‘Ku Zauna Cikin Maganata’
‘Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.’—YOHANNA 8:31, 32.
Abin da Hakan Yake Nufi: ‘Maganar’ Yesu tana nufin koyarwarsa wadda ta fito daga wurin Allah. Yesu ya ce: “Amma Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.” (Yohanna 12:49) Sa’ad da yake yin addu’a ga Ubansa da ke sama, Jehobah Allah, Yesu ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” Yana yawan kaulin Kalmar Allah don ya goyi bayan abin da yake koyarwa. (Yohanna 17:17; Matta 4:4, 7, 10) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya suna ‘zaune cikin maganarsa,’ wato sun karɓi Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, a matsayin “gaskiya” da kuma tushen imaninsu har da abubuwan da suke yi.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Kamar Yesu, manzo Bulus ya daraja Kalmar Allah. Ya rubuta: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne.” (2 Timotawus 3:16) Mazan da aka naɗa su koyar da ’yan’uwansu Kiristoci suna bukatar su riƙe ‘tabbatacciyar maganar Allah kankan.’ (Titus 1:7, 9, Littafi Mai Tsarki) An gargaɗi Kiristoci na farko su ƙi ‘ilimi da ruɗi na banza, bisa al’adar mutane, bisa ga al’adun duniya, ba bisa ga koyarwar Kristi ba.’—Kolosiyawa 2:8.
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Dogmatic Constitution on Divine Revelation, na Batikan wanda aka soma amfani da shi a shekara ta 1965 kuma aka yi kaulinsa a littafin nan Catechism of the Catholic Church, ya ce: “Ba daga Nassi Mai Tsarki kaɗai ba ne aka ɗauko dukan abubuwan da Cocin [Katolika] ta gaskata da su ba. Saboda haka, dole ne a ɗauki al’ada mai tsarki da muhimmanci kamar yadda aka ɗauki Nassi Mai Tsarki da muhimmanci.” Wani talifi a cikin jaridar Maclean’s ya yi kaulin wata fasto a Toronto, tana cewa: “Me za mu yi da ja-gorancin wani mai ‘neman sauyi’ da ya rayu shekaru dubu biyu da suka shige? Muna da namu ra’ayoyin masu kyau sosai amma koyarwar Yesu da kuma Nassi suna yi musu zagon ƙasa.”
Game da Shaidun Jehobah, littafin New Catholic Encyclopedia ya ce: “Sun ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin ainihin tushen imaninsu da abubuwan da suke yi.” Kwanan baya, wani mutumi a ƙasar Kyanada ya katse maganar wata Mashaidiyar Jehobah sa’ad da take son ta gabatar da kanta. Ya nuna Littafi Mai Tsarki da ke hannunta, kuma ya ce, “Na san ko ke wace ce, domin tambarinku.”