Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 8/1 pp. 8-13
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Tashin Matattu Suka Karɓi Na Su da Suka Mutu
  • Ɗan Allah Ya Tayar da Matattu
  • Wasu Tashin Matattu Sun Ƙarfafa Begenmu
  • Tashin Matattu—Bege ne da Ya Daɗe
  • Tabbaci Daga Doka da Kuma Zabura
  • Ƙarfafa ta Wurin Begen Tashin Matattu
  • Tashin Matattu —Koyarwa Da Ta Shafe Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Ina da Bege ga Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Za A Yi Tashin Matattu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Begen Tashin Matattu Yana Da iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 8/1 pp. 8-13

Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!

“Ina da bege ga Allah . . . za a yi tashin matattu.”—AYUKAN MANZANNI 24:15.

1. Me ya sa za mu yi begen tashin matattu?

JEHOVAH ya ba mu dalili mai ƙwari na begen tashin matattu. Muna da maganarsa cewa matattu za su tashi, za su sake tashiwa zuwa rai. Kuma nufinsa ga matattu babu shakka zai cika. (Ishaya 55:11; Luka 18:27) Hakika, Allah ya riga ya nuna ikonsa na tayar da matattu.

2. Ta yaya begen tashin matattu zai amfane mu?

2 Bangaskiya ga tanadi da Allah ya yi na tada matattu ta wurin Ɗansa Yesu Kristi, zai iya riƙe mu a lokacin wahala. Tabbacin begen tashin matattu zai iya taimakonmu mu riƙe aminci wa Ubanmu na samaniya har zuwa mutuwa. Wataƙila, begenmu na tashin matattu zai ƙarfafa mu idan muka bincika dawowa da wasu zuwa rai da aka rubuta cikin Littafi Mai-Tsarki. Dukan waɗannan mu’ujizoji an yi su ne da ikon Mai Ikon Mallaka Sarki Jehovah.

Ta Tashin Matattu Suka Karɓi Na Su da Suka Mutu

3. Me aka ba Iliya ikon ya yi lokacin da ɗan wata gwauruwa ya mutu a Zarefat?

3 A wani maimaitawa mai ban sha’awa na yadda shaidun Jehovah kafin lokacin Kiristoci suka nuna bangaskiya, manzo Bulus ya rubuta: “Mata suka karɓi matattunsu, daga cikin mutuwa aka tashe su.” (Ibraniyawa 11:35; 12:1) Ɗaya cikin waɗannan wata matalauciya gwauruwa ce a birnin Finikiya na Zarefat. Domin kirkin da ta yi wa annabin Allah Iliya da ta karɓe shi, garinta da kuma mai ba su ƙare ba cikin mu’ujiza a lokacin fari wanda da ya kashe ta da ɗanta. Da yaron ya mutu daga baya, Iliya ya kwantar da shi a kan gado, ya yi addu’a, ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya yi roƙo: “Ya Ubangiji Allahna, ina roƙonka, ka bar ran yaron nan ya sake shiga cikinsa.” Allah ya sa kurwa, ko kuma rai, ya shiga jikin yaron. (1 Sarakuna 17:8-24) Ka ga yadda wannan gwauruwa za ta yi murna yayin da aka albarkaci bangaskiyarta ta wajen tashin macacce na farko da aka rubuta—na ɗanta da take ƙauna!

4. Wace mu’ujiza ce Elisha ya yi a Shunem?

4 Wata mace kuma da ta karɓi na ta da ya mutu ta tashin matattu tana da zama ne a birnin Shunem. Matar wani tsoho, ta nuna alheri ga annabi Elisha da kuma baransa. An albarkace ta da ɗa. Shekaru da yawa daga bisani, ta kira annabin wanda ya zo ya sami yaro macacce a gidanta. Bayan Elisha ya yi addu’a da kuma wasu abubuwa, ‘a hankali sai jikin yaron ya yi ɗumi.’ Sai ‘yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.’ Babu shakka wannan tashin macaccen ya faranta ran uwar da ɗanta ƙwarai. (2 Sarakuna 4:8-37; 8:1-6) Amma za su fi farin ciki lokacin da aka tashe su su rayu cikin duniya a lokacin “tashi mafi kyau”—wanda zai ba su damar su rayu ba tare da sun mutu ba kuma! Lalle dalili ne na yin godiya ga Allah mai ƙauna wanda zai tada matattu, Jehovah!—Ibraniyawa 11:35.

5. Ta yaya Elisha ya kasance cikin mu’ujiza har ma bayan mutuwarsa?

5 Har bayan da Elisha ya mutu aka binne shi ma, Allah ya ba wa ƙasusuwansa iko ta ruhu mai tsarki. Mun karanta: “Ananan [wasu Isra’ilawa] suna cikin binne wani mutum, sai suka hangi mahara [Mowabawa]; suka jefarda mutumin [da ya mutu] cikin kabarin Elisha: da mutumin ya taɓa ƙasusuwan Elisha, sai ya wartsake, ya tsaya bisa ƙafafunsa.” (2 Sarakuna 13:21) Mutumin nan lalle ya yi mamaki da kuma murna! Ka ga yadda za a yi murna lokacin da aka tashi ƙaunatattunmu zuwa rai daidai da nufin Allah Jehovah wanda ba zai faɗi banza ba!

Ɗan Allah Ya Tayar da Matattu

6. Wace mu’ujiza ce Yesu ya yi a kusa da birnin Nayin, kuma yaya wannan aukuwar za ta shafe mu?

6 Ɗan Allah, Yesu Kristi, ya ba mu dalili mai ƙwari na yarda da cewa matattu za a tashe su a tashin matattu, da damar samun rai madawwami. Abin da ya auku kusa da birnin Nayin zai iya taimaka mana mu fahimci cewa irin wannan mu’ujizar za ta yiwu ta wurin ikon da Allah ya bayar. Wani lokaci, Yesu ya tarar da masu makoki suna ɗauke da gawar wani saurayi suna fitowa daga cikin birnin don su binne. Ɗan tilo ne na wata gwauruwa. Yesu ya ce mata: ‘Daina kuka.’ Sai ya taɓa makarar kuma ya ce: ‘Saurayi, na ce maka, Ka tashi.’ Sai mamacin ya tashi zaune ya fara magana. (Luka 7:11-15) Wannan mu’ujizar babu shakka ta ƙarfafa tabbacinmu cewa begen tashin matattu tabbacacce ne.

7. Me ya faru da yake da alaƙa da ’yar Yayirus?

7 Ka yi la’akari kuma da abin da ya auku da ya haɗa da Yayirus, shugaban majami’a a Kafarnahum. Ya roƙi Yesu ya zo ya taimake ’yarsa ’yar shekara 12 da yake ƙauna, wadda take bakin mutuwa. Bai daɗe ba aka ce yarinyar ta mutu. Ya aririci Yayirus wanda ya cika da baƙin ciki ya ba da gaskiya, Yesu ya bi shi zuwa gidansa, inda jama’a suke kuka. Suka yi dariya da Yesu ya ce musu: ‘Yarinyar ba macacciya take ba, amma barci take yi.’ Hakika ta mutu, amma Yesu yana bakin nuna cewa za a tashi mutane zuwa rai daidai kamar yadda za a tashe su a barci mai zurfi. Ya kama hannun yarinyar ya ce mata: “Yarinya, ki tashi.” Nan take ta tashi, kuma ‘iyayenta suka yi farin ciki ƙwarai.’ (Markus 5:35-43; Luka 8:49-56) Babu wata tantama, iyalai za su yi ‘farin ciki ƙwarai’ lokacin da aka tashi ƙaunatattunsu da suka mutu zuwa rai a aljanna a duniya.

8. Menene Yesu ya yi a kabarin Li’azaru?

8 Li’azaru ya mutu da kwana huɗu yayin da Yesu ya kai kabarinsa ya sa aka cire dutse da ya rufe kabarin. Bayan ya yi addu’a a idon mutanen da suke wajen domin su sani cewa ya dangana ne bisa ikon da Allah ya ba shi, sai Yesu ya kira da babbar murya: “Li’azaru, ka fito.” Sai ya fito! Hannayensa da ƙafafuwansa suna ɗaure da likkafani, fuskarsa kuma da alawayyo. Yesu ya ce: ‘Ku kwance masa ya tafi.’ Ganin wannan mu’ujiza ya sa da yawa da suka zo su yi wa ’yan’uwan Li’azaru Maryamu da Marta ta’aziyya, suka ba da gaskiya ga Yesu. (Yohanna 11:1-45) Wannan bai cika ka da begen cewa za a tada ƙaunatattunka zuwa rai a sabuwar duniya ta Allah ba?

9. Me ya sa za mu tabbata cewa a yanzu Yesu zai iya tada matattu?

9 Lokacin da Yohanna mai baftisma yake gidan yari, Yesu ya aika masa wannan saƙo mai ƙarfafawa: “Makafi suna karɓan ganin gari, . . . ana tada matattu.” (Matta 11:4-6) Tun da lokacin da yake duniya Yesu ya tada matattu, babu shakka zai iya yin haka da ya zama babbar halitta ta ruhu da Allah ya ba shi iko. Yesu ne ‘tashin matattu, shi ne rai,’ lalle yana ba da ƙarfafa sanin cewa ba da jimawa ba “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29; 11:25.

Wasu Tashin Matattu Sun Ƙarfafa Begenmu

10. Yaya za ka kwatanta tada macacciya ta farko da manzo ya yi?

10 Lokacin da Yesu ya aika manzanninsa su zama masu wa’azin Mulki, ya ce: “Ku tada matattu.” (Matta 10:5-8) Don su yi wannan babu shakka, dole su dogara ga ikon Allah. A Yafa a shekara ta 36 K.Z., tsarkakkiya Dokas (Tabita) ta rasu. Kyawawan ayyukanta sun haɗa da tsaka tufafi ga gwauraye da suke da bukata, tsakaninsu kuwa mutuwarta ta jawo kuka sosai. Almajiran suka shirya ta don a binne, sai suka aika wa manzo Bitrus, wataƙila don ta’aziyya. (Ayukan Manzanni 9:32-38) Ya ce kowa ya fita daga benen, sai ya yi addu’a, ya ce: “Tabita, ki tashi.” Ta buɗe idanunta, ta tashi zaune, ta riƙe hannun Bitrus kuma ya tada ta tsaye. Wannan rahoton tada macacciya ta farko da manzo ya yi ya sa mutane da yawa suka zama masu bi. (Ayukan Manzanni 9:39-42) Wannan ya ƙara mana dalilin begen tashin matattu.

11. Wane labari aka rubuta na tashin matattu na ƙarshe a cikin Littafi Mai-Tsarki?

11 Tashi daga matattu na ƙarshe da yake rubuce a cikin Littafi Mai-Tsarki ya auku ne a Taruwasa. Da Bulus ya tsaya a can a lokacin tafiyarsa ta uku ta wa’azi, ya yi dogon jawabi har tsakar dare. Wani saurayi mai suna Aftikos ya gaji wataƙila domin zafin fitilu da kuma matsin waje a taron domin yawan jama’a, barci ya kwashe shi, sai ya faɗo ta taga daga bene hawa na uku. Aka “ɗauke shi matacce,” ba a sume ba. Sai Bulus ya faɗi a kansa, ya rungume shi, ya gaya wa masu kallo: “Kada ku yi kuka; gama ransa yana cikinsa.” Abin da Bulus yake nufi shi ne an mayar wa saurayin ransa. Waɗanda suke wajen “suka sami ta’aziyya ba kaɗan ba.” (Ayukan Manzanni 20:7-12) A yau, bayin Allah suna samun ta’aziyya daga sanin cewa abokanansu a ayyukan Allah za su ga cikar bege na tashin matattu.

Tashin Matattu—Bege ne da Ya Daɗe

12. Wane tabbaci ne Bulus ya furta lokacin da yake gaban Filikus Gwamnan Roma?

12 Da ake tuhumarsa a gaban Filikus Gwamnan Roma, Bulus ya shaida: “Ina gaskatawa dukan abin da ke bisa ga Attaurat, da waɗanda an rubuta cikin annabawa: ina da bege ga Allah, . . . za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:14, 15) Ta yaya ɓangaren Kalmar Allah, kamar su “Doka,” suka nuna tashin matattu?

13. Me ya sa za a iya cewa Allah ya yi magana game da tashin matattu lokacin da ya yi annabcinsa na farko?

13 Allah da kansa ya yi maganar tashin matattu lokacin da ya yi annabci a Adnin. Da yake wa “tsohon macijin,” Shaiɗan Iblis hukunci, Allah ya ce: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; Farawa 3:14, 15) Ƙuje duddugen ɗan matar na nufin kashe Yesu Kristi. Idan kuma Ɗan zai ƙuje kan macijin daga baya, to, sai an tashi Kristi daga matattu ke nan.

14. Ta yaya Jehovah “ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai”?

14 Yesu ya sanar: “Amma ga zancen matattu da tashinsu, ko Musa ya gwada wannan a cikin nassi na sarƙaƙiya, inda ya ce da Ubangiji, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub kuma. Shi dai ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai: gama duka suna rayuwa gareshi.” (Luka 20:27, 37, 38; Fitowa 3:6) Ibrahim, Ishaƙu, da kuma Yaƙub duka sun mutu, amma nufin Allah ya ta da su tabbatacce ne ƙwarai saboda haka suna rayuwa a gareshi.

15. Me ya sa Ibrahim yake da hujjar yin begen tashin matattu?

15 Ibrahim yana da hujjar yin bege ga tashin matattu, domin lokacin da shi da matarsa, Saratu, suka tsufa sosai, matattu ga haifan yara, Allah cikin mu’ujiza ya mai da musu ikon haihuwa. Wannan daidai yake da tashin matattu. (Farawa 18:9-11; 21:1-3; Ibraniyawa 11:11, 12) Lokacin da ɗansu, Ishaƙu, yake da kusan shekara 25 da haihuwa, Allah ya gaya wa Ibrahim ya yi hadaya da shi. Daidai lokacin da yake so ya kafa masa wuka, mala’ikan Jehovah ya riƙe hannunsa. Ibrahim “ya aza Allah yana da iko ya tada [Ishaƙu], ko daga matattu; inda ya sake karɓe shi kuma cikin misali.”—Ibraniyawa 11:17-19; Farawa 22:1-18.

16. Ibrahim yanzu yana kwance matacce yana jiran menene?

16 Ibrahim ya yi begen tashin matattu a ƙarƙashin sarautar Almasihu, Ɗan alkawarin. A ɗaukakarsa kafin ya zama mutum, Ɗan Allah ya lura da bangaskiyar Ibrahim. Da Yesu Kristi ya zama mutum daga baya, ya gaya wa Yahudawa: “Ubanku Ibrahim ya yi murna da ganin ranata; har ya gan ta, zuciyarsa ta yi fari kuma.” (Yohanna 8:56; Misalai 8:30, 31) Ibrahim yanzu yana kwance matacce, yana jiran a ta da shi daga matattu zuwa rayuwa ta aljanna a ƙarƙashin Mulkin Almasihu na Allah.—Ibraniyawa 11:8-10, 13.

Tabbaci Daga Doka da Kuma Zabura

17. Ta yaya ‘abin da aka rubuta cikin Dokar’ ya yi maganar tashin Yesu Kristi?

17 Begen tashin matattu da Bulus ya yi, ya jitu da ‘abin da aka rubuta cikin Dokar.’ Allah ya gaya wa Isra’ilawa: “Za ku kawo damin ’ya’yan fari na girbinku wurin [firist]: shi kuma [a 16 ga Nisan] za ya yi malelekuwa da damin a gaban Ubangiji, domin a karɓe ku.” (Leviticus 23:9-14) Wataƙila da wannan dokar ne a zuci, Bulus ya rubuta: “An tada Kristi daga matattu, ’ya’yan fari daga cikin waɗanda ke barci.” Kamar yadda yake “ ’ya’yan fari,” an tashi Yesu a 16 ga Nisan, shekara ta 33 K.Z. Daga baya, a lokacin bayyanuwarsa, tashin ‘ ’ya’ya na baya’ zai kasance—mabiyansa waɗanda ruhu ya shafa.—1 Korinthiyawa 15:20-23; 2 Korinthiyawa 1:21; 1 Yohanna 2:20, 27.

18. Ta yaya Bitrus ya nuna cewa an annabta tashin Yesu daga matattu a cikin Zabura?

18 Zabura ma ta ba da goyon baya ga tashin matattu. A ranar Fentikos na shekara ta 33 K.Z., manzo Bitrus ya yi magana daga Zabura 16:8-11, yana cewa: “Gama Dauda ya ambace[Kristi], ya ce, Na ga Ubangiji tuttur a gaban fuskata, gama yana ga hannun damana, domin kada in jijjigu: Domin wannan zuciyata ta yi fari, harshena ya yi murna, har kuma jikina za ya zauna cikin bege, gama ba za ka bar raina cikin kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai-tsarkinka shi ga ruɓa ba.” Bitrus ya daɗa: “[Dauda] domin ya rigaya ya ga wannan, zancen tashin Kristi ya yi da ya ce ba a bar shi cikin Lahira ba, jikinsa kuma ba ya ga ruɓa ba. Wannan Yesu, Allah ya tashe shi.”—Ayukan Manzanni 2:25-32.

19, 20. Yaushe Bitrus ya ɗauko aya daga Zabura 118:22, kuma ta yaya wannan yake da alaƙa da mutuwar Yesu da kuma tashinsa?

19 Bayan wasu kwanaki, Bitrus ya tsaya a gaban majalisa kuma ya ɗauko ayoyi daga Zabura. Da aka tambaye shi ta yaya ya warkar da gurgu mai bara, sai manzon ya ce: “Bari wannan ya zama sananne gareku duka, da jama’ar Isra’ila duka, cikin sunan Yesu Kristi na Nazarat, wanda kuka [rataye], wanda Allah ya tashe shi daga matattu, a cikinsa mutumin nan yana tsaye a gabanku lafiyayye. [Yesu] shi ne dutsen da ku magina kuka waƙala, wanda an maishe shi kan ƙusurwa. Kuma babu ceto ga waninsa: gama babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.”—Ayukan Manzanni 4:10-12.

20 A nan Bitrus ya ɗauko aya daga Zabura 118:22, ya yi amfani da abin da suka faɗa game da mutuwar Yesu da kuma tashinsa. Yahudawa suka ƙi Yesu domin zugi daga shugabannan addininsu. (Yohanna 19:14-18; Ayukan Manzanni 3:14, 15) ‘Ƙin dutsen da magina suka yi’ ya kai ga mutuwar Kristi, amma ‘dutsen ya zama kan ƙusurwa’ yana nufin tashinsa zuwa ɗaukaka a ruhu a sama. Kamar yadda mai Zabura ya ce, ‘wannan dai daga Jehovah kansa.’ (Zabura 118:23) Mayar da “dutsen” Kan ƙusurwa yana haɗe da ɗaukaka shi Zaɓaɓɓen Sarki.—Afisawa 1:19, 20.

Ƙarfafa ta Wurin Begen Tashin Matattu

21, 22. Wane bege ne Ayuba ya nuna, kamar yadda yake rubuce cikin Ayuba 14:13-15, kuma ta yaya wannan zai yi wa waɗanda suka yi rashi ta’aziyya a yau?

21 Ko da yake mu da kan mu ba mu taɓa ganin wani ya tashi daga matattu ba, mun ga wasu labaran Nassosi da suka tabbatar mana da tashin matattu. Saboda haka, za mu iya begen abin da mutum mai tawali’u Ayuba ya yi. Lokacin da yake wahala, ya yi roƙo: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira, . . . ka sanya mini rana, sa’annan ka tuna da ni! Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa? . . . Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayuba 14:13-15) Allah zai ‘yi marmarin aikin hannunsa,’ zai yi muradin ta da Ayuba. Wannan ya ba mu bege ƙwarai!

22 Wani a iyali mai tsoron Allah zai iya yin rashin lafiya mai tsanani, kamar yadda Ayuba ya yi, har ma ya faɗa cikin hannun abokin gaba, mutuwa. Waɗanda suka yi rashi za su yi hawaye don baƙin ciki, kamar yadda Yesu ya yi kuka saboda mutuwar Li’azaru. (Yohanna 11:35) Yana ba da ƙarfafa ƙwarai mu san cewa Allah zai yi kira kuma dukan waɗanda ya tuna da su za su amsa! Zai kasance kamar sun dawo ne daga tafiya—ba da ciwo ko kuma lahani ba, amma da cikakken koshin lafiya.

23. Ta yaya wasu suka nuna tabbacinsu ga begen tashin matattu?

23 Mutuwar wata tsohuwar Kirista ya motsa ’yan’uwa Kiristoci suka rubuta: “Muna yi maka ta’aziyya bisa mutuwar mamarka. Ba zai jima ba za mu yi mata maraba—kyakkyawa kuma cike da kuzari!” Iyaye da suka yi rashin ɗansu suka ce: “Muna saurarar ranar da Jason zai tashi! Zai duba ya ga aljannar da ya yi marmarinta. . . . Wannan abu wanda zai motsa mu da muke ƙaunarsa mu kasance a can mu ma.” Hakika, za mu yi godiya cewa begen tashin matattu tabbatacce ne!

Mecece Amsarka?

• Ta yaya bangaskiya ga tanadi da Allah ya yi na ta da matattu zai amfane mu?

• Wace aukuwa ce aka rubuta cikin Nassosi ta ba mu dalilin yin begen tashin matattu?

• Me ya sa za a iya cewa tashin matattu bege ne da ya daɗe?

• Wane bege ne mai ƙarfafawa za mu iya riƙewa game da matattu?

[Hoto a shafi na 8]

Da iko daga wurin Jehovah, Iliya ya mayar da rai ga ɗan gwauruwa

[Hoto a shafi na 10]

Lokacin da Yesu ya ta da ’yar Yayirus zuwa rai, iyayenta sun yi murna ƙwarai

[Hoto a shafi na 13]

A ranar Fentikos na 33 K.Z., manzo Bitrus ya yi shaida da gaba gaɗi cewa an ta da Yesu daga matattu

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba