Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 9/1 pp. 24-29
  • Ka Mai Da Hankali Da“muryar Baƙo”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Mai Da Hankali Da“muryar Baƙo”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Wanda Bai Shiga ta Ƙofar Ba’
  • Sa’ad da Aka Soma Jin Muryar Baƙo
  • Yadda Ake Jin Muryar Baƙo a Yau
  • ‘Ku Jaraba Ruhun Ku Gani’
  • ‘Za Su Guje Shi’
  • Inda Za Ka Sami Ta’aziyya
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 9/1 pp. 24-29

Ka Mai Da Hankali Da“muryar Baƙo”

“Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”—Yahaya 10:5.

1, 2. (a) Yaya Maryamu ta aikata sa’ad da Yesu ya kira ta da sunanta, wannan aukuwa ya kwatanta wane furcin Yesu na dā? (b) Menene ke taimaka mana mu yi kusa da Yesu?

YESU da ya tashi daga matattu ya lura cewa matar ta tsaya kusa da kabarinsa da ba kome. Ya san ta sosai. Maryamu Magadaliya ce. Kusan shekara biyu da ta shige, ya fitar mata aljanu. Tun lokacin tana binsa da manzanninsa, tana biyan bukatunsu na kullum. (Luka 8:1-3) Amma, yanzu Maryamu tana kuka, tana baƙin ciki sosai domin ta ga Yesu ya mutu kuma yanzu babu jikinsa! Sai Yesu ya tambaye ta: “Uwargida, don me kike kuka? Wa kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa: “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.” Sai Yesu ya ce: “Maryamu!” Nan da nan, ta gane yadda yake mata magana. Da farin ciki ta ce “malam!” Sai ta rungume shi.—Yahaya 20:11-18.

2 Wannan labarin na sosuwar rai ya kwatanta abin da Yesu ya faɗa dā. Da yake gwada kansa da makiyayi kuma mabiyansa da tumaki, ya ce makiyayi yana kiran tumakinsa da sunansu kuma sun san muryarsa. (Yahaya 10:3, 4, 14, 27, 28) Hakika, yadda tumaki suke gane makiyayinsu, haka Maryamu ta san Makiyayinta, Kristi. Haka yake game da mabiyan Yesu a yau. (Yahaya 10:16) Yadda kunnen fahimi na tumaki ke taimaka musu su kasance kusa da makiyayin, haka fahiminmu na ruhaniya ke taimaka mana mu yi tafiya a sawun Makiyayinmu Mai Kyau, Yesu Kristi.—Yahaya 13:15; 1 Yahaya 2:6; 5:20.

3. Waɗanne tambayoyi ne kwatancin Yesu na garken tumaki suke tunasar mana?

3 Amma, bisa ga wannan kwatanci, da yake tumaki na iya gane muryar ’yan Adam yana taimaka musu su san abokansu da kuma magabtansu. Wannan yana da muhimmanci domin muna da ’yan hamayya masu ruɗu. Su wanene su? Yaya suke aiki? Yaya za mu tsare kanmu? Don mu sani, bari mu ga wani abin da Yesu ya ce a kwatancinsa game da garke.

‘Wanda Bai Shiga ta Ƙofar Ba’

4. Bisa kwatancin makiyayi, wanene tumakin suka bi, kuma wanene ba su bi ba?

4 Yesu ya ce: “Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje. Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye na shi, domin sun san murya tasa. Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.” (Yahaya 10:2-5) Ka lura cewa Yesu ya yi amfani da kalmar nan ‘murya’ sau uku. Ya yi maganar muryar makiyayi sau biyu, amma na ukun ya yi maganar “muryar baƙo.” Wane irin baƙo ne Yesu yake maganarsa?

5. Me ya sa ba ma yi wa baƙo da aka ambata a Yahaya sura 10 alheri?

5 Yesu ba ya maganar baƙo da za mu so mu yi masa alheri—furcin a yaren Littafi Mai Tsarki na asali yana nufin “ƙaunar baƙi.” (Ibraniyawa 13:2) A kwatancin Yesu, ba a gayyaci baƙon ba. Bai “shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu.” “Ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.” (Yahaya 10:1) Wanene na farko da aka ambata cikin Kalmar Allah da ya zama ɓarawo da kuma ɗan fashi? Shaiɗan Iblis ne. Mun ga tabbacin a littafin Farawa.

Sa’ad da Aka Soma Jin Muryar Baƙo

6, 7. Me ya sa ya dace da aka kira Shaiɗan baƙo kuma ɓarawo?

6 Farawa 3:1-5 ta kwatanta yadda aka soma jin muryar baƙo a duniya. Labarin ya ce Shaiɗan ya je wajen mace na farko, Hauwa’u, ta wurin maciji kuma ya yi mata magana a hanyar ruɗu. Hakika, a wannan labarin ba a kira Shaiɗan a zahiri “baƙo” ba. Duk da haka, ayyukansa a hanyoyi da yawa ya nuna cewa yana kama da baƙo da aka kwatanta a misalin Yesu da ke rubuce a Yahaya sura 10 ne. Ga wasu kamaninsa.

7 Yesu ya ce baƙon ya je wajen waɗanda yake so ya kama a garken tumakin a kaikaice. Haka nan ma, Shaiɗan ya je wajen wanda yake son ya kama a kaikaice, ya yi amfani da maciji. Yadda Shaiɗan ya je da wayo ya nuna irin halinsa—mai kutsa kansa ne cikin zance da ba nasa ba. Ƙari ga haka, baƙon a garken tumaki yana son ya kwace tumakin daga makiyayinsu. Hakika, ya fi ɓarawo muni domin manufarsa shi ne ya yi “kisa da hallakarwa.” (Yahaya 10:10) Haka nan ma, Shaiɗan ɓarawo ne. Da ya ruɗe Hauwa’u, ya sace amincinta ga Allah. Bugu da ƙari, Shaiɗan ya sa mutane suna mutuwa. Saboda haka, shi mai kisan kai ne.

8. Ta yaya Shaiɗan ya murguɗe kalmomin Jehovah da nufinsa?

8 An ga rashin gaskiyar Shaiɗan a yadda ya murguɗe kalmomin Jehovah da nufinsa. Ya tambayi Hauwa’u: ‘Ko Allah ya ce, ba za ku ci daga wani itace ba?’ Shaiɗan ya yi kamar yana mamaki, kamar yana cewa: ‘Yaya Allah zai yi irin wannan abu?’ Ya daɗa: “Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe.” Ka lura da kalmominsa: “Allah ya sani.” Kamar dai Shaiɗan ya ce: ‘Na san abin da Allah ya sani. Na san nufinsa, ba mai kyau ba ne.’ (Farawa 2:16, 17; 3:1, 5) Abin baƙin ciki, Hauwa’u da Adamu sun saurari muryar wannan baƙon. Sun yi biyayya da ita kuma suka jawo wa kansu da zuriyarsu wahala.—Romawa 5:12, 14.

9. Me ya sa za mu yi tsammanin jin muryar baƙo a yau?

9 Shaiɗan yana amfani da irin wannan hanyoyi ya ruɗi mutanen Allah a yau. (Wahayin Yahaya 12:9) “Uban ƙarairayi” ne kuma waɗanda kamarsa suka yi ƙoƙarin su yaudari bayin Allah yaransa ne. (Yahaya 8:44) Bari mu lura da wasu hanyoyi da ake jin muryar baƙo a yau.

Yadda Ake Jin Muryar Baƙo a Yau

10. Wace hanya ɗaya ce ake jin muryar baƙo?

10 Tunanin ruɗu. Manzo Bulus ya ce: “Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku.” (Ibraniyawa 13:9) Wace irin koyarwa? Tun da yake suna iya ‘bauɗar da mu,’ a bayyane yake cewa Bulus yana maganar koyarwa da ke raunanar da ruhaniyarmu. Su wa suke yin irin wannan baƙuwar koyarwa? Bulus ya gaya wa wani rukunin Kiristoci dattawa: “A cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.” (Ayyukan Manzanni 20:30) Hakika, a yau yadda yake a kwanakin Bulus, wasu da dā suke cikin ikilisiyar Kirista yanzu suna ƙoƙari su yaudari tumakin ta faɗan “maganganun da ba sa kan hanya”—rabin gaskiya da ƙaryace-ƙaryace kai tsaye. Yadda manzo Bitrus ya faɗa, suna amfani da “tsararrun labaru”—kalmomi da kamar gaskiya ne amma na banza ne.—2 Bitrus 2:3.

11. Yaya kalmomi da ke 2 Bitrus 2:1, 3 ya fallasa hanyoyi da manufar ’yan ridda?

11 Bitrus ya ci gaba da fallasa hanyoyin ’yan ridda cewa “za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa.” (2 Bitrus 2:1, 3) Yadda ɓarawo cikin kwatancin Yesu na garken tumaki bai “shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu,” hakan nan ’yan ridda suke zuwa wurin mu a kaikaice. (Galatiyawa 2:4; Yahuza 4) Menene manufarsu? Bitrus ya daɗa: “Za su ribace ku.” Hakika, ko menene ’yan ridda za su faɗa don su ba da hujjar kansu, manufar ɓarayi ita ce don su yi “sata da kisa da hallakarwa.” (Yahaya 10:10) Ku mai da hankali da irin waɗannan baƙi!

12. (a) Ta yaya tarayyarmu zai iya sa mu ji murya baƙo? (b) Wane kamani ke tsakanin dabarun Shaiɗan da na baƙo a yau?

12 Tarayya mai lahani. Ana iya jin muryar baƙo ta wurin waɗanda muke tarayya da su. Tarayya mai lahani na shafan matasa musamman. (1 Korantiyawa 15:33) Ka tuna cewa Shaiɗan ya sami Hauwa’u—wadda ita ce ƙarama kuma marar wayo. Ya tabbatar mata cewa Jehovah ya hana ta ’yanci, da a kashin gaskiya ba haka ba ne. Jehovah yana ƙaunar halittarsa mutane kuma yana kula da zaman lafiyarsu. (Ishaya 48:17) Haka nan ma a yau, baƙi suna ƙoƙarin rinjayar ku matasa cewa iyayenku Kirista na hana ku ’yanci. Ta yaya irin waɗannan baƙi za su shafe ku? Wata yarinya Kirista ta ce: “Abokan ajina sun raunanar da bangaskiyata na ɗan lokaci. Suka ci gaba da cewa addinina na da hani kuma hakan bai dace ba.” Duk da haka, gaskiyar ita ce cewa iyayenku na ƙaunar ku. Saboda haka, lokacin da abokan makaranta suka yi ƙoƙari su rinjaye ku ku yi rashin aminci da iyayenku, kada a ruɗe ku yadda aka yi wa Hauwa’u.

13. Wane irin tafarki mai kyau Dauda ya bi, a wace hanya za mu yi koyi da shi?

13 Game da tarayya mai lahani, mai Zabura Dauda ya ce: “Ba na tarayya da mutanen banza, ba abin da ya gama ni da masu riya.” (Zabura 26:4) Ka lura cewa halin baƙo ne wannan? Yana ɓoye kamaninsa—yadda Shaiɗan ya ɓoye irin mutumin da yake ta yin amfani da maciji. A yau, wasu mutane masu lalata suna ɓoye kamaninsu da nufinsu na gaske ta yin amfani da Intane. A wurin hira na Intane, manya suna iya ce su matasa ne don su sa ku fāɗa cikin tarko. Matasa, don Allah ku mai da hankali don kada ku sami lahani na ruhaniya.—Zabura 119:101; Karin Magana 22:3.

14. Wani lokaci, yaya hanyar watsa labarai suke ba da rahoton muryar baƙo?

14 Tuhumar ƙarya. Ko da ana ba da wasu labarai mai kyau game da Shaidun Jehovah, wani lokaci ana amfani da hanyar watsa labarai a yaɗa tuhumar ƙarya ta muryar baƙo. Alal misali, a wata ƙasa wani rahoto ya faɗi ƙarya cewa Shaidu sun goyi bayan mulkin Hitler a lokacin Yaƙin Duniya na II. A wata ƙasa kuma, wani rahoto ya zargi Shaidun cewa sun yi kaca-kaca da wani ginin coci. A ƙasashe da yawa, hanyar watsa labarai na zargin Shaidun cewa ba sa jinyar yaransu kuma da gangan suna amince da mugun zunubai da ’yan’uwa masu bi suke yi. (Matiyu 10:22) Duk da haka, mutane masu gaskiya da suka san mu sun san cewa wannan tuhumar ƙarya ce.

15. Me ya sa ba shi da kyau mu gaskata kowane abu da aka yaɗa a hanyar watsa labarai?

15 Menene ya kamata mu yi idan muna fuskantar tuhuma da muryar irin waɗannan baƙi suke yaɗawa? Ya kamata mu yi biyayya da gargaɗin Karin Magana 14:15: “Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la’akari yana lura da takawarsa.” Ba shi da kyau mu gaskata da kowane abu da aka watsa a labarai. Ko da ba ma ƙin amince da dukan labaran duniya, mun sani cewa ‘duniya duka kuwa tana hannun Mugun.’—1 Yahaya 5:19.

‘Ku Jaraba Ruhun Ku Gani’

16. (a) Yaya halin tumaki na zahiri ya kwatanta gaskiyar kalmomin Yesu da ke Yahaya 10:4? (b) Menene Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi?

16 To, ta yaya za mu sani ko muna sha’ani da aboki ko kuma magabci? To dai, Yesu ya ce tumakin na bin makiyayin “domin sun san murya tasa.” (Yahaya 10:4) Ba surar makiyayin ke motsa tumakin su bi shi ba; amma muryarsa ce. Wani littafi a kan ƙasashen Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin yadda wani baƙo ya yi da’awa cewa tumaki na gane makiyayinsu ta tufafinsa, ba muryarsa ba. Wani makiyayi ya ce muryarsa ce suka sani. Don ya tabbatar da wannan, ya yi musanyar tufafinsa da baƙon. Da ya sa tufar makiyayin, baƙon ya kira tumakin, amma ba su amsa ba. Ba su san muryarsa ba. Amma, sa’ad da makiyayin ya kira su, ko da ya canja tufarsa, tumakin suka ruga gare shi. Da haka, wani zai iya yin shigen makiyayi, amma ga tumakin wannan ba ya nuna cewa shi makiyayi ne. Da haka, tumakin sun jaraba muryar mai kiransu, sun gwada ta da muryar makiyayin. Kalmar Allah ta gaya mana mu yi hakan—“ku jarraba ku gani ko na Allah ne.” (1 Yahaya 4:1; 2 Timoti 1:13) Menene zai taimake mu mu yi hakan?

17. (a) Yaya za mu sarƙu da muryar Jehovah? (b) Sanin Jehovah zai taimake mu mu yi menene?

17 Hakika, idan mun san muryar Jehovah ko saƙonsa sosai, za mu iya gane muryar baƙo da kyau. Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda za mu sami irin wannan sani. Ya ce: “Za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, ‘Ga hanyan nan, ku bi ta.’ ” (Ishaya 30:21) Wannan ‘murya’ a bayanmu Kalmar Allah ce. Kowane lokaci da muka karanta Kalmar Allah, a alamance, muryar Makiyayinmu Mai Girma, Jehovah ne. (Zabura 23:1) Saboda haka, idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki, za mu daɗa sarƙu da muryar Allah. Wannan cikakken sani zai taimake mu mu san muryar baƙo babu ɓata lokaci.—Galatiyawa 1:8.

18. (a) Menene sanin muryar Jehovah ya ƙunsa? (b) In ji Matiyu 17:5, me ya sa ya kamata mu yi biyayya da muryar Yesu?

18 Sanin muryar Jehovah ya ƙunshi menene? Ban da ji, ya ƙunshi yin biyayya. Ka lura da Ishaya 30:21 kuma. Kalmar Allah ta ce: “Ga hanyan nan.” Hakika, ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki, muna jin ja-gorar Jehovah. Bayan haka ya ba da umurni: “Ku bi ta.” Jehovah yana son mu yi amfani da abin da muka ji. Ta yin amfani da abin da muka koya, muna nuna cewa ba kawai mun ji muryar Jehovah ba amma muna biyayya da ita. (Maimaitawar Shari’a 28:1) Yin biyayya da muryar Jehovah na kuma nufin yin biyayya da muryar Yesu, domin Jehovah ya gaya mana mu yi hakan. (Matiyu 17:5) Menene Yesu, Makiyayi Mai Kyau ya gaya mana mu yi? Ya koya mana mu yi almajirai kuma mu amince da “amintaccen bawan nan mai hikima.” (Matiyu 24:45; 28:18-20) Yin biyayya da muryarsa zai sa mu sami rai madawwami.—Ayyukan Manzanni 3:23.

‘Za Su Guje Shi’

19. Yaya ya kamata mu aikata ga murya baƙo?

19 To, me za mu yi game da muryar baƙo? Abin da tumaki suke yi. Yesu ya ce: “Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi.” (Yahaya 10:5) Za mu aikata a hanyoyi biyu. Na farko, ba za mu “bi baƙo ba.” Hakika za mu ƙi shi sam sam. Na biyu, za mu “guje shi” ko kuma juya daga wajensa. Haka ne kawai ya dace a aikata ga waɗanda koyarwarsu bai jitu da muryar Makiyayi Mai Kyau ba.

20. Yaya za mu aikata sa’ad da muka fuskanci (a) ’yan ridda masu ruɗu, (b) tarayya mai lahani, (c) labaran ƙarya?

20 Saboda haka, sa’ad da muka sadu da waɗanda suke furta ra’ayin ’yan ridda, ya dace mu yi abin da Kalmar Allah ta ce: ‘Ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.’ (Romawa 16:17; Titus 3:10) Haka nan ma, ya kamata Kiristoci matasa da suke fuskantar tarayya mai lahani su yi amfani da gargaɗin Bulus zuwa ga matashi Timoti: ‘Ka guje wa mugayen sha’awace-sha’awacen ƙuruciya.’ Kuma sa’ad da muka ji tuhumar ƙarya a hanyar watsa labarai, za mu tuna da gargaɗi da Bulus ya daɗa wa Timoti: ‘[Waɗanda suka saurari muryar baƙo] za su karkata ga jin tatsuniyoyi. Kai kuwa, sai ka natsu cikin kowane hali.’ (2 Timoti 2:22; 4:3-5) Ko yaya muryar baƙo take da daɗi, za mu guje wa dukan abin da zai halaka bangaskiyarmu.—Zabura 26:5; Karin Magana 7:5, 21; Wahayin Yahaya 18:2, 4.

21. Wace albarka ce ke jiran waɗanda suka ƙi da muryar baƙo?

21 Ta wajen ƙi da muryar baƙo, Kiristoci da aka shafa da ruhu sun bi kalmomin Makiyayi Mai Kyau da ke Luka 12:32. A wajen Yesu ya ce musu: “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo cikin Mulkin.” Haka nan ma, “waɗansu tumaki” suna ɗokin jin kalmomin Yesu: “Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.” (Yahaya 10:16; Matiyu 25:34) Wannan albarka ce mai daɗaɗa zuciya da ke jiranmu idan mun yi tsayayya da “muryar baƙo”!

Ka Tuna?

• Ta yaya kwatancin baƙo da aka ambata a misalin Yesu game da garken tumaki ya dace da Shaiɗan?

• Yaya ake jin muryar baƙo a yau?

• Yaya za mu iya gane muryar baƙo?

• Me ya kamata mu aikata game da muryar baƙo?

[Hoto a shafi na 26]

Maryamu ta gane Kristi

[Hoto a shafi na 27]

Baƙo ba ya zuwa wurin tumaki kai tsaye

[Hoto a shafi na 29]

Yaya muke yi game da muryar baƙo?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba