cewa ƙungiyarsa tana tafiya, wato, yin nufin Jehobah. Daniyel ya kuma ga an ba wani “mai-kama da ɗan mutum,” wato Yesu, iko bisa sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya. Sarautar Yesu bisa ’yan Adam ba ta ’yan shekaru ba ce. Amma, sarautar “madawwamiya ce, wanda ba za ta shuɗe ba, mulkinsa kuma wanda ba shi hallakuwa.” (Dan. 7:13, 14) Wannan wahayin ya motsa mu mu dogara ga Jehobah kuma mu fahimci abin da yake cim ma. Ya ba da “sarauta da daraja, da mulki” ga Ɗansa Yesu, wanda shi nagari na kowa ne. Jehobah ya amince da Ɗansa. Saboda haka, ya kamata mu ma mu amince da Yesu a matsayin shugabanmu.
8. Ta yaya wahayin da Jehobah ya saukar wa Ezekiyel da Ishaya ya shafe su, kuma yaya ya kamata ya shafe mu ma?
8 Mene ne wannan wahayi na ƙungiyar Jehobah ya kamata ya motsa mu mu yi? Abin da Jehobah yake cim ma ya burge Ezekiyel sosai, mu ma haka. (Ezek. 1:28) Annabi Ishaya ma ya ga wahayin abin da ke faruwa a cikin sama. Sa’ad da ya samu zarafin sanar da mutane game da abin da Jehobah yake yi, sai ya yi amfani da shi nan da nan. (Karanta Ishaya 6:5, 8.) Ishaya ya shawo kan kowane ƙalubale, domin ya san cewa Jehobah yana goyon bayansa. Hakazalika, ya kamata mu goyi bayan ƙungiyar Jehobah ta wajen daɗa yin ƙwazo a hidimarsa. Muna samun ƙarfafa sosai domin mun san cewa muna ƙungiyar da ke ƙoƙarin yin nufin Jehobah.
SASHEN ƘUNGIYAR JEHOBAH DA KE DUNIYA
9, 10. Me ya sa ake bukatar sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya?
9 Akwai wani shiri da Jehobah ya sa Ɗansa ya yi a duniya, kuma wannan shirin ya jitu da sashen ƙungiyarsa da ke sama. Ana bukatar wannan shirin domin a cim ma aikin da aka ambata a littafin Matta 24:14. Me ya sa? Ga dalilai uku.
10 Na farko, Yesu ya ce almajiransa za su yi wa’azi har “iyakar duniya.” (A. M. 1:8) Na biyu, waɗanda za su yi wa’azi za su bukaci koyarwar Littafi Mai Tsarki da kuma ƙarfafa. (Yoh. 21:15-17) Na uku, za su bukaci yin taro don bauta wa Jehobah tare kuma su koya yadda za su yi wa’azi. (Ibran. 10:24, 25) Almajiran Yesu za su bukaci tsari don su cim ma waɗannan abubuwan.
11. Ta yaya za mu goyi bayan ƙungiyar Jehobah?
11 Ta yaya za mu iya goyon bayan ƙungiyar Jehobah? Hanya ɗaya ita ce amincewa da ’yan’uwan da suke ja-gora a aikin wa’azi. Jehobah da Yesu sun amince da waɗannan ’yan’uwan, ya kamata mu ma mu yi hakan. Waɗannan ’yan’uwan za su iya yin amfani da lokacinsu da kuma kuzarinsu don biɗan abin duniya. Amma ba su yi hakan ba. Yanzu za mu tattauna abin da sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya take mai da wa hankali.
SUN MAI DA HANKALI GA “MAFIFITAN AL’AMURA”
12, 13. Ta yaya dattawa suke cika hakkinsu, kuma me ya sa hakan yake ƙarfafa ka?
12 An naɗa dattawa Kiristoci ƙwararru don su kula da kuma yi ja-goranci a wa’azin Mulkin a ƙasashen da suke hidima. Yayin da waɗannan ’yan’uwan suke tsai da shawara, suna ƙyale Kalmar Allah ta zama ‘fitila ga sawayensu da kuma haske ga tafarkinsu,’ kuma suna addu’a ga Jehobah don ya ja-gorance su.—Zab. 119:105; Mat. 7:7, 8.
13 Kamar yadda dattawa na ƙarni na farko suka yi, haka ma dattawa da suke tsara aikin wa’azi a yau suke saka “hidimar kalman” farko. (A. M. 6:4) Suna farin ciki sosai ganin ci gaban da ake samu a wa’azin bishara da ake yi a yankunansu da kuma a dukan duniya. (A. M. 21:19, 20) Maimakon ƙafa wa bayin Allah dokoki masu yawa, sun fi mai da hankali ga yaɗa bishara. Suna yin hakan da taimakon Littafi Mai Tsarki da kuma ruhu mai tsarki. (Karanta Ayyukan Manzanni 15:28.) Ta hakan, waɗannan dattawan suna ƙafa wa ikilisiyoyi misali mai kyau.—Afis. 4:11, 12.
14, 15. (a) Wane shiri ne ake yi don a taimaka mana mu yi wa’azi a dukan duniya? (b) Yaya kake ji game da yadda kake saka hannu a aikin wa’azi?
14 ’Yan’uwanmu da yawa suna aiki kullum wajen shirya littattafai da taron ikilisiya da kuma taron gunduma. Alal misali, dubban ’yan’uwa da suka ba da kansu suna aiki tuƙuru wajen fassara littattafanmu zuwa fiye da harsuna 600. A sakamako, mutane da yawa suna koyon “ayyuka masu-girma na Allah” a yarensu. (A. M. 2:7-11) ’Yan’uwa matasa maza da mata suna aiki tuƙuru wajen buga littattafanmu da taimakon maɗaba’a. Bayan haka, ana tura littattafan zuwa ikilisiyoyi dabam-dabam har da waɗanda suke wurare masu nisa.
15 A yankinmu ma, akwai wasu da suke taimaka mana mu mai da hankali ga aikin wa’azi. Alal misali, dubban ’yan’uwa sun ba da kansu don gina Majami’un Mulki da kuma Majami’un Manyan Taro. Wasu kuma suna taimaka wa ’yan’uwa da bala’i ya auko musu ko suke jinya. Wasu kuma suna tsara taron da’ira da na musamman da kuma na gunduma, kuma wasu suna koyarwa a makarantun Littafi Mai Tsarki. Mene ne manufar waɗannan ayyukan? Suna taimaka mana mu yi wa’azi, kuma mu samu ci gaba a cikin gaskiya domin mu taimaki mutane da yawa su bauta wa Jehobah. Hakika, sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya ya fi mai da hankali ga mafifitan al’amura.
KA BI MISALIN ƘUNGIYAR JEHOBAH
16. Me za ka iya yin bincike a kai a bautarku ta iyali ko kuma nazari na kai?
16 Shin muna ɗaukan lokaci a kai a kai don mu yi tunani a kan abubuwan da ƙugiyar Jehobah take yi? Wasu suna yin amfani da lokacin bautarsu ta iyali ko nazari na kai don yin bincike a kan ƙungiyar Jehobah, kuma suna yin bimbini sosai. Alal misali, za ka iya nazari a kan wahayin da aka saukar wa Ishaya da Ezekiyel da Daniyel da kuma Yohanna. Wannan littafin Jehovah’s Witnesses —Proclaimers of God’s Kingdom da kuma wasu littattafai ko kuma su Dibidi na Hausa, suna koya mana abubuwa da yawa game da ƙugiyar Jehobah.
17, 18. (a) Ta yaya ka amfana daga wannan talifin? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata ka yi wa kanka?
17 Yin bimbini a kan abin da Jehobah yake cim ma ta ƙungiyarsa zai taimaka mana. Kamar ƙungiyar Jehobah, ya kamata mu mai da hankali ga mafifitan al’amura. Yin hakan zai sa mu kasance da ra’ayin manzo Bulus, wanda ya ce: “Da ya ke fa muna da wannan hidima, kamar yadda muka sami jinƙai, ba mu yi yaushi ba.” (2 Kor. 4:1) Ya kuma ƙarfafa ’yan’uwansa cewa: “Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.”—Gal. 6:9.
18 Shin kai da iyalinka kuna bukatar ku yi wasu canje-canje ne domin ku saka mafifitan al’amura farko? Za ka iya sauƙaƙa salon rayuwanka don ka daɗa ƙwazo a aikin wa’azi? A talifi na gaba, za mu tattauna abubuwa biyar da za su taimaka mana mu bi misalin ƙungiyar Jehobah, kuma mu ci gaba da yin ƙwazo a hidimar Allah.