RAYUWAR KIRISTA
Ba a Ɓarnatar da Kome Ba
Bayan Yesu ya ciyar da maza 5,000 da kuma mata da yara ta hanyar mu’ujiza, ya umurci almajiransa cewa: “Ku tattara gutsattsarin da suka ragu domin kada kome ya lalace.” (Yoh 6:12) Yesu ya nuna cewa ya daraja tanadin da Jehobah ya yi, shi ya sa bai yi ɓarna da abincin da ya ragu ba.
A zamaninmu, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna koyi da Yesu ta wurin yin amfani da kuɗin ƙungiyar yadda ya kamata. Alal misali, ’yan’uwa sun zaɓi tsarin gini da zai sa ba za a kashe kuɗi sosai ba a lokacin da ake gina hedkwatarmu da ke Warwick, a New York.
TA YAYA ZA MU GUJI ƁARNATAR DA KUƊI . . .
sa’ad da muke taro a ikilisiya?
sa’ad da muke karɓan littattafan da za mu karanta? (km 5/09 3 sakin layi na 4)
sa’ad da muke karɓan littattafan da za mu yi wa’azi da su? (mwb17.02 4 sakin layi na 1)
sa’ad da muke wa’azi? (mwb17.02 4 sakin layi na 2, da akwati)