Maya Haihuwa—Ta Yaya Take Faruwa?
YESU yana gaya wa Nikodimu muhimmancin maya haihuwa, wanda yake yinta, manufarta da kuma yadda maya haihuwar take faruwa. Yesu ya ce: “In ba an haifi mutum ta ruwa da ta Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:5) Saboda haka, ana sake haifar mutum ne wajen ruwa da kuma ruhu mai tsarki. To ga menene wannan furci “ruwa da ruhu” yake nufi?
“Ruwa da Ruhu” Menene Ake Nufi da Su?
Da yake shi shugaban addini ne ya Yahudawa, Nikodimu babu shakka ya san hanyoyin da Nassosin Ibraniyawa suka yi amfani da furcin nan “ruhun Allah,” Ikon Allah da zai iya rinjayar mutane su yi ayyuka na musamman. (Farawa 41:38; Fitowa 31:3; 1 Samuila 10:6) Saboda haka, da Yesu ya yi amfani da kalmar nan “ruhu,” Nikodimu ya fahimci cewa yana nufin ruhu mai tsarki, ikon Allah.
To yaya kuma ruwa da Yesu ya ambata? Ka yi la’akari da abin da aka rubuta kafin da kuma bayan tattaunawar da Nikodimu. Wannan ya nuna cewa Yohanna mai Baftisma da kuma almajiran Yesu suna yin baftisma cikin ruwa. (Yohanna 1:19, 31; 3:22; 4:1-3) Wannan ya kasance sanannen abu a Urushalima. Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi maganar ruwa, Nikodimu zai fahimci abin da Yesu yake magana a kai, ba ga kowane irin ruwa ba amma ruwa na baftisma.a
Baftisma da “Ruhu Mai Tsarki”
Idan ‘haifar mutum ta ruwa’ yana da nasaba da baftisma cikin ruwa, menene yake nufi a ‘haifi mutum ta ruhu’? Kafin Nikodimu ya tattauna da Yesu, Yohanna mai Baftisma ya sanar da cewa ba ruwa kawai har ruhu ma zai shafi baftisma. Ya ce: “Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi [Yesu] da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.” (Markus 1:7, 8) Marubucin Linjila Markus ya kwatanta yadda irin wannan baftismar ta faru da farko. Ya rubuta: “Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun. Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu na sauko masa kamar kurciya.” (Markus 1:9, 10) Sa’ad da aka nisar da Yesu cikin Urdun, an yi masa baftisma da ruwa. A wannan lokaci kuma ya sami ruhu daga sama, an yi masa baftisma da ruhu mai tsarki.
Bayan kamar shekara uku da yin baftismarsa, Yesu ya tabbatar wa almajiransa: “Kafin ‘yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.” (Ayukan Manzanni 1:5) Yaushe hakan ya faru?
A ranar Fentikos ta shekara ta 33 A.Z., sa’ad almajiran Yesu wajen 120 suka taru a wani gida a Urushalima. “Ba labari, sai wani motsi kamar na hucin iska mai-ƙarfi ya fito sama, duk ya gama gida wurin da su ke zaune. Harsuna kuma mararraba da juna, kamar na wuta, suka bayyanu garesu; . . . Aka cika dukansu da Ruhu Mai-tsarki.” (Ayukan Manzanni 2:1-4) A wannan rana aka ba wasu a Urushalima umurni su yi baftisma cikin ruwa. Manzo Bitrus ya gaya wa taron jama’a: “Ku tuba, a yi ma kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma.” Yaya suka amsa? “Waɗannan fa da suka karɓi maganatasa, aka yi musu baftisma: a cikin wannan rana fa aka ƙara musu masu-rai wajen talata.”—Ayukan Manzanni 2:38, 41.
Abubuwa Biyu
Menene waɗannan baftisma suka nuna game da maya haihuwa? Sun nuna cewa maya haihuwa tana faruwa ne ta wajen abubuwa biyu. Ka lura cewa Yesu da farko ya yi baftisma cikin ruwa. Sai kuma ya sami ruhu mai tsarki. Hakazalika, almajirai na fari da farko sun yi baftisma cikin ruwa (wasu a hannun Yohanna mai Baftisma), sai kuma suka sami ruhu mai tsarki. (Yohanna 1:26-36) Haka nan kuma, mutane 3,000 da suka tuba da farko an yi musu baftisma da ruwa, sai suka sami ruhu mai tsarki.
Tunawa da baftisma da aka yi a Fentikos na shekara ta 33 K.Z., ta yaya za mu zaci wannan maya haihuwa za ta faru a yau? Kamar yadda ta fara da Yesu da manzanninsa da kuma almajirai na farko. Da farko mutum zai tuɓa daga zunubansa, ya guji muguwar hanya, ya keɓe ransa ga Jehobah domin bauta masa, kuma ya nuna a fili cewa ya keɓe kansa ta wajen baftisma cikin ruwa. Sa’annan, idan Allah ya zaɓe shi ya zama sarki a Mulkinsa, sai a naɗa shi da ruhu mai tsarki. Ɓangare na farko na abubuwan nan biyu (baftisma cikin ruwa) mutum ne zai nemi a yi masa; ɓangare na biyun (baftisma da ruhu) Allah ne yake wannan. Sa’ad da mutum ya yi waɗannan baftisma biyu, to lalle an sake haifansa.
To, me ya sa Yesu a tattaunawarsa da Nikodimu ya yi amfani da furcin nan ‘haifar mutum ta ruwa da ta ruhu’? Ka tuna cewa waɗanda suka yi baftisma da ruwa da kuma ruhu za su yi canji ƙwari da gaske. Talifi na gaba zai mai da hankali bisa wannan ɓangare na maya haihuwa.
[Hasiya]
a Hakan kuma manzo Bitrus ya ce a lokacin wani baftisma: “Akwai mai iya hana ruwan?”—Ayukan Manzanni 10:47.
[Hotunan da ke shafi na 9]
Yohanna ya yi wa Isra’ilawa da suka yi tuba baftisma ta ruwa