Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
A Ina Aljannar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Take?
▪ Yesu ya yi wa wani mutum alkawari wanda ke gab da mutuwa kuma ya furta imaninsa a gare shi: “Za ka kasance tare da ni a cikin Al’janna.” (Luka 23:43, NW) A ina ne mutumin zai kasance? Aljannar za ta kasance a sama ne, a duniya, ko kuma a wani wuri dabam inda mutane suke jiran hukunci?
Kakanninmu na farko sun zauna ne a Aljanna. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ubangiji Allah kuma ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin; can kuwa ya sanya mutumin da ya sifanta. . . . Sai Ubangiji Allah ya ɗauki mutum, ya sanya shi cikin gonar Adnin domin shi aikace ta, shi tsare ta kuma.” (Farawa 2:8, 15) Sa’ad da aka fassara waɗannan kalaman zuwa Helenanci, an kira wannan gonar “aljanna.”
Kamar yadda ma’aurata za su ƙara faɗin gidansu yayin da yaransu ke ƙaruwa, haka aka so iyayenmu na farko su faɗaɗa Aljanna ta wuce Adnin yayin da iyalin mutane ke ƙaruwa. Allah ya gaya musu: “Ku mamaye duniya, ku mallake ta.”—Farawa 1:28.
Manufar Mahaliccinmu ita ce, mutane su zauna kuma su haifi yara a cikin Aljanna a nan duniya. Za su zauna ne a cikin lambu a duniya har abada ba tare da sun yi kaburbura ba. Ya kamata duniya ta zama wurin zama na dindindin ga dukan ’yan Adam. Shi ya sa abubuwan da Allah ya halitta a duniyarmu suke burge mu sosai! An halicce mu ne mu zauna a kyakkyawar duniya.
Manufar Allah ta canja ne? A’a. Jehobah ya ba mu wannan tabbacin: “Haka nan kuma maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina za ta zama: ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.” (Ishaya 55:11) Fiye da shekaru 3,000 bayan an halicci mutum, Littafi Mai Tsarki ya ce game da “Mai-sifanta duniya Mai-yinta kuma” cewa bai “halicce ta ba wofi” amma “ya kamanta ta domin wurin zama.” (Ishaya 45:18) Nufin Allah bai canja ba. Duniya za ta zama aljanna.
Wani abin sha’awa shi ne, wurare da yawa da suka yi magana game da Aljanna a cikin Littafi Mai Tsarki suna yin nuni ne ga yadda rayuwa za ta kasance a duniya. Alal misali, wani annabcin Ishaya ya ce: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu.” (Ishaya 65:21) A ina ne ake gina gidaje kuma ake yin gonaki? A ina ake cin ’ya’yan itace? A duniya ce. Misalai 2:21 ta ce dalla-dalla: “Gama masu-adalci za su zauna cikin ƙasan.”
Yesu ma ya yi magana game da aljanna a duniya. Hakika, ya yi alkawarin aljanna ta samaniya, amma mutane kaɗan ne kawai aka zaɓa domin wannan manufar. (Luka 12:32) Bayan mutuwa, ana ta da su zuwa Aljanna ta samaniya kuma su haɗu da Kristi don su yi sarauta bisa Aljanna ta duniya. (Ru’ya ta Yohanna 5:10; 14:1-3) Waɗannan abokan sarauta na samaniya za su tabbatar da cewa an shugabanci Aljanna a duniya kuma ana kula da ita bisa ga yadda Allah ya tsara.
Yesu ya san cewa hakan ne nufin Allah ga duniya. Balle ma, yana sama tare da Ubansa sa’ad da aka halicci lambun Adnin. Rayuwa a aljanna a duniya a nan gaba tana buɗe ne ga dukan mutanen da suka ba da gaskiya a yau. (Yohanna 3:16) Ga irin waɗannan mutanen, Yesu ya yi alkawari: Za ku kasance “tare da ni cikin Al’janna (Paradise).”—Luka 23:43.
[Inda Aka Ɗauko Hoto shafi na 26]
© FORGET Patrick/SAGAPHOTO.COM/Alamy