Ka Kasance Da Irin Halin Almasihu
“Allah mai ba da haƙuri da ta’aziyya, ya ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu, Yesu.”—ROMAWA 15:5.
1. Ta yaya halin mutum zai iya shafan rayuwarsa?
HALI muhimmin abu ne cikin rayuwa. Hali na rashin kula ko halin ƙwazo, halin kirki ko mummuna, hali na faɗā ko na haɗin kai, halin gunaguni ko kuma na godiya zai iya taɓa yadda mutum zai bi da yanayi da kuma yadda wasu mutane za su ɗauke shi. Da halin kirki, mutum zai iya zama mai farin ciki ko a yanayi mai wuya ma. Ga wanda yake da mummunan hali, ba abin da ke daidai gare shi, ko idan ma—a ce cikin yanayi da—rayuwa tana da kyau.
2. Ta yaya mutum yake koyar halaye?
2 Hali—mai kyau ko mara kyau—za a iya koya. Hakika, sai an koya. Da yake magana game da jariri, Collier’s Encyclopedia ya ce: “Duk halin da ya kasance da shi lalle ya samo ne ko kuma ya koya, kamar dai yadda ake koyar wani yare ko kuma wata sana’a.” Ta yaya muke koyan halaye? Ko da yake abubuwa da yawa suna ƙunshe ciki, wurin da muke da zama da kuma abokananmu sukan shafe mu sosai. Kundin sanin nan da aka ambata ya lura da cewa: “Muna koya ko kuma bi, kamar a ce soso da ya jiƙe, haka halayen waɗanda abokanmu ne suke shafen mu.” Shekaru dubbai da suka shige, Littafi Mai Tsarki ya ambata abu mai kama da shi: “Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.”—Karin Magana 13:20; 1 Korantiyawa 15:33.
Tafarki don Halin Kirki
3. Wanene halinsa misali ne mafi kyau, kuma ta yaya za mu iya yin koyi da shi?
3 Kamar a dukan abu, haka ma a zancen hali Yesu Kristi ya kafa tafarki mafi kyau. Ya ce: “Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku.” (Yahaya 13:15) Kafin mu zama kamar Yesu, dole ne sai mun koya game da shi.a Muna nazarin rayuwar Yesu da nufin mu yi abin da manzo Bitrus ya ce: “Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.” (1 Bitrus 2:21) Burinmu shi ne, mu zama kamar Yesu idan zai yiwu. Wannan ya ƙunshi gina irin halinsa.
4, 5. Wane fannin halin Yesu ne aka taƙaita a Romawa 15:1-3, kuma ta yaya Kiristoci za su yi koyi da shi?
4 Menene kasancewa da irin halin Kristi Yesu ya ƙunsa? Sura ta 15 ta wasiƙar Bulus zuwa ga Romawa za ta taimake mu amsa wannan tambayar. A cikin ayoyi na farko na wannan surar, Bulus ya yi nuni ga halin musamman na Yesu yayin da ya ce: “To, mu da ke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai. Kowannenmu ya faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa da kuma inganta shi. Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa ‘Zagin da waɗansu suka yi maka duk ya komo kaina.’ ”—Romawa 15:1-3.
5 A yin koyi da halin Yesu, an ƙarfafa Kiristoci su yi shiri su taimaka wa masu bukatu cikin tawali’u maimakon neman su faranta wa kansu rai kawai. Hakika, irin halin taimaka wa wasun nan ‘ƙarfaffu’ ne. Yesu, wanda ya fi kowane mutum da ya taɓa rayuwa ƙarfi a ruhaniya, ya ce game da kansa: “Kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” (Matiyu 20:28) Mu Kiristoci, za mu so mu kai ga yin ma wasu hidima, haɗe da ‘raunannu.’
6. A wace hanya ce za mu iya yin koyi da yadda Yesu ya aikata wajen hamayya da zagi?
6 Wani hali nagari da Yesu ya nuna tafarki ne na yin tunani da kuma ayyuka da kullum suna da kyau. Bai taɓa ƙyale mummunar halin wasu ya rinjayi nasa hali mai kyau ba game da bauta wa Allah; mu ma kada mu ƙyale. Lokacin da aka zage shi kuma tsananta masa domin bauta wa Allah cikin aminci, Yesu ya jure cikin haƙuri ba tare da gunaguni ba. Ya sani cewa waɗanda suke ƙoƙarin su faranta wa maƙwabcinsu rai “a yin abu mai kyau domin amfaninsa” da za su yi zaton hamayya za ta zo daga duniya mara bi da kuma ganewa.
7. Ta yaya Yesu ya nuna haƙuri, kuma me ya sa za mu yi hakanan?
7 Yesu ya nuna hali nagari a wasu hanyoyi. Bai taɓa nuna rashin haƙuri ba ga Jehovah amma ya jira shi cikin haƙuri Ya cika Ƙudurinsa. (Zabura 110:1; Matiyu 24:36; Ayyukan Manzanni 2:32-36; Ibraniyawa 10:12, 13) Bugu da ƙari, Yesu bai yi rashin haƙuri da mabiyansa ba. Ya gaya musu: “Ku kuma koya a gare ni”; tun da yake shi “mai tawali’u” ne, koyarwarsa mai ginawa ce kuma mai wartsakewa ce. Kuma domin “marar girmankai” ne, bai taɓa nuna kumburi ko girman kai ba. (Matiyu 11:29) Bulus ya ƙarfafa mu mu yi koyi da irin wannan fannin halin Yesu ɗin, da ya ce: “Ku ɗauki halin Almasihu Yesu, wanda, ko da ya ke surar Allah yake, bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.”—Filibiyawa 2:5-7.
8, 9. (a) Me ya sa muke bukatar mu yi ƙoƙari don mu koyi hali mara son kai? (b) Me ya sa bai kamata mu karaya ba idan mun kasa bin tafarkin da Yesu ya bar mana, kuma ta yaya Bulus misali ne mai kyau a zancen nan?
8 Yana da sauƙi mu ce muna son mu yi ma wasu hidima kuma cewa muna son mu sa bukatunsu a gaba da namu. Amma idan muka bincika halayenmu da gaske wajen za mu ga cewa zukatanmu ba su da niyyar yin hakan. Me ya sa? Na farko, domin mun gaji son kai daga Adamu da Hauwa’u; na biyu, domin muna cikin duniya da take ɗaukaka son kai. (Afisawa 4:17, 18) Don a gina hali mara son kai, sau da yawa yana nufin a gina irin tunani da ya saɓa da yanayinmu na ajizanci. Wannan yana bukatar niyya da kuma fama.
9 Ajizancinmu, da ya saɓa sarai da kamilcaccen tafarki da Yesu ya bar mana, zai iya sa mu karaya a wasu lokatai. Muna iya shakkar cewa zai yiwu mu kasance da irin halin Yesu. Amma bari mu lura da kalmomin ƙarfafa na Bulus: “Na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da ke daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu. Nagarin abin da nake niyya kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa. Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da Shari’ar Allah. Amma ina ganin wata ka’ida dabam a gaɓoɓina, wadda ke yaƙi da ka’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ka’idan nan ta zunubi, wadda ke zaune a gaɓoɓina.” (Romawa 7:18, 19, 22, 23) A gaskiya kam, ajizancin Bulus ya hana shi sau da yawa daga cika nufin Allah yadda yake so, amma halinsa—hanyar da yake tunani da kuma yadda yake ji game da Jehovah da Dokarsa—misali mai kyau ne a gare mu. Za mu iya yin haka mu ma.
Gyara Halaye Marasa Kyau
10. Wane hali ne Bulus ya ƙarfafa Filibiyawa su koya?
10 Zai yiwu kuwa a ce wasu suna bukatar su gyara halayen da ba su da kyau? I. Wannan gaskiya ne a zancen wasu Kiristoci a ƙarni na farko. Bulus ya yi zancen kasance da hali da ke daidai a wasiƙarsa zuwa ga Filibiyawa. Ya rubuta: “Ba wai na riga na kai ga waɗannan [rai a samaniya ta tashin matattu na farko] ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a’a, sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi. Ya ’yan’uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa abin da ke gaba. Ina nacewa gaba gaba zuwa manufan nan, domin in sami ladan kiran nan zuwa sama da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu. Saboda haka ɗakwacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra’ayi.”—Filibiyawa 3:12-15, tafiyar tsutsa tamu ce.
11, 12. A waɗanne hanyoyi ne Jehovah yake bayyana mana hali da ke daidai?
11 Kalmomin Bulus sun nuna cewa duk wani bayan ya zama Kirista, idan bai ga dalilin ci gaba ba, ba hali ba ne mai kyau. Bai bi halin Kristi ba ke nan. (Ibraniyawa 4:11; 2 Bitrus 1:10; 3:14) Mutumin ba zai iya yin gyara ba ke nan? Zai iya. Allah zai iya taimakonmu mu gyara hali, idan da gaske muna son mu yi hakanan. Bulus ya ci gaba da cewa: “In kuwa game da wani abu ra’ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.”—Filibiyawa 3:15.
12 Amma, idan muna son Jehovah ya bayyana mana hali mai kyau, dole ne mu yi namu sashen. Yin nazarin Kalmar Allah da addu’a da kuma taimakon littattafai na Kirista da ake samu ta wurin “amintaccen bawan nan mai hikima” zai sa waɗanda ‘ra’ayinsu ya sha bambam’ su gina hali da ya dace. (Matiyu 24:45) Dattawan Kirista, waɗanda ruhu mai tsarki ya naɗa su su yi “kiwon Ikklisiyar Allah,” za su yi farin cikin taimakawa. (Ayyukan Manzanni 20:28) Muna godiya sosai da Jehovah ya tuna cewa mu ajizai ne kuma yana ba mu taimako mai kyau! Bari mu amshe shi.
Koya Daga Wajen Wasu
13. Menene muka koya daga hali mai kyau daga labarin Littafi Mai Tsarki na Ayuba?
13 A Romawa sura 15, Bulus ya nuna cewa yin bimbini a kan misalai na tarihi zai taimake mu mu gyara halinmu. Ya rubuta: “Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta ne domin a koya mana, domin mu ɗore cikin sa zuciyar nan tamu ta haƙuri da ta’aziyyar da Littattafai ke yi mana.” (Romawa 15:4) Wasu bayin Jehovah a lokatan dā sun bukaci su gyara halayensu. Alal misali, galibi dai Ayuba yana da hali mai kyau. Bai taɓa haɗa Jehovah da yin mugunta ba, kuma bai taɓa ƙyale wahala ta girgiza amincinsa ga Allah ba. (Ayuba 1:8, 21, 22) Duk da haka, ya ɗauki kansa ba shi da aibi. Jehovah ya sa Elihu ya taimake Ayuba ya gyara irin wannan hali. Maimakon ya ɗauka an raina shi, Ayuba ya yi na’am da bukatar gyara halinsa da yake da shi kuma ya shirya don ya yi haka.—Ayuba 42:1-6.
14. Ta yaya za mu zama kamar Ayuba idan aka gargaɗe mu game da halinmu?
14 Za mu iya yin kamar yadda Ayuba ya yi idan ɗan’uwa Kirista ya gaya mana cewa muna da ɗan halin da ba shi da kyau? Kamar Ayuba, ba mu taɓa “sa wa Allah laifi” ba. (Ayuba 1:22) Idan muna shan wahala ba dalili, ba za mu yi gunaguni ba ko mu ɗaura wa Jehovah alhakin wahalarmu. Bari mu guje wa ƙoƙarin ɗaura wa kanmu gaskiya, mu tuna cewa ko da mecece gatarmu cikin hidimar Jehovah, har ila mu “bayi ne marasa amfani.”—Luka 17:10.
15. (a) Wane irin hali mara kyau ne wasu mabiyan Yesu suka nuna? (b) Ta yaya Bitrus ya nuna hali mai kyau?
15 A cikin ƙarni na farko, wasu da suka saurari Yesu sun nuna hali da bai dace ba. A wani lokaci, Yesu ya faɗi aba da take da wuyar fahimta. Domin haka, “da yawa daga cikin almajiransa suka ce, ‘Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?’ ” Waɗanda suka yi irin wannan maganar lalle ba su da hali da ya dace. Kuma wannan halinsu ya sa suka daina sauraron Yesu. Labarin ya ce: “Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.” Dukansu ne suke da hali mara kyau? A’a. Labarin ya ci gaba: “Sai Yesu ya ce wa sha biyun, ‘Ku ma kuna so ku tafi ne?’ Bitrus ya amsa masa ya ce, ‘Ya Ubangiji, gun wa za mu je?’ ” Sai Bitrus ya amsa tambayar da ya yi: “Kai ke da maganar rai madawwami.” (Yahaya 6:60, 66-68) Wannan hali ne mai kyau! Yayin da muka fuskanci bayani ko sabuwar fahimtar Nassosi waɗanda da farko muka iske su da wuya mu amince da su, ba daidai ba ne mu nuna hali irin wanda Bitrus ya nuna? Lalle wauta ce idan muka daina bauta wa Jehovah ko kuma muka yi magana da ya saɓa wa “sahihiyar magana,” domin kawai wasu abubuwa sun zama da wuyar fahimta da farko!—2 Timoti 1:13.
16. Wane irin mummunar hali ne shugabannan addinin Yahudawa na zamanin Yesu suka nuna?
16 Shugabannan addini na Yahudawa a ƙarni na farko sun ƙi su nuna irin hali da Yesu ya kasance da shi. Yadda suka shawarta ba za su saurare Yesu kuma ba, ya bayyana lokacin da ya tashi Li’azaru daga matattu. Duk wanda yake da hali mai kyau, mu’ujizar za ta zama tabbaci ce mai kyau ta cewa Yesu daga wajen Allah ya fito. Amma, mun karanta: “Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara ’yan majalisa, suka ce, ‘Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu’ujizai da yawa haka? In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗabe jama’armu.’ ” Me suka shawarci za su yi? “Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.” Ban da ƙullawa su kashe Yesu, suka shirya su halaka wanda tabbaci ne da zai nuna shi mai mu’ujiza ne. “Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li’azaru, shi ma.” (Yahaya 11:47, 48, 53; 12:9-11) Lalle zai zama da muni sosai idan muka nuna hali mai kama da wannan mu yi fushi ko ji haushi game da abubuwan da ya kamata mu yi farin ciki a kansu! Hakika, yana da haɗari!
Yin Koyi da Halin Kirki na Yesu
17. (a) A cikin waɗanne yanayi ne Daniyel ya nuna hali na gaba gaɗi? (b) Ta yaya Yesu ya nuna kansa mai ƙarfin hali?
17 Bayin Jehovah suna riƙe halin kirki. Lokacin da magabtan Daniel suka ƙulla a kafa doka da za ta hana yin addu’a ga wani alla ko mutum sai sarki na kwana 30, Daniyel ya sani cewa wannan zai shafe dangantakarsa da Jehovah Allah. Zai daina yin addu’a ga Allah na kwana 30 ne? A’a, ya ci gaba da yin addu’a babu tsoro sau uku a rana, yadda ya saba. (Daniyel 6:6-17) Haka ma Yesu bai ƙyale magabtansa su tsoratar da shi ba. A ranar wata Assabaci, ya gamu da wani mutum mai shanyayyen hannu. Yesu ya sani cewa Yahudawa da yawa da suke wajen ba za su yi murna ba idan suka ga ya warkar da wani a ranar Assabaci. Ya tambaye su kai tsaye ya ji ra’ayinsu game da al’amarin. Da suka ƙi su ce uffan, sai Yesu ya ci gaba ya warkar da mutumin. (Markus 3:1-6) Yesu bai taɓa ja da baya ba a cikin aikinsa duk lokacin da ya ga ya dace.
18. Me ya sa wasu suke yin hamayya da mu, amma yaya ya kamata mu bi da mummunar halinsu?
18 Shaidun Jehovah sun sani a yau cewa su ma ba za su ƙyale wani abin da masu hamayya za su yi ya tsoratar da su ba. Idan ba haka ba, zai zama ba sa nuna halin Yesu. Mutane da yawa da suke hamayya da Shaidun Jehovah, wasu domin ba su san gaskiya game da su ba ne, wasu kuma domin sun tsani Shaidun ne ko kuma saƙonsu. Amma kar mu yarda irin halinsu mara kyau ya shafi halinmu mai kyau. Bai kamata mu ƙyale wasu su gaya mana hanyar da za mu yi sujjada ba.
19. Ta yaya za mu iya nuna hali irin na Yesu Kristi?
19 Kullum Yesu yana nuna hali mai kyau wajen mabiyansa da kuma wajen tsarin Allah, ko yaya wuyarta. (Matiyu 23:2, 3) Ya kamata mu bi misalinsa. Gaskiya ne, ’yan’uwanmu ajizai ne, hakanan muke mu ma. Kuma a ina za mu sami abokai masu kyau kuma masu aminci fiye da daga cikin ’yan’uwanci na duniya duka? Jehovah bai ba mu cikakken fahimin Kalmarsa da ke a rubuce ba tukuna, amma wane rukunin addini ne suka fi mu fahimtarta? Bari ko wane lokaci mu riƙe hali mai kyau, halin da Yesu Kristi ya kasance da shi. Cikin wasu abubuwa, ya ƙunshi sanin yadda za a jira Jehovah, yadda za mu tattauna cikin talifi na biye.
[Hasiya]
a Littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc. ne suka buga, ya tattauna rayuwa da kuma hidimar Yesu.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya halinmu yake shafan rayuwarmu?
• Ka kwatanta halin Yesu Kristi.
• Menene za mu koya daga halin Ayuba?
• Menene hali mai kyau da za mu kasance da shi cikin hamayya?
[Hotuna a shafi na 17]
Kirista wanda yake da hali na kirki zai so ya taimake wasu
[Hoto a shafi na 19]
Nazarin Kalmar Allah tare da addu’a yana taimakonmu mu kasance da halin Kristi