Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 pp. 20-23
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mala’ika Ya Kai Ziyara
  • Abin da Maryamu ta Gaya Wa Jibra’ilu
  • Ziyartar Alisabatu
  • Maryamu da Yusufu
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Mala’ika Ya Ziyarci Maryamu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 pp. 20-23

Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu

“Ga ni, Baiwar Ubangiji”

MARYAMU ta kalli sama, idanunta a buɗe sa’ad da baƙon ya shiga gidanta. Bai nemi ganin mahaifinta ko mahaifiyarta ba. Ita ce ya zo gani! Ta tabbata cewa ba daga Nazarat ya zo ba. Domin garin da take, ɗan ƙarami ne, kuma baƙo bai da wuyan ganewa. A ko’ina, za a gane cewa wannan baƙo ne. Ya gaida Maryamu a hanyar da ba ta saba ji ba, ya ce: “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke.”—Luka 1:28.

Da waɗannan kalaman ne Littafi Mai Tsarki ya gabatar da mu ga Maryamu, ɗiyar Heli Banazarat, da ke Galili. Littafi Mai Tsarki ya gabatar da ita ne a lokacin da za ta yanke shawarwari masu muhimmanci a rayuwarta. An riga an sanya ranar auren Maryamu da Yusufu kafinta, mutum marar arziki amma mai aminci. Saboda haka, za a iya cewa ta riga ta tsara yadda rayuwarta za ta kasance, za ta taimaka wa maigidanta Yusufu, kuma su yi renon yaransu tare. Kwaram, sai ga wannan baƙon da ya kawo mata saƙo daga Allahnta, wato, gatan da zai canja rayuwarta.

Wataƙila za ka yi mamakin jin cewa Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abubuwa masu yawa game da Maryamu ba. Ya gaya mana abubuwa kaɗan ne kawai game da yadda ta girma, da kuma halayenta, amma bai gaya mana komi ba game da kamaninta. Duk da haka, abin da Kalmar Allah ta ce game da ita ya bayyana abubuwa masu yawa.

Domin mu san Maryamu sosai, muna bukatar mu duba fiye da ra’ayoyi masu yawa da addinai dabam dabam suke ɗaukakawa game da ita. Bari mu ajiye hotuna da siffofi da aka yi na Maryamu a gefe ɗaya. Ba za mu kuma tattauna rikitaccen ilimin addini da kuma koyarwar ƙarya da suka ba wannan mata mai tawali’u manyan laƙabi ba, kamar “Mamar Allah” da kuma “Sarauniyar Sama.” Maimakon haka, bari mu mai da hankali a kan ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya bayyana. Hakan zai sa mu fahimci bangaskiyarta sosai da kuma yadda za mu yi koyi da ita.

Mala’ika Ya Kai Ziyara

Wataƙila kamar yadda ka sani, baƙon Maryamu ba mutum ba ne. Mala’ika Jibra’ilu ne. Sa’ad da ya kira Maryamu “mai-samun alheri,” sai “hankalinta ya tashi ƙwarai” domin kalamansa, kuma ta yi mamakin irin wannan gaisuwar. (Luka 1:28, 29) A wajen wanene ta sami alheri sosai? Maryamu ba ta sa ran samun alheri sosai daga wurin mutane ba. Amma mala’ikan yana magana ne game da alherin Jehobah Allah. Al’amarin ya dame ta sosai. Duk da haka, ba ta soma yin fahariyar cewa ta sami alherin Allah ba. Idan muna so mu sami alherin Allah, kuma ba ma fahariya cewa mun riga mun same shi, za mu koyi darassi mai muhimmanci da Maryamu ta koya sosai. Allah ya ƙi jinin masu girman kai, amma yana ƙauna kuma yana tallafa wa masu tawali’u da sauƙin kai.—Yaƙubu 4:6.

Maryamu tana bukatar irin wannan tawali’un, domin mala’ikan ya ba ta irin gatan da ba ta taɓa zato ba. Ya bayyana mata cewa za ta haifi ɗan da zai zama mafi muhimmanci a cikin mutane. Jibra’ilu ya ce: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yakubu har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luka 1:32, 33) Maryamu ta san alkawarin da Allah ya yi wa Dauda fiye da shekaru dubu ɗaya da suka shige, inda ya ce wani a cikin zuriyarsa zai yi sarauta har abada. (2 Samuila 7:12, 13) Wato, ɗanta zai zama Almasihun da mutanen Allah suke ta begen gani tun ƙarnuka masu yawa da suka shige!

Ƙari ga hakan, mala’ikan ya gaya mata cewa za a kira ɗanta “Ɗan Maɗaukaki.” Ta yaya mace bil’adama za ta haifi Ɗan Allah? Hakika, ta yaya Maryamu za ta iya haifar ɗa. An sa mata rana da Yusufu amma ba su yi aure ba tukuna. Hakan ya sa Maryamu ta yi wannan tambayar: “Ƙaƙa wannan za shi zama, da shi ke ban san namiji ba?” (Luka 1:34) Ka lura cewa Maryamu ba ta ji kunyar faɗin cewa ita budurwa ce ba. Akasin haka, ta ɗauki budurcinta da tamani. A yau, yawancin matasa suna ɗokin kawar da budurcinsu kuma su yi wa waɗanda ba su yi hakan ba ba’a. Wannan duniyar ta canja. Amma, Jehobah bai canja ba. (Malakai 3:6) Kamar zamanin Maryamu, Jehobah yana ɗaukan waɗanda suka manne wa mizanansa na ɗabi’a da tamani.—Ibraniyawa 13:4.

Ko da yake ita baiwar Allah ce mai aminci, Maryamu ajiza ce. Ta yaya za ta iya haihuwar ɗa kamiltacce, Ɗan Allah? Jibra’ilu ya yi bayani: “Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantadda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.” (Luka 1:35) Tsarki yana nufin abin da ke da tsabta. Da ma yara suna gadōn zunubi daga iyayensu. A wannan kuwa, Jehobah zai yi mu’ujizar da ba a taɓa yi ba. Zai mai da ran Ɗansa daga sama zuwa cikin mahaifar Maryamu kuma ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki ya “inuwantadda” Maryamu, wanda hakan zai kāre yaron daga samun zunubi. Maryamu ta gaskata da alkawarin da mala’ikan ya yi kuwa? Menene ta ce?

Abin da Maryamu ta Gaya Wa Jibra’ilu

Waɗanda suke shakkar wannan mu’ujizar tare da wasu ’yan tauhidin Kiristendom ba su yarda ba cewa budurwa za ta iya haihuwa. Duk da iliminsu, sun kasa fahimtar gaskiya marar wuya. Kamar yadda Jibra’ilu ya ce, “babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.” (Luka 1:37) Maryamu ta yarda cewa abin da Jibra’ilu ya faɗa gaskiya ne, domin ita budurwa ce mai bangaskiya sosai. Kuma wannan bangaskiyar ba makauniya ba ce. Kamar duk wani mutumi mai tunani, Maryamu tana bukatar alamun da za ta ɗora bangaskiyarta a kai. Jibra’ilu yana shirye ya daɗa ga gaskiyar da ta sani. Ya gaya mata game da ’yar’uwarta Alisabatu tsohuwa, wadda ba ta taɓa haihuwa ba. Ta hanyar mu’ujiza, Allah ya sa ta ɗauki ciki!

Menene Maryamu za ta yi? Ga aikin da aka ba ta a gabanta kuma tana da shaidar da ta tabbatar da ita cewa Allah zai yi dukan abin da Jibra’ilu ya ce. Kada mu yi zaton cewa wannan gatan bai ba ta tsoro ba, ko kuma marar wuya ne. Dalili na farko shi ne, tana bukatar ta yi tunani sosai domin an riga an sa wa ita da Yusufu rana. Ta yaya zai aure ta idan ya gane cewa ta yi ciki? Wani dalilin kuma shi ne, aikin da aka ba ta jan aiki ne. Za ta ɗauki ran halitta mafi muhimmanci cikin dukan waɗanda Allah ya halitta, wato, ƙaunataccen Ɗansa! Tana bukatar ta kula da shi sa’ad da yake jariri kuma ta kāre shi a wannan muguwar duniya. Wannan jan aiki ne!

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa maza masu ƙarfi kuma masu aminci sun yi jinkirin karɓan aiki mai wuya daga wurin Allah. Musa ya yi kukan cewa shi mai nauyin baki ne saboda haka bai cancanci zama kakakin Allah ba. (Fitowa 4:10) Irmiya ya ce shi “yaro ne,” wai ya yi ƙanƙantar yin aikin da Allah ya ba shi. (Irmiya 1:6) Yunana kuma ya gudu daga aikin da aka ba shi! (Yunana 1:3) Maryamu fa?

Har yanzu ana karanta kalamanta masu sauƙi da suke cike da tawali’u da biyayya. Ta gaya wa Jibra’ilu: “Ga ni, baiwar Ubangiji; bisa ga faɗinka shi zama mani.” (Luka 1:38) Yarinya baiwa ita ce mafi ƙanƙanta a cikin bayi, rayuwarta gabaki ɗaya tana hannun ubangidanta. Yadda Maryamu ta ɗauki Ubangijinta ke nan, Jehobah. Ta san cewa tana ƙarƙashin kāriyarsa, Allah yana nuna aminci ga waɗanda suka kasance da aminci, kuma zai albarkace ta sa’ad da take iya ƙoƙarinta wajen cika wannan jan aikin da ke gabanta.—Zabura 18:25.

A wasu lokatai Allah ya kan ce mu yi wani abin da a ganinmu yana da wuya, ko kuma wanda ba zai yiwu ba. Amma, a cikin Kalmarsa ya ba mu dalilai masu yawa da za su sa mu gaskata da shi, kuma mu dogara gare shi kamar yadda Maryamu ta yi. (Misalai 3:5, 6) Za mu yi hakan kuwa? Idan muka yi hakan, zai ba mu lada, wanda hakan dalilai ne na kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi a gare shi.

Ziyartar Alisabatu

Kalaman da Jibra’ilu ya faɗa game da Alisabatu suna da muhimmanci sosai ga Maryamu. A cikin dukan matan da ke duniya babu wadda za ta fahimci yanayinta kamar Alisabatu. Nan da nan Maryamu ta tafi tsaunukan Yahudiya, tafiyar wajen kwana uku ko huɗu. Sa’ad da ta shiga gidan Alisabatu da Zakariya firist, Jehobah ya sake ba ta ƙwaƙƙwaran alama don ya ƙarfafa bangaskiyarta. Sa’ad da Alisabatu ta ji muryar Maryamu, nan da nan jaririn da ke cikin cikinta ya motsa don murna. An cika ta da ruhu mai tsarki kuma ta kira Maryamu “uwar Ubangijina.” Allah ya nuna wa Alisabatu cewa ɗan Maryamu zai zama Ubangijinta, Almasihu. Bugu da ƙari, an hure ta ta yaba wa Maryamu saboda biyayyar da take yi cikin aminci, ta ce: “Ita fa da ta bada gaskiya mai-albarka ce.” (Luka 1:45) Hakika, dukan alkawuran da Jehobah ya yi wa Maryamu za su cika!

Bayan haka, sai Maryamu ta soma magana. Kalaman da ta faɗa suna nan a rubuce a cikin Luka 1:46-55. Wannan shi ne furci mafi tsawo na Maryamu da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ya bayyana abubuwa masu yawa game da ita. Ya nuna halinta na nuna godiya, yayin da take yaba wa Jehobah domin gatan da ya ba ta na zama mahaifiyar Almasihu. Maganar da ta yi ya nuna irin bangaskiyar da take da shi sa’ad da ta ce Jehobah yana ƙasƙantar da masu girman kai da masu iko, kuma yana taimaka wa masu tawali’u da talakawa da suke son su bauta masa. Hakan kuma ya bayyana zurfin saninta. In ji wani kimantawa da aka yi, ta yi ƙolin Nassosin Ibrananci fiye da sau ashirin!

Babu shakka, Maryamu ta yi tunani sosai a kan Kalmar Allah. Duk da haka, ta kasance mai tawali’u, ta gwammace Nassosi su bayyana yanayinta maimakon ta yi hakan da kanta. Jaririn da ke girma a cikin mahaifarta ya nuna irin wannan halin sa’ad da ya girma, ya ce: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.” (Yohanna 7:16) Zai dace mu tambayi kanmu: ‘Ina nuna irin wannan darajar ga Kalmar Allah? Ko kuwa na fi son nawa ra’ayoyin da kuma koyarwa?’ Amsar da Maryamu ta bayar na kai tsaye ne.

Maryamu ta zauna tare da Alisabatu har tsawon wata uku, kuma babu shakka, sun ƙarfafa juna. (Luka 1:56) Waɗannan matan sun tuna mana muhimmancin abota. Idan muka yi abota da waɗanda suke ƙaunar Jehobah Allahnmu sosai, muna da tabbacin cewa za mu girma a ruhaniya kuma za mu kusanci Allah sosai. (Misalai 13:20) A ƙarshe, lokaci ya yi da Maryamu za ta koma gida. Menene Yusufu zai ce idan ya gane yanayin da take ciki?

Maryamu da Yusufu

Maryamu ba ta jira har sai cikinta ya bayyana kafin ta gaya wa Yusufu ba. Tana bukatar ta gaya wa Yusufu. Kafin ta yi hakan, wataƙila ta yi tunanin yadda wannan mutumin mai tsoron Allah zai ji idan ta gaya masa. Duk da haka, ta je ta gaya masa duk abin da ya same ta. Kamar yadda kake zato, abin ya dami Yusufu sosai. Yana son ya gaskata da ita, amma abin da ta gaya masa bai taɓa faruwa ba. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana irin tunanin da ya yi a zuciyarsa ba. Amma ya gaya mana cewa ya yanke shawarar sakinta, domin waɗanda aka sa wa rana a zamanin dā ana ɗaukansu kamar ma’aurata. Domin ba ya son ya kunyatata a gaban jama’a ko a yi mata horo, sai ya zaɓi ya sake ta a ɓoye. (Matta 1:18, 19) Maryamu ba ta ji daɗin ganin wannan mutumin mai adalci yana ɓata rai saboda irin wannan yanayin da bai taɓa faruwa ba. Duk da haka, Maryamu ba ta yi fushi ba.

Jehobah bai ƙyale Yusufu ya ɗauki matakin da yake son ya ɗauka ba. A cikin mafarki, mala’ikan Allah ya gaya masa cewa cikin da Maryamu take da shi mu’ujiza ce. Hakan ya kwantar masa da hankali! A yanzu, Yusufu ya yi abin da Maryamu ta yi tuntuni, wato, yin nufin Jehobah. Ya auri Maryamu, kuma ya ɗauki nauyin kula da Ɗan Jehobah.—Matta 1:20-24.

Ya kamata ma’aurata da waɗanda suke tunanin yin aure a nan gaba su bi misalin waɗannan ma’auratan na shekaru 2,000 da suka shige. Sa’ad da Yusufu ya ga yadda matarsa take cika aikinta a cikin gida kuma take kula da yaronta, ya yi farin cikin cewa mala’ikan Jehobah ya yi masa ja-gora. Yusufu ya ga muhimmancin dogara ga Jehobah sa’ad da ake yanke shawarwari masu muhimmanci. (Zabura 37:5; Misalai 18:13) Babu shakka, ya mai da hankali sosai kuma ya nuna sanin ya kamata sa’ad da yake yanke shawarwari a matsayin shugaban iyali.

A wani ɓangare kuma, menene za mu iya koya daga yardar da Maryamu ta nuna wajen auren Yusufu? Duk da cewa a dā bai yarda da labarin da ta ba shi ba, ta ci gaba da yi masa biyayya a matsayin mutumin da zai zama shugaban iyali. Wannan darassi ne mai kyau a gare ta, da kuma mata Kiristoci a yau. A ƙarshe, waɗannan abubuwan da suka faru sun koya wa Yusufu da Maryamu muhimmancin kasancewa mai aminci da kuma tattaunawa da juna.

Waɗannan ma’auratan sun gina aurensu a kan tushe mai kwari. Su biyun suna ƙaunar Jehobah Allah fiye da komi kuma suna ɗokin yin abin da yake so a matsayinsu na iyaye masu kula. Babu shakka, albarka mai girma tana jiransu da kuma ayyuka masu yawa. Suna da hakkin yin renon Yesu, wanda zai girma ya zama mutumi mafi girma a duniya.

[Hoto a shafi na 23]

Ƙaunar Allah ita ce tushe mafi kyau a aure

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba