Fahimtar “Nufin Kristi”
“Wanene ya gane nufin Ubangiji, da za ya koya masa? Amma nufin Kristi yana wurinmu.”—1 KORINTHIYAWA 2:16.
1, 2. A cikin Kalmarsa, menene Jehovah ya ga ya dace ya bayyana game da Yesu?
YAYA kamanin Yesu yake? Wane launi ne gashinsa? fatarsa? da kuma ƙwayoyin idanunsa? Yaya tsawonsa? Yaya nauyinsa? Yadda aka zana Yesu a cikin dukan ƙarnuka ya bambanta daga mai kyau har zuwa wanda ba daidai ba. Wasu sun zana shi namiji ne mai hankali, wasu kuma sun zana shi rago mara fara’a.
2 Amma dai, Littafi Mai-Tsarki, bai mai da hankali ga kamanin Yesu ba. Maimakon haka, Jehovah ya ga ya dace ya bayyana abin da ya fi muhimmanci: irin mutumin da Yesu yake. Labaran Lingila sun faɗi abin da Yesu ya yi, ban da haka ma ta bayyana zurfin juyayi da irin tunani da ya rinjayi furci da kuma ayyukansa. Waɗannan hurarrun labarai guda huɗu sun taimake mu mu bincika abin da manzo Bulus ya kira “nufin Kristi.” (1 Korinthiyawa 2:16) Yana da muhimmanci mu san tunani, juyayi, da kuma mutumtakar Yesu. Me ya sa? Aƙalla saboda dalilai guda biyu.
3. Sarƙuwa da nufin Kristi zai ba mu wane fahimi?
3 Na farko, nufin Kristi ya sa mu ɗan leƙa nufin Jehovah Allah. Yesu ya sarƙu da Ubansa ƙwarai shi ya sa ya ce: “Dukan abu Ubana ya bayas a gareni: kuma ba wanda ya sansance ko wanene Ɗan, sai Uban; ba kuwa wanda ya sansance ko wanene Uban, sai Ɗan, da dukan wanda Ɗan ya ke nufa shi bayana masa.” (Luka 10:22) Kamar dai Yesu yana cewa ne, ‘Idan kana so ka san yadda Jehovah yake, ka kalle ni.’ (Yohanna 14:9) Saboda haka, yayin da muka yi nazarin abin da Lingila ta bayyana game da yadda Yesu yake tunani da kuma yadda yake juyayi, a taƙaice, muna koyon yadda Jehovah yake tunani ne da kuma juyayi. Irin wannan sanin yana taimaka mana mu matsa kusa da Allahnmu.—Yaƙub 4:8.
4. Idan da gaske za mu aikata abu kamar yadda Kristi ya yi, menene dole mu koya da farko, kuma me ya sa?
4 Na biyu, im mun san nufin Kristi zai taimake mu ‘mu bi sawunsa a tsanake.’ (1 Bitrus 2:21) Bin Yesu ba batun maimaita kalmominsa da kuma yin abin da ya yi ba ne kawai. Tun da tunani da juyayi suna rinjayar furci da kuma ayyukan mutum, bin Kristi yana bukatar mu kasance da “hali” da yake da shi. (Filibbiyawa 2:5) A wata hanya, idan muna so da gaske mu zama kamar Kristi, tilas ne da farko mu koyi yin tunani da juyayi kamar nasa, iyakar gwargwadon iyawarmu ajizai. Saboda haka, bari mu bincika nufin Kristi ta wurin taimakon marubutan Lingila. Da farko za mu bayyana abubuwa da suka rinjayi yadda Yesu ya yi tunani da kuma juyayi.
Rayuwarsa Kafin Ya Zama Mutum
5, 6. (a) Wane tasiri abokanmu za su iya yi a kanmu? (b) Wace dangantaka ce Ɗan fari na Allah yake da shi a sama kafin ya zo duniya, kuma wane tasiri wannan ya yi a kansa?
5 Abokanmu na kurkusa za su iya shafan rayuwarmu, za su iya su rinjayi tunaninmu, juyayinmu, ayyukanmu ya zama nagari ko mummuna.a (Misalai 13:20) Ka yi la’akari da dangantaka na Yesu a sama kafin ya zo duniya. Lingilar Yohanna ta yi maganar rayuwar Yesu kafin ya zama mutum, cewa “Kalman” ne, ko kuwa Kakaki na Allah. Yohanna ya ce: “A cikin farko akwai Kalma, Kalman kuwa tare da Allah ne, Kalman kuwa wani allah ne. Wannan a cikin farko tare da Allah yake.” (Yohanna 1:1, 2, NW ) Tun da yake Jehovah ba shi da mafari, zaman Kalman tare da Allah “cikin farko” yana nufin fara halitta ne da Allah ya yi. (Zabura 90:2) Yesu “ɗan fari ne gaban dukan halitta.” Saboda haka, ya rayu kafin wasu halittu na ruhu da kuma sararin samaniya ta zahiri.—Kolossiyawa 1:15; Ru’ya ta Yohanna 3:14.
6 Wasu masana kimiyya sun kimanta, cewa sararin samaniya ta zahiri ta wanzu na aƙalla shekara biliyan 12. Idan kimantawar gaskiya ce, Ɗan fari na Allah ya more dangantaka na kurkusa da Ubansa na shekaru aru-aru kafin a halicci Adamu. (Gwada da Mikah 5:2.) Da haka, ƙauna da kuma gami na ƙwarai ya kasance tsakanin su biyun. Da aka kwatanta shi da hikima, Ɗan farin nan kafin ya zama mutum yana cewa: “Kowace rana ni ne abin daulassa [Jehovah], kullum ina farinciki a gabansa.” (Misalai 8:30) Babu shakka ɓad da shekaru babu iyaka na dangantaka ta kurkusa da Tushen ƙauna ya yi tasiri sosai bisa Ɗan Allah! (1 Yohanna 4:8) Wannan Ɗan ya gano tunani, juyayi, da kuma hanyoyin Ubansa ya kuma bayyana su yadda babu wani wanda zai iya.—Matta 11:27.
Rayuwa a Duniya da Kuma Tasiri
7. Wane dalili ɗaya ne ya sa ya zama wajibi wa Ɗan fari na Allah ya zo duniya?
7 Ɗan Allah yana da abubuwa da yawa da zai koya, domin nufin Jehovah shine ya shirya Ɗansa ya zama Babban Firist da zai iya ‘tausaya ma kumamancinmu.’ (Ibraniyawa 4:15) Don ya cika abin da ake bukata don wannan aikin shine dalili ɗaya da ya sa Ɗan ya zama mutum ya zo duniya. Anan, da ya zama mutum mai nama da jini, Yesu ya fuskanci yanayi da tasiri waɗanda a dā lura kawai yake yi daga samaniya. Yanzu ya ji yadda mutane suke ji kuma da damuwarsu da kansa. A wasu lokutta ya gaji, ya ji ƙishi, da kuma yunwa. (Matta 4:2; Yohanna 4:6, 7) Fiye da haka ma, ya jimre wuya iri iri da kuma wahala. Da haka ya “koya biyayya,” ya zama cikakke da ya cancanta ya zama a matsayinsa na Babban Firist.—Ibraniyawa 5:8-10.
8. Menene muka sani game da lokacin da Yesu yake ƙarami a duniya?
8 Yaya batun abubuwa da Yesu ya fuskanta lokacin da yake yaro a duniya? Labarin yarantakarsa ba shi da tsawo. Matta da Luka ne kawai suka bada labarin abubuwan da suka faru lokacin haihuwarsa. Marubutan Lingila sun sani cewa Yesu ya rayu a sama kafin ya zo duniya. Wancan rayuwarsa kafin ya zama mutum, ya bayyana irin mutumin da ya zama, fiye da kome. Duk da haka, Yesu mutum ne cikakke. Ko da yake kamili ne, dole ne ya yi girma daga jariri ya yi yarantaka ya yi samartaka ya isa mutum, a duk wannan lokacin yana koyo. (Luka 2:51, 52) Littafi Mai-Tsarki ya bayyana wasu abubuwa game da lokacin da Yesu yake ƙarami wanda babu shakka ya shafe shi.
9. (a) Menene ya nuna cewa an haifi Yesu a cikin iyali mai talauci? (b) A cikin wane irin yanayi ne mai yiwuwa Yesu ya yi girma?
9 Hakika, an haifi Yesu a cikin iyali mai talauci. Hadaya da Yusufu da Maryamu suka kawo haikali kusan kwanaki 40 bayan haihuwar Yesu ne ya nuna haka. Maimakon su kawo ɗan rago don hadaya ta ƙonawa da kuma ’yar ƙurciya ko tantabara don hadayan zunubi, sun kawo “kurciya biyu, ko ’yan tantabarai biyu.” (Luka 2:24) Bisa ga Dokar Musa, wannan hadaya tanadi ne wa matalauta. (Leviticus 12:6-8) Da shigewar lokaci, wannan iyali mara abin hannu ya yi girma. Yusufu da Maryamu suka haifi aƙalla ƙarin ’ya’ya shida bisa halin halitta bayan haihuwar Yesu ta mu’ujiza. (Matta 13:55, 56) Saboda haka Yesu ya yi girma a iyali mai girma, mai yiwuwa a yanayi da ba na almubazzaranci ba.
10. Me ya nuna cewa Maryamu da Yusufu mutane ne masu tsoron Allah?
10 Iyaye masu tsoron Allah ne suka yi renon Yesu waɗanda suka kula da shi. Uwarsa, Maryamu, mace ce ta ƙwarai. Ka tuna lokacin da Jibrailu ya gaishe ta ya ce: “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke.” (Luka 1:28) Yusufu ma mutum ne mai ibada. Kowace shekara cikin aminci yana tafiya kilomita 150 zuwa Urushalima don idin Faska. Maryamu ma ta halarta, ko da yake maza ne kawai aka bukace su su yi haka. (Fitowa 23:17; Luka 2:41) A irin wannan lokacin, Yusufu da Maryamu, bayan sun neme shi a hankali, sun sami Yesu ɗan shekara 12 a cikin haikali a tsakanin malamai. Ga iyayensa da sun damu, Yesu ya ce: “Ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin sha’anin Ubana?” (Luka 2:49) ‘Uba’—wannan kalmar babu shakka ta cika ɗan yaro Yesu da nufi mai kyau na ƙauna. Babu shakka, an gaya masa cewa Jehovah ne Ubansa na ainihi. Ƙari ga haka, lallai Yusufu uban rana ne mai kyau na Yesu. Babu wata tantama cewa Jehovah ba zai zaɓi mutum matsananci ko azzalumi ya yi renon Ɗansa da Yake ƙauna ba!
11. Wane aiki Yesu ya koya, kuma a lokuttan Littafi Mai-Tsarki, menene wannan aikin ya ƙunsa?
11 Cikin shekaru da ya yi a Nazarat, Yesu ya koyi sassaƙa, mai yiwuwa a wurin ubansa na rana, Yusufu. Yesu ya ƙware a aikin har shi kansa an kira shi “masassaƙin.” (Markus 6:3) A lokuttan Littafi Mai-Tsarki, ana ɗaukan masassaƙa a aikin gina gidaje, ƙaga kayayyakin ɗaki (haɗe da teburā, kujeru, da bencuna), da kuma yin kayayyakin noma. Justin Martyr, na ƙarni na biyu A.Z. ya rubuta game da Yesu a cikin Dialogue With Trypho: “Yana da halin aikin sassaƙa lokacin da yake tsakanin mutane, yana yin garemani da kuma taula.” Irin wannan aikin ba shi da sauƙi, domin masassaƙi na dā wataƙila ba zai sayi katakonsa ba. Mai yiwuwa, zai je ya zaɓi itace, ya tsare, ya kwashi katako zuwa gida. Saboda haka Yesu ya san kalubalan neman abinci, hurɗa da masu ciniki, da kuma biyan bukata.
12. Menene ya nuna cewa babu shakka Yusufu ya mutu kafin Yesu, kuma menene wannan ya nufa ma Yesu?
12 Tun da yake shine ɗan fari, wataƙila Yesu ya taimaka wajen kula da iyalin, musamman ma tun da yake Yusufu ya mutu kafin Yesu.b Zion’s Watch Tower na 1 ga Janairu, 1900 (Turanci), ta ce: “Al’ada ta nuna cewa Yusufu ya mutu lokacin da Yesu yana ƙarami, kuma cewa na bayan ya ɗauki sana’an masassaƙa kuma ya zama mai lura da iyalin. Wannan yana da goyon bayan Nassi inda aka kira Yesu da kansa masassaƙi, aka ambaci uwarsa da yan’uwansa, amma aka ƙyale Yusufu. (Markus 6:3) . . . Da alamar cewa, shekara ɗai ɗai har goma sha takwas na rayuwar Ubangijinmu, daga lokacin aukuwa [da ke rubuce a cikin Luka 2:41-49] zuwa lokacin baftismarsa, ya ɓad da su wajen tafiyar da rayuwan yau da kullum ne.” Maryamu da ’ya’yanta, haɗe da Yesu, mai-yiwuwa ne sun san zafin yin rashin Uba ƙaunatacce da kuma maigida.
13. Lokacin da Yesu ya fara hidimarsa, me ya sa ya yi hakan da sani, fahimi, da kuma juyayi mai zurfi da babu wani mutum da ya taɓa kasance da shi?
13 Babu shakka, ba a haifi Yesu cikin rayuwar jin daɗi ba. Maimakon haka, ya fuskanci rayuwar matalauta da kansa. Sai, a shekara ta 29 K.Z., lokaci ya kai da Yesu zai ɗauki aiki da ke jiransa wanda Allah ya ba shi. A farkon shekarar, aka yi masa baftisma cikin ruwa kuma aka haife shi ya zama Ɗan Allah a ruhaniya. ‘Sama ta buɗe masa,’ babu shakka wannan yana nuna cewa zai iya tuna rayuwarsa a sama kafin ya zama mutum, haɗe da tunani da kuma juyayi da ke ciki. (Luka 3:21, 22) Saboda haka lokacin da Yesu ya fara hidimarsa, ya yi hakan da sani, fahimi, da kuma juyayi mai zurfi da babu wani mutum da ya taɓa kasance da shi. Da kyakkyawan dalili marubutan Lingila suka bada ƙarfi a rubutunsu game da aukuwa na hidimar Yesu. Duk da haka, sun kasa rubuta dukan abin da ya ce da kuma abin da ya yi. (Yohanna 21:25) Amma abin da aka hure su su rubuta ya taimake mu mu bincika nufin mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa.
Yadda Yesu Yake Yayin da Yake Mutum
14. Ta yaya marubutan Lingila suka kwatanta Yesu mutum ne wanda yake da sauƙin kai kuma da juyayi na ƙwarai?
14 Mutumtakar Yesu da ke bayane a cikin Lingila, na mutum ne wanda yake da sauƙin kai da kuma juyayi na ƙwarai. Ya nuna damuwa mai yawa: ya tausaya wa kuturu (Markus 1:40, 41); ya yi baƙin ciki domin mutane da ba sa na’am (Luka 19:41, 42); ya yi fushi akan masu musanyan kuɗi masu haɗama (Yohanna 2:13-17). Mutum ne mai juyayi, Yesu ya yi hawaye, kuma bai ɓoye damuwarsa ba. Lokacin da abokinsa Li’azaru ya mutu, da ya ga Maryamu ƙanwar Li’azaru tana kuka, sai abin ya taɓa Yesu ƙwarai, shi kansa ya yi hawaye, ya yi kuka a idon mutane.—Yohanna 11:32-36.
15. Yaya damuwa na Yesu ya bayyana a yadda yake ɗaukan wasu da kuma yadda yake bi da su?
15 Juyayi na Yesu musamman ma sun bayyana ne a yadda yake ɗaukan wasu da kuma yadda yake bi da su. Ya je wajen matalauta da kuma waɗanda ake zalunta su, ya taimake su suka ‘sami wartsakewa.’ (Matta 11:4, 5, 28-30) Bai shagala ba yadda ba zai iya biyan bukatun waɗanda suke wahala, ko ta mace mai zuban jini da ta taɓa rigarsa a ɓoye ko makaho mai bara da ya ƙi yin shuru. (Matta 9:20-22; Markus 10:46-52) Yesu yana duba halin kirki ne da mutane suke da shi kuma ya yaba masu; duk da haka, yana bada gargaɗi inda bukata ta kama. (Matta 16:23; Yohanna 1:47; 8:44) A lokaci da ’yancin mata kaɗan ne kawai, Yesu ya bi da su cikin daraja da ladabi daidai wa daida. (Yohanna 4:9, 27) Saboda haka, wani rukunin mata suka yi masa hidima daga cikin nasu aljihu.—Luka 8:3.
16. Me ya nuna cewa Yesu ya ɗauki rayuwa yadda ya kamata da kuma abin duniya?
16 Yesu ya ɗauki rayuwa yadda ya kamata. Abin duniya ba su ne suka sha masa kai ba. Dukiya ma, kusan kamar ba shi da ita. Ya ce bai da “wurin da za ya kwanta.” (Matta 8:20) A wannan lokacin, Yesu ya ƙara ma wasu farinciki. Lokacin da ya halarci wani bikin aure—abu ne wanda ake kaɗe-kaɗe, waƙe-waƙe, da kuma murna—babu shakka cewa ba ya je don ya tada bikin ba. Hakika, a wurin Yesu ya yi mu’ujizansa ta farko. Lokacin da giya ya ƙare, ya mayar da ruwa ya zama giya mai kyau, barasa da take “sa zuciyar mutum ta wartsake.” (Zabura 104:15; Yohanna 2:1-11) Da haka bikin ya ci gaba, babu shakka ya kawar da ango da amarya daga shan kunya. Daidaitawarsa ta bayyana kuma a wasu lokutta da aka ambata Yesu ya yi aiki sosai kuma na dogon lokaci a hidimarsa.—Yohanna 4:3.
17. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa Yesu Ƙwarerren Malami ne, kuma menene koyarwarsa ta nuna?
17 Yesu Ƙwarerren Malami ne. Da yawa cikin koyarwarsa ya nuna gaskiyar rayuwa na yau da kullum, wanda ya sani sosai. (Matta 13:33; Luka 15:8) Yadda yake koyarwa ba ta da kama—a bayyane sarai, da sauƙi, kuma da sauƙin aikatawa. Wanda ma ya fi muhimmanci shine abin da ya koyar. Koyarwarsa ya nuna muradin zuciyarsa na son ya sanar ma masu sauraronsa, tunani, juyayi, da kuma tafarkin Jehovah.—Yohanna 17:6-8.
18, 19. (a) Da wane irin kwatanci Yesu ya kwatanta Ubansa? (b) Menene za a bayyana a cikin talifi na gaba?
18 Sau da yawa ta yin amfani da alamu, Yesu ya bayyana Ubansa sarai da kwatanci da ba za a manta da shi da wuri ba. Abu ɗaya ne a yi maganar jinƙai na Allah galiba. Wani abu ne dabam kuma a kwatanta Jehovah da uba mai gafartawa wanda ganin ɗansa da ya komo ya motsa shi ‘ya ruga a guje, ya faɗa ma wuyansa, ya yi ta yi masa sumba.’ (Luka 15:11-24) Ya ƙi al’ada mai tsanani wanda shugabannan addini suke ƙyamar talakawa, Yesu ya yi bayani cewa Ubansa Allah wanda za a iya zuwa gabansa ne wanda ya gwamance addu’ar mai karɓan haraji maimakon addu’ar Ba-farisi mai fahariya. (Luka 18:9-14) Yesu ya kwatanta Jehovah cewa Allah ne mai kula wanda ya san lokacin da ɗan ƙaramin gwarare ya faɗi ƙasa. “Kada ku ji tsoro fa; kun fi gwarare masu-yawa daraja,” Yesu ya tabbatar ma almajiransa. (Matta 10:29, 31) Babu shakka, mutane sun yi mamakin ‘hanyar koyarwar’ Yesu kuma suka matso kusa da shi. (Matta 7:28, 29) Shi ya sa, wani lokaci “taro mai-yawa” suka zauna tare da shi kwana uku, babu abinci!—Markus 8:1, 2.
19 Za mu yi godiya wa Jehovah da ya bayyana nufin Kristi a cikin Kalmarsa! Yaya kuwa, za mu gina nufin Kristi kuma mu yi amfani da shi a sha’aninmu da wasu? Za a bayyana wannan a cikin talifi na gaba.
[Hasiya]
a Ru’ya ta Yohanna 12:3, 4, ta nuna cewa halittu na ruhu ma tarayyarsu suna iya rinjayar su. A can an kwatanta Shaitan da “dragon” wanda ya yi amfani da tasirinsa ya rinjayi wasu “taurari,” ko ’ya’yan ruhu, su bi shi a tafarkin tawaye.—Gwada da Ayuba 38:7.
b Ƙarshen ambatan Yusufu kai saye shine tun lokacin da Yesu yana ɗan shekara 12 da aka same shi a cikin haikali. A farkon hidimar Yesu, ba a ambaci cewa Yusufu yana wajen bikin aure a Cana ba. (Yohanna 2:1-3) A shekara ta 33 K.Z., Yesu da aka rataye shi ya danka Maryamu a hannun manzo da yake ƙauna Yohanna. Wannan abu ne da ƙila Yesu ba zai yi ba idan Yusufu yana da rai a lokacin.—Yohanna 19:26, 27.
Ka Tuna?
• Me ya sa yana da muhimmanci mu san “nufin Kristi”?
• Wace dangantaka ce Yesu ya yi a rayuwarsa kafin ya zama mutum?
• Lokacin rayuwarsa a duniya, wane yanayi da kuma tasiri ne Yesu ya fuskanta da kansa?
• Menene Lingila ta bayyana game da mutumtakar Yesu?
[Hoto a shafi na 3]
Yesu ya yi girma ne a cikin babban iyali, mai-yiwuwa a yanayi da ba na almubazaranci ba
[Hotuna a shafi na 5]
Malaman sun yi mamakin fahimta na Yesu ɗan shekara 12