‘Ku Zauna Lafiya Da Dukan Mutane’
‘Idan ya yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.’—ROM. 12:18.
1, 2. (a) Wane gargaɗi ne Yesu ya ba mabiyansa? (b) A ina ne za mu samu shawarar yadda za mu bi da hamayya?
YESU ya gargaɗi mabiyansa cewa za su fuskanci hamayya daga al’ummai na duniya, kuma a darensa na ƙarshe kafin mutuwarsa, ya bayyana abin da ya sa. Ya gaya wa manzanninsa: ‘Da na duniya ne ku, da duniya ta yi ƙaunar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana ƙinku.’—Yoh. 15:19.
2 Manzo Bulus ya shaida gaskiyar kalmomin Yesu. A cikin wasiƙarsa ta biyu ga abokinsa matashi Timotawus, Bulus ya rubuta: “Ka bi koyarwata, da tasarrufina, da nufina, da bangaskiyata, da tsawon jimrewata, da ƙaunata, da hanƙurina, da shan tsanani nawa, da wahalaina.” Sai Bulus ya daɗa: “Dukan waɗanda suke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Tim. 3:10-12) A cikin sura ta 12 ta wasiƙarsa ga Kiristocin da ke Roma, Bulus ya ba da shawara mai kyau a kan yadda za su aikata ga hamayya. Kalmominsa za su iya yi mana ja-gora a waɗannan kwanaki na ƙarshe.
“Ku Yi Tattalin Al’amura” Masu Kyau
3, 4. Ta yaya za a yi amfani da gargaɗin da aka ba da a Romawa 12:17 (a) a gidan da ba kowa ba ne ke bauta wa Jehobah? (b) a sha’aninmu da maƙwabta?
3 Karanta Romawa 12:17. Bulus ya bayyana cewa sa’ad da muke fuskantar ƙiyayya, kada mu rama. Yin biyayya ga gargaɗinsa yana da muhimmanci musamman a gidajen da ba kowa ke bauta wa Jehobah ba. Mai bi zai tsayayya wa gwajin ramawa da baƙar magana ko kuma aikata rashin alheri. Ba shi da amfani mu rama ‘mugunta da mugunta.’ Akasin haka, irin wannan halin zai sa yanayin ya daɗa muni.
4 Bulus ya faɗi abin da ya fi kyau: “Ku yi tattalin al’amura na girma a gaban dukan mutane.” A gida, matar da take yi wa mijinta kirki bayan ya yi baƙar magana game da imaninta za ta hana jayayya tasowa. (Mis. 31:12) Carlos, wanda yanzu yake hidima a Bethel, ya faɗi yadda mamarsa ta sha kan hamayya mai tsanani da babansa yake nunawa ta wajen yi masa kirki da kuma kula da gidan yadda ya kamata. “Ta ƙarfafa mu yara mu riƙa daraja shi a kowane lokaci. Ta nace na riƙa yin wani irin wasa da shi ko da yake ba wasan da nake son yi ba ne. Amma hakan yana sa shi farin ciki.” Daga baya ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya yi baftisma. A batun yin “tattalin al’amura” masu kyau a gaban dukan mutane, sau da yawa Shaidun Jehobah sun sha kan wariya ta wajen taimaka wa maƙwabtansu sa’ad da bala’i ya auku.
Kawar da Hamayya da “Garwashin Wuta”
5, 6. (a) A wane azanci ne ake “garwashin wuta” a kan maƙiyi? (b) Ka ba da labarin da ya nuna yadda bin gargaɗin da ke Romawa 12:20 zai iya kawo sakamako mai kyau.
5 Karanta Romawa 12:20. Sa’ad da ya zaɓi kalaman da ke rubuce a wannan ayar, kamar Bulus ya yi ƙaulin Misalai 25:21, 22 ne: “Idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci: Idan yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha: Gama da yin haka nan za ka tulla masa garwashin wuta a kansa, Ubangiji kuma za ya ba ka lada.” A gargaɗinsa da ke Romawa sura 12, Bulus ba ya nufin cewa wannan garwashi na kwatanci horo ne ko kuma kunyatar da mai hamayya. Maimakon haka, misalin, da kuma makamancin kalaman da Bulus ya rubuta wa Romawa, kamar dai yana nuni ne ga yadda ake narkar da kuza a dā. Masanin Turanci na ƙarni na goma sha tara, Charles Bridges ya ce: “Ana kewaye ƙarfen ta wajen zuba garwashin wuta a kansa da kuma a ƙarƙashinsa. Mutane ƙalilan ne kawai za su ci gaba da taurara zuciyarsu sa’ad da aka yi haƙuri, sadaukarwa, kuma aka nuna ƙauna sosai.”
6 Kamar “garwashin wuta,” ayyukan alheri za su iya faranta zukatan ’yan hamayya kuma wataƙila su daina nuna ƙiyayya ga bayin Allah. Ayyukan alheri za su iya sa mutane su karɓi mutanen Jehobah da kuma saƙon Littafi Mai Tsarki da suke wa’azinsa da hannu biyu-biyu. Manzo Bitrus ya rubuta: “Kuna al’amura na dacewa wurin al’ummai; domin, yayinda suke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.”—1 Bit. 2:12.
‘Ku Zauna Lafiya da Dukan Mutane’
7. Wace salama ce Kristi ya bar wa almajiransa, kuma me ya kamata ta motsa mu mu yi?
7 Karanta Romawa 12:18. A dare na ƙarshe da Yesu ya yi da manzanninsa, ya gaya musu: “Salama ina bar muku; salamata na ke ba ku.” (Yoh. 14:27) Salama da Kristi ya bar wa almajiransa ita ce kwanciyar rai da suke da ita domin Jehobah Allah da Ɗansa ƙaunatacce suna ƙaunarsu kuma sun amince da su. Ya kamata wannan kwanciyar rai ya motsa mu mu zauna lafiya da mutane. Kiristoci na gaskiya suna son zaman lafiya kuma suna iya ƙoƙarinsu su zauna lafiya da mutane.—Mat. 5:9.
8. Yaya za mu zama masu son zaman lafiya a gida da kuma cikin ikilisiyarmu?
8 Hanya ɗaya da za mu kasance masu son zaman lafiya a cikin iyali ita ce magance matsaloli nan da nan maimakon mu bar yanayin ya taɓarɓare. (Mis. 15:18; Afis. 4:26) Hakan ya shafi ikilisiyar Kirista. Manzo Bitrus ya haɗa biɗar salama da kame harshe. (1 Bit. 3:10, 11) Bayan da Yaƙub ya ba da gargaɗi sosai a kan yin amfani da harshe yadda ya dace da kuma guje wa kishi da masifa, ya rubuta: “Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, marar-kokanto, marar-riya ce. Kuma ana shuka ɗiyan adalcin cikin salama domin masu-yin salama.”—Yaƙ. 3:17, 18.
9. Yayin da muke ƙoƙarin mu zauna “lafiya da dukan mutane,” menene ya kamata mu tuna?
9 A cikin furcinsa da ke Romawa 12:18, abin da Bulus ya ce ya wuce son zaman lafiya a cikin iyali da ikilisiya. Ya ce mu zauna ‘lafiya da dukan mutane.’ Hakan ya haɗa da maƙwabta, abokan aiki, abokan makaranta, da kuma mutanen da muke saduwa da su a hidimarmu ta fage. Amma, a gargaɗinsa, manzon ya ce: “Idan ya yiwu.” Hakan yana nufin cewa mu yi iya ƙoƙarinmu mu zauna “lafiya da dukan mutane” amma ba tare da ƙetare mizanan Allah masu adalci ba.
Ɗaukar Fansa ta Jehobah Ce
10, 11. Me ya sa bai kamata mu ɗauki fansa da kanmu ba?
10 Karanta Romawa 12:19. Dole ne mu yi “haƙuri” kuma mu aikata da “tawali’u” ga “masu jayayya” da aikinmu da saƙonmu, har da masu hamayya da mu kai tsaye. (2 Tim. 2:23-25) Bulus ya gargaɗi Kiristoci kada su ɗauki fansa amma su “kauce wa fushi.” Hakika, za mu kauce wa fushi, domin Allah ya ɗauki fansa. A matsayin Kiristoci, mun san cewa bai kamata mu ɗauki fansa ba. Mai zabura ya rubuta: “Ka dena yin fushi, ka rabu da hasala: Kada ka dami ranka, wannan ba ya kawo komi ba sai mugunta.” (Zab. 37:8) Sulemanu ya ba da gargaɗi: “Kada ka ce, zan rama mugunta: ka saurari Ubangiji, shi kuwa za ya cece ka.”—Mis. 20:22.
11 Idan ’yan hamayya suka yi mana lahani, abu mafi hikima da ya kamata mu yi shi ne mu bar wa Jehobah ya hukunta su idan ya ga cewa yin hakan ya dace. Don ya nuna cewa yana maganar fushin Jehobah ne, Bulus ya daɗa: “An rubuta, ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” (Gwada Kubawar Shari’a 32:35) Idan muka yi ƙoƙarin ɗaukan fansa da kanmu, muna nuna girman kai ke nan, wato, muna son mu yi abin da Jehobah ya ce hakkinsa ne. Ƙari ga haka, muna nuna rashin bangaskiya ga alkawarin Jehobah: “Ni zan yi sakamako.”
12. A wane lokaci ne Jehobah zai bayyana fushinsa, kuma ta yaya?
12 A farkon wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya ce: “Fushin Allah ya bayyana daga sama bisa dukan rashin ibada da rashin adalci na mutane, masu-danne gaskiya cikin rashin adalci.” (Rom. 1:18) Jehobah zai nuna fushinsa daga sama ta hanyar Ɗansa a lokacin “babban tsananin.” (R. Yoh. 7:14) Hakan zai kasance “ainin shaida . . . ta shari’a mai-adalci ta Allah,” kamar yadda Bulus ya bayyana a ɗaya daga cikin hurarrun wasiƙunsa: “Idan abu mai-adalci ne a gaban Allah a sāka ma waɗanda ke ƙuntata ku da ƙunci; domin ku da aka tsananta ku sami hutu tare da mu, a lokacin bayyanuwar Ubangiji Yesu daga sama tare da mala’ikun ikonsa cikin wuta mai-huruwa, yana ɗaukan ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.”—2 Tas. 1:5-8.
Rinjayar Mugunta da Nagarta
13, 14. (a) Me ya sa ba ma mamaki sa’ad da muka fuskanci hamayya? (b) Ta yaya za mu yi wa waɗanda suke tsananta mana albarka?
13 Karanta Romawa 12:14, 21. Domin muna da cikakken tabbaci cewa Jehobah zai cika manufofinsa, za mu mai da dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a kan aikin da ya ba mu, wato, yin wa’azin “bishara kuwa ta mulki” a cikin “iyakar duniya.” (Mat. 24:14) Mun san cewa wannan aiki na Kirista zai sa maƙiyanmu su yi fushi, domin Yesu ya gaya mana: “Za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Mat. 24:9) Saboda haka, ba ma mamaki ko kuma sanyin gwiwa sa’ad da muka fuskanci hamayya. Manzo Bitrus ya rubuta: “Ƙaunatattu, kada ku ga abin mamaki ne tsanani mai-zafin nan da kuke sha, wanda ke auko muku domin ya auna ku, sai ka ce wani baƙon al’amari ya same ku: amma da ya ke kuna tarayya cikin azabai na Kristi sai ku yi murna.”—1 Bit. 4:12, 13.
14 Maimakon mu nuna ƙiyayya ga masu tsananta mana, za mu ƙoƙarta mu koyar da su, sanin cewa wataƙila wasu a cikinsu suna aikatawa ne cikin jahilci. (2 Kor. 4:4) Muna ƙoƙarin mu bi shawarar Bulus: “Ku albarkaci waɗanda ke tsananta ku; ku albarkace su, kada ku la’anta su.” (Rom. 12:14) Hanya ɗaya na yi wa waɗanda ke hamayya da mu albarka ita ce yin addu’a domin su. Yesu ya ce a Huɗubarsa a kan Dutse: “Ku yi ƙaunar magabtanku, ku yi wa maƙiyanku nagarta, ku albarkaci masu-zaginku; waɗanda su ke wulakanta ku, ku yi masu addu’a.” (Luk 6:27, 28) Daga abin da manzo Bulus ya shaida, ya san cewa ɗan hamayya zai iya zama almajiri mai aminci na Kristi da kuma bawan Jehobah mai himma. (Gal. 1:13-16, 23) A cikin wata wasiƙa, Bulus ya ce: “Ana zaginmu, muna sa albarka; ana tsanantanmu, muna haƙuri; ana yi mana ƙire, muna bada haƙuri.”—1 Kor. 4:12, 13.
15. Wace hanya ce mafi kyau na rinjayar mugunta da nagarta?
15 Shi ya sa, Kirista na gaskiya zai yi biyayya da aya ta ƙarshe na Romawa sura 12: “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” Shaiɗan Iblis ne tushen mugunta. (Yoh. 8:44; 1 Yoh. 5:19) A wahayin da aka ba manzo Yohanna, Yesu ya bayyana cewa ’yan’uwansa shafaffu sun “yi nasara da shi [Shaiɗan] sabili da jinin Ɗan rago, saboda maganar shaidarsu kuma.” (R. Yoh. 12:11) Hakan ya nuna cewa hanya mafi kyau na yin nasara bisa Shaiɗan da kuma mugun tasirinsa bisa wannan zamanin ita ce yin nagarta ta aikinmu na ba da shaida, wato, wa’azin bisharar Mulki.
Yin Murna Domin Bege
16, 17. Menene Romawa sura 12 ta koya mana game da (a) yadda za mu yi amfani da rayuwarmu? (b) yadda za mu aikata a cikin ikilisiya? (c) yadda za mu bi da waɗanda suke hamayya da imaninmu?
16 Ɗan tattauna sura 12 na wasiƙar Bulus ga Kiristocin da ke Roma ya tuna mana abubuwa masu yawa. Mun koyi cewa a matsayin bayin Jehobah da suka keɓe kansu, muna bukatan mu yi sadaukarwa da son rai. Da yake ruhun Allah ne yake motsa mu, muna yin waɗannan sadaukarwar da son rai domin hankalinmu ya tabbatar da mu cewa hakan nufin Allah ne. Muna huruwa a cikin ruhu kuma muna amfani da baiwarmu dabam-dabam da himma. Muna hidima da tawali’u da filako, muna yin iyaka ƙoƙarinmu don mu kasance da haɗin kai a matsayin Kirista. Muna nuna karimci da juyayi.
17 Romawa sura 12 ta kuma ba mu shawara sosai a kan yadda za mu bi da hamayya. Bai kamata mu ɗauki fansa ba. Ya kamata mu ƙoƙarta mu sha kan hamayya da ayyukan alheri. Idan ya yiwu, ba tare da ƙetare mizanan Littafi Mai Tsarki ba, ya kamata mu zauna lafiya da dukan mutane. Hakan ya haɗa da cikin iyali, ikilisiya, da maƙwabta, a wajen aiki, a makaranta, da kuma hidimarmu na fage. Har sa’ad da muka fuskanci ƙiyayya kai tsaye, mu yi iya ƙoƙarinmu mu rinjayi mugunta da nagarta, mu tuna cewa ɗaukan fansa na Jehobah ne.
18. Waɗanne shawarwari guda uku aka ba da a Romawa 12:12?
18 Karanta Romawa 12:12. Ƙari ga waɗannan shawarwari masu kyau, Bulus ya ba da faɗakarwa guda uku. Tun da yake ba za mu iya yin dukan waɗannan abubuwan ba tare da taimakon Jehobah ba, manzon ya shawarce mu mu “lizima cikin addu’a.” Hakan zai taimaka mana mu bi gargaɗinsa mu yi “haƙuri cikin ƙunci.” A ƙarshe, muna bukatan mu ƙafa zuciyarmu a kan abubuwan da Jehobah ya yi mana alkawari a nan gaba kuma mu yi “murna cikin bege” na rai madawwami a sama ko kuma a duniya.
Ta Hanyar Bita
• Yaya za mu bi da hamayya?
• A waɗanne wurare ne ya kamata mu zama masu son zaman lafiya, kuma ta yaya?
• Me ya sa bai kamata mu nemi ɗaukan fansa da kanmu ba?
[Hotunan da ke shafi na 8]
Ba da taimako ga maƙwabtanmu zai taimaka mana mu sha kan wariya
[Hotunan da ke shafi na 9]
Kana ƙoƙari ka zama mai son zaman lafiya a cikin ikilisiya?