Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 7/1 pp. 11-13
  • Kana Cin Gurasa Mai Ba da Rai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Cin Gurasa Mai Ba da Rai?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • GURASA DA KE RAYAR DA ƊAN ADAM
  • GURASA MAI BA DA RAI
  • Me Muka Koya Daga Yadda Yesu Ya Ciyar da Mutane da Burodi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • “Menene Za Mu Ci?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 7/1 pp. 11-13

Kana Cin Gurasa Mai Ba da Rai?

MASU yawon buɗe idon sun soma jin yunwa. Yawon da suka yi don ganin kayayyakin tarihi a cikin tsohon birnin Bai’talami ya sa su marmarin cin ainihin abincin birnin. Sai wani a cikinsu ya hango shagon da ake sayar da wani irin abinci da ake kira falafel. Ana yin wannan abincin ne da wani irin wake da tumatiri da albasa da dai wasu kayan lambu kuma ana cin sa da gurasar pita bread. Wannan abincin ya ba su ƙarfin ci gaba da yawon buɗe idon.

Waɗannan baƙin ba su san cewa wannan gurasar tana ɗaya daga cikin kayayyakin tarihi mafi muhimmanci da suka gani a ranar ba. Wannan suna Bai’talami, yana nufin “Gidan Gurasa” ne, kuma an yi dubban shekaru ana toya gurasa a birnin. (Ruth 1:22; 2:14) A yau, gurasar pita bread tana ɗaya daga cikin ainihin gurasar birnin Bai’talami.

Shekaru kusan dubu huɗu da suka shige, matar Ibrahim, wato Saratu, ta toya gurasa wa baƙi guda uku da suka samu, a lokacin da suke zama kusa da Bai’talami daga ta kudu. (Farawa 18:5, 6) “Gari mai-laushi” da Saratu ta yi amfani da shi wataƙila da alkama ko kuma sha’ir aka yi shi. Saratu ta toya gurasar da sauri, kuma mai yiwuwa ta yi amfani da duwatsu masu zafi a yin hakan.—1 Sarakuna 19:6.

Kamar yadda wannan labarin ya nuna, iyalin Ibrahim suna toya gurasarsu da kansu. Wataƙila domin irin rayuwar makiyaya da suke yi a lokacin, Saratu ko kuma bayinta ba su toya gurasarsu a tanderu kamar yadda ake yi a ƙasar Ur, garin su Saratu ba. Ta yi garin da irin hatsin da suke da shi. Babu shakka wannan aikin ba shi da sauƙi domin da dutsen niƙa ne ake yi, kuma a wasu lokatai, akan yi amfani da turmi da taɓarya.

Shekaru 400 bayan hakan, Doka da aka bayar ta hannun Musa ta ce bai dace mutum ya karɓi dutsen niƙa don jingina ba, da yake “ran mutum” ne, wato, da shi ake niƙa garin abinci. (Kubawar Shari’a 24:6) Allah ya ɗauki dutsen niƙa da muhimmanci domin da ita ne iyalai suke niƙa garin da suke yin gurasa ko kuma abinci da shi kowace rana.—Ka duba akwatin nan “Yadda Ake Yin Niƙa da Kuma Gurasa a Zamanin Dā.”

GURASA DA KE RAYAR DA ƊAN ADAM

Littafi Mai Tsarki ya ambata gurasa sau da yawa. Hakan ya nuna cewa gurasa abinci ne mai muhimmanci a zamanin dā. Saboda muhimmancinta marubutan Littafi Mai Tsarki suna yawan yin amfani da kalmar nan gurasa a madadin abinci. Yesu ya nuna cewa waɗanda suke bauta wa Allah za su iya yin addu’a cewa: “Ka ba mu yau abincin yini.” (Matta 6:11) A nan Yesu yana nuna cewa za mu iya jingina ga Allah don ya biya bukatunmu na yau da kullum.—Zabura 37:25.

Amma akwai wani abu da ya fi gurasa ko kuma abinci muhimmanci. Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) Yesu yana magana ne game da lokacin da Isra’ilawa ba su da wanda yake yi musu tanadi sai Allah, wato jim kaɗan bayan sun bar Masar. A lokacin, sun yi wajen wata guda a Hamadar Sinai kuma abincinsu ya soma ƙarewa. Hakan ya sa suka soma tsoro cewa za su mutu da yunwa a wannan hamadar kuma suka soma gunaguni suna cewa: ‘Da ma . . . muna cin gurasa mu ƙoshi’ a Masar.—Fitowa 16:1-3.

Babu shakka cewa gurasar ƙasar Masar ta yi daɗi sosai. A zamanin Musa, ƙwararrun matoya suna toya wa Masarawa gurasa da kuma waina iri-iri. Amma ba nufin Jehobah ba ne ya bar mutanensa da yunwa. Ya yi musu alkawari cewa: “Ga shi, zan zubo muku da abinci daga sama.” Da safe, “wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo” ko kuma raɓa ya zubo daga sama. Da ganin wannan abin, sai Isra’ilawa suka soma tambaya: “Mece ce wannan?” Sai Musa ya bayyana musu cewa: “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.” Daga nan suka soma kiransa mannaa kuma shi ne abincin da suka ci har shekaru 40.—Fitowa 16:4, 13-15, 31, Littafi Mai Tsarki.

Da farko, Isra’ilawa sun ji daɗin wannan manna da aka yi tanadinsa ta mu’ujiza sosai. Ɗanɗanonsa “kamar waina ce da ake yi da zuma,” kuma kowa yana ci ya ƙoshi. (Fitowa 16:18) Amma a kwana a tashi, suka soma kwaɗayin ire-iren abincin da suka ci a Masar. Sun ce: “Ba mu da wani abu a nan, sai dai mu ga wannan manna kawai.” (Littafin Lissafi 11:6) Daga baya, sun fusata kuma suka ce: “Ranmu ya gundura da wannan mummunan abinci.” (Littafin Lissafi 21:5) Hakika wannan “abincin sama” ya zama abin ƙyama a gare su.—Zabura 105:40.

GURASA MAI BA DA RAI

Hakika, gurasa yana ɗaya daga cikin wasu abubuwa da ba a cika ɗauka da muhimmanci. Amma Littafi Mai Tsarki ya yi maganar wani irin gurasa na musamman da bai kamata a raina ba ko da wasa. Wannan gurasar da Yesu ya kwatanta da manna da Isra’ilawa suka tsana za ta iya kawo albarka na dindindin.

Yesu ya ce wa masu sauraronsa: “Ni ne gurasa ta rai. Ubanninku suka ci manna a cikin jeji, suka mutu kuma. Gurasa ke nan wadda ke saukowa daga cikin sama, har mutum ya ci, kada ya mutu. Ni ne gurasan rai mai-saukowa daga cikin sama; idan kowane mutum ya ci wannan gurasa zai rayu har abada: I kuwa, gurasa wadda zan bayar namana ne, sabili da ran duniya.”—Yohanna 6:48-51.

Masu sauraron Yesu da yawa ba su fahimci abin da yake nufi da “gurasa” da kuma ‘nama’ ta alama ba. Amma kwatancin da Yesu ya yi da waɗannan kalmomin ya dace sosai. Kamar yadda manna ta rayar da Isra’ilawa har shekaru 40 a cikin jeji, haka ma gurasa take rayar da Yahudawan kowace rana. Ko da yake Allah ne ya ba da manna, amma waɗanda suka ci ba su rayu har abada ba. Amma hadayar Yesu ta buɗe hanyar samun rai na har abada ga waɗanda suka ba da gaskiya gare shi. Hakika, Yesu ne “gurasa ta rai.”

Mai yiwuwa idan ka ji yunwa, kakan nemi gurasa ka ci kuma kakan gode wa Allah domin ya ba ka gurasa, ko kuma “abincin yini.” (Matta 6:11) Hakika, muna godiya don abinci mai daɗi. Duk da haka, kada mu manta da muhimmancin “gurasa ta rai,” wato Yesu Kristi.

Akasin Isra’ilawa marasa godiya a zamanin Musa, ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don tanadin wannan gurasar? Yesu ya ce: ‘Idan kuna ƙaunata za ku kiyaye dokokina.’ (Yohanna 14:15) Ta wajen bin dokokin Yesu, za mu iya kasancewa da begen cin gurasa har abada.—Kubawar Shari’a 12:7.

a Mai yiwuwa kalmar nan “manna” daga furucin Ibranancin nan “man hu’?” ne, wanda ke nufin “mece ce wannan?”

Yadda Ake Yin Niƙa da Kuma Gurasa a Zamanin Dā

Niƙa gārin. Mata sukan niƙa garinsu da hannu kowace rana, kuma wannan yana ɗaya daga cikin ayyukan da suke yi da safe. (Misalai 31:15; Matta 24:41) A zamanin dā, irin alkamar da mutane suka fi nomewa ita ce emmer, kuma ɓawonta ba ya barin tsabar da wuri. Wannan aikin yana da wuya domin sai an surfe hatsin a turmi ko kuma a dutsen niƙa. Da farko, ana jiƙa alkamar kuma a daka ta, sai a busar da ita. Bayan hakan, ana sheƙa alkamar domin a cire dusar kafin a soma niƙa ta.

Niƙa garin da iyali za ta ci yakan ɗauki awoyi da yawa, kuma a dā, ana yawan jin “amon dutsen niƙa” a garuruwa da dama. (Irmiya 25:10) A wasu lokatai, masu niƙa ne sukan yi niƙan a maimakon mata, ta wajen yin amfani da manya-manyan duwatsun niƙa da dabbobi suke juyawa.

Yin gurasar. Mata suna yin gurasar kowace rana bayan an yi niƙan. Matar aure takan kwaɓa garin, ta cuɗa shi, sa’an nan ta gasa gurasar. (Farawa 18:5, 6) A wasu gidaje, akan gasa gurasar da duwatsu masu zafi, amma wasu suna amfani da tanderu. (Levitikus 2:4; Ishaya 44:15) Manyan mutane kamar su Fir’auna, suna da ƙwararrun masu yi musu gurasa, amma daga baya gurasa ta zama abinci da ko talakawa ma suna iya saya. (Farawa 40:17; 1 Sama’ila 8:13) A zamanin Irmiya, an yi wata unguwar da ake kira “tafarkin matoya” kuma a zamanin Nehemiya, akwai wata hasumiya da aka sani da sunan nan “Hasumiya ta Matoya.” Dukansu a Urushalima suke.—Irmiya 37:21; Nehemiya 12:38.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba