Za Ku Zama “Mulki na Firistoci”
“Za ku zama mulki na firistoci a gare ni, al’umma mai-tsarki.”—FIT. 19:6.
1, 2. Wace kāriya ce zuriyar macen take bukata, kuma me ya sa?
ANNABCI na farko da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu fahimci yadda nufin Jehobah yake cika. Sa’ad da Allah ya yi alkawari a cikin Adnin, ya ce: “Tsakaninka [Shaiɗan] da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta.” Magabtakar za ta yi tsanani sosai. Jehobah ya ce: “Shi [zuriyar matar] za ya ƙuje kanka [Shaiɗan], kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Far. 3:15) Magabtakar da ke tsakanin macijin da matar za ta yi tsanani sosai kuma Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa don ya halaka zuriyarta.
2 Shi ya sa marubucin zabura ya yi addu’a game da mutanen Allah, ya ce: “Ga shi, abokan gābanka suna hargowa: Maƙiyanka sun tada kai. Suna yi ma mutanenka makirci, suna gangama shawara a kan ɓoyayyunka. Sun ce, mu zo, mu datse su, kasancewarsu al’umma ta ƙare.” (Zab. 83:2-4) Saboda haka, wajibi ne a kāre zuriyar don kada Shaiɗan ya halaka kuma ya ɓata iyalin da wannan zuriyar za ta fito daga ciki. Don a cim ma hakan, Jehobah ya yi yarjejeniyoyi da za su tabbatar da cikar nufinsa.
ALKAWARIN DA YA KĀRE ZURIYAR
3, 4. (a) Yaushe aka soma bin sharuɗan alkawari bisa Doka, kuma mene ne Al’ummar Isra’ila ta amince za ta yi? (b) An yi alkawari bisa Doka don ya hana gurɓacewar mene ne?
3 Bayan da iyalan Ibrahim da Ishaku da Yakubu suka ƙaru sosai, sai Jehobah ya mai da su al’umma, wannan ita ce Isra’ila ta dā. Jehobah ya yi yarjejeniya da su kuma ya ba su Doka ta hannun Musa, kuma al’ummar Isra’ila ta yarda ta yi biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Musa] ya ɗauki litafin alkawari, ya karanta a kunnuwan mutane: su kuma suka ce, Dukan abin da Ubangiji ya faɗi mu a yi, mu yi biyayya.’ Kuma Musa ya ɗauki jinin, [shanun hadayar] ya yayyafa bisa mutane, ya ce, Ga jinin alkawarin, wanda Ubangiji ya yi da ku a bisa dukan waɗannan zantattuka.”—Fit. 24:3-8.
4 Al’ummar ta soma bin sharuɗan alkawarin, wato alkawari bisa Dokar da aka ba da ta hannun Musa a Dutsen Sinai a shekara ta 1513 kafin zamaninmu. Ta wurin wannan alkawarin ne aka keɓe Isra’ila ta dā a matsayin al’ummar da Allah ya zaɓa. A lokacin ne Jehobah ya zama ‘Mai-mulkinsu . . . Mai-ba da shari’a’ da kuma ‘Sarki’ a gare su. (Isha. 33:22) Tarihin al’ummar Isra’ila ya nuna abin da yake iya faruwa idan an bi dokokin Allah da kuma idan an yi banza da su. Tun da Dokar ta hana auren arna da kuma saka hannu a bautar ƙarya, hakan ya nuna cewa an tsara Dokar don ta hana gurɓacewar zuriyar Ibrahim.—Fit. 20:4-6; 34:12-16.
5. (a) Alkawari bisa Doka ya ba wa Isra’ilawa wace dama? (b) Me ya sa Allah ya yi watsi da al’ummar Isra’ila?
5 Alkawari bisa Doka ya tanadar da tsarin naɗa firistoci, kuma hakan ya yi nuni ga wani tsari mai muhimmanci da zai biyo baya. (Ibran. 7:11; 10:1) Ta wajen alkawarin, Isra’ilawa sun sami dama da kuma gatan kasancewa “mulki na firistoci” idan suka ci gaba da bin dokokin Jehobah. (Karanta Fitowa 19:5, 6.) Amma, Isra’ila ba ta cika wannan sharaɗin ba. A maimakon al’ummar ta amince da Almasihu, wanda shi ne ainihin zuriyar Ibrahim, ta yi watsi da shi. Saboda haka, Allah ya yi watsi da al’ummar.
6. Mene ne Dokar ta cim ma?
6 Da yake al’ummar Isra’ila ta ƙi kasancewa da aminci ga Jehobah, ba ta tanadar da mulki na firistoci ba. Amma hakan ba ya nufin cewa Dokar tana da aibi. Dokar ta kāre zuriyar kuma ta sa mutane su san ko wane ne Almasihu. Ƙari ga haka, Dokar ta cika aikinta sa’ad da aka san cewa Yesu shi ne Almasihu ko kuma Kristi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kristi matuƙar shari’a” ne. (Rom. 10:4) Duk da haka, akwai wata tambaya da ta rage: Su wane ne za su sami gatan kasancewa mulki na firistoci? Jehobah Allah ya yi wata yarjejeniya na tsara wata sabuwar al’umma.
AN KAFA SABUWAR AL’UMMA
7. Wane annabci game da sabon alkawari ne Jehobah ya hure Irmiya ya yi?
7 Kafin a daina amfani da alkawari bisa Doka, Jehobah ya yi annabci ta wurin annabi Irmiya cewa zai yi wani “sabon alkawari” da al’ummar Isra’ila. (Karanta Irmiya 31:31-33.) Wannan sabon alkawarin ba kamar alkawari bisa Doka ba don ba za a bukaci hadayar dabbobi kafin a gafarta zunubai ba. Ta yaya hakan zai yiwu?
8, 9. (a) Mene ne aka cim ma da jinin hadayar Yesu? (b) Wace dama ce waɗanda suke cikin sabon alkawarin suka samu? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)
8 Ƙarnuka bayan haka, Yesu ya ƙaddamar da Jibin Maraice na Ubangiji a ranar 14 ga Nisan a shekara ta 33 kafin zamaninmu. Sa’ad da Yesu yake magana ga manzanninsa guda 11 game da ƙoƙon ruwan inabi, ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” (Luk 22:20) Bisa ga Linjilar Matta, Yesu ya ce: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane da yawa zuwa gafarar zunubai.”—Mat. 26:27, 28.
9 Jinin hadayar Yesu ya tabbatar da sabon alkawarin. Jinin ya sa Allah ya gafarta mana zunubanmu har abada. Yesu ba ya cikin waɗanda suka yi sabon alkawarin don shi ba mai zunubi ba ne. Amma Allah zai iya amfani da jinin hadayar wajen taimaka wa ’yan Adam. Ƙari ga haka, jinin ya ba wasu damar kasancewa “’ya’yan” Allah sa’ad da ya shafa su da ruhu mai tsarki. (Karanta Romawa 8:14-17.) Za su kasance marasa zunubi a gaban Allah kamar Ɗansa Yesu, marar zunubi. Waɗannan da aka shafa za su zama “masu-tarayyan gādo da Kristi” kuma za su sami damar zama “mulki na firistoci.” Wannan gatan ne al’ummar Isra’ila ta rasa. Manzo Bitrus ya yi magana game da “masu-tarayyan gādo da Kristi,” ya ce: “Ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.” (1 Bit. 2:9) Babu shakka, wannan sabon alkawarin yana da muhimmanci! Ya ba almajiran Yesu damar zama sauran waɗanda suka ƙunshi zuriyar Ibrahim.
SABON ALKAWARIN YA SOMA AIKI
10. Yaushe ne aka soma amfani da sabon alkawari, kuma me ya sa aka jira sai lokacin?
10 Yaushe ne aka soma amfani da sabon alkawari? Ba a lokacin da Yesu ya yi maganarsa a Jibin Maraice na Ubangiji ba. Wajibi ne Yesu ya zub da jininsa kuma ya koma sama don ya nuna wa Jehobah amfanin hadayar kafin alkawarin ya soma ci. Ƙari ga haka, ana bukatar ruhu mai tsarki ya sauko a kan “masu-tarayyan gādo da Kristi.” Saboda haka, sabon alkawarin ya soma aiki ne a Fentakos ta shekara ta 33 a lokacin da aka shafa amintattun almajiran Yesu da ruhu mai tsarki.
11. Ta yaya sabon alkawarin ya ba wa Yahudawa da mutanen Al’ummai damar kasancewa cikin Isra’ila na Allah kuma mutane nawa ne sabon alkawarin zai shafa?
11 Ko da yake alkawari bisa Doka ya zama “daɗaɗe,” wato ya daina inganci sa’ad da Jehobah ya hure Irmiya ya annabta cewa zai ƙulla sabon alkawari da al’ummar Isra’ila, amma ba a daina amfani da shi ba sai lokacin da aka soma aiki da sabon alkawari. (Ibran. 8:13) Sa’ad da hakan ya faru, sai Allah ya ba wa Yahudawa masu bi da ’yan al’umma masu bi zarafi ɗaya, da yake “kaciya kuwa ta zuciya ce, cikin ruhu, ba cikin harufa ba.” (Rom. 2:29) Ta wajen wannan sabon alkawarin, Allah zai saka dokarsa “a cikin hankalinsu” kuma a “bisa zuciyarsu [zai] rubuta su.” (Ibran. 8:10) Adadin waɗanda suke cikin wannan sabon alkawarin zai zama 144,000, kuma za su zama sabuwar al’ummar, wato “Isra’ila na Allah.”—Gal. 6:16; R. Yoh. 14:1, 4.
12. Mene ne bambanci da kuma alaƙa da ke tsakanin alkawari bisa Doka da kuma sabon alkawari?
12 Mene ne alaƙa da kuma bambancin da ke tsakanin alkawari bisa Doka da sabon alkawari? Alkawari bisa Doka yarjejeniya ce tsakanin Jehobah da al’ummar Isra’ila, amma sabon alkawari tsakanin Jehobah ne da Isra’ila na Allah. A alkawari na dā, Musa shi ne mai shiga tsakani, amma a sabon alkawari, Yesu ne Mai shiga tsakani. An kafa alkawari bisa Doka da jinin dabba ne amma an yi sabon alkawari da jinin hadayar Yesu. Kamar yadda aka tsara al’ummar Isra’ila a ƙarƙashin Alkawari bisa Doka, an tsara waɗanda suke cikin sabon alkawari a ƙarƙashin Yesu wanda shi ne Shugaban ikilisiya.—Afis. 1:22.
13, 14. (a) Ta yaya sabon alkawari ya shafi Mulkin? (b) Mene ne ake bukata kafin waɗanda ke cikin Isra’ila na Allah su yi mulki tare da Kristi a sama?
13 Sabon alkawari yana da alaƙa da Mulkin don ya haifar da al’umma mai tsarki kuma waɗanda suke cikin wannan al’ummar sun sami gatan zama sarakuna da firistoci a Mulkin sama. Su ne waɗanda suka ƙunshi sauran zuriyar Ibrahim. (Gal. 3:29) Saboda haka, wannan sabon alkawarin ya tabbatar da cikar alkawarin da aka yi da Ibrahim.
14 Sabon alkawari ya haifar da Isra’ila na Allah kuma ya ba waɗanda ke cikin wannan al’ummar gatan zama “masu-tarayyan gādo da Kristi.” Amma kafin su yi mulki tare da Yesu a matsayin sarakuna da firistoci a sama, ana bukatar a yi wani alkawari don tabbatar da hakan. Wane alkawari ne wannan?
ALKAWARIN DA YA BA WASU DAMAR YIN SARAUTA DA KRISTI
15. Wane alkawari ne Yesu ya yi da amintattun almajiransa?
15 Bayan Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji, ya yi wani alkawari da amintattun almajiransa, kuma wannan shi ne alkawari na Mulki. (Karanta Luka 22:28-30.) Wannan alkawarin ba kamar sauran ba don bai shafi Jehobah ba, alkawari ne da Yesu ya yi da almajiransa kawai. Sa’ad da Yesu ya ce: “Kamar yadda Ubana ya sanya mani,” babu shakka yana nuni ne ga alkawarin da Jehobah ya yi da shi na zama ‘firist . . . har abada bisa ɗabi’ar’ Melchizedek.—Ibran. 5:5, 6.
16. Mene ne alkawari na Mulki ya tabbatar wa shafaffun Kiristoci?
16 Amintattun manzannin Yesu guda 11 sun ‘lizimce shi a cikin ƙuncinsa.’ Alkawari na Mulki ya tabbatar musu cewa za su kasance tare da shi a sama don su yi sarauta da kuma hidima a matsayin firistoci. Amma ba su kaɗai ne ke da wannan gatan ba. Sa’ad da Yesu ya koma sama, ya bayyana ga manzo Yohanna a wahayi cewa: “Wanda ya yi nasara, zan ba shi zaman tare da ni cikin kursiyina, kamar yadda ni kuma na yi nasara, na zauna kuma tare da Ubana cikin nasa kursiyi.” (R. Yoh. 3:21) Saboda haka, an yi alkawari na Mulki da shafaffun Kiristoci 144,000 ne. (R. Yoh. 5:9, 10; 7:4) Wannan alkawarin ne ya tabbatar cewa za su yi sarauta tare da Yesu a sama. Za mu iya kwatanta matsayinsu da macen da za ta auri sarki kuma ta sami gatan yin sarauta tare da shi. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shafaffun Kiristoci a matsayin ‘amaryar’ Kristi da kuma “budurwa mai-tsabta” da aka yi mata alkawarin aure da Kristi.—R. Yoh. 19:7, 8; 21:9; 2 Kor. 11:2.
KA BA DA GASKIYA SOSAI GA MULKIN ALLAH
17, 18. (a) Ka ɗan bayyana alkawura guda shida da muka tattauna da suke da alaƙa da Mulkin. (b) Me ya sa ya kamata mu kasance da bangaskiya sosai ga Mulkin?
17 Dukan waɗannan alkawura da muka tattauna suna da alaƙa da wasu sassa na Mulkin Almasihu. (Ka duba jadawalin nan “Yadda Allah Zai Cim ma Nufinsa.”) Hakan ya nuna cewa an kafa Mulkin bisa yarjejeniyoyi. Saboda haka, muna da kwararan dalilai na dogara ga Mulkin Almasihu a matsayin abin da Allah zai yi amfani da shi wajen cim ma ainihin nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam.—R. Yoh. 11:15.
18 Babu shakka, abubuwan da Mulkin zai cim ma za su amfani ’yan Adam har abada, ko ba haka ba? Saboda haka, bari mu yi wa’azi da himma cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan Adam!—Mat. 24:14.