Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 30-32
  • Darussa Daga Littafin Yohanna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Yohanna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “DUBA, GA ƊAN RAGO NA ALLAH”
  • (Yoh. 1:1–11:54)
  • ‘KA CI GABA DA BIN SA’
  • (Yoh. 11:55–21:25)
  • “Lokaci Ya Yi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Lokacinsa Bai Yi Ba Tukuna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 30-32

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Yohanna

YOHANNA—“almajirin nan wanda Yesu yana ƙaunatasa” shi ne mutumi na ƙarshe da ya rubuta huraren labari game da rayuwar Kristi. (Yoh. 21:20) Ya rubuta shi a kusan shekara ta 98 K.Z., Linjilar Yohanna ta maimaita kaɗan ne daga cikin abubuwa da sauran Lingilar guda uku suka ƙunsa.

Manzo Yohanna ya rubuta Linjilar da wata manufa a zuciyarsa. Game da abubuwan da ya rubuta, ya ce: “Amma an rubuta waɗannan, domin ku bada gaskiya Yesu Kristi ne, Ɗan Allah: cikin bada gaskiya kuma ku sami rai a cikin sunansa.” (Yoh. 20:31) Saƙon yana da muhimmanci a gare mu.—Ibran. 4:12.

“DUBA, GA ƊAN RAGO NA ALLAH”

(Yoh. 1:1–11:54)

Sa’ad da ya ga Yesu, Yohanna mai Baftisma ya sanar da gaba gaɗi cewa: “Duba, ga Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya!” (Yoh. 1:29) Yesu ya yi tafiya zuwa Samariya, Galili, Yahudiya, da kuma birnin da ke gabashin Jodan, yana wa’azi, yana koyarwa, kuma yana yin ayyuka masu ban al’ajabi, “mutane da yawa suka gaskata da shi.”—Yoh. 10:41, 42.

Wani mu’ujiza mai ban al’ajabi da Yesu ya yi shi ne sa’ad da ya ta da Li’azaru daga matattu. Mutane da yawa suka gaskata da Yesu sa’ad da suka ga mutumin da ya mutu kwana huɗu ya tashi. Babban Firist da Farisiyawa suka yi shawara za su kashe Yesu. Saboda haka, Yesu ya tashi daga wurin zuwa wani “ƙasa da ke kusa da jeji, ya shiga wani birni wanda ana ce da shi Ifrayimu.”—Yoh. 11:53, 54.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:35, 40—Banda Andarawus, wane almajiri ne yake tsaye da Yohanna mai Baftisma? Sau da yawa mai ba da labarin yana kiran Yohanna mai Baftisma “Yohanna” amma bai taɓa ambatar sunansa ba a cikin Linjila. Saboda haka, babu shakka almajirin da ba a ambata sunansa ba shi ne Yohanna marubucin Linjila.

2:20—Wane haikali ne aka gina a cikin “shekara arbain da shidda”? Yahudawa suna nufin sake ginin haikalin Zarubabel da Sarki Hirudus na Yahudiya ya yi ne. Dan Tarihi Josephus ya ce wannan aikin ya soma a shekara ta 18 a cikin sarautar Hirudus, ko kuma a shekara ta 18 zuwa 17 K.Z. An gina mazaunin haikalin da wasu gine-gine a cikin shekara takwas. Amma, an ci gaba da gini a haikalin har bayan Idin Ƙetarewa na shekara 30 A.Z. shi ya sa Yahudawa suka ce ginin ya kai har shekaru 46.

5:14—Zunubi ne yake kawo cuta? Ba wajibi ba ne. Mutumin da Yesu ya warƙar ya yi shekaru 38 yana ciwo saboda ya gaji ajizanci ne. (Yoh. 5:1-9) Abin da Yesu yake nufi shi ne yanzu da aka yi masa jinƙai, dole ne ya bi hanyar da za ta kai shi ga ceto kuma kada ya yi zunubin ganganci, idan ba haka ba wani abu fiye da ciwo zai same shi. Mutumin zai iya yin zunubin da ba za a yafe masa ba, wanda zai kai ga mutuwa na dindindin.—Mat. 12:31, 32; Luk 12:10; Ibran. 10:26, 27.

5:24, 25—Su waye ne za su “ratsa mutuwa zuwa cikin rai”? Yesu yana magana game da mutanen da a dā sun raunana a ruhaniya, amma bayan da suka saurari kalamansa sai suka gaskata da shi kuma suka daina yin abubuwa marasa kyau. Sun “ratsa mutuwa zuwa cikin rai” saboda an cire musu azabar mutuwa, an ba su begen rayuwa ta har abada saboda bangaskiyarsu ga Allah.—1 Bit. 4:3-6.

5:26; 6:53—Menene ake nufi da “rai a cikin kansa”? Ga Yesu Kristi, wannan yana nufin samun abubuwa guda biyu a wajen Allah, wato, hakan zai ba mutane zarafin samun dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ikon tada matattu. Ga mabiyan Yesu, “rai a cikin kansa” yana nufin samun rayuwa ta har abada. Shafaffun Kiristoci sun sami irin wannan rayuwa sa’ad da aka ta da su daga matattu zuwa rayuwa a samaniya. Amintattu da suke da begen rayuwa a duniya za su sami rai na har abada bayan sun yi nasara a gwaji na ƙarshe da zai kasance bayan ƙarshen Sarautar Shekara Dubu ta Yesu.—1 Kor. 15:52, 53; R. Yoh. 20:5, 7-10.

6:64—Yesu ya sani cewa Yahuda Iskariyoti zai bashe shi tun a lokacin da ya zaɓe shi? A bayyane yake cewa bai sani ba. A wani lokaci a shekara ta 32 A.Z., Yesu ya gaya wa manzaninsa cewa: “Ɗaya fa a cikinku shaiɗan ne.” Wataƙila a lokacin ne Yesu ya soma lura da mugun halin Yahuda Iskariyoti.—Yoh. 6:66-71.

Darussa Dominmu:

2:4. Yesu ya gaya wa Maryamu cewa a matsayinsa na shafaffe Ɗan Allah da ya yi baftisma, dole ne ya bi umurnin Ubansa na samaniya. Ko da yake Yesu ya soma hidimarsa ne, yana sane da lokacin da aikinsa har da mutuwarsa na hadaya. Ba zai yarda kowa daga cikin iyalinsa har Maryamu ta tsoma baki a aikinsa na yin nufin Allah ba. Mu bauta wa Jehobah Allah da irin wannan ƙuduri.

3:1-9. Misalin Nikodimu shugaban Yahudawa ya koya darussa guda biyu. Na farko, Nikodimu ya nuna tawali’u, da basira, kuma ya nuna cewa yana bukatar ruhaniya, ya fahimci cewa wannan ɗan masassaƙi malami ne daga wurin Allah. Kiristoci na gaskiya suna bukatar tawali’u a yau. Na biyu, Nikodimu ya ƙi ya zama almajiri sa’ad da Yesu yake duniya. Wataƙila saboda tsoron mutane, da kuma matsayin da yake da shi a Majalisa, ko kuma don son arziki. Za mu koyi darassi mai muhimmanci daga wannan misalin: Kada mu yarda irin waɗannan ra’ayin ya hana mu ‘ɗaukan gungumenmu na azaba mu bi Yesu.’—Luk 9:23.

4:23, 24. Don Allah ya amince da bautarmu, dole ne mu yi biyayya da gaskiya da ke bayyane a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma ja-gorar ruhu mai tsarki.

6:27. Don mu yi aikin neman “abinci wanda ya dawama zuwa rai na har abada” dole ne mu yi ƙoƙari mu ci abinci na ruhaniya. Za mu yi farin ciki idan muka yi hakan.—Yoh. 6:27.

6:44. Jehobah yana kula da mu. Yakan kai mu wurin Ɗansa ta wurin aikin wa’azi da kuma taimakonmu mu fahimci kuma mu yi amfani da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da taimakon ruhunsa mai tsarki.

11:33-36. Nuna juyayi ba kumamanci ba ne.

‘KA CI GABA DA BIN SA’

(Yoh. 11:55–21:25)

Yesu ya koma Bait’anya a lokacin da Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z. ya kusa. A ranar 9 ga Nisan, ya je Urushalima a bisa jaki. A ranar 10 ga Nisan kuma, Yesu ya je haikali. Domin sunan Ubansa ya ɗaukaka, wani murya daga sama ya ce: “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”—Yoh. 12:28.

Sa’ad da suke cin jibin bikin Ƙetarewa, Yesu ya yi wa mabiyansa umurnin mai muhimmanci domin ya kusa barin su. Bayan da aka kama shi, aka tsananta shi, kuma aka rataye shi, Yesu ya tashi.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

14:2—Yaya ne Yesu zai “shirya” wa amintattun bayinsa wuri a sana? Wannan zai bukaci Yesu ya yi biyayya ga sabon alkawari ta wurin kasancewa a gaban Allah kuma ya miƙa Masa amfanin jininsa. Shirin kuma zai kunshi Yesu ya karɓi iko, bayan haka tashin matattu na shafaffun bayinsa zai soma.—1 Tas. 4:14-17; Ibran. 9:12, 24-28; 1 Bit. 1:19; R. Yoh. 11:15.

19:11—Yesu yana nufin Yahuda Iskariyoti ne sa’ad da yake magana da Bilatus game da mutumin da ya bashe shi ne? Maimakon Yahuda ko kuma wani mutum, Yesu yana nufin dukan waɗanda suka sa hannu a kashe shi. Wannan ya haɗa da “Manyan malamai kuwa da dukan fadanci,” da kuma “taron” mutane da aka rinjaye su su ce a saki Barabbas.—Mat. 26:59-65; 27:1, 2, 20-22.

20:17—Me ya sa Yesu ya ce wa Maryamu Magadaliya kada ta rungume shi? Wataƙila dalilin da ya sa Maryamu ta rungumi Yesu shi ne tana ganin kamar zai koma sama ne kuma ba za ta sake ganin sa ba. Don ya tabbatar mata da cewa bai yi shirin komawa ba, Yesu ya ce mata ta daina rungumar sa ta je ta gayawa almajiransa cewa ya tashi.

Darussa Dominmu:

12:36. Domin mu zama “yayan haske,” ko kuma mai ɗauke da haske, muna bukatar cikakken sani daga Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Sannan dole ne mu yi amfani da sanin mu kawo ciro mutane daga ruhaniya mai duhu zuwa hasken Allah.

14:6. Babu yadda za mu sami tagomashin Allah sai ta wurin Yesu Kristi. Idan muka gaskata da Yesu kuma muka bi misalinsa ne kawai za mu kusaci Jehobah.—1 Bit. 2:21.

14:15, 21, 23, 24; 15:10. Yin biyayya ga nufin Allah ne zai taimakemu mu ci gaba da kasancewa a ƙaunar Allah da kuma Ɗansa.—1 Yoh. 5:3.

14:26; 16:13. Ruhun Jehobah yana koyarwa kuma yana tuna mana abubuwan da muka koya. Yana kuma aiki don ya bayyana gaskiya. Hakan zai taimaka mana mu ƙara ilimi, hikima, basira, shari’a da kuma hankali. Ya kamata mu nace da yin addu’a, musamman don roƙon wannan ruhu.—Luk 11:5-13.

21:15, 19. Yesu ya tambayi Bitrus yana ƙaunarsa fiye da “waɗannan,” wato, kifayen da suke gabansu. Yesu ya aririce Bitrus ya bi shi na cikakken lokaci maimakon aikin kamun kifi. Bayan da muka yi la’akari da labarin Lingila, mu kuɗiri aniya mu ƙaunaci Yesu fiye da duk abubuwan da za su rinjaye mu. Hakika, bari mu ci gaba da binsa da zuciya ɗaya.

[Hoto a shafi na 31]

Menene za mu iya koya daga misalin Nikodimu?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba