Shugabancin Kristi Gaskiya Ne Kuwa A Gare Ka?
“Kada kuwa a ce da ku [shugabanni]: gama ɗaya ne [shugabanku], Kristi.”—MATTA 23:10.
1. Wanene ne kaɗai Shugaban Kiristoci na gaskiya?
RANAR Talata ce, 11 ga watan Nisan. Bayan kwana uku, za a kashe Yesu Kristi. Wannan ita ce ziyararsa ta ƙarshe a haikali. A wannan ranar, Yesu ya koyar da koyarwa mai muhimmanci ga jama’a da suka taru a wurin da kuma almajiransa. Ya ce: “Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne. Kuma kada ku ce da kowane mutum a duniya ubanku: gama ɗaya ne Ubanku, shi na sama. Kada kuwa a ce da ku [shugabanni]: gama ɗaya ne [Shugabanku], Kristi.” (Matta 23:8-10) Hakika, Yesu Kristi ne Shugaban Kiristoci na gaskiya.
2, 3. Yaya sauraron Jehovah da kuma yin na’am da Shugaban da ya naɗa yake shafar rayuwarmu?
2 Shugabancin Yesu yana da fa’ida ƙwarai a rayuwarmu idan muka karɓe shi! Da yake annabta zuwan wannan Shugaban, Jehovah Allah ya ce ta bakin annabi Ishaya: “Ya ku, kowane ɗayanku mai-jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye, har da shi wanda ba shi da kuɗi; ku zo, ku saya, ku ci; i, ku zo, ku sayi ruwan anab da madara, ba da kuɗi, ba da abin biya ba. . . . Ku sauraro gareni da kyau, ku ci abin da ke nagari, ranku ya yi daɗi da kitse. . . . Ga shi, na sanya shi shaida ga al’ummai, shugaba da [kwamanda] ga al’ummai.”—Ishaya 55:1-4.
3 Ishaya ya yi amfani da abin sha na kullum—ruwa, madara, da ruwan anab—wajen salon magana a nuna yadda yake shafar rayukanmu sa’ad da muka saurari Jehovah kuma muka bi Shugaba kuma Kwamanda da Ya ba mu. Sakamakon yana wartsakarwa. Kamar shan ruwan sanyi ne a rana mai zafi. Ƙishinmu domin gaskiya da adalci yana cika. Madara tana ƙarfafa jarirai kuma tana taimakonsu su yi girma, ‘madarar kalmar’ tana ƙarfafa mu kuma tana kawo girma ta ruhaniya a dangantakarmu da Allah. (1 Bitrus 2:1-3) Kuma wa zai musanta cewa ruwan anab yana ƙara farin ciki a lokacin biki? Hakanan, bauta wa Allah na gaskiya da kuma bin sawun Shugaba da ya naɗa yana sa rayuwa ta “cika da murna.” (Kubawar Shari’a 16:15) Saboda haka, yana da muhimmanci ga dukanmu—manya da yara, maza da mata—mu nuna cewa shugabancin Kristi da gaske ne a gare mu. To, ta yaya za mu nuna a rayuwarmu ta yau da kullum cewa Almasihu Shugabanmu ne?
Matasa—Ku Ci Gaba da ‘Cin Gaba Cikin Hikima’
4. (a) Me ya faru sa’ad da Yesu ɗan shekara 12 ya ziyarci Urushalima a lokacin Idin Faska? (b) Yaya ilimin Yesu yake lokacin da ɗan shekara 12 ne kawai?
4 Ka yi la’akari da misalin da Shugabanmu ya kafa wa matasa. Ko da yake kaɗan aka sani game da yarantakar Yesu, wata aukuwa ta ba da bayani. Sa’ad da Yesu yana ɗan shekara 12, iyayensa suka je da shi Idin Faska na shekara shekara a Urushalima. A wannan lokaci ya shagala cikin tattauna Nassosi, iyayensa ba labari suka bar shi a baya. Bayan kwanaki uku iyayensa da suka damu, Yusufu da Maryamu, suka same shi a cikin haikali, “yana zaune tsakiyar malamai, yana jinsu, yana kuwa yi musu tantambaya.” Bugu da ƙari, “dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da maganar da ya ke mayarwa.” Ka yi tunani, a shekararsa 12 kawai, Yesu ba kawai yana yin tambayoyi masu sa tunani na ruhaniya ba amma kuma yana ba da amsa cikin basira! Babu shakka, koyarwa ta iyaye ta taimake shi.—Luka 2:41-50.
5. Ta yaya matasa za su binciki halayensu game da nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali?
5 Wataƙila matashi ne kai. Idan iyayenka bayin Allah ne masu ibada, wataƙila da akwai tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai a gidanku. Yaya halinka yake game da nazari na iyali? Me ya sa ba za ka yi bimbini a kan tambayoyi kamar su: ‘Ina tallafa wa tsarin nazari na iyali da zuciya ɗaya kuwa? Ina ba da haɗin kai kuwa, ba tare da yin wani abin da zai wargaza tsarin ba?’ (Filibbiyawa 3:16) ‘Ina saka hannu kuwa cikin nazarin? Sa’ad da ya dace, ina yin tambayoyi kuwa game da batun kuma in yi furci game da yadda za a yi amfani da ita? Yayin da nake girma a ruhaniya, ina koyon marmarin “abinci mai-ƙarfi [da ke] domin isassun mutane”?—Ibraniyawa 5:13, 14.
6, 7. Yaya muhimmancin tsarin karatun Littafi Mai Tsarki kullum yake ga matasa?
6 Tsarin karatun Littafi Mai Tsarki kullum ma yana da muhimmanci. Mai Zabura ya rubuta: “Mai-albarka ne mutum wanda ba ya bi ta shawarar miyagu ba, . . . Amma marmarinsa cikin shari’a ta Ubangiji ya ke; kuma a cikin shari’arsa ya kan riƙa tunani dare da rana.” (Zabura 1:1, 2) Magajin Musa, Joshua, ‘ya yi karatun Littafin doka dare da rana.’ Wannan ya sa ya yi aiki cikin hikima kuma ya yi nasara wajen yin aikin da Allah ya ba shi. (Joshua 1:8) Shugabanmu Yesu Kristi ya ce: “An rubuta, Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) Idan muna bukatar abinci na zahiri kowace rana, to, lallai za mu fi bukatar abinci na ruhaniya a kai a kai!
7 Da ta fahimci bukatarta ta ruhaniya, Nicole ’yar shekara 13 ta fara karatun Littafi Mai Tsarki kullum.a Yanzu tana shekara 16, ta karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya sau ɗaya kuma yanzu ta kusan tsakiya na sau biyun. Tsarin ta yana da sauƙi. “Na ƙudura aniya na karanta aƙalla Sura ɗaya kowacce rana,” in ji ta. Ta yaya karatunta na Littafi Mai Tsarki kullum ya taimake ta? Ta amsa: “Munanan rinjaya a yau suna da yawa. Kowacce rana ina fuskantar matsi a makaranta da kuma wasu wurare da suke ƙalubalantar bangaskiya ta. Karatun Littafi Mai Tsarki kowacce rana ya taimake ni in tuna umurnin da kuma mizanan Littafi Mai Tsarki da wuri, da suke ƙarfafa ni na tsaya wa irin waɗannan matsi. Domin haka, ina jin ina kusa da Jehovah da kuma Yesu.”
8. Mecece al’adar Yesu game da Majami’a, kuma ta yaya matasa za su yi koyi da shi?
8 Yesu ya kasance da al’ada ta sauraro da kuma karatu a Majami’a. (Luka 4:16; Ayukan Manzanni 15:21) Yana da kyau yara su bi wannan misali ta wajen halartar taron Kirista a kai a kai, inda ake karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki! Da yake godiya ga waɗannan taron, Richard ɗan shekara 14 ya ce: “Taron suna da muhimmanci a gare ni. Ana tunasar da ni koyaushe abin da yake da kyau da marar kyau, abin da yake bisa ɗabi’a da kuma abin da ya fice daga ɗabi’a, abin da yake na Kristi da abin da bai kasance ba. Ba sai na sha wuya ba—ta wajen fuskantar abin.” Hakika, “shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa mara-sani ya zama mai-hikima.” (Zabura 19:7) Nicole ma ta ƙudura aniyar ta halarci dukan taron ikilisiya biyar kowane mako. Tana yin awoyi daga biyu zuwa uku wajen shirya taron.—Afisawa 5:15, 16.
9. Ta yaya ku matasa za ku iya “yin gaba a cikin hikima”?
9 Ƙuruciya lokaci ne mai kyau na ‘sanin Allah makaɗaici na gaskiya, da kuma wanda ya aiko Yesu Kristi.’ (Yohanna 17:3) Wataƙila ka san yara waɗanda suke ɓata lokaci da yawa wajen karatun littattafan ba da dariya, suna kallon telibijin, suna wasan bidiyo, ko kuma suna bincika Intane. Me ya sa za ka yi koyi da su yayin da za ka iya yin koyi da kamiltaccen Shugabanmu? Sa’ad da yake yaro, yana farin ciki wajen koyo game da Jehovah. Kuma menene sakamakon haka? Domin ƙaunarsa ga abubuwa na ruhaniya, “Yesu kuwa yana yin gaba a cikin hikima.” (Luka 2:52) Kai ma za ka iya hakan.
‘Ku Miƙa Kai ga Junanku’
10. Menene zai taimake iyali ta zama tushen salama da farin ciki?
10 Gida zai iya zama wurin salama da wadatar zuci ko kuma filin yaƙi da husuma. (Misalai 21:19; 26:21) Karɓan shugabancin Kristi yana kawo salama da farin ciki ga iyali. Misalin Yesu babu shakka, shi ne abin koyi na dangantaka ta iyali. Nassosi suka ce: “Kuna sarayadda kanku ga junanku cikin tsoron Kristi. Mata, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne, shi da kansa fa mai-ceton jiki ne. . . . Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afisawa 5:21-25) Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiya ta Kolossi: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da iyayenku cikin kowane abu, gama wannan abin yarda ne cikin Ubangiji.” (Kolossiyawa 3:18-20)
11. Ta yaya maigida zai nuna cewa shugabancin Kristi da gaske ne a gare shi?
11 Bin wannan gargaɗin yana nufin cewa maigida zai yi ja-gorar iyali, mata za ta taimake mijinta cikin aminci, kuma yara za su yi wa iyayensu biyayya. Ja-gorar namiji za ta kasance abin farin ciki ne idan yana yinta daidai. Maigida mai hikima dole ya koyi yadda zai yi ja-gora ta wajen koyi da Mai Ja-Gorarsa kuma Shugabansa, Kristi Yesu. (1 Korinthiyawa 11:3) Ko da yake daga baya Yesu ya zama ‘shugaba bisa kome a ikilisiya,’ ya zo duniya ba “domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma waɗansu.” (Afisawa 1:22; Matta 20:28) Hakanan, maigida Kirista yake yin ja-gora, ba domin son kai ba, amma domin ya kula da matarsa da ’ya’yansa—hakika, dukan iyalin. (1 Korinthiyawa 13:4, 5) Yana ƙoƙarin ya yi koyi da halayen ibada na shugabansa, Yesu Kristi. Kamar Yesu, yana da tawali’u kuma mai ƙasƙantar zuciya ne. (Matta 11:28-30) Irin waɗannan kalmomi kamar su “ki yi haƙuri” da kuma “gaskiyarki ce” ba su da wuya ya faɗe su sa’ad da ya yi kuskure. Misalinsa mai kyau yana sa ya yi wa matarsa sauƙi ta zama ‘mataimakiya,’ kuma ‘abokiya’ ga irin wannan mutumin, tana koya daga wurinsa kuma tana aiki tare da shi.—Farawa 2:20; Malachi 2:14.
12. Menene zai taimaki mace ta kiyaye mizanin shugabanci?
12 Mace kuma za ta kasance a ƙarƙashin mijinta. Amma, idan ruhun duniya ya shafe ta, wannan zai fara yi wa yadda take ɗaukar mizanin shugabanci zangon ƙasa, kuma batun cewa za ta kasance a ƙarƙashin mijinta ba zai yi mata daɗi ba. Nassosi ba su ba da shawarar cewa namiji ya zama mamallaki ba, amma an bukaci mata su kasance ƙarƙashin mazansu. (Afisawa 5:24) Littafi Mai Tsarki kuma ya ce maigida ko kuma uba shi ke da hakki, kuma idan an yi amfani da gargaɗinsa, wannan yana kawo salama da kuma zaman lafiya a iyali.—Filibbiyawa 2:5.
13. Wane misali ne na miƙa kai Yesu ya bari ga yara?
13 Yara su yi biyayya ga iyayensu. A wannan batun, Yesu ya kafa misali mafi kyau. Bayan abin da ya faru a haikali sa’ad da Yesu yana ɗan shekara 12 lokacin da aka bar shi a baya na kwana uku, “ya tafi tare da [iyayensa], ya zo Nazarat; yana biyayya da su.” (Luka 2:51) Yara kasancewarsu a ƙarƙashin iyayensu yana ƙara salama da jituwa ta iyali. Sa’ad da kowa a cikin iyali ya kasance ƙarƙashin shugabancin Kristi, sakamakon wannan iyali ne mai farin ciki.
14, 15. Menene zai taimake mu mu yi nasara sa’ad da muke fuskantar yanayi mai wuya a gida? Ka ba da misali.
14 Har idan yanayi mai wuya ya faru a gida, mabuɗin nasara shi ne yin koyi da Yesu da kuma karɓar ja-gorarsa. Alal misali, auren Jerry ɗan shekara 35 da Lana, uwar wata baliga, ya fuskanci ƙalubale da babu wanda ya yi tsammanin wannan a tsakaninsu. Jerry ya yi bayani: “Na sani cewa domin in zama maigidan kirki, ina bukatar in bi mizanai na Littafi Mai Tsarki da yake kawo nasara a wasu iyalai. Amma ba da daɗewa ba na fahimci cewa dole ne in yi amfani da su cikin hikima da fahimi.” Agolarsa tana ganinsa kamar wani ne da ya zo ya shiga tsakaninta da mamarta sai ta tsane shi ƙwarai da gaske. Jerry yana bukatar fahimi domin ya ga cewa halinsa ya shafi maganar da kuma ayyukan yarinyar. Yaya ya magance wannan yanayi? Jerry ya amsa: “Ni da Lana muka shirya cewa a yanzu, Lana za ta cika aikin horo na iyaye yayin da ni kuma na mai da hankali ga matsowa kusa da agolata. Da shigewar lokaci, wannan ya kawo sakamako mai kyau.”
15 Sa’ad da muke fuskantar yanayi mai wuya a gida, muna bukatar fahimi mu gano dalili da ya sa wasu cikin iyali suke magana da kuma ayyuka yadda suke yi. Muna kuma bukatar hikima mu yi amfani da mizanai na ibada da kyau. Alal misali, Yesu, ya fahimci ƙwarai abin da ya sa mace da take wahala daga zuban jini ta taɓa shi, kuma ya bi da ita cikin hikima da kuma tausayi. (Leviticus 15:25-27; Markus 5:30-34) Hikima da fahimi halaye ne na Shugabanmu. (Misalai 8:12) Muna farin ciki idan muka aikata abu yadda zai yi.
‘Ku Biɗi Mulkin Allah Farko’
16. Menene ya kamata ya ɗauki waje na farko a rayuwarmu, kuma ta yaya Yesu ya nuna haka ta wajen misalinsa?
16 Yesu ya bayyana sarai abin da zai ɗauki waje na farko a rayuwar waɗanda suka karɓi shugabancinsa. Ya ce: “Ku fara biɗan mulkin [Allah], da adalcinsa.” (Matta 6:33) Kuma ta wajen misalinsa, ya nuna mana yadda za mu yi hakan. Bayan kwanaki 40 na azumi, bimbini, da addu’a da suka biyo baftismarsa, Yesu ya fuskanci jarraba. Shaiɗan Iblis ya miƙa masa sarauta bisa “dukan mulkokin duniya.” Ka yi tunanin irin rayuwar da Yesu zai yi idan ya karɓi kyautar Iblis! Amma, Kristi ya mai da hankali bisa yin nufin Ubansa. Kuma ya fahimci cewa, irin wannan rayuwa a duniya ta Shaiɗan gajeriya ce. Ba wani ɓata lokaci, ya ƙi kyautar Iblis, yana cewa: “An rubuta, Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” Ba da daɗewa ba bayan haka, “Yesu ya soma wa’azi, ya ce, Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.” (Matta 4:2, 8-10, 17) Daga nan zuwa ƙarshen rayuwarsa ta duniya, Kristi ya kasance mai shelar Mulkin Allah na cikakken lokaci.
17. Ta yaya za mu nuna cewa batutuwan Mulki suna da waje na farko a rayuwarmu?
17 Ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi koyi da Shugabanmu kuma kada mu ƙyale duniyar Shaiɗan ta rinjaye mu ta yin aiki da ake biyan kuɗi da yawa ya zama ainihin burinmu a rayuwa. (Markus 1:17-21) Zai kasance wauta a gare mu idan muka kamu cikin tarko na biɗan abin duniya kuma batutuwa da suka shafi Mulkin suka kasance a wuri na biyu! Yesu ya danka mana aikin wa’azin Mulki da kuma na almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Hakika, wataƙila muna da iyali ko kuma wasu hakkoki da za mu cika, amma ba ma farin ciki ne mu yi amfani da yamma da kuma ƙarshen mako mu cika hakkinmu na Kirista na wa’azi da koyarwa? Abin ƙarfafa ne cewa a shekarar hidima ta 2001, mutane 780,000 sun yi hidima na cikakken lokaci, ko kuma majagaba!
18. Me yake taimakonmu mu ji daɗin hidima?
18 Linjila ta kwatanta Yesu cewa mutum ne mai aiki, kuma mutum ne mai juyayi. Da ya ga bukata ta ruhaniya na waɗanda suka kewaye shi, ya ji tausayinsu ya ɗoki ya taimake su. (Markus 6:31-34) Hidimarmu za ta zama na farin ciki idan muka gaya wa wasu domin ƙauna da kuma muradi na gaske mu taimake su. Amma ta yaya za mu koyi irin wannan muradi? “Sa’ad da nake cikin ƙuruciya ta,” in ji wani matashi mai suna Jayson, “ba na jin daɗin hidima.” Menene ya taimake shi ya so aikin? Jayson ya amsa: “A iyalinmu, kowacce safiyar Asabar domin hidimar fage ne. Wannan ya yi mini kyau domin da zarar na fita hidima, hakan nake ganin abu mai kyau da take cim ma, kuma hakan nake jin daɗinta.” Mu ma ya kamata mu riƙa fita hidima a kai a kai kuma da ƙwazo.
19. Menene ya kamata mu ƙuduri aniyar yi game da shugabancin Kristi?
19 Hakika yana wartsakarwa da kuma kawo albarka mu karɓi shugabancin Kristi. Idan muka yi hakan, ƙuruciya sai ta kasance lokaci ne na ci gaba a ilimi da hikima. Rayuwar iyali ta kasance da salama da kuma farin ciki, kuma hidima ta kasance aiki da take kawo farin ciki da gamsuwa. Ko ta yaya, mu ƙuduri aniyar nunawa a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma shawarar da muke yankewa cewa shugabancin Kristi da gaske ne a gare mu. (Kolossiyawa 3:23, 24) Ko da yake, Yesu Kristi ya yi tanadin shugabanci har ila a wata hanya—ikilisiyar Kirista. Talifi na gaba zai tattauna yadda za mu amfana daga wannan tanadin.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
Ka Tuna?
• Ta yaya bin Shugabanmu da Allah ya naɗa yake mana amfani?
• Ta yaya matasa za su nuna cewa suna so su bi shugabancin Yesu?
• Yaya shugabancin Kristi yake shafar rayuwar iyalan da suka miƙa kai gare shi?
• Ta yaya hidimarmu za ta nuna cewa shugabancin Kristi da gaske ne a gare mu?
[Hotuna a shafi na 11]
Ƙuruciya lokaci ne mai kyau na samun sanin Allah da kuma na Shugabanmu da aka naɗa
[Hoto a shafi na 12]
Miƙa kai ga shugabancin Kristi yana ƙara farin ciki ta iyali
[Hotuna a shafi na 14]
Yesu ya biɗi Mulkin da farko. Kai fa?