Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 3/15 pp. 24-28
  • Ka Kasance Da Shiri!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Shiri!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance a Shirye Kamar Nuhu
  • Nuhu da Iyalinsa Sun Kasance da Shiri
  • Musa Ya Kasance a Faɗake
  • Ka Yi Tsaro!
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Nuhu Ya Gina Jirgi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Kasancewarmu A Faɗake Ya Fi Gaggawa Yanzu Da Dā
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 3/15 pp. 24-28

Ka Kasance Da Shiri!

“Ku zama da shiri: gama cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.”—MAT. 24:44.

1, 2. (a) Waɗanne aukuwa ne da aka annabta a cikin annabcin Littafi Mai Tsarki ne za a iya gwada da farmakin wata babbar ’yar’uwar damisa? (b) Ta yaya farmaki da ke zuwa ya shafe ka?

A CIKIN shekaru da yawa, wani sanannen ɗan wasa yana sa masu kallon wasansa dariya ta wajen yin wasa da wata babbar ’yar’uwar damisa ta ƙasar Bengal. Ya ce: “Idan dabba ta amince da kai, za ka ji kamar an ba ka kyauta da ta fi kyau a duniya.” Amma, a ranar 3 ga Oktoba ta shekara ta 2003, wannan amincin ya ƙare. Babu gaira ba dalili, ɗaya cikin dabobbinsa, wato, wata farar babbar ’yar’uwar damisa mai nauyin kilo 172, ta kai masa hari. Ɗan wasan bai san cewa wannan dabbar za ta kai masa hari ba, kuma bai yi shiri ba.

2 Yana da kyau a lura cewa Littafi Mai Tsarki ya annabta harin wata ‘dabba’ kuma muna bukatar mu kasance a shirye. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:15-18.) Wane ne wannan dabbar take kai wa hari? Farat ɗaya abubuwa suka canja, duniyar Iblis tana gāba da juna. Dabbar mai launi ja wur tana wakiltar Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ‘ƙahoni goman’ suna wakiltar dukan ’yan siyasa masu iko. Waɗannan za su kai wa Babila Babba hari, wato, daular duniya na addinan ƙarya mai kama da karuwa, kuma su halaka ta. A wane lokaci ne hakan zai faru? Ba mu san ranar da sa’ar ba. (Mat. 24:36) Mun san cewa a sa’ar da ba mu yi tsammani ba ne hakan zai faru kuma lokacin da ya rage kafin a kai wannan harin kaɗan ne. (Mat. 24:44; 1 Kor. 7:29) Saboda haka, yana da muhimmanci mu kasance a shirye a ruhaniya domin sa’ad da aka kai wannan harin kuma Kristi ya zo a matsayin Mai Zartar da Hukunci, zai kuma zama Mai Cetonmu! (Luk 21:28) Don mu kasance a shirye, za mu iya koya darasi daga bayin Allah masu aminci waɗanda suka kasance a shirye kuma ta hakan suka ga cikar alkawuran Allah. Shin za mu riƙa tunawa da waɗannan labaran kuwa?

Ka Kasance a Shirye Kamar Nuhu

3. Waɗanne yanayi ne suka sa ya yi wa Nuhu wuya ya bauta wa Allah da aminci?

3 Duk da mummunar yanayi da ya kasance a duniya a zamanin Nuhu, ya kasance a shirye don ya ga cikar alkawarin Allah. Ka yi tunanin ƙalubale da Nuhu ya fuskanta yayin da mala’iku masu tawaye suka canja zuwa siffar ’yan Adam kuma suka soma auren kyawawan mata! Waɗannan aure-auren da ba su dace ba sun sa suka haifi yara ƙattai, “ƙarfafan mutane” waɗanda suka yi amfani da ƙarfinsu don su zalunci mutane. (Far. 6:4) Ka yi tunanin mugunta da aka yi yayin da waɗannan gwarzaye suka jawo rikici duk inda suka shiga. A sakamako, mugunta ta yaɗu sosai kuma tunanin ’yan Adam da halinsu suka lalace gabaki ɗaya. Ubangiji Jehobah Mai Ikon Mallaka ya ƙayyade lokacin da za a halaka wannan muguwar duniya.—Karanta Farawa 6:3, 5, 11, 12.a

4, 5. A waɗanne hanyoyi ne yanayi na zamaninmu suka yi daidai da na zamanin Nuhu?

4 Yesu ya annabta cewa yanayi a zamaninmu zai yi daidai da na kwanakin Nuhu. (Mat. 24:37) Alal misali, muna kuma shaida yadda miyagun ruhohi suke saka hannu a harkokin ’yan Adam. (R. Yoh. 12:7-9, 12) Waɗannan mala’iku da suka zama aljanu sun canja siffarsu zuwa na ’yan Adam a zamanin Nuhu. Ko da yake an hana su canja siffarsu a yanzu, suna ƙoƙari su rinjayi yara duk da manya. Waɗannan miyagun mala’iku suna jin daɗin ayyukan mugunta na waɗanda za su iya ɓata a duniya, ba tare da sanin mutane ba.—Afis. 6:11, 12.

5 Kalmar Allah ta kwatanta Iblis a matsayin “mai-kisan kai” kuma ta ce yana “da ikon mutuwa.” (Yoh. 8:44; Ibran. 2:14) Wannan ba ya nufin cewa ikonsa na kisa ba shi da iyaka. Duk da haka, yana iya sa mutane su yi abin da zai sa su sha wahala kuma su mutu. Yana kuma rinjayar tunanin mutane su tsane wasu kuma su so kashe mutane. Tun da yake nuna ƙarfi ya yi yawa, kana ganin cewa Jehobah ba ya lura da wannan a yau fiye da yadda ya yi a zamanin Nuhu? Shin zai yi shiru ne kawai?

6, 7. Yaya Nuhu da iyalinsa suka nuna bangaskiya da tsoron Allah?

6 Bayan haka, an sanar wa Nuhu shawarar Allah na kawo rigyawa a duniya, don ya halaka dukan masu rai. (Far. 6:13, 17) Jehobah ya umurci Nuhu ya gina jirgi mai siffar babban akwati. Nuhu da iyalinsa suka soma gina jirgin. Mene ne ya taimake su su yi biyayya kuma su kasance da shiri sa’ad da Allah ya kawo hukuncin?

7 Kasancewa da bangaskiya sosai da kuma tsoron Allah sun motsa iyalinsa su yi daidai abin da Allah ya umurce su. (Far. 6:22; Ibran. 11:7) A matsayin shugaban iyali, Nuhu ya kasance a faɗake a ruhaniya kuma ya guje wa ɓatanci na wancan duniyar. (Far. 6:9) Ya san cewa iyalinsa tana bukatar ta guji bin hanyoyi na nuna ƙarfi da kuma halin mugunta na mutane da ke kewaye da su. Yana da muhimmanci cewa ba su shagala da kowanne ayyukan rayuwa na yau da kullum ba. Allah yana da aiki da za su yi, kuma yana da muhimmanci cewa dukan iyalin sun mai da hankali ga aikin.—Karanta Farawa 6:14, 18.

Nuhu da Iyalinsa Sun Kasance da Shiri

8. Me ya nuna cewa waɗanda ke iyalin Nuhu sun yi ayyukan ibada?

8 Labaran Littafi Mai Tsarki sun mai da hankali ga Nuhu, shugaban iyalin, amma matar Nuhu da yaransa da kuma matansu ma sun bauta wa Jehobah. Annabi Ezekiel ya tabbatar da hakan. Ya faɗa cewa da Nuhu yana da rai a zamanin Ezekiel, da yaransa ba za su yi zato cewa za su tsira ba bisa ga adalcin mahaifinsu. Sun isa su yi biyayya ko kuma su ƙi yin biyayya. Saboda haka, sun riga sun nuna cewa suna ƙaunar Allah da kuma hanyoyinsa. (Ezek. 14:19, 20) Iyalin Nuhu sun karɓi umurnansa, sun goyi bayan bangaskiyarsa, kuma ba su bar rinjayar mutane ta hana su yin aikin da Allah ya ba su ba.

9. Waɗanne misalai na zamani na waɗanda suke da bangaskiya kamar Nuhu ne za mu iya ba da?

9 Abin ban ƙarfafa ne a ga magidanta waɗanda suke cikin ’yan’uwanci na dukan duniya da suke iya ƙoƙarinsu su yi koyi da Nuhu! Sun fahimci cewa bai isa kawai su yi tanadin abinci da tufafi da gida da kuma ilimi ba. Wajibi ne magidanta su kula da bukatun ruhaniya ta iyalinsu. Ta yin hakan, suna nuna cewa suna a shirye ga abin da Jehobah zai yi ba da daɗewa ba.

10, 11. (a) Sa’ad da suke cikin jirgin, yaya Nuhu da iyalinsa suka ji? (b) Wace tambaya ce ta dace mu yi wa kanmu?

10 Wataƙila Nuhu da iyalinsa sun yi shekara hamsin suna gina jirgin. Ka yi tunanin aiki tuƙuru da suka yi: Suka shafe jirgin da kwalta. Sun saka abinci a ciki. Sun shigar da dabbobin cikin jirgin. Suna shiga da fita daga jirgin. Bayan duk wannan aikin, a rana ta sha bakwai na wata na biyu a shekara ta 2370 K.Z. (sa’ad da Nuhu yake da shekara ɗari shida), a ƙarshe sai rigyawar ta zo. Ka yi tunanin wannan yanayin. A wannan ranar, sun shiga cikin jirgin kuma suka zauna a ciki. Jehobah ya rufe ƙofar jirgin kuma aka soma ruwa. (Far. 7:11, 16) Mutane da ba sa cikin jirgin sun mutu kuma an ceci waɗanda suke ciki. Yaya iyalin Nuhu suka ji? Babu shakka, sun yi godiya sosai ga Allah. Kuma hakika, sun yi tunani, ‘Mun yi farin ciki cewa mun yi tafiya da Allah na gaskiya kuma mun kasance a shirye!’ (Far. 6:9) Kana ganin kanka a wancan ɓangare na Armageddon, kana irin wannan godiya da dukan zuciyarka kuwa?

11 Babu abin da zai iya hana Maɗaukaki Duka ya cika alkawarinsa na kawo ƙarshe ga wannan zamani na Shaiɗan. Ka tambayi kanka, ‘Ina da cikakken tabbaci cewa babu alkawuran Allah da ba za su cika ba ko ɗan kaɗan ne kuma dukansu za su cika a lokacinsu?’ Idan haka ne, ka kasance a shirye ta wajen sauraron “ranar Allah” da ke tafe da gaggawa.—2 Bit. 3:12.

Musa Ya Kasance a Faɗake

12. Da mene ne zai iya janye hankalin Musa?

12 Bari mu yi la’akari da wani misali. Daga ra’ayin ’yan Adam, kamar Musa yana da matsayi mai girma sosai a cikin duniyar Masar. A matsayin ɗa da ’yar Fir’auna ta ɗauko riƙo, wataƙila an ɗaukaka shi sosai kuma ya more abinci mafi kyau, ya sa tufafi mafi kyau, kuma ya zauna a mahalli mafi kyau. Ya yi makaranta sosai. (Karanta Ayyukan Manzanni 7:20-22.) Wataƙila da ya samu gādo mai girma.

13. Ta yaya Musa ya mai da hankali ga alkawuran Allah?

13 Wataƙila koyarwa da iyayensa suka yi masa tun yana yaro ne ya sa Musa ya fahimci wautar bautar gunki da Masarawa suke yi. (Fit. 32:8) Tsarin ilimantarwa na ƙasar Masar da dukiyar gidan sarauta ba su sa Musa ya yasar da bauta ta gaskiya ba. Mai yiwuwa ya yi bimbini sosai a kan alkawuran da Allah ya yi wa kakanninsa kuma yana son ya nuna yana a shirye ya yi nufin Allah. Ballantana ma, Musa ya gaya wa Isra’ilawa: “Yahweh . . . Allah na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub, ya aike ni gare ku.”—Karanta Fitowa 3:15-17.

14. Yaya aka gwada bangaskiya da gaba gaɗin Musa?

14 Jehobah, Allah na gaskiya ya kasance da gaske ga Musa, ba kamar dukan gumaka da suke wakiltar alloli marasa rai na ƙasar Masar ba. Ya yi rayuwa kamar yana ganin “wanda ba shi ganuwa.” Musa yana da bangaskiya cewa za a ’yantar da mutanen Allah, amma bai san ko a wane lokaci ne za a yi hakan ba. (Ibran. 11:24, 25, 27) An ga cewa yana son a ’yantar da Ibraniyawa ta wurin yadda ya kāre wani Ba’isra’ila wanda aka zalunta. (Fit. 2:11, 12) Amma, lokacin da Jehobah yake son ya yi hakan bai kai ba tukun, saboda haka Musa ya yi zaman ɗan gudun hijira a wata ƙasa mai nisa. Babu shakka, ya yi masa wuya ya gudu daga mahallin fadar Masar inda yake more rayuwa kuma ya koma zama a jeji. Duk da haka, Musa ya kasance a shirye ta wajen bin kowane umurni da Jehobah ya ba shi. Saboda haka, Allah ya yi amfani da shi don ya kawo sauƙi ga ’yan’uwansa bayan ya yi shekaru 40 a ƙasar Midiya. Musa ya koma ƙasar Masar sa’ad da Allah ya umurce shi ya yi hakan. Lokaci ya yi da Musa zai aikata umurnin Allah kuma ya yi aikin yadda Allah yake so. (Fit. 3:2, 7, 8, 10) Musa ‘mai-tawali’u ƙwarai, gaba da kowane mutum’ yana bukatar bangaskiya da gaba gaɗi don ya zo gaban Fir’auna a ƙasar Masar. (Lit. Lis. 12:3) Ya yi hakan ba sau ɗaya kawai ba, amma a kai a kai yayin da annobar ta ci gaba, da yake bai san yawan annobar da za a yi ba, da kuma sau nawa da zai bukaci ya zo gaban Fir’auna ba.

15. Duk da sanyin gwiwa, mene ne ya motsa Musa ya nemi zarafin ɗaukaka Ubansa na samaniya?

15 A cikin shekaru 40 na gaba, sa’ad da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji, Musa ya yi sanyin gwiwa. Duk da haka, ya nemi zarafin ɗaukaka Jehobah kuma da dukan zuciyarsa ya ƙarfafa ’yan’uwansa Isra’ilawa su yi hakan. (K. Sha 31:1-8) Me ya sa? Domin yana ƙaunar sunan Jehobah da kuma ikon mallakarsa fiye da nasa. (Fit. 32:10-13; Lit. Lis. 14:11-16) Dole ne mu ma mu ci gaba da tallafa wa sarautar Allah duk da fid da zuciya ko kuma sanyin gwiwa, muna tabbata cewa yadda yake abubuwa ne ya fi hikima da adalci da kuma kyau. (Isha. 55:8-11; Irm. 10:23) Haka ne kake ji?

Ka Yi Tsaro!

16, 17. Me ya sa Markus 13:35-37 yake da ma’ana sosai a gare ka?

16 “Ku yi lura, ku yi tsaro, ku yi addu’a: gama ba ku san lokacinda sa’a ta ke ba.” (Mar. 13:33) Yesu ya ba da wannan kashedin sa’ad da yake tattauna abin da zai nuna cewa muna zama a ƙarshen wannan mugun zamani. Ka yi la’akari da kalaman kammalawa na annabci mai girma na Yesu da ke rubuce a littafin Markus: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku san lokacin da ubangijin gida yana zuwa, ko da maraice, ko da tsakiyar dare, ko da carar zakara, ko da safe; kada ya iske ku kuna barci da zuwansa ba labari. Abin da ni ke ce maku, ina faɗa wa duka; Ku yi tsaro.”—Mar. 13:35-37.

17 Gargaɗin Yesu yana sa mutum tunani. Ya ambata lokatai huɗu dabam dabam na yin tsaro da daddare. Zai yi wuya a kasance a faɗake a lokacin tsaro na ƙarshe don yana somawa daga ƙarfe uku na safe har fitowar rana. Gwanayen yaƙi sun ga cewa lokacin ne ya fi kyau a kai wa magabta farmaki, hakan zai ba su zarafi mafi kyau na kama su suna “barci.” Haka nan ma, a yanzu da mutanen duniya suke barci sosai a azanci na ruhaniya, muna iya yin kokawa sosai don mu kasance a faɗake. Shin muna shakka ne cewa muna bukatar mu “yi tsaro” kuma mu “yi lura” don ƙarshe da aka annabta da kuma cetonmu?

18. A matsayin Shaidun Jehobah, wane gata mai girma ne muke da shi?

18 Mai horar da dabbobi da aka ambata a farkon wannan talifin ya tsira wa hari da wata babbar ’yar’uwar damisa ta ƙasar Bengal ta kai masa. Amma annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa addinin ƙarya da sauran mutane na wannan mugun tsari ba za su tsira wa ƙarshe da ke gabatowa ba. (R. Yoh. 18:4-8) Bari dukan bayin Allah, yara da manya su ga muhimmancin yin dukan abin da za su iya yi don su kasance da shiri don ranar Jehobah yadda Nuhu da iyalinsa suka yi. Muna zama a duniya da ba ta ɗaukaka Allah wadda malaman addinin ƙarya da mulhidi da masu musun wanzuwar Allah, suke yi wa Mahaliccin ba’a da furcinsu. Amma ba za mu ƙyale ra’ayinsu ya shafe mu ba. Bari mu tuna da misalai da muka tattauna kuma mu yi tsaro don samun zarafin kāre da kuma ɗaukaka Jehobah a matsayin “Allahn alloli” domin hakika shi “Allah ne mai-girma, mai-iko mai-ban tsoro.”—K. Sha 10:17.

[Hasiya]

a Game da “shekara ɗari da ashirin” da aka ambata a littafin Farawa 6:3, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 2010, shafi na 30.

Ka Tuna?

• Me ya sa Nuhu yake bukatar ya mai da hankali ga bukatun ruhaniya na iyalinsa?

• Yaya zamaninmu ya yi kama da na Nuhu?

• Duk da sanyin gwiwa, me ya sa Musa ya mai da hankali ga alkawuran Jehobah?

• Waɗanne annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ne suke motsa ka ka yi tsaro a ruhaniya?

[Hoton da ke shafi na 25]

Nuhu da iyalinsa sun mai da hankali ga aikin Jehobah

[Hoton da ke shafi na 26]

Tabbatattun alkawuran Allah sun taimaki Musa ya yi tsaro

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba