Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 2/1 pp. 4-7
  • Kada Ka Ba Iblis Dama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Ba Iblis Dama
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ka yi Koyi da Babban Maƙaryaci
  • Ka Guje wa Hanyoyin Ainihin Mai Kisankai
  • Ka Dage Gāba da Sarkin Maƙaryata
  • Ka Ƙi Fitaccen Ɗan Ridda
  • Kada Ka Ƙyale Mai Mulkin Duniyar Nan ya Rinjaye Ka
  • Kada ka ba Iblis Dama
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Shin Iblis Yana Wanzuwa da Gaske?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Wane ne ko kuma mene ne Iblis?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 2/1 pp. 4-7

Kada Ka Ba Iblis Dama

“Kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.”—AFISAWA 4:27, Littafi Mai Tsarki.

1. Me ya sa yawancin mutane masu da’awar cewa su Kiristoci ne suke shakkar wanzuwar Iblis?

TUN ƙarnuka da yawa, yawancin mutane sun ɗauka cewa Shaiɗan yana da ƙaho, yana da kofato a kafa, yana sanye da jar riga, kuma yana amfani da tebur mai haƙora wajen jefa mugayen mutane cikin wuta. Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan waɗannan ra’ayoyin ba. Babu shakka, irin waɗannan ra’ayoyin sun sa miliyoyin mutane masu da’awar cewa su Kiristoci ne su yi shakkar wanzuwar Iblis, kuma ya sa sun yi tunanin cewa wannan kalmar tana nufin aikata mugunta.

2. Waɗanne gaskiya daga Nassi ne suka tabbatar da wanzuwar Iblis?

2 Littafi Mai Tsarki ya ba da shaida kuma ya tabbatar da wanzuwar Iblis. Yesu Kristi ya san shi a duniyar ruhu a samaniya kuma ya yi magana da shi a nan duniyar. (Ayuba 1:6; Matta 4:4-11) Ko da yake Nassosi ba su faɗi ainihin sunan wannan halittar ruhu ba, sun kira shi Iblis (wanda ke nufin “Maƙaryaci”) domin ya yi ƙarya game da Allah. Ana kiran shi Shaiɗan (wanda ke nufin “Ɗan Hamayya”), tun da yake yana hamayya da Jehobah. Ana kiran Shaiɗan Iblis “tsohon macijin,” wataƙila domin ya yi amfani da maciji ya ruɗi Hauwa’u. (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 1 Timothawus 2:14) Kuma an kira shi “mugun.”—Matta 6:13.a

3. Wace tambaya ce za mu tattauna?

3 Mu bayin Jehobah, ta kowace hanya ba ma son mu bi misalin Shaiɗan, wanda shi ne babban magabcin Allah na gaskiya. Dole ne mu bi shawarar manzo Bulus: “Kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.” (Afisawa 4:27, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, waɗanne halaye na Shaiɗan ne ba za mu yi koyi da su ba?

Kada Ka yi Koyi da Babban Maƙaryaci

4. Ta yaya ne “mugun” ya yi ƙarya game da Allah?

4 “Mugun” ya cancanci a kira shi Iblis, domin maƙaryaci ne. Ƙarya na nufin faɗan abin da ba gaskiya ba game da wani don a ɓata masa suna. Allah ya umurci Adamu: “Daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:17) An sanar da Hauwa’u wannan umurnin. Amma Iblis ya ce mata ta bakin maciji: “Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” (Farawa 3:4, 5) Wannan baƙin ƙarya ne game da Jehobah Allah!

5. Me ya sa Diyoturifis ya cancanci ya ba da lissafin ƙaryar da ya yi?

5 An umurci Isra’ilawa: “Ba za ka yi yawon kai da kawowa kana yawon tsegumi a cikin mutanenka.” (Leviticus19:16) Manzo Yohanna ya ce game da ƙarya a zamaninsa: “Na rubuta wani abu ga ikilisiya, amma Diyoturifis, wanda yake so ya sami shugabanci a cikinsu, ba shi karɓanmu. Ni fa, idan na zo, sai in tuna da ayukansa da yake aika, miyagun zantattukan da yake ambatonmu da su.” (3 Yohanna 9, 10) Diyoturifis yana yin ƙarya game da Yohanna, saboda haka ya cancanci ya ba da lissafin abin da ya yi. Wane Kirista mai aminci ne zai so ya zama kamar Diyoturifis kuma ya bi misalin Shaiɗan, wanda shi ne babban maƙaryaci?

6, 7. Me ya sa ya kamata mu guji yin ƙarya game da mutane?

6 A yawancin lokaci ana ɓata wa bayin Jehobah suna kuma ana yi musu tuhumar ƙarya. “Manyan malamai da marubuta suka tsaya suna ta sarassa [Yesu] da tsanani ƙwarai.” (Luka 23:10) Babban Firist Hananiya da wasu mutane sun yi wa Bulus zargin ƙarya. (Ayukan Manzanni 24:1-8) Kuma Littafi Mai Tsarki ya kira Shaiɗan “mai-saran ’yan’uwanmu, . . . wanda ya ke sarassu dare da rana a gaban Allahnmu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Waɗannan ’yan’uwan da ake yi wa zargin ƙarya sune Kiristoci shafaffu da suke zaune a duniyar nan a wannan zamani na ƙarshe.

7 Babu Kirista da zai so ya yi wa wani tsegumi ko kuwa ya yi masa zargin ƙarya. Amma, hakan na iya faruwa idan ba mu da cikakken bayani kafin mu je mu ba da shaida. A cikin Dokar Musa, shaidar zur na iya jawo mutuwa ga wanda ya yi ta. (Fitowa 20:16; Kubawar Shari’a 19:15-19) Bugu da ƙari, ɗaya daga cikin abubuwa da Jehobah yake ƙyama shi ne “mai-shaidan zur wanda ya ke furtawa da ƙarya.” (Misalai 6:16-19) Hakika, ba ma son mu bi misalin babban mai ƙarya kuma ɗan hamayya.

Ka Guje wa Hanyoyin Ainihin Mai Kisankai

8. Ta yaya ne Iblis ya zama “mai-kisan kai . . . tun daga farko”?

8 Iblis mai kisan kai ne. Yesu ya ce Iblis “mai-kisan kai ne tun daga farko.” (Yohanna 8:44) Sa’ad da ya janye Adamu da Hauwa’u daga Allah, Shaiɗan ya zama mai kisan kai. Ya jawo wa mutane biyu na farko da ’ya’yansu mutuwa. (Romawa 5:12) Tabbatacce ne cewa mutum ne kawai zai iya aikata wannan, ba kawai tunanin zuciya ba.

9. Kamar yadda aka nuna a 1 Yohanna 3:15, ta yaya za mu iya zama masu kisan kai?

9 Ɗaya daga cikin Dokoki Goma da aka ba Isra’ila ta ce, “ba za ka yi kisankai ba.” (Kubawar Shari’a 5:17) Sa’ad da yake yi wa Kiristoci magana, manzo Bitrus ya rubuta: “Kada wani daga cikinku ya sha wuya kamar mai-kisankai.” (1 Bitrus 4:15) Saboda haka, mu bayin Jehobah ba za mu kashe wani ba da gangan. Duk da haka, za mu ɗauki alhaki a gaban Allah idan muka ƙi jinin ɗan’uwa Kirista har muna fatan ya mutu. “Dukan wanda ya ƙi ɗan’uwansa mai-kisankai ne,” in ji manzo Yohanna, “kun sani babu mai-kisankai wanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune.” (1 Yohanna 3:15) An umurci Isra’ilawa: ‘Ba za ku ƙi ɗan’uwanku cikin zuciyarku ba.’ (Leviticus 19:17) Bari mu yi saurin warware duk wata matsalar da ta taso tsakaninmu da ɗan’uwa mai bi, saboda kada mai kisan kai Shaiɗan ya lalata haɗin kanmu ta Kirista.—Luka 17:3, 4.

Ka Dage Gāba da Sarkin Maƙaryata

10, 11. Menene muke bukatar mu yi idan muna so mu dage gāba da shugaban ƙarya Shaiɗan?

10 Iblis maƙaryaci ne. “Sa’anda ya ke yin ƙarya,” in ji Yesu, “don kansa ya ke yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.” (Yohanna 8:44) Shaiɗan ya yi wa Hauwa’u ƙarya, amma Yesu ya zo duniya ne domin ya ba da shaida ga gaskiya. (Yohanna 18:37) Idan mu mabiyan Kristi muna so mu dage gāba da Iblis, muna bukatar mu guje wa ƙarya da ruɗi. Dole ne mu “faɗi gaskiya.” (Zechariah 8:16; Afisawa 4:25) Jehobah “Allah na gaskiya” yana yi wa Shaidunsa masu gaskiya ne kawai albarka. Mugu kuwa ba shi da ikon ya wakilce shi.—Zabura 31:5; 50:16; Ishaya 43:10.

11 Idan muna daraja ’yancinmu ta ruhaniya daga ƙaryar Shaiɗan, za mu manne wa Kiristanci, wato “hanyar gaskiya.” (2 Bitrus 2:2; Yohanna 8:32) Dukan koyarwa ta Kirista ta ƙunshi “gaskiyar bishara.” (Galatiyawa 2:5, 14) Samun cetonmu ta dangana ne a kan “tafiya cikin gaskiya,” wato, manne wa gaskiya da kuma dage gāba da “uban ƙarya.”—3 Yohanna 3, 4, 8.

Ka Ƙi Fitaccen Ɗan Ridda

12, 13. Yaya ya kamata mu bi da ’yan ridda?

12 Wannan halitta na ruhu wadda ta zama Iblis a dā tana cikin gaskiya. Amma “ba ya tsaya a kan gaskiya,” ba in ji Yesu, “domin babu gaskiya a cikinsa.” (Yohanna 8:44) Fitaccen ɗan ridda ya bi tafarkin tsayayya wa “Allah na gaskiya.” Wasu cikin Kiristoci na ƙarni na farko sun faɗa cikin “tarkon Shaiɗan,” mai yiwuwa sun faɗa hannunsa ne domin an ruɗe su kuma sun bijire daga gaskiya. Saboda haka, Bulus ya umurci abokin aikinsa Timoti ya koyar da su cikin tawali’u domin su iya warkewa a ruhaniya kuma su ’yantar da kansu daga tarkon Shaiɗan. (2 Timothawus 2:23-26) Hakika, manne wa gaskiya ya fi maimakon mu faɗa tarkon ra’ayoyin ɗan ridda.

13 Domin sun saurari Iblis kuma ba su ƙi ƙaryar da ya yi musu ba, mutane biyu na farko suka zama ’yan ridda. Saboda haka, zai dace mu saurari ’yan ridda, mu karanta littattafansu, ko kuwa mu bincika dandalinsu a Duniyar gizonsu a cikin Intane? Idan muna ƙaunar Allah da kuma gaskiya, ba za mu yi haka ba. Bai kamata mu ƙyale ’yan ridda su shiga gidanmu ba ko kuwa mu gai da su, domin yin haka zai sa mu yi ‘tarayya cikin miyagun ayyukansu.’ (2 Yohanna 9-11) Bari kada mu yarda mu faɗa cikin dabarar Iblis ta wajen ƙyale “hanyar gaskiya” ta wajen bin malaman ƙarya waɗanda suke son su gabatar da ‘ra’ayoyi masu haɗari’ kuma su janye mu da “maganganun rikici.”—2 Bitrus 2:1-3.

14, 15. Wane gargaɗi ne Bulus ya yi wa dattawa da ke Afisa da kuma abokin aikinsa Timoti?

14 Bulus ya gaya wa Kiristoci dattawa da suke zaune a Afisa: “Ku tsare kanku, da dukan garke kuma, wanda Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki, garin ku yi kiwon ikilisiyar Allah, wadda ya sayi da jinin kansa. Na sani bayan tashina kerketai masu-zafin hali za su shiga wurinku, ba za su kewaye ma garke ba; daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (Ayukan Manzanni 20:28-30) Hakika, waɗannan ’yan riddan sun bayyana kuma sun faɗi “karkatattun zantattuka.”

15 A kusan shekara ta 65 A.Z., manzon ya umurci Timoti ya “rarrabe kalmar gaskiya sosai.” Bulus ya rubuta, “amma ka guje ma zantattukan banza na saɓo: gama za su yi gaba cikin rashin-ibada, maganassu kuwa za ta ci kamar zuganye: irinsu ke nan su Himinayus da Filitus; mutane masu-kuskure wajen gaskiya, suna cewa, tashin ya rigaya ya wuce, su kan kuwa jirkitadda bangaskiyar waɗansu.” An soma riddan! Bulus ya daɗa, “amma tushe mai-tsayawa na Allah ya tabbata.”—2 Timothawus 2:15-19.

16. Duk da ruɗin ɗan ridda na farko, me ya sa muka kasance da aminci ga Allah da kuma Kalmarsa?

16 Shaiɗan ya sha yin amfani da ’yan ridda don ya gurɓata bauta ta gaskiya, amma bai yi nasara ba. A kusan shekara ta 1868, Charles Taze Russell ya soma bincika koyarwar cocin Kiristendom kuma ya ga yadda suka juya ma’anar abin da ke cikin Nassosi. Russell da wasu mutane ƙalilan masu neman gaskiya sun kafa ajin nazarin Littafi Mai Tsarki a Pittsburgh, Pennsylvania ta Amirka. Tun daga lokacin kusan shekara 140 ke nan, bayin Jehobah sun ƙaru a sani da kuma ƙaunar Allah da Kalmarsa. Duk da ruɗun ɗan ridda na farko, tsaro na rukunin amintaccen bawan nan mai hikima ya taimaka wa Kiristoci na gaskiya su kasance da aminci ga Jehobah da Kalmarsa.—Matta 24:45.

Kada Ka Ƙyale Mai Mulkin Duniyar Nan ya Rinjaye Ka

17-19. Mecece duniyar da take kwance cikin ikon Iblis, kuma me ya sa bai kamata mu ƙaunace ta ba?

17 Wata hanya kuma da Shaiɗan ke amfani da ita don ya kama mu a cikin tarkonsa ita ce, ta wajen rinjayarmu mu ƙaunaci wannan duniyar, wato ’yan adam marasa aminci waɗanda bare suke ga Allah. Yesu ya kira Iblis “sarkin duniya” kuma ya ce: “Ba shi da komi a cikina.” (Yohanna 14:30) Kada mu yarda mu shiga tarkon Shaiɗan! Mun sani cewa “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Shi ya sa Shaiɗan ya ce zai ba Yesu “dukan mulkokin duniya,” idan ya bauta masa, amma Ɗan Allah ya ƙi wannan tayin faufau. (Matta 4:8-10) Wannan duniyar da Shaiɗan ke sarauta ta ƙi mabiyan Kristi. (Yohanna 15:18-21) Babu shakka, shi ya sa manzo Yohanna ya yi mana gargaɗi kada mu ƙaunaci duniya!

18 Yohanna ya rubuta: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne. Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:15-17) Bai kamata mu ƙaunaci duniya ba domin hanyoyinta ta kwaɗayin jiki ne, wanda hakan bai jitu da mizanan Jehobah Allah ba.

19 Idan muna ƙaunar wannan duniyar a zuciyarmu fa? Bari mu yi addu’a ga Allah don ya taimaka mana mu sha kan wannan ƙaunar da kuma sha’awoyi na jiki da ke tattare da ita. (Galatiyawa 5:16-21) Idan muka tuna cewa “rundunai masu-ruhaniya na mugunta” marar ganuwa sune “mahukuntan wannan zamani” marar aminci, hakika za mu yi ƙoƙari mu ‘tsare kanmu marar-aibi daga duniya.’—Yaƙub 1:27; Afisawa 6:11, 12; 2 Korinthiyawa 4:4.

20. Me ya sa za a iya cewa ‘mu ba na duniya ba ne’?

20 Game da almajiransa, Yesu ya ce: “Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:16) Kiristoci shafaffu da kuma abokanansu keɓaɓɓu suna ƙoƙarin kasancewa da tsabta a ɗabi’a da ruhaniya, kuma sun keɓe kansu daga wannan duniyar. (Yohanna 15:19; 17:14; Yaƙub 4:4) Wannan duniyar marar aminci ba ta ƙaunarmu domin mun keɓe kanmu daga gareta kuma mu masu “shelan adalci” ne. (2 Bitrus 2:5) Hakika, muna zaune ne a cikin mutanen da suka haɗa da mazinata, masu ƙwace, masu bautar gumaka, ɓarayi, maƙaryata, da mashaya. (1 Korinthiyawa 5:9-11; 6:9-11; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Amma, ba ma bin “ruhun duniya,” domin ba ma ƙyale wannan iko na zunubi ya sarrafa mu.—1 Korinthiyawa 2:12.

Kada ka ba Iblis Dama

21, 22. Ta yaya za ka yi amfani da shawarar Bulus da ke rubuce a Afisawa 4:26, 27?

21 Maimakon mu ƙyale “ruhun duniya” ya motsa mu, ruhun Allah ne ke yi mana ja-gora, wanda hakan ya sa muke da halaye kamar su ƙauna da kamewa. (Galatiyawa 5:22, 23) Waɗannan suna taimaka mana mu yi tsayayya da harin da Iblis ke kawo wa bangaskiyarmu. Yana so mu zama masu “hasala,” amma ruhun Allah na taimaka mana mu “dena yin fushi.” (Zabura 37:8) Hakika, a wasu lokatai wataƙila muna da kyakkyawan dalili na yin fushi, amma Bulus ya yi mana gargaɗi: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.”—Afisawa 4:26, 27.

22 Fushinmu na iya zama zunubi. Idan muka kasance da irin wannan halin, za mu ba Iblis damar ɗaukaka rashin haɗin kai a cikin ikilisiya ko kuwa yana iya sa mu aikata ayyukan mugunta. Saboda haka, muna bukatar mu daidaita matsalolin da ke tsakaninmu da wasu da wuri kuma a hanyar da Allah ke so. (Leviticus 19:17, 18; Matta 5:23, 24; 18:15, 16) Saboda haka, bari mu ƙyale ruhun Allah ya yi mana ja-gora, mu ci gaba da nuna kamewa, kuma kada mu ƙyale fushi ya jawo ƙiyayya da kuma hasala.

23. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifinmu na gaba?

23 Mun tattauna wasu halayen Iblis da bai kamata mu bi ba. Amma wasu masu karatu suna iya yin mamaki: Ya kamata mu ji tsoron Shaiɗan ne? Me ya sa yake haddasa wa Kiristoci tsanani? Ta yaya za mu guji faɗawa hannun Iblis?

[Hasiya]

a Ka dubi talifofin nan “Is the Devil Real?” da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2005 na Turanci.

Mecece Amsarka?

• Me ya sa bai kamata mu yi ƙarya ba game da wani?

• Cikin jituwa da 1 Yohanna 3:15, ta yaya za mu guji zama masu kisan kai?

• Yaya ya kamata mu ɗauki ’yan ridda, kuma me ya sa?

• Me ya sa bai kamata mu ƙaunaci duniya ba?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba