Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 p. 32
  • Sa’ad Da Aka Rairaye Kiristoci Kamar Alkama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sa’ad Da Aka Rairaye Kiristoci Kamar Alkama
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 p. 32

Sa’ad Da Aka Rairaye Kiristoci Kamar Alkama

KAFIN mutuwarsa, Yesu ya gargaɗi almajiransa: “Ga Shaiɗan ya roƙa ya same ku, domin shi rairaye ku kamar alkama.” (Luk 22:31) Menene yake nufi?

A zamanin Yesu, girbe alkama na ɗaukan dogon lokaci da kuma aiki tuƙuru. Da farko, masu girbin za su je su yanko alkamar daga gona. Bayan haka, za su bugi alkamar ko kuwa su yi amfani da wata na’urar sussuka da dabbobi suke ja don su cire alkamar. Wannan ne ke cire hatsin daga karan da kuma ɓawon. Bayan haka, sai manoman su je su sheƙa ta. Ainihin hatsin zai faɗi ƙasa yayin da iska zai ɗauke ɓawon. A ƙarshe, sai a rairaye duk dattin da ke cikin hatsin.

Kamar yadda Yesu ya faɗa, sau da yawa Shaiɗan ya kai wa almajiran Yesu hari a wannan lokacin, hakazalika, a yau ma yana kawo mana hari. (Afis. 6:11) Mun yarda cewa ba dukan matsalolin da muke fuskanta a rayuwa ba ne Shaiɗan yake jawowa. (M. Wa. 9:11) Duk da haka, Shaiɗan yana son ya yi amfani da duk wata dabarar da yake da ita don ya karya amincinmu. Alal misali, yana iya jarraba mu mu nemi abin duniya, mu zaɓi nishaɗi marar kyau, ko kuwa mu yi lalata. Yana iya yin amfani da abokanmu a makaranta ko a wurin aiki da kuma ’yan’uwanmu da ba masu bi ba ne su matsa mana mu biɗi duk wani abin da wannan duniyar za ta iya ba da a makaranta da wajen aiki. Bugu da ƙari, Shaiɗan yana iya yin amfani da tsanantawa na kai tsaye don ya karya amincinmu ga Allah. Babu shakka, akwai hanyoyi masu yawa da Shaiɗan yake amfani da su a alamance don ya rairaye mu.

Ta yaya za mu iya yin tsayayya da wannan maƙiyin mai ƙarfi? Ba za mu iya yin hakan da ƙarfinmu ba. Shaiɗan ya fi mu ƙarfi, amma mun san cewa Jehobah ya fi Shaiɗan ƙarfi nesa ba kusa ba. Idan muka dogara ga Jehobah sosai, muka roƙe shi ya ba mu hikima da gaba gaɗi don jimrewa, kuma muka dogara ga ja-gorarsa, zai ƙarfafa mu mu yi tsayayya da hare-haren Shaiɗan.—Zab. 25:4, 5.

Sa’ad da muke fuskantar gwaji, muna bukatar mu iya bambanta “nagarta da mugunta” kuma mu guji rinjayar makidodin Shaiɗan. (Ibran. 5:13, 14) Jehobah zai iya taimaka mana mu sami wannan iyawar. Bayan haka, muna bukatar mu manne wa tafarki na gaskiya, ko da menene zai faru. Idan muka bi ja-gorar Jehobah, babu shakka, zai tallafa wa ƙudurin da muka yi na yin abin da ya dace.—Afis. 6:10.

Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya rairaye mu kamar alkama. Amma da ikon Jehobah, za mu iya yin tsayayya da shi, kuma mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi. (1 Bit. 5:9) Hakika, Kalmar Jehobah ta ba mu tabbaci cewa: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—Yaƙ. 4:7.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba