Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 10/1 pp. 9-14
  • “Lokaci Ya Yi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Lokaci Ya Yi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ranar Shigar Nasara na Yesu
  • Aikatawa da Gaba Gaɗi—Sai Kuma Koyarwa na Ceton Rai
  • Ranar Hukunci
  • Yesu Ya ‘Ƙaunaci Mutanensa har Matuƙa’
  • An Ɗaukaka Ɗan Mutum!
  • “Lokacinsa Bai Yi Ba Tukuna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 10/1 pp. 9-14

“Lokaci Ya Yi”

“Lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba.”—YAHAYA 13:1.

1. Da Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z. ke kusatowa, Urushalima suna tsammanin wanene, kuma don me?

ALOKACIN baftismarsa a shekara ta 29 A.Z., Yesu ya soma aikin da zai kai “lokacin” mutuwarsa, tashi daga matattu, da kuma ɗaukaka. Lokacin rani ne na shekara ta 33 A.Z. Makonni kaɗan ne kawai suka shige tun lokacin da babban kotu na Yahudiya, ’yan Majalisa, suka ƙulla su kashe Yesu. Da ya fahimci abin da suka ƙulla, wataƙila daga Nikodimu, ɗaya daga cikin ’yan Majalisar da abokinsa ne, Yesu ya bar Urushalima, ya tafi ƙasarsa a ƙetaren Kogin Urdun. Da Idin Ƙetarewa ya kusa, mutane da yawa daga ƙasar suna zuwa Urushalima, birnin ya cika da tsammanin Yesu. “Me kuka gani?” mutane suna tambayan juna. “Zai zo idin kuwa?” Manyan firistoci da Farisiyawan sun daɗa sa mutane suna tsammaninsa ta wajen ba da umarni cewa wanda ya ga Yesu ya faɗa musu.—Yahaya 11:47-57.

2. Menene Maryamu ta yi da ya kawo jayayya, amma yadda Yesu ya goyi bayanta ya nuna menene game da sanin “lokacinsa”?

2 Ranar 8 ga watan Nisan kafin Idin Ƙetarewan, Yesu ya dawo kusa da Urushalima. Ya zo Bait’anya—garin abokanansa ƙaunatattu Marta, Maryamu, da Li’azaru—wurin misalin mil ɗaya da rabi ne daga Urushalima. Jumma’a da yamma ne, a wurin Yesu ya yi Asabaci. Washegari da yamma da Maryamu take shafa masa mai mai ƙanshi, almajiran suka tsargi hakkan. Yesu ya amsa: “A ƙyale ta, ta ajiye shi domin tanadin ranar jana’izata. Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.” (Yahaya 12:1-8; Matiyu 26:6-13) Yesu ya san cewa “lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba.” (Yahaya 13:1) Sauran kwana biyar ya “ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” (Markus 10:45) Daga yanzu, azancin gaggawa yana shafan kome da Yesu yake yi da kuma koyarwa. Lalle wannan ya tanadar mana misali mai girma yayin da muke ɗokiya a jiran ƙarshen wannan tsarin abubuwa! Yi la’akari da abin da ya faru da Yesu washegari.

Ranar Shigar Nasara na Yesu

3. (a) Ta yaya Yesu ya shiga Urushalima a ranar Lahadi 9 ga watan Nisan, yaya yawancin mutanen da ke kusa da shi suka yi? (b) Wace amsa Yesu ya ba Farisiyawa waɗanda suka kawo ƙaran jama’ansa?

3 Ranar Lahadi 9 ga watan Nisan, Yesu cikin nasara ya zo Urushalima. Da yake kusato birnin—yana kilisa a kan jaki a cikar Zakariya 9:9—yawancin mutanen da sun taru wajensa suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, wasu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo. Suna ihu: “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji!” Wasu Farisiyawa da suke cikin jama’an suna son Yesu ya kwaɓi almajiransa. Amma Yesu ya amsa: “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, ko duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”—Luka 19:38-40; Matiyu 21:6-9.

4. Me ya sa Urushalima ta ruɗe yayin da Yesu ya shiga birnin?

4 Makonni kaɗan ne kawai, mutane da yawa cikin jama’ar suka ga Yesu ya tashi Li’azaru. Waɗannan suka ci gaba da gaya wa wasu game da mu’ujizar. Saboda haka da Yesu ya shiga Urushalima dukan birnin ya ruɗe. Mutane suna tambaya, “wanene wannan?” Sai jama’a suka ci gaba da cewa: “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.” Da suke ganin abin da yake faruwa, Farisiyawan suka yi baƙin ciki suna cewa: “Ai, duk duniya na bayansa.”—Matiyu 21:10, 11; Yahaya 12:17-19.

5. Menene ya faru lokacin da Yesu ya je haikali?

5 Yadda ya saba yi in ya zo Urushalima, Yesu Babban Malamin, ya tafi haikali ya koyar. A wurin, makafi da guragu sukan zo wajensa, ya kuma warkar da su. Yayin da manyan firistoci da marubuta suka ga wannan kuma suka ji yara suna sowa cikin haikali, “Hosanna ga Ɗan Dauda!” sai suka ji haushi. Suka ce, “Kana jin abin da waɗannan ke faɗa?” Yesu ya amsa, “I.” “Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, ‘kai ne ka shiryar da ’yan yara da masu shan mama su yabe ka’?” Yayin da Yesu ya ci gaba da koyarwa, ya duba sosai ya ga abin da yake faruwa cikin haikalin.—Matiyu 21:15, 16; Markus 11:11.

6. Ta yaya yadda Yesu yake abubuwa yanzu dabam ne da dā, kuma me ya sa?

6 Yesu ya aikata abu dabam yanzu daga abin da ya yi wata shida da ta shige! Lokacin yana zuwa Urushalima don Idin Bukkoki “a ɓoye, ba a fili ba.” (Yahaya 7:10) Kuma koyaushe yana neman hanyar tsira lokacin da ya ga ransa yana cikin haɗari. Yanzu a fili ya shiga birnin da aka ba da umarni a kama shi! Yesu kuma ba ya shelar kansa cewa shi Almasihu ne. (Ishaya 42:2; Markus 1:40-44) Ba ya son shelar ɓaɓatu ko murɗaɗen labarai game da shi yana tafiya daga baki zuwa baki. Yanzu jama’ar suna sanarwa a fili shi Sarki ne kuma Mai Ceto—Almasihun—ya kuma yi banza da maganar shugabanan addinai na ya sa su yi shuru! Me ya sa ya canja haka? Domin “lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum,” yadda ya sanar washegari.—Yahaya 12:23.

Aikatawa da Gaba Gaɗi—Sai Kuma Koyarwa na Ceton Rai

7, 8. Yaya ayyukan Yesu a ranar 10 ga Nisan, 33 A.Z., suka bayyana abin da ya yi a cikin haikali a Idin Ƙetarewa na 30 A.Z.?

7 Da ya isa haikalin ranar Litinin 10 ga watan Nisan, Yesu ya aikata a kan abin da ya gani da rana a ranar da ta shige. Ya soma ‘korar masu saye da sayarwa cikin haikalin, ya kuma birkice teburorin ’yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tantabarai, ya kuma hana kowa ya ɗauki wani abu daga haikalin.’ Da yake hukunta masu laifin, ya ce: “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu’a na dukan al’ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon ’yan fashi.”—Markus 11:15-17.

8 Abin da Yesu ya yi ya bayyana abin da ya yi shekara uku da ta shige lokacin da ya ziyarci haikalin a Idin Ƙetarewa na shekara ta 30 A.Z. Amma hukuncin yanzu ya fi ban haushi. Yanzu an kira masu kasuwanci a cikin haikali “ ’yan fashi.” (Luka 19:45, 46; Yahaya 2:13-16) Haka yake, saboda suna sayar wa waɗanda suke sayan dabbobi don hadaya da tsada ƙwarai. Manyan firistoci, marubuta, da dattawa cikin mutanen suka ji abin da Yesu yake yi kuma suka nemi hanyar da za su kashe shi. Amma, ba su san yadda za su halaka shi ba, tun da yake dukan mutanen na mamaki da koyarwarsa, suna kuwa zuwa wurinsa su ji shi.—Markus 11:18; Luka 19:47, 48.

9. Wane darasi Yesu ya koyar, wace gayyata ya miƙa wa masu sauraronsa cikin haikalin?

9 Da Yesu ya ci gaba da koyarwa cikin haikalin, sai ya ce: “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.” I, ya san cewa yana da kwanaki kaɗan ne kawai na rayuwarsa ta mutum. Bayan ya faɗa yadda dole ƙwayar alkama ta mutu don ta hayayyafa—daidai take da yadda zai mutu ya kuma zama hanyar kawo rai na har abada ga wasu—Yesu ya gayyace masu sauraronsa, ya ce: “Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa ke bauta mini, Uba zai girmama shi.”—Yahaya 12:23-26.

10. Yaya Yesu ya ji game da mutuwa ta azaba da ke jiransa?

10 Da yake tunani game da mutuwarsa ta azaba da kwana huɗu kawai ta rage, Yesu ya ci gaba: “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci.’ ” Amma Yesu ba zai guje wa abin da ke jiransa ba. Ya ce: “A’a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci.” Hakika, Yesu ya yarda da dukan shirin Allah. Ya ƙuduri aniyar ya yarda nufin Allah ya ja-goranci ayyukansa har mutuwarsa ta hadaya. (Yahaya 12:27) Lalle ya kafa mana misali mai kyau—ta cikakkiyar biyayya ga nufin Allah!

11. Me Yesu ya koya wa jama’ar da suka ji murya daga sama?

11 Ya damu ƙwarai yadda mutuwarsa za ta shafi sunan Ubansa, Yesu ya yi addu’a: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Ga mamakin jama’a da ke cikin haikalin, murya ta fito daga sama, ta ce: “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” Babban Malamin ya yi amfani da wannan zarafi ya gaya wa jama’ar dalilin da ya sa aka ji muryar, abin da sakamakon mutuwarsa za ta zama, da kuma abin da ya sa ya kamata su ba da gaskiya. (Yahaya 12:28-36) Kwanaki biyu na ƙarshe babu shakka sun cika da ayyuka wa Yesu. Amma rana da take da muhimmanci na gaba tukuna.

Ranar Hukunci

12. Ranar Talata, 11 ga watan Nisan, yaya shugabanan addinai suka yi ƙoƙarin su kama Yesu, kuma da wane sakamako?

12 Ranar Talata 11 ga watan Nisan, Yesu ya je haikali ya koyar. Jama’a da abokan gaba duk suna jiransa. Da suke magana game da ayyukan Yesu na jiya, manyan firistoci da dattawa suka tambaye shi: “Da wane izni kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka iznin?” Babban Malamin ya ba su kunya da amsarsa, ya ba su misalai uku—biyu cikinsu game da garkar anab ne ɗaya kuma game da bikin aure—waɗannan sun fallasa muguntar ’yan hamayyarsa. Da suka fusata domin abin da suka ji, shugabanan addinan suna so su kama shi. Amma suna jin tsoron jama’ar, waɗanda suka ɗauke Yesu annabi ne. Sai suka nemi su ruɗe shi ya faɗi abin da zai sa su tsare shi. Amsa da Yesu ya bayar ta sa suka yi shuru.—Matiyu 21:23–22:46.

13. Wane gargaɗi ne Yesu ya ba masu sauraronsa game da marubuta da Farisiyawa?

13 Da shi ke marubuta da Farisiyawa suna da’awa wai suna koyar da Dokar Allah, Yesu ya aririce masu sauraronsa: “Ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.” (Matiyu 23:1-3) Lalle wannan hukunci ne mai ƙarfi! Amma Yesu bai gama da su ba tukuna. Wannan ranarsa ta ƙarshe ce cikin haikali, da gaba gaɗi ya fallasa su sosai—yana ba su bi da bi kamar tsawa.

14, 15. Wane hukunce-hukunce masu tsanani ne Yesu ya yi wa marubuta da Farisiyawa?

14 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai!” Yesu ya faɗa sau shida. Haka suke bisa ga bayaninsa, domin yadda sun toshe wa mutane ƙofar Mulkin sama, suna hana masu niyyar shiga su shiga. Waɗannan munafukai suna kewaye ƙasashe da tekuna don su samu almajiri ɗaya tak, don su mai da shi ɗan halaka har abada. Yayin da suke yar da “muhimman jigajigan Attaura, wato gaskiya, da jinƙai, da aminci,” suna mai da hankali ga biyan ushiri. Wato, suna “wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari” domin ruɓewa da ɗoyi da ke cikinsu a lamunin nuna ibada. Ƙari ga haka, sukan gina kuma ƙawata kaburburan annabawa, don su jawo hankali ga ayyukansu na jinƙai, ko da su ne “ ’ya’yan masu kisan annabawa.”—Matiyu 23:13-15, 23-31.

15 A hukunta rashin daraja abubuwa na ruhaniya na abokan gabansa, Yesu ya ce: “Kaitonku, makafin jagora.” Sun makanta a halayensu domin sun nace a kan muhimmancin zinariyar haikali maimakon daraja ta ruhaniya ta wurin sujjada. Yesu ya ci gaba da faɗin kalmomin hukunci masu ƙarfi. “Ku macizai,” ya ce, “yaya za ku tsere wa hukuncin [Jahannama, NW ]?” Hakika, Yesu yana gaya musu cewa don muguntarsu, za a halaka su har abada. (Matiyu 23:16-22, 33) Bari mu ma mu nuna gaba gaɗi a shelar saƙon Mulki, ko lokacin da ya ƙunshi fallasa addinin ƙarya ma.

16. Da suke zama a Dutsen Zaitu, wane annabci mai muhimmanci ne Yesu ya ba almajiransa?

16 Yesu ya bar haikalin yanzu. A faɗuwar rana, shi da manzanninsa suka hau Dutsen Zaitu. Da suke zama a wajen, Yesu ya ba da annabci game da halaka haikalin da alamar bayyanuwarsa da ƙarewar tsarin abubuwa. Ma’anar waɗannan kalmomin annabci ta kai har zamaninmu. Ranar da yamma, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a [rataye, NW ] shi.”—Matiyu 24:1-14; 26:1, 2.

Yesu Ya ‘Ƙaunaci Mutanensa har Matuƙa’

17. (a) Lokacin Idin Ƙetarewa a 14 ga watan Nisan, wane darasi ne Yesu ya koya wa almajiransa 12? (b) Wane biki ne Yesu ya girƙa bayan ya sallami Yahuza Iskariyoti?

17 Kwana biyu da suka rage—12 da 13 na watan Nisan—Yesu bai nuna kansa a fili cikin haikalin ba. Shugabanan addinai suna nema su kashe shi, ba ya son kome ya hana shi yin Idin Ƙetarewa da manzanninsa. Alhamis da yamma ce ranar 14 ga watan Nisan ta soma—rana ta ƙarshe ta rayuwar Yesu ta mutum a duniya. Da maraice, Yesu da manzanninsa suka taru a wani gida a Urushalima inda aka shirya su yi Idin Ƙetarewa. Da suke jin daɗin Idin Ƙetarewar tare, ya koya wa manzanninsa 12 darasi mai kyau na tawali’u ta wurin wanke ƙafafunsu. Bayan ya sallami Yahuza Iskariyoti, wanda ya ci amanar Ubangijinsa don azurfa 30—farashin bawa bisa Dokar Musa—sai Yesu ya gabatar da Bikin Tunawa da mutuwarsa.—Fitowa 21:32; Matiyu 26:14, 15, 26-29; Yahaya 13:2-30.

18. Me Yesu ya ƙara koya wa manzanninsa 11 masu aminci cikin ƙauna, kuma yaya ya shirya su don tafiyarsa na nan da nan?

18 Bayan ya girƙa Bikin Tunawan, manzanni suka soma jayayya a kan waye ne cikinsu ya fi girma. Maimakon ya tsauta musu, Yesu cikin haƙuri ya koya musu amfanin yi wa wasu hidima. Nuna godiya cewa sun bi shi lokacin jaraba, ya yi alkawarin mulki da su. (Luka 22:24-30) Yesu ya kuma umarce su su ƙaunaci juna yadda ya ƙaunace su. (Yahaya 13:34) Yayin da ya daɗe a ɗakin nan, Yesu ya shirya su da kyau don tafiyarsa na nan da nan. Ya tabbatar musu da abotansa, ya ƙarfafa su su ba da gaskiya, ya yi musu alkawarin taimako na ruhu mai tsarki. (Yahaya 14:1-17; 15:15) Kafin ya bar gidan, Yesu ya roƙi Ubansa: “Lokaci ya yi, Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka.” Hakika, Yesu ya shirya manzanninsa don tafiyarsa, babu shakka ya ‘ƙaunaci mutanensa har matuƙa.’—Yahaya 13:1; 17:1.

19. Me ya sa Yesu ya yi baƙin ciki sosai cikin gonar Jathsaimani?

19 Yesu da manzanninsa 11 masu aminci suka kai lambun Jathsaimani wajen asubar fari. Ya je wurin sau da yawa da manzanninsa. (Yahaya 18:1, 2) Cikin sa’o’i yanzu, Yesu zai mutu kamar mugu da ba shi da amfani. Azaba da zai fuskanta da yadda ƙila zai kawo kunya ga Ubansa ya yi tsanani har da lokacin da Yesu yake addu’a, guminsa ya yi ƙauri kamar jini da ke ɗiga. (Luka 22:41-44) “Lokaci ya yi!” Yesu ya gaya wa manzanninsa. “Kun ga, ga mai bashe ni ɗin nan ya matso!” Da yake magana, Yahuza Iskariyoti ya iso, da taron mutane riƙe da tocila da takuba da kulake. Sun zo su kama Yesu. Bai ƙi ba. Ya bayyana, “To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai kan lalle wannan abu ya kasance?”—Markus 14:41-43; Matiyu 26:48-54.

An Ɗaukaka Ɗan Mutum!

20. (a) Waɗanne wahaloli ne Yesu ya sha da aka kama shi? (b) Kusan ya mutu, me ya sa Yesu ya yi kuka: “An gama”?

20 Da aka kama shi, shaidun ƙarya sun zargi Yesu, alƙalai sun kama shi da laifi, Bilatus Babunti ya yi masa hukuncin kisa, firistoci da taron ’yan banza sun ba’anta shi, an yi masa ba’a, sojoji kuma suka gana masa azaba. (Markus 14:53-65; 15:1, 15; Yahaya 19:1-3) Ranar Jumma’a da rana, aka kafa shi a gungume inda ya sha azaba yayin da nauyin jikinsa yake ɓarke ciwon da ƙusa ya yi wa hannayensa da ƙafafunsa. (Yahaya 19:17, 18) Wajen ƙarfe uku na rana, Yesu ya yi kuka: “An gama!” Hakika, ya gama dukan abin da ya zo ya yi a duniya. Da ya miƙa ruhunsa wa Allah, ya sunkuyar da kansa ya mutu. (Yahaya 19:28, 30; Matiyu 27:45, 46; Luka 23:46) A rana ta uku, Jehovah ya tashi Ɗansa. (Markus 16:1-6) Kwanaki arba’in bayan tashinsa daga matattu, Yesu ya hau zuwa sama aka ɗaukaka shi.—Yahaya 17:5; Ayyukan Manzanni 1:3, 9-12; Filibiyawa 2:8-11.

21. Yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

21 Ta yaya za mu ‘bi hanyar Yesu’ sosai? (1 Bitrus 2:21) Kamarsa, bari mu mazakuta kanmu sosai a wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa, mu kasance da ƙarfin zuciya da gaba gaɗi a yin maganar Allah. (Matiyu 24:14; 28:19, 20; Ayyukan Manzanni 4:29-31; Filibiyawa 1:14) Kada mu manta cewa muna cikin lokaci na ƙarshe ko mu kasa ta da juna a tsimi don ƙauna da nagargarun ayyuka. (Markus 13:28-33; Ibraniyawa 10:24, 25) Mu bar nufin Jehovah Allah da sanin cewa muna a “ƙarshen lokaci,” ya ja-goranci tafarki da muke bi.—Daniyel 12:4.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya sanin cewa mutuwarsa ta kusa ya shafi hidimar Yesu ta ƙarshe cikin haikali a Urushalima?

• Menene ya nuna cewa Yesu ya ‘ƙaunaci mutanensa har matuƙa’?

• Menene abubuwa da suka faru sa’o’i kaɗan na ƙarshe ya nuna game da Yesu?

• Ta yaya za mu yi koyi da Kristi Yesu a hidimarmu?

[Hoto a shafi na 12]

Yesu ya “ƙaunace su har matuƙa”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba