Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 pp. 8-12
  • Sun Jira Zuwan Almasihu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Jira Zuwan Almasihu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Mutane Suke Jiran Almasihu?
  • Annabce-Annabce Game da Sa’ad da Yake Ƙarami
  • Almasihu Ya Soma Hidimarsa!
  • Ƙarin Annabce-Annabce Game da Almasihu
  • Annabci Game da Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ta Hanyar Almasihu Ne Allah Zai Kawo Ceto
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Almasihu Ya Bayyana
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 pp. 8-12

Sun Jira Zuwan Almasihu

“Taron fa suna cikin sauraro, mutane duka kuwa suna zato a cikin zukatansu a kan Yohanna, ko wataƙila shi [Almasihu] ne.”—LUK 3:15.

1. Wane albishiri ne mala’ika ya gaya wa makiyayan?

DARE ya yi, kuma makiyaya suna waje suna kula da tumakinsu. Sai farat ɗaya, mala’ikan Jehobah ya tsaya kusa da su kuma haske ya haskaka kusa da su! Sun ji tsoro, amma sun saurari albishirin da mala’ikan ya gaya musu: “Kada ku ji tsoro; gama, ga shi, na kawo maku bishara ta farinciki mai-girma wanda za ya zama ga dukan mutane: gama yau . . . an haifa maku Mai-ceto, shi ne Kristi Ubangiji.” Jaririn da mala’ikan yake maganarsa shi ne wanda zai zama Kristi, ko Almasihu. Mala’ikan ya gaya wa makiyayan cewa za su sami jaririn a sakarkari a garin da ke kusa da wurin. Sai mala’iku da yawa suka bayyana farat ɗaya. Sun yabi Jehobah suna cewa: “Alhamdu ga Allah a cikin mafi ɗaukaka, a duniya kuma salama wurin mutanen da ya ke murna da su sarai.”—Luk 2:8-14.

2. Mene ne Almasihu yake nufi, kuma ta yaya mutane za su san shi?

2 Babu shakka, makiyayan sun san cewa a Ibrananci, kalmar nan “Almasihu” ko “Kristi” tana nufin “Shafaffe” na Allah. (Fit. 29:5-7) Amma, ta yaya waɗannan makiyaya da kuma wasu za su iya daɗa saninsu kuma su sa mutane su gaskata cewa Jehobah ya zaɓi wannan jaririn ya zama Almasihu? Da farko suna bukatar su yi nazarin annabce-annabce a cikin Nassosi game da Almasihu, kuma suna bukatar su ga ko waɗannan annabce-annabcen sun cika a rayuwar wannan yaron.

Me Ya Sa Mutane Suke Jiran Almasihu?

3, 4. Ta yaya annabcin da ke Daniyel 9:24, 25 suka cika?

3 Bayan shekaru da yawa, Yohanna Mai Baftisma ya soma aikinsa na wa’azi. Wasu mutane suka soma tunani cewa wataƙila shi ne Almasihu domin abin da ya faɗa da kuma yi. (Karanta Luka 3:15.) Amma a cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai annabci da ya yi magana game da bakwai bakwai har saba’in, kuma ya taimaka wa mutane su san lokacin da Almasihu zai bayyana. Annabcin ya ce: “Daga loton fitowar doka a maida Urushalima, a gine ta kuma, har zuwa loton Masiya sarki, za a yi bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu.” (Dan. 9:24, 25) Masanan Littafi Mai Tsarki sun yarda cewa waɗannan ba makonni na kwanaki ba ne amma makonni na shekaru ne. Saboda haka, kowanne cikin waɗannan makonni yana da tsawon shekara bakwai. Daniyel 9:24 a juyin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu.”

4 Mutanen Jehobah a yau sun fahimci cewa makonni 69 na Daniyel 9:25 sun yi daidai da shekaru 483 kuma sun soma a shekara ta 455 K.Z. A wannan lokacin ne Sarki Artaxerxes na Fasiya ya gaya wa Nehemiya ya gyara kuma ya sake gina Urushalima. (Neh. 2:1-8) Waɗannan shekaru 483 sun ƙare a shekara ta 29 sa’ad da Yesu ya yi baftisma. A wannan lokacin, Jehobah ya shafa shi da ruhu mai tsarki kuma ya zama Almasihu.—Mat. 3:13-17.a

5. Waɗanne annabce-annabce ne za mu tattauna yanzu?

5 Bari mu tattauna wasu cikin annabce-annabce da yawa da aka yi game da haihuwar Almasihu da rayuwarsa a matsayin yaro da mutum da kuma hidimarsa. Za mu koya yadda waɗannan annabce-annabce suka cika a lokacin da Yesu yake duniya. Wannan zai ƙarfafa bangaskiyarmu game da Littafi Mai Tsarki kuma ya nuna cewa Yesu ne Almasihun da mutane suke jira.

Annabce-Annabce Game da Sa’ad da Yake Ƙarami

6. Ka bayyana yadda Farawa 49:10 ya cika.

6 Almasihun zai fito daga ƙabilar Yahuda a Isra’ila. Ba da daɗewa ba kafin Yakubu ya mutu, ya albarkaci ’ya’yansa maza, kuma ya gaya wa Yahuda: “Kandirin ba za ya rabu da Yahuda ba, Sandar mai-mulki kuma daga tsakanin sawayensa, har Shiloh ya zo; zuwa gareshi kuma biyayyar al’ummai za ta nufa.” (Far. 49:10) Malaman Yahudawa da yawa sun gaskata cewa kalaman Yakubu ga Yahuda game da Almasihu ne. Farawa daga sarautar Sarki Dauda Bayahude, kandari, wato ikon sarauta da kuma sandar mai mulki, wato, ikon ba da umurni, ta kasance a kabilar Yahuda. Sunan nan “Shiloh,” yana nufin “Wanda yake da ikon sarauta.” A ƙarshe, Shiloh ne zai zama sarkin da zai yi sarauta har abada, domin Allah ya gaya wa Zedekiya wanda shi ne sarki na ƙarshe a Yahuda cewa za a ba sarkin da ke da iko wannan matsayin. (Ezek. 21:26, 27) Bayan Zadakiya, Yesu ne kaɗai zuriyar Dauda da aka yi alkawari cewa zai yi sarauta. Kafin a haifi Yesu, mala’ika Jibrailu ya gaya wa Maryamu: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yaƙub har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luk 1:32, 33) Babu shakka, Yesu Kristi ne Shiloh, wanda zuriyar Yahuda da kuma Dauda ne.—Mat. 1:1-3, 6; Luk 3:23, 31-34.

7. Ta yaya annabci game da haihuwar Almasihu ya cika?

7 Za a haifi Almasihu a Baitalahmi. Annabi Mikah ya rubuta: “Ke, Baitalahmi Ephrathah, wadda ki ke ƙanƙanuwa da za ki zama a cikin dangin Yahuda, daga cikinki wani za ya fito mini, wanda za ya zama mai-mulki cikin Isra’ila; mafitansa tun daga zamanin dā, tun fil’azal.” (Mi. 5:2) Annabcin ya gaya mana cewa za a haifi Almasihun a Baitalahmi, wani gari a Yahuda a dā da ake kira Ephrathah. Ko da yake mahaifiyar Yesu, Maryamu da mijinta Yusufu, suna zama a Nazarat, amma umurnin da sarkin Roma ya ba da cewa mutane su koma birnin da aka haifi mahaifinsu don su yi rajista ya sa suka koma Baitalahmi inda aka haifi Yesu a shekara ta 2 K.Z. (Mat. 2:1, 5, 6) Saboda haka, an haifi Yesu daidai yadda aka annabta!

8, 9. Mene ne annabcin ya faɗa game da haihuwar Almasihu kuma mene ne zai faru bayan an haife shi?

8 Budurwa ce za ta haifi Almasihu. (Karanta Ishaya 7:14.) Wannan ayar ta nuna cewa budurwar za ta haifi ɗa. An yi amfani da wannan kalmar ga Rifkatu kafin ta yi aure. (Far. 24:16, 43) Ruhu mai tsarki na Allah ya ja-goranci Matta ya rubuta cewa Ishaya 7:14 ya samu cikawa sa’ad da aka haifi Yesu. A wannan ayar bai yi amfani da kalmar da ake kiran “budurwa” a Helenanci ba. Ya yi amfani da kalmar nan parthenos, wato, “budurwa” da ake amfani da ita a Helenanci. Marubutan Linjila Matta da Luka sun ce Maryamu budurwa ce kuma ta yi ciki ta wajen ruhu mai tsarki na Allah.—Mat. 1:18-25; Luk 1:26-35.

9 Za a kashe ƙananan yara bayan an haifi Almasihu. Wannan ya yi kama da abin da ya faru shekaru da yawa kafin a haifi Almasihu. Fir’auna na ƙasar Masar ya ba da umurni cewa a jefa duk yara maza na Ibraniyawa a cikin Kogin Nil. (Fit. 1:22) Wani annabci da ke Irmiya 31:15, 16 ya faɗa cewa “[Rahila] tana kuka domin ’ya’yanta” saboda maƙiya sun kashe su. Mutane sun ji kukanta tun daga Ramah, da ke Banyamin a arewancin Urushalima. Matta ya gaya mana cewa wannan annabci ya cika sa’ad da Sarki Hirudus ya ba da umurni a kashe dukan yara maza a Baitalahmi. (Karanta Matta 2:16-18.) Ka yi tunanin baƙin cikin da mutane suka yi!

10. Ta yaya annabcin da ke Hosiya 11:1 ya cika a Yesu?

10 Za a kirawo Almasihu daga ƙasar Masar. (Hos. 11:1) Don a ceci Yesu daga hannun Sarki Hirudus, mala’ika ya gaya wa Yusufu da Maryamu su bar Isra’ila kuma su kai Yesu ƙasar Masar. Sun komar da Yesu Isra’ila bayan da Hirudus ya mutu. Abin da Jehobah ya gaya wa Hosiya ya faru: “Daga cikin Masar na kirawo ɗana.” (Mat. 2:13-15) Hakika, ba zai yiwu ba Yesu ya hana abubuwa da suka faru a lokacin haihuwarsa da kuma sa’ad da yake ƙarami ba.

Almasihu Ya Soma Hidimarsa!

11. Yaya aka shirya wa Almasihu hanya?

11 Wani manzo zai shirya wa Almasihu hanya. Malakai ya faɗa cewa wani zai zo kafin Almasihu don ya shirya masa hanya. Zai taimaka wa mutane su kasance a shirye su amince da Almasihu sa’ad da ya zo. Malakai ya kira shi annabi Iliya. (Karanta Malakai 4:5, 6.) Yesu ya faɗa cewa Yohanna Mai Baftisma ne ya zama kamar Iliya. (Mat. 11:12-14) Markus ya faɗa cewa Yohanna ya shirya hanyar. Ainihin abin da Ishaya ya yi annabcinsa ke nan. (Isha. 40:3; Mar. 1:1-4) Yesu bai gaya wa Yohanna ya shirya masa hanya ba. Allah yana son mutane su san Almasihun. Saboda haka, Allah ne ya zaɓi Yohanna ya yi irin aikin da Iliya ya yi kuma ya shirya mutanen su marabce Almasihu.

12. Wane aiki na musamman ne Allah ya ba Almasihu?

12 Allah zai ba Almasihu aiki na musamman da zai yi. Wata rana Yesu yana cikin majami’a a Nazarat, garin da ya yi girma. Yesu ya buɗe naɗaɗɗen littafi kuma ya karanta kalaman Ishaya. Ga abin da ya karanta: “Ruhun Ubangiji yana bisa na, Gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa: Ya aike ni domin in yi wa ɗaurarru shela ta saki, da mayarwar gani ga makafi, in kwance waɗanda an ƙulle su, in yi shelar shekara ayananniya ta Ubangiji.” Yesu ya faɗa cewa wannan annabcin game da shi ne. Shi ne ainihin Almasihun. Shi ya sa Yesu yake da ikon ya faɗa: “Yau an cika wannan nassin a cikin kunnuwanku.”—Luk 4:16-21.

13. Ta yaya aka annabta somawar hidimar da Yesu zai yi a Galili?

13 An annabta sa’ad da Almasihu zai soma hidimarsa a Galili. Ishaya ya yi annabci game da ƙasar “Zebulun” da “Naphtali” da kuma “Galilee na al’ummai.” Ya rubuta: “Mutanen da ke tafiya cikin duhu suka ga haske mai-girma: mazauna cikin ƙasa ta inuwar mutuwa, a bisansu haske ya ɓullo.” (Isha. 9:1, 2) Yesu ya soma hidimarsa a Galili, a garin da ake kira Kafarnahum. Ya kuma koyar a yankunan Zebulun da Naphtali. Yesu ya taimaka wa mutanen da ke waɗannan wurare ta wajen koya musu gaskiya da ta haskaka kamar haske mai girma. (Mat. 4:12-16) A ƙasar Galili ne Yesu ya ba da Huɗubarsa a kan Dutse, ya zaɓi manzanninsa kuma yi mu’ujizarsa ta farko. A ƙasar Galili ne kuma Yesu ya bayyana ga fiye da almajirai 500 bayan ya tashi daga matattu. (Mat. 5:1–7:27; 28:16-20; Mar. 3:13, 14; Yoh. 2:8-11; 1 Kor. 15:6) Saboda haka, annabcin Ishaya ya cika sa’ad da Yesu ya yi wa’azi a “ƙasar Zebulun da ƙasar Naphtali.” Yesu ya kuma yi wa’azin Mulkin a wasu wurare a Isra’ila.

Ƙarin Annabce-Annabce Game da Almasihu

14. Ta yaya Zabura 78:2 ta cika?

14 Almasihu zai yi amfani da labarai da kwatanci don ya koyar da mutane. A cikin wata zabura, Asaph ya rera waƙa: “Zan buɗe bakina da misali.” (Zab. 78:2) Matta ya gaya mana yadda wannan annabcin ya cika. A koyaushe, Yesu ya yi amfani da kwatanci ko kuma misalai don ya yi koyarwa. Matta ya rubuta game da lokacin da Yesu ya yi amfani da ƙwayar mustad da yisti a matsayin misalai don ya koyar da mutane game da Mulkin Allah. Ya rubuta: “Ba ya faɗa masu kome ba sai tare da misali: domin abin da aka faɗi ta bakin annabi ya cika, cewa, in buɗe bakina da misalai; in furtarda abin da ke ɓoye tun kafawar duniya.” (Mat. 13:31-35) Labarai da kwatancin da Yesu ya yi amfani da su sun taimaki mutane da yawa su fahimci gaskiya game da Jehobah.

15. Ta yaya annabcin da ke Ishaya 53:4 ya cika?

15 Almasihu zai warkar da mutane. Ishaya ya yi annabci: “Lallai da kayan cutarmu ya nawaita, ya ɗauki baƙincikinmu.” (Isha. 53:4) Sa’ad da surkuwar Bitrus take rashin lafiya, Yesu ya warkar da ita. Bayan hakan mutane da yawa suka zo gidan Bitrus kuma Yesu ya warkar da su ma. Matta ya ce wannan ya cika abin da aka faɗa ta wurin annabi Ishaya, cewa: “Shi da kansa ya karɓi kumamancinmu, ya ɗauki cututtukanmu.” (Mat. 8:14-17) Amma ba a wannan lokacin ba ne kaɗai Yesu ya warkar da mutane ba. Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan lokatai da yawa da Yesu ya warkar da mutane.

16. Mene ne manzo Yohanna ya rubuta da ya nuna cewa Ishaya 53:1 game da Yesu ne?

16 Mutane da yawa ba za su gaskata ba cewa Yesu ne Almasihu, ko da yake ya yi nagargarun ayyuka. (Karanta Ishaya 53:1.) Manzo Yohanna ya ce wannan annabcin ya cika. Ya rubuta: “Ko da ya yi alamu da yawa haka a gabansu, duk da wannan ba su bada gaskiya gare shi ba: domin magana wadda annabi Ishaya ya faɗi ta cika, Ubangiji, wa ya gaskanta shaidarmu? A wurin wa kuma hannun Ubangiji ya bayanu?” (Yoh. 12:37, 38) Bayan shekaru da yawa, sa’ad da manzo Bulus ya yi wa’azin bishara, ba mutane da yawa ba ne suka gaskata cewa Yesu ne Almasihu ba.—Rom. 10:16, 17.

17. Ta yaya annabcin da ke Zabura 69:4 ya cika?

17 Mutane za su ƙi Almasihu ba dalili. (Zab. 69:4) Yesu ya ce: “Da ban yi ayyuka waɗanda wani bai yi ba, a wurinsu, da ba su da zunubi: Amma yanzu sun gan ni, sun ƙi ni kuma, duk da Ubana. Amma wannan ya zama domin a cika magana da aka rubuta a cikin Attaurarsu, suka ƙi ni ba dalili ba.” (Yoh. 15:24, 25) “Attaura” da aka ambata a nan tana nufin dukan Nassosi da suke da shi a wannan lokacin. (Yoh. 10:34; 12:34) Abin da muka karanta game da Yesu a cikin Linjila ya nuna cewa mutane da yawa sun ƙi Yesu, musamman shugabannin addinan Yahudawa. Bugu da ƙari, Yesu ya ce: “Duniya ba ta iya ƙinku ba; amma ni ta ke ƙi, domin ni kan shaida ta, ayyukanta miyagu ne.”—Yoh. 7:7.

18. Mene ne za mu koya a talifi na gaba?

18 Almajiran Yesu a ƙarni na farko sun tabbata cewa Yesu ne Almasihu. Sun san cewa Yesu ya cika dukan annabce-annabce da ke cikin Nassosin Ibraniyawa game da Almasihu. (Mat. 16:16) A wannan talifin mun koya cewa annabce-annabce game da haihuwar Yesu da kuma hidimarsa sun cika. Amma da akwai annabce-annabce da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna ko wane ne Almasihun. Za mu koya game da su a talifi na gaba. Idan muka yi tunani sosai game da waɗannan annabce-annabcen, ba za mu taɓa shakka ba cewa Yesu ne Jehobah ya zaɓa ya zama Almasihu.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da “bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu,” ka duba Rataye na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, shafuffuka na 197-199.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne annabce-annabce game da haihuwar Yesu ne suka cika?

• Ta yaya aka shirya hanya don zuwan Almasihu?

• Ta yaya annabce-annabcen Ishaya sura 53 suka cika?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba