Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 2/1 pp. 21-26
  • “Kuna Da Ƙauna Ga Junanku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kuna Da Ƙauna Ga Junanku”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Yalwata Gaba Gaba”
  • Tunkiya da ta Ɓata da Kuma Kuɗin Azurfa da Ya Ɓata
  • Ta Ɓata Amma Tana da Daraja
  • Ku Fita Nema
  • Ka Kasance Mai Laushin Hali
  • Ka Kasance da Ƙwazo
  • ‘Ni da Kaina Zan Nemi Tumakina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • “Mu Taimaki Marasa Karfi”
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • “Ku Juyo Gare Ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Inda Za Ka Sami Ta’aziyya
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 2/1 pp. 21-26

“Kuna Da Ƙauna Ga Junanku”

“Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—YOHANNA 13:35.

1. Wane hali ne Yesu ya yi nanaci a kai ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa?

“’YA’YA ƙanƙanana.” (Yohanna 13:33) Yesu ya kira manzanninsa da wannan furci mai daɗi a maraicen da zai mutu. Ba mu ga inda Yesu ya yi amfani da wannan furcin ba kafin wannan lokaci a cikin Linjila a magana da su. A wannan dare na musamman, ya motsa ya yi amfani da wannan furcin ya nuna zurfin ƙaunar da yake da ita ga mabiyansa. Yesu ya yi maganar ƙauna sau 30 a wannan dare. Me ya sa ya yi nanaci haka a kan wannan hali?

2. Me ya sa nuna ƙauna take da muhimmanci ga Kiristoci?

2 Yesu ya yi bayanin abin da ya sa ƙauna take da muhimmanci haka. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35; 15:12, 17) Zama mabiyin Kristi yana da nasaba ta kusa da ƙaunar ’yan’uwa. Ana bambance Kiristoci na gaskiya ba ta wurin irin tufafi da suke sakawa ba ko kuma ta wata al’ada da ta bambanta, amma ta wajen ƙauna da suke nuna wa juna. Kasancewa da irin wannan ƙauna ta musamman ta biyu ce cikin abubuwa uku da ake bukata daga almajirin Kristi da aka ambata a talifin da ya gabata. Menene zai taimake mu mu ci gaba da cika wannan bukata?

“Ku Yalwata Gaba Gaba”

3. Wane gargaɗi game da ƙauna manzo Bulus ya yi?

3 Kamar yadda take a tsakanin mabiyan Kristi a ƙarni na farko, wannan ƙauna ta musamman ana iya lura da ita a tsakanin almajiran Kristi na gaskiya a yau. Zuwa ga Kiristoci na ƙarni na farko manzo Bulus ya rubuta: “A kan zancen ƙauna ga ’yan’uwa ba ku bukata a rubuta muku ba: gama ku da kanku koyayyu ne na Allah ku ƙaunaci junanku; hakika fa kuna yin haka ga dukan ’yan’uwa.” Duk da haka, Bulus ya daɗa gargaɗi: “Ku yalwata gaba gaba.” (1 Tassalunikawa 3:12; 4:9, 4:10) Mu ma muna bukatar mu bi gargaɗin Bulus mu “yalwata gaba gaba” wajen nuna ƙauna ga juna.

4. In ji Bulus da kuma Yesu, ga su waye ya kamata mu mai da hankali musamman?

4 A cikin wasiƙarsa da aka hore, Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwa masu bi su “ƙarfafa masu-raunanan zukata,” kuma su “tokare marasa-ƙarfi.” (1 Tassalunikawa 5:14) A wani lokaci kuma ya tunasar da Kiristoci cewa waɗanda “ke ƙarfafa ya wajaba [s]u ɗauki kumamancin raunana.” (Romawa 15:1) Yesu ma ya ba da umurni game da taimakon waɗanda suka raunana. Bayan ya annabta cewa a daren da za a kama shi Bitrus zai guje shi, Yesu ya gaya wa Bitrus: “Kai ma lokacin da ka sāke juyowa, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” Me ya sa? Domin su ma za su guji Yesu saboda haka za su bukaci taimako. (Luka 22:32; Yohanna 21:15-17) Saboda haka, Kalmar Allah ta umurce mu mu miƙa ƙaunarmu ga waɗanda suka raunana a ruhaniya da kuma waɗanda suka daina tarayya da ikilisiyar Kirista. (Ibraniyawa 12:12) Me ya sa za mu yi haka? Misalai biyu da Yesu ya bayar sun amsa wannan tambayar.

Tunkiya da ta Ɓata da Kuma Kuɗin Azurfa da Ya Ɓata

5, 6. (a) Waɗanne gajerun misalai biyu ne Yesu ya bayar? (b) Menene waɗannan misalai suka bayyana game da Jehovah?

5 Domin ya koya wa masu sauraronsa yadda Jehovah yake ɗaukan waɗanda suka bauɗe, Yesu ya ba da gajerun misalai biyu. Na farko, game da makiyayi ne. Yesu ya ce: “Wane mutum a cikinku, kadan yana da tumaki ɗari, ɗaya a cikinsu ta ɓace masa, ba za ya bar casa’in da taran nan a cikin jeji ba, ya je neman abin da ya ɓace har ya samu? Sa’anda ya same ta, ya ɗibiya ta bisa kafaɗunsa, yana murna. Sa’anda ya isa gida, ya kirawo abokansa da maƙwabtansa, ya tara su, ya ce musu, Ku yi murna tare da ni, gama na sami tunkiyata wadda ta ɓace. Ina ce muku, hakanan kuma za a yi murna cikin sama bisa mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba, ta fi ta bisa mutum casa’in da tara masu-adalci waɗanda ba su da bukatar tuba ba.”—Luka 15:4-7.

6 Misali na biyu game da wata mace ce. Yesu ya ce: “Ina mace wadda tana da azurfa goma, kadan ɗaya ta ɓace mata, ba za ta kunna fitila ba, ta share gida, ta nema da aniya har ta samu? Sa’anda ta samu, sai ta kirawo abokanta da maƙwabtanta, ta tara su, ta ce, Ku yi murna tare da ni, gama na sami ɗayan da ta ɓace mini. Hakanan kuma, ina ce muku, akwai murna a wurin mala’ikun Allah a kan mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba.”—Luka 15:8-10.

7. Waɗanne darussa biyu ne waɗannan misalai na tunkiya da ta ɓata da kuɗin azurfa da ya ɓata suka ƙunsa?

7 Menene za mu koya daga waɗannan gajerun misalai? Na (1) sun nuna mana yadda ya kamata mu ji game da waɗanda suka raunana, na (2) abin da ya kamata mu yi domin mu taimake su. Bari mu bincika waɗannan batutuwa.

Ta Ɓata Amma Tana da Daraja

8. (a) Menene makiyayi da matar suka yi domin abin su da ya ɓata? (b) Menene abin da suka yi ya gaya mana game da yadda suke ji game da abin da suka mallaka?

8 A dukan misalan biyu da akwai abin da ya ɓata, amma ka lura da abin da masu shi suka yi. Makiyayin bai ce: ‘Me ake yi da tunkiya ɗaya, ga shi ina da 99? Zan yi tafiyata ko babu ita.’ Matar ba ta ce ba: ‘Me ya sa zan damu domin azurfa ɗaya? Tara da nake da su sun ishe ni.’ Maimakon haka, makiyayin ya nemi tunkiyar kamar ita ɗaya tak yake da ita. Kuma matar ta ji zafin ɓacewar kuɗin azurfar da kamar ɗaya tak take da shi. A dukan misalan biyu abin da ya ɓata ya kasance da tamani a zukatan masu su. Menene wannan ya nuna?

9. Menene damuwa na makiyayi da kuma matar ta nuna?

9 Ka lura da yadda Yesu ya kammala a yanayi biyun: “Hakanan kuma za a yi murna cikin sama bisa mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba,” da cewa “hakanan kuma, ina ce muku, akwai murna a wurin mala’ikun Allah a kan mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba.” Saboda haka, damuwar makiyayin da ta matar ta nuna a ƙaramar hanya yadda Jehovah da halittunsa na sama suke ji. Kamar yadda abin da ya ɓata ya kasance da tamani a wurin makiyayin da kuma matar, haka nan waɗanda suka bauɗe daga mutanen Allah har ila suna da tamani a wurin Jehovah. (Irmiya 31:3) Ƙila irin waɗannan mutanen sun raunana a ruhaniya ne, ba lallai ne cewa su ’yan tawaye ba. Duk da raunana da suka yi, zai yiwu suna nan suna kiyaye wasu umurnin Jehovah. (Zabura 119:176; Ayukan Manzanni 15:29) Shi ya sa, a lokaci da ya shige, Jehovah ba ya hanzarin “ya taɓadda su daga gareshi.”—2 Sarakuna 13:23.

10, 11. (a) Yaya muke so mu ɗauki waɗanda suka bauɗe daga ikilisiya? (b) In ji misalai biyu na Yesu, ta yaya za mu nuna damuwarmu?

10 Kamar Jehovah da Yesu, mu ma muna damuwa ƙwarai da waɗanda suka raunana kuma ba sa zuwa ikilisiya ta Kirista. (Ezekiel 34:16; Luka 19:10) Muna ɗaukan mutumin da ya raunana kamar tunkiya da ta ɓata—ba wanda aka tsine wa ba. Ba ma tunanin cewa: ‘Me ya sa za a damu da wanda ya raunana? Ba tare da shi ba ikilisiya ai tana cin gaba da kyau.’ Maimakon haka, kamar Jehovah, muna ɗaukan waɗanda suka bauɗe amma da suke so su komo da tamani.

11 Amma, ta yaya za mu iya nuna cewa mun damu? Misalai biyu na Yesu sun nuna cewa za mu iya yin haka (1) ta wajen fita nema, (2) ta wajen kasancewa da ƙauna da kuma kirki, kuma na (3) ta wajen kasancewa da ƙwazo. Bari mu bincika waɗannan da ɗai-ɗai.

Ku Fita Nema

12. Menene kalmomin nan “ya je neman abin da ya ɓace” suke gaya mana game da halin makiyayin?

12 A misali na farko, Yesu ya ce makiyayin ya “je neman abin da ya ɓace.” Makiyayin ne da farko ya fita neman tunkiya da ta ɓace. Wahala, haɗari, da kuma nisan wurin ba su hana shi ba. Makiyayin ya nace “har ya samu.”—Luka 15:4.

13. Ta yaya mutanen dā masu aminci suka mai da hankali ga bukatun waɗanda suka raunana, kuma ta yaya za mu bi irin wannan misali na Littafi Mai Tsarki?

13 Hakazalika, taimakon mutumin da yake bukatar ƙarfafa sau da yawa na bukatar mai ƙarfi, shi zai fara zuwa ba da taimako. Mutanen dā masu aminci sun fahimci haka. Alal misali, sa’ad da Jonathan, ɗan Sarki Saul, ya lura cewa amininsa Dauda yana bukatar ƙarfafa, Jonathan “ya tashi, ya tafi wurin Dauda cikin kurmin, ya ƙarfafa hannunsa cikin Allah.” (1 Samu’ila 23:15, 16) Ƙarnuka bayan haka, sa’ad da Gwamna Nehemiah ya ga cewa wasu ’yan’uwansa Yahudawa sun raunana, shi ma ya ‘tashi nan da nan’ ya ƙarfafa su ‘su tuna da Jehovah.’ (Nehemiah 4:14) Mu ma a yau za mu so mu “tashi”—mu fita nema—domin mu ƙarfafa waɗanda suka raunana. Amma waye a cikin ikilisiya ya kamata ya yi haka?

14. Su wa a cikin ikilisiyar Kirista ya kamata su taimaki waɗanda suka raunana?

14 Dattawa Kiristoci musamman suke da hakkin su “ƙarfafa hannuwa marasa-ƙarfi, [s]u ƙarfafa raunanan guwawu” kuma su ce wa “waɗanda ke da zuciya mai-tsoro . . . Ku Ƙarfafa, kada ku ji tsoro.” (Ishaya 35:3, 4; 1 Bitrus 5:1, 2) Amma, ku lura cewa shawarar Bulus “ku ƙarfafa masu-raunanan zukata,” da kuma “ku tokare marasa-ƙarfi” ba ga dattawa ba kawai aka bayar. Maimakon haka, kalmomin Bulus domin dukan “ikilisiya ta Tassalunikawa” ce. (1 Tassalunikawa 1:1; 5:14) Saboda haka, taimakon waɗanda suka raunana aikin dukan Kiristoci ne. Kamar makiyayi na misalin, ya kamata kowanne Kirista ya fita “neman abin da ya ɓace.” Hakika, za a yi wannan a hanya mafi kyau tare da ba da haɗin kai ga dattawa. Za ka iya yin wani abu ka taimaka wa wanda ya raunana a ikilisiyarku?

Ka Kasance Mai Laushin Hali

15. Me ya sa makiyayin ya aikata yadda ya yi?

15 Menene makiyayin ya yi sa’ad da ya sami tunkiya da ta ɓata? “Ya ɗibiya ta bisa kafaɗunsa.” (Luka 15:5) Lallai wannan ya ƙara ba da bayani mai kyau ƙwarai! Tunkiyar ƙila ta yi ta yawo dare da rana a wuraren da ba ta sani ba, ƙila ma ta fuskanci haɗarin haɗuwa da zakuna. (Ayuba 38:39, 40) Babu shakka tunkiyar ta raunana saboda rashin abinci. Ta raunana ƙwarai da ba ta da ƙarfin da za ta guje wa cikas da za ta fuskanta a hanyarta ta komowa garke. Saboda haka, makiyayin ya sunkuya, ya ɗauki tunkiyar a hankali, ya ɗauke ta ya mai da ita garke duk da cikas da ta fuskanta. Ta yaya za mu nuna irin ƙauna da makiyayin nan ya nuna?

16. Ta yaya za mu nuna ƙauna da makiyayi ya nuna ga tunkiyar da ta bauɗe?

16 Mutumin da ya daina saduwa da ikilisiya zai gaji a ruhaniya. Kamar tunkiya da ta rabu da makiyayi, irin wannan mutumin wataƙila ya yi ta yawo a cikin wurare masu haɗari na wannan duniyar. Babu kāriya daga garke, ikilisiyar Kiristoci, ya fuskanci farmakin Iblis fiye da dā, wanda yake “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Bugu da ƙari, ya raunana domin rashin abinci na ruhaniya. Saboda haka, ba tare da taimako ba mai yiwuwa ya raunana ƙwarai ya guje wa cikas da zai fuskanta a hanyarsa ta komo ikilisiya. Saboda haka, muna bukata kamar dai a ce mu sunkuya, mu ɗauki wannan raunanne, mu dawo da shi. (Galatiyawa 6:2) Ta yaya za mu cim ma wannan?

17. Ta yaya za mu yi koyi da manzo Bulus sa’ad da muka ziyarci mutumin da ya raunana?

17 Manzo Bulus ya ce: “Wanene rarrauna, ni ban zama rarrauna kuwa?” (2 Korinthiyawa 11:29; 1 Korinthiyawa 9:22) Bulus yana da juyayin mutane, haɗe da waɗanda suka raunana. Ya kamata mu ma mu riƙa nuna irin wannan juyayi ga waɗanda suka raunana. Sa’ad da ka ziyarci Kirista da ya raunana, ka ƙarfafa shi cewa yana da muhimmanci a idanun Jehovah kuma ’yan’uwa Shaidu suna rashinsa ƙwarai. (1 Tassalunikawa 2:17) Ka sanar da shi cewa suna shirye su tallafa masa kuma suna shirye su kasance wajensa “ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” (Misalai 17:17; Zabura 34:18) Furcinmu na ƙauna zai ƙarfafa shi ya motsa shi ya koma cikin garke. Menene za mu yi daga nan? Misalin mace da kuɗin azurfarta da ta ɓace za ta yi mana ja-gora.

Ka Kasance da Ƙwazo

18. (a) Me ya sa matar da take cikin misali ba ta sallamar ba? (b) Wane ƙoƙari matar ta yi, kuma menene sakamakon haka?

18 Matar da kuɗin azurfarta ta ɓace ta sani cewa yanayin yana da wuya amma babu dalilin sallamawa. Da kuɗin azurfar ta faɗi cikin kurmi ne ko kuma cikin fadama, ƙila sai ta sallama ta ce ba za a iya samu ba. Amma, da yake ta sani cewa kuɗin azurfar tana wani wuri a cikin gidanta, wurin da za ta iya samu, sai ta fara nema da ƙwazo. (Luka 15:8) Da farko ta kunna fitila ta haskaka gidanta mai duhu. Sa’an nan ta share daben ɗakinta, tana begen za ta ji ƙararta. A ƙarshe, ta bincika dukan wani lungu a hankali da fitila har sai da fitilar ta haskaka kuɗin azurfar. Ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu!

19. Waɗanne darussa don taimakon wanda ya raunana za mu iya koya daga abin da matar misalin kuɗin azurfa da ta ɓace ta yi?

19 Kamar yadda bayanin wannan misalin ya bayyana mana, hakki na Kirista daga Nassi na a taimaki wanda ya raunana bai fi ƙarfinmu ba. Amma kuma, mun fahimci cewa yana bukatar ƙwazo. Tun da ma, manzo Bulus ya gaya wa dattawan Afisus: “Da wahalar kanku hakanan ya kamata ku taimaki marasa-ƙarfi.” (Ayukan Manzanni 20:35a) Ka tuna cewa matar ba ta sami kuɗin azurfar ta wajen duba nan da can ba kawai, ko kuma domin ta yi sa’a. A’a, ta yi nasara ne domin ta bincika da kyau “har ta samu.” Hakazalika, sa’ad da muke ƙoƙarin mu taimaki mutumin da ya raunana a ruhaniya, hanyar da muka bi ta kamata ta kasance da dalili da kuma ma’ana. Menene za mu iya yi?

20. Menene za a iya yi domin a taimaki waɗanda suka raunana?

20 Ta yaya za mu iya taimakon wanda ya raunana ya gina bangaskiya da kuma godiya? Nazarin Littafi Mai Tsarki cikin littattafan Kirista da ya dace ƙila abin da ake bukata ke nan kawai. Hakika, yin nazari da wanda ya raunana zai sa mu taimake shi a hanyar da ta dace kuma da take daidai. Wataƙila shugaban hidima zai iya sanin wanda zai iya ba da taimako da ake bukata. Zai iya ba da shawarar darussa da za a yi nazari da shi da kuma littafin da zai fi ba da taimako. Kamar yadda matar a misalin ta cika aikinta ta wurin amfani da abubuwa da suka dace, haka a yau muna da abubuwa da suka dace, da za mu cika hakkin da Allah ya ba mu domin mu taimake waɗanda suka raunana. Biyu cikin sababbin kayayyakin aikinmu, ko kuma littattafai, za su taimaka wajen wannan aikin. Su ne littattafan nan Ka Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya da kuma Ka Kusaci Jehovah.a

21. Ta yaya taimakon waɗanda suka raunana yake kawo albarka ga duka?

21 Taimakon waɗanda suka raunana yana kawo albarka ga duka. Wanda aka taimaka zai yi farin cikin sake haɗa kai da abokane na gaskiya. Muna samun farin cikin da bayarwa ce kawai take kawowa. (Luka 15:6, 9; Ayukan Manzanni 20:35b) Ikilisiya baki ɗaya za ta yi girma wajen ƙauna sa’ad da kowanne ciki ya nuna ƙauna ga wasu. Fiye da duka, daraja ta tabbata ga Makiyayanmu masu ƙauna, Jehovah da Yesu, kamar yadda muradinsu su taimaki waɗanda suka raunana ya bayyana cikin bayinsu na duniya. (Zabura 72:12-14; Matta 11:28-30; 1 Korinthiyawa 11:1; Afisawa 5:1) Kyakkyawan dalili ne kuwa muke da shi na ci gaba da ‘ƙaunar juna’!

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa nuna ƙauna yake da muhimmanci ga kowannenmu?

• Me ya sa za mu yi ƙaunar waɗanda suka raunana?

• Wane darasi misalin tunkiya da ta ɓata da kuma kuɗin azurfa da ya ɓata suka koya mana?

• Menene za mu iya yi mu taimaki wanda ya raunana?

[Hotuna a shafuffuka na 24, 25]

A wajen taimakon waɗanda suka raunana, muna fita nema kuma muna da laushin hali da kuma ƙwazo

[Hoto a shafi nas4, 25]

Taimaka wa waɗanda suka raunana yana kawo albarka ga duka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba