Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
Ka taɓa damuwa sosai saboda wani ƙalubale ko kuma wani hakki da ba ka taɓa tsammanin zai zo gare ka ba? Kana gajiya don ƙoƙarin da kake yi koyaushe na neman abin biyan bukata? Wataƙila kana cikin miliyoyin mutane da suka ruɗe kuma suka razana saboda dole suka bar ƙasarsu suka yi gudun hijira. Wanene a cikinmu bai yi baƙin ciki ba da kuma kewa bayan ya yi rashin wani wanda yake ƙauna?
KA SAN cewa Maryamu, uwar Yesu, ta fuskanci duka waɗannan ƙalubale? Duk da haka, ta yi nasara! Me za mu iya koya daga misalinta?
Hakika, a duniya duka an san Maryamu. Wannan ba abin mamaki ba ne saboda ta kasance da matsayi da babu kamarsa a cikar nufin Allah. Amma, mutane da yawa suna bauta wa Maryamu. Cocin Katolika suna bauta mata a matsayin ƙaunatacciyar Uwa da kuma abin koyi wajen bangaskiya da bege da kuma sadaka. An koya wa mutane da yawa cewa Maryamu ce take bishe ’yan adam ga Allah.
Yaya ka ɗauki uwar Yesu? Mafi muhimmanci, yaya Allah ya ɗauke ta?
Aiki Mai Muhimmanci
Maryamu, ɗiyar Heli, ta fito ne daga ƙabilar Yahuda ta Isra’ila. Inda aka yi maganarta na farko a cikin Littafi Mai Tsarki dangane ne da wani abu mai ban al’ajabi. Wani mala’ika ya ziyarce ta kuma ya ce: “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke.” Da farko, hankalin Maryamu ya tashi, “ta yi zulumi kuwa a ranta ko wace irin gaisuwa ce wannan.” Sai mala’ikan ya ce mata an zaɓe ta ta yi wani aiki mai ban mamaki amma kuma mai muhimmanci, wato, na ɗaukar ciki, haihuwa, da kuma renon Ɗan Allah.—Luka 1:26-33.
Lallai wannan hakki ne mai muhimmanci da aka ɗaura a wuyar wannan budurwa! Menene ta yi? Wataƙila Maryamu ta yi tunanin cewa wanene zai yarda da wannan labari na ta. Wannan cikin zai sa ta rasa Yusufu ne wanda take so ta aura ko kuma ya sa ta kunya? (Kubawar Shari’a 22:20-24) Ba ta yi shakkar karɓan wannan babban aiki ba.
Bangaskiya mai ƙarfi da Maryamu take da shi ne ya sa ta yi biyayya ga Allahnta Jehobah. Ta tabbata cewa zai kula da ita. Sai ta ce: “Ga ni, baiwar Ubangiji; bisa ga faɗinka shi zama mani.” Maryamu ta yarda za ta fuskanci ƙalubale da ke tafe saboda ta ɗauki gata na ruhaniya da aka ba ta da muhimmanci.—Luka 1:38.
Sa’ad da Maryamu ta gaya wa Yusufu cewa tana da ciki, ya so ya raba dangantakarsu. Wannan lokaci ne mai wuya sosai ga kowannensu. Littafi Mai Tsarki bai faɗi tsawon wannan lokaci mai wuya ba. Amma Maryamu da Yusufu sun sami kwanciyar hankali sosai sa’ad da mala’ikan Jehobah ya yi magana da Yusufu. Wannan mala’ikan ya yi bayani game da wannan ciki na ban al’ajabi da ta ɗauka, kuma ya ce wa Yusufu ya aure ta.—Matta 1:19-24.
Lokatai Masu Wuya
A yau, mata masu ciki sukan yi watanni suna shiri don haihuwar jariri, kuma wataƙila Maryamu ma ta yi hakkan. Wannan ne ɗanta na farko. Duk da haka, abubuwan da ba ta tsammani ba sun sa kome ya yi wuya. Kaisar Agustus ya ba da doka a yi ƙirge, kuma ana bukatar kowa ya je a ƙirga shi a garin da aka haife shi. Sai Yusufu ya ɗauki Maryamu, yanzu cikinta ya kai wata tara, suka yi tafiyar mil 90, wataƙila a bisa jaki! Bai’talami ta cika da mutane kuma Maryamu tana bukatar inda ba mutane don ta haihu, amma babu wuri sai barga. Haihuwa a barga wataƙila ya yi wa Maryamu wuya sosai. Wataƙila ta ji kunya kuma ta tsorata sosai.
A wannan lokaci mai wuya a rayuwarta, Maryamu ta yi addu’a ga Jehobah, da tabbaci cewa zai kula da ita da ɗanta. Daga baya, wasu makiyaya suka iso, suna ɗokin ganin jaririn. Sun faɗi cewa mala’iku sun kira wannan yaron “Mai-ceto, shi ne Kristi Ubangiji.” Sai muka karanta: “Maryamu ta kiyayadda waɗannan al’amura, tana bimbini da su a cikin zuciyatta.” Ta yi bimbini bisa waɗannan kalaman kuma ta ƙarfafa daga gare su.—Luka 2:11, 16-19.
Mu kuma fa? Wataƙila za mu fuskanci azaba a rayuwa. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ‘lokaci da zarafi’ sukan iya shafan kowannenmu, su sa mu cikin wahala da ƙalubale. (Mai-Wa’azi 9:11) Idan hakan ya faru, muna yin fushi, kuma mu ɗaura wa Allah laifi? Zai yi kyau mu yi koyi da halin Maryamu kuma mu kusaci Jehobah Allah ta wurin koya daga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, kuma mu yi bimbini a kan abin da muka koya. Yin hakan zai taimake mu mu jimre gwaji.
Talauci da kuma Gudun Hijira
Maryamu ta fuskanci wasu wahala kuma, wato har da talauci da kuma barin ƙasarsu nan da nan. Ka taɓa fuskantar irin wannan ƙalubale kuwa? Wani rahoto ya ce: “Kusan mutane biliyan uku suna rayuwa ne a kan abin da bai kai dala biyu ba kowace rana,” kuma mutane da yawa suna ƙoƙari su sami abin biyan bukata ko da ma suna zama a ƙasashen da ke da arziki. Kai kuma fa? Neman wa iyali abinci kowace rana, sutura, da wajen kwana yakan gajiyar da kai, ya kuma sa ka damuwa?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yusufu da Maryamu talakawa ne. Yaya muka san haka? Abin da Linjilar Matta, Markus, Luka, da kuma Yohanna suka ambata game da wannan ma’aurata shi ne bayan kwana arba’in da haihuwar Yesu, Maryamu da Yusufu sun je haikali don su yi hadaya kamar yadda ake bukata, wato “kurciya biyu, ko yan tantabarai biyu.”a (Luka 2:22-24) An yi tanadin irin wannan hadayar ce don talakawa da ba za su iya ba da ɗan rago ba. Hakika, samun abin biyan bukata ba shi da sauki ga Yusufu da Maryamu. Duk da haka, sun yi nasara wajen kafa dangantaka mai kyau na iyali. Babu shakka, abubuwa na ruhaniya ne na farko a iyalinsu.—Kubawar Shari’a 6:6, 7.
Ba da daɗewa ba bayan haihuwar Yesu, rayuwar Maryamu ta sake canjawa gaba ɗaya. Mala’ika ya gaya wa Yusufu ya ɗauki iyalinsa ya gudu zuwa ƙasar Masar. (Matta 2:13-15) Wannan ne na biyu da Maryamu za ta bar inda ta saba zama, amma wannan karon za ta ƙaura zuwa wata ƙasa. A ƙasar Masar akwai Yahudawa da yawa, saboda haka wataƙila Maryamu da Yusufu sun zauna tare da mutanensu. Duk da haka, zama a wata ƙasa tana cike da ƙalubale da wahala. Kai da iyalinka kuna cikin miliyoyin mutane da suka bar ƙasarsu, wataƙila don neman abin biyan bukata na rayuwa ko kuma don ku guje wa haɗari? Idan haka ne, za ka fahimci irin wahalar da Maryamu ta fuskanta a ƙasar Masar.
Mace da kuma Uwa Mai Aminci
Banda lokacin haihuwar Yesu da kuma sa’ad da yake jariri, ba a ambata Maryamu sosai a cikin Linjila ba. Duk da haka, mun san cewa Maryamu da Yusufu suna da aƙalla yara shida bayan Yesu. Mai yiwuwa za ka yi mamaki. Amma, ka yi la’akari da abin da Linjila suka ce.
Yusufu ya daraja gatar da aka ba Maryamu na haifan Ɗan Allah. Saboda haka, bai yi jima’i da ita ba kafin a haifi Yesu. Matta 1:25; LMT ta ce Yusufu ‘bai san ta ba, sai bayan ta haifi ɗanta.’ Wannan kalmar “sai bayan” a wannan aya ta nuna cewa bayan haihuwar Yesu, Yusufu da Maryamu sun sadu. Linjilar ta ce, sakamakon haka, Maryamu ta haifa wa Yusufu yara, maza da mata. Yaƙub, Yusufu, Saminu, da Yahuda ’yan’uwan Yesu ne, uwarsu ɗaya amma ubansu dabam da Yesu. Tana kuma da aƙalla ’ya’ya mata biyu. (Matta 13:55, 56) Amma, an yi cikin waɗannan yara ta hanyar da aka saba.b
Maryamu mace ce mai ruhaniya. Ko da yake doka ba ta ce dole mata su halarci bikin Idin Ƙetarewa ba, Maryamu tana bin Yusufu zuwa Urushalima don idin. (Luka 2:41) Wannan tafiyar takan kai tsawon kusan mil 190 kowace shekara, tare da iyali mai girma. Amma wannan tafiyar abin farin ciki ne ga iyalin.
Mata da yawa a yau suna yin koyi da misali mai kyau da Maryamu ta kafa. Suna aiki sosai da kuma saɗaukar da kai don su cika hakkinsu na ruhaniya. Sau da yawa waɗannan mata masu aminci suna kasancewa da haƙuri, jimrewa, da kuma tawali’u. Yin la’akari da halin Maryamu zai taimake su su sa abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarsu. Kamar Maryamu, sun san cewa bauta wa Allah tare da mazansu da yaransu zai ƙarfafa kuma ya haɗa kan iyalin.
Lokacin da Maryamu da Yusufu suke dawowa daga idin a Urushalima, wataƙila tare da wasu ’yan’uwan Yesu, sai suka lura cewa Yesu mai shekara 12 ba ya tare da su. Za ka iya tunanin irin baƙin cikin da Maryamu ta yi a lokacin da suka yi kwana uku suna neman ɗanta? Sa’ad da ita da Yusufu suka gan shi a haikali, Yesu ya ce: “Ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin sha’anin Ubana?” Labarin ya ci gaba, Maryamu “ta riƙe dukan al’amuran nan a cikin zuciyarta.” Wannan kuma ya nuna irin ruhaniyar da Maryamu take da shi. Ta yi bimbini sosai game da dukan abubuwan da suka faru game da Yesu. Shekaru da suka wuce, wataƙila ta ambata wa waɗanda suka rubuta Linjila wannan abun da kuma wasu abubuwa da suka faru sa’ad da Yesu yake ƙarami.—Luka 2:41-52.
Jimrewa a Lokacin Wahala da Rashi
Me ya faru da Yusufu, uban Yesu na duniya? Bayan da aka yi maganarsa a lokacin da Yesu yake matashi, ba a sake ambatarsa kuma ba a cikin Linjila. Wasu sun ce wataƙila Yusufu ya mutu ne kafin Yesu ya soma hidimarsa.c Ko da menene ya faru, kamar Maryamu ta zama gwauruwa a ƙarshen hidimar Yesu. Saboda kafin ya mutu Yesu ya ba manzo Yohanna amanar mamarsa. (Yohanna 19:26, 27) Idan Yusufu yana da rai Yesu ba zai yi hakan ba.
Maryamu da Yusufu sun fuskanci abubuwa da yawa tare! Mala’ika ya ziyarce su, sun tsira daga hannun azzalumi, sau da yawa sun yi ƙaura daga inda suke da zama, kuma sun yi renon yara da yawa. Sau nawa ne suke zama tare da yamma suke tattaunawa game da Yesu, suke tunanin abin da zai fuskanta a nan gaba, suka damu ko suna yi masa wasiha kuma suna shirya shi a hanyar da ta dace? Ba da daɗewa ba sai Maryamu ta rage ita kaɗai.
Ka taɓa rasa matarka? Har yanzu kana jin zafin rashin da kuma kewa da irin wannan rashi yake kawowa har ma bayan shekaru da yawa? Babu shakka, Maryamu ta sami ƙarfafawa a addininta da kuma sanin cewa akwai ranar tashin matattu.d (Yohanna 5:28, 29) Waɗannan alkawuran masu ƙarfafawa ba su cire wa Maryamu matsaloli ba. Kamar mata gwauraye a yau, ta yi wahalar kula da yaranta ba tare da maigidanta ba.
Za a iya yarda cewa Yesu ne ya zama mai yi wa iyalin tanadin abinci lokacin da Yusufu ya mutu. Sa’ad da ’yan’uwan Yesu suka yi girma, za su karɓi na su hakkin na kula da iyalin. Sa’ad da Yesu “yana wajen shekara talatin” ya bar gida kuma ya soma hidimarsa. (Luka 3:23) Yawancin iyaye sukan yi murna da kuma baƙin ciki idan yaro ya bar gida. Iyaye suna ba da lokaci sosai, kuma suna nuna ƙauna ga yara, shi ya sa suke baƙin ciki sosai sa’ad da suka bar gida. Wani ɗanka ko ’yarka ta ko ya bar gida don su cim ma makasudinsu? Kana alfahari da su, amma wani lokaci kana jin kamar da suna kusa da kai? Idan haka ne, ka yi tunanin yadda Maryamu ta ji sa’ad da Yesu ya bar gida.
Ƙalubale da Ba a Zata Ba
Wani ƙalubale shi ne wanda Maryamu ba ta taɓa tsammani ba. Yayin da Yesu yake wa’azi, mutane da yawa sun bi shi, amma banda ’yan’uwansa. Nassin ya ce: “’yan’uwansa ba su bada gaskiya gareshi ba.” (Yohanna 7:5) Babu shakka, Maryamu ta gaya musu abin da mala’ikan ya ce mata, cewa Yesu “Ɗan Allah” ne. (Luka 1:35) Duk da haka, ga Yaƙub, Yusufu, Saminu, da kuma Yahuda, Yesu ɗan’uwansu ne kawai. Maryamu ta kasance a cikin iyali mai addini dabam dabam.
Maryamu ta daina ƙoƙarin da take yi don ta canja ra’ayin yaranta ne? A’a! Wani lokaci sa’ad da Yesu yake wa’azi a Galili, ya je wani gida don ya ci abinci, sai mutane suka taro don su saurare shi. Su wanene suke nemansa a waje? Maryamu da ’yan’uwan Yesu. Sa’ad da Yesu ya yi kusa da gidansu, ta bi shi tare da yaranta, wataƙila za su canja ra’ayinsu game da shi.—Matta 12:46, 47.
Wataƙila kana fuskantar matsi don kana bin Yesu amma sauran iyalinka ba sa son so bi shi. Kada ka yi sanyin gwiwa kuma kada ka daina ƙarfafa iyalinka su bi Yesu! Kamar Maryamu, mutane da yawa suna jimrewa a wajen ƙarfafa iyalinsu har na shekaru da yawa kafin su ga wani canji a halinsu. Irin wannan jimrewa yana da tamani a wajen Allah, ko da mutane sun canja ko ba su canja ba.—1 Bitrus 3:1, 2.
Ƙalubale Mafi Wuya
Wannan gwaji na ƙarshe ga Maryamu kamar yadda aka rubuta a Nassosi, wato, wataƙila shi ne ya jawo mata ɓacin ciki sosai. Tana kallo ƙaunataccen ɗanta ya mutu cikin azaba bayan da mutanen garinsu suka ƙi shi. Mutuwar yaro kamar yadda aka kwatanta shi ne “babban rashi,” “mutuwa mai ɓarna,” ko yaron matashi ne ko babba. Kamar yadda aka faɗa shekaru goma da suka wuce, Maryamu ta ji kamar an soke ta da takobi.—Luka 2:34, 35.
Maryamu ta bar wannan gwaji na ƙarshe ya lalata ko kuma ya sa bangaskiyarta ga Jehobah ya yi sanyi ne? A’a. Sa’ad da aka sake ambata Maryamu a cikin Littafi Mai Tsarki, tana tare da almajiran Yesu, ‘tana lizima cikin addu’a’ tare da su. Kuma ba ita kaɗai ba ne. Sauran ’ya’yanta maza, waɗanda yanzu sun ba da gaskiya ga yayansu, suna tare da ita. Hakan ya ƙarfafa Maryamu sosai!e—Ayukan Manzanni 1:14.
Maryamu ta yi rayuwa mai gamsarwa a matsayinta ta mace, da kuma uwa mai aminci. Tana da albarka da yawa na ruhaniya. Ta sha kan gwaji da jarrabobi da yawa. Sa’ad da muka fuskanci ƙalubale da ba mu zata ba ko kuma idan muna damuwa saboda matsalar iyali, za mu iya koyo daga misalinta na jimrewa cikin aminci.—Ibraniyawa 10:36.
Duk da haka, me za a iya cewa game da bauta wa Maryamu? Labarin Maryamu a cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ta cancanci a bauta mata ne?
[Hasiya]
a Ta ba da ɗaya daga cikin tsuntsun hadaya ta zunubi. (Leviticus 12:6, 8) Ta wurin ba da hadayar, Maryamu ta fahimci cewa, kamar dukan ’yan adam ajizai, ta gāji zunubin Adamu, mutum na farko.—Romawa 5:12.
b Ka dubi akwatin nan “Yesu Yana da ’Yan’uwa Maza da Mata?”
c An lura cewa rashin ambatar Yusufu a labarin hidimar Yesu ya nuna cewa ya riga ya rasu, saboda an ambaci wasu daga cikin iyalinsa, kamar mamarsa, ’yan’uwansa maza da mata. A bikin aure da aka yi a Kana, alal misali, mun ji cewa Maryamu tana kai da komowa har ta yi wa Yesu magana ya taimaka, amma ba a ambata Yusufu ba. (Yohanna 2:1-11) A wani lokaci kuma, mun karanta cewa wasu mutane daga garinsu Kristi suna kiran Yesu, “ɗan Maryamu” ba ɗan Yusufu ba.—Markus 6:3.
d Don karin bayani game da alkawarin tashin matattu a cikin Littafi Mai Tsarki, ka duba babi na 7 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
e Ka duba akwatin nan “Ta Kasance da Gaba Gaɗi don ta Canja Addininta,” a shafi na 7.
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 6]
Shin Yesu Yana da ’Yan’uwa Maza da Mata Ne?
Hakika, yana da su. Wasu ’yan tauhidi sun yi ƙoƙari su ƙaryata wannan batun, ko da yake sau da yawa Linjila sun faɗi hakan. (Matta 12:46, 47; 13:54-56; Markus 6:3) Amma, masanan Littafi Mai Tsarki sun faɗi abubuwa biyu game da ra’ayoyi da ya sa suka ce Maryamu ba ta haifi wasu ’ya’ya ba. Na farko, akwai dalilin da ya sa ake ɗaukaka waɗannan ra’ayoyin, don a goyi bayan koyarwa da ta taso ne daga baya, wato, koyarwar da coci take yi cewa Maryamu ta kasance budurwa har ƙarshen rayuwarta. Na biyu, idan aka nazarci ra’ayoyin za a ga cewa ba su da gaskiya.
Alal misali, ɗaya daga cikin ra’ayoyin shi ne “’yan’uwan” Yesu da aka ambata ’ya’yan Yusufu ne daga matarsa ta farko. Wannan zance ba shi da gaskiya ko kaɗan, saboda idan haka ne Yesu ba zai kasance ɗan fari da zai gaji sarautar Dauda ba.—2 Samuila 7:12, 13.
Wani hasashe kuma shi ne wai waɗannan ’yan’uwan Yesu ’ya’yan kawunsa ne, ko da yake Nassosin Hellenanci sun yi amfani da kalamai dabam dabam wa “ɗan’uwa,” “ɗan kawu,” da kuma “dangi.” Saboda haka, wani masani Frank E. Gaebelein ya ce wannan hasashe ba gaskiya ba ne. Ya kammala da cewa: “Yadda ya kamata a fahimci wannan kalmar ‘’yan’uwa’ . . . shi ne yana nufin ’ya’yan Maryamu da Yusufu kuma ’yan’uwan Yesu, uwa ɗaya.”
[Akwati da ke shafi na 7]
Ta Kasance da Gaba Gaɗi Ta Yi Canji
An haifi Maryamu a iyalin Yahudawa, kuma tana bin addinin Yahudawa. Tana zuwa majami’a, wato, inda Yahudawa suke zuwa bauta, kuma tana zuwa haikali a Urushalima. Sa’ad da ta sami ƙarin sanin nufin Allah, sai ta fahimta cewa Allah bai amince da al’adun iyayenta ba. Shugabannin addinin Yahudawa ne suka kashe ɗanta Almasihu. Kafin hakan ya faru, Yesu ya sanar da su: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Matta 23:38) Allah zai janye albarkarsa daga addinin da aka yi renon Maryamu ciki.—Galatiyawa 2:15, 16.
Sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, wataƙila Maryamu ta kusa shekara 50. Menene za ta yi? Ta yi tunanin cewa an haife ta a cikin addinin Yahudawa kuma tana son ta kasance da aminci ga al’adun iyayenta? Ta ce ta tsufa ba za ta iya yin canji ba? A’a! Maryamu ta fahimci cewa albarkar Allah tana tare da ikilisiyar Kirista, shi ya sa ta gaskata kuma ta kasance da gaba gaɗi don ta canja addininta.
[Hotunan da ke shafi na 5]
Gudun hijira zuwa ƙasar Masar
[Hotunan da ke shafi na 8]
Baƙin ciki sosai da uwa za ta iya fuskanta