Maya Haihuwa—Menene Take Cim ma Wa?
ME YA SA Yesu ya yi wannan furcin ‘haifi mutum ta ruhu’ sa’ad da yake maganar baftisma ta ruhu mai tsarki? (Yohanna 3:5) Sa’ad da aka yi amfani da ita wajen adon magana, kalmar nan “haihuwa” tana nufin “farko,” kama a furcin nan “haifar sabuwar al’umma.” Saboda haka, furcin nan “maya haihuwa” yana nufin “sabon mafari.” Domin haka, adon maganar nan “haihuwa” da kuma “maya haihuwa” sun nanata cewa za a sami wani sabon mafari wajen danganta tsakanin Allah da kuma waɗanda aka yi masu baftisma da ruhu mai tsarki. Ta yaya wannan canji yake faruwa?
Wajen bayana yadda Allah ya shirya mutane domin sarauta a samaniya, manzo Bulus ya ba da misali da rayuwar iyali. Ya rubuta wa Kiristoci na zamaninsa cewa za a mai da su a “matsayin ’ya’yan” kuma saboda haka, Allah zai yi sha’ani da su a matsayin “’ya’yansa.” (Galatiyawa 4:5; Ibraniyawa 12:7) Domin ka fahimci yadda wannan misali na mai da mutum a matsayin ɗan zai taimaka wajen fahimtar irin canji da ya faru sa’ad da mutum ya yi baftisma ta ruhu mai tsarki, ka yi la’akari da misalin nan na yaro wanda yake so ya shiga makaranta da aka keɓe domin ’yan gari.
Canji da Zama Ɗan Yake Kawowa
A misalin, yaron bai sami shiga makarantar ba domin shi ba ɗan garin ba ne. Yanzu, ka yi tunanin wani babban canji ya faru. Wani mutum ɗan garin ya ɗauke shi a matsayin ɗansa. Ta yaya hakan zai shafi yaron? To, da yake an ɗauke shi a matsayin ɗa, shi ma yanzu yana da dama daidai na yara ’yan gari, har da damar ya shiga makarantar. Ɗaukansa a matsayin ɗa ya canja yanayinsa.
Wannan ya kwatanta abin da yake faruwa ga waɗanda aka maya haifarsu. Ka yi la’akari da kamani da ke tsakaninsu. Yaron zai samu shiga makarantar amma idan ya cika dukan bukatun shiga makarantar, wato, idan ya kasance shi ɗan gari ne. Duk da haka, ba zai iya biyan waɗannan bukatu da kansa ba. Hakazalika, wasu ’yan adam za su sami wuri a cikin Mulkin Allah, ko kuma gwamnatin samaniya, amma idan suka cika dukan bukatun shiga, wato na “sake haifarsu. Duk da haka, da kansu ba za su iya cika wannan bukata na sake haifarsu ba domin sake haifar mutum ta dangana ne ga Allah.
Menene ya canja wannan yanayi? Ɗaukan mutum a matsayin ɗa. Hakika, wannan yanayi bai canja yaron ba. Bayan an ɗauke shi a matsayin ɗa, kasance kamar yadda yake a dā. Duk da haka, sa’ad da aka cika wannan abu na doka, yaron ya sami sabon matsayi. Hakika, ya sami sabon mafari, sabon haihuwa. Ya zama ɗa, wanda ya ba shi damar shiga makaranta ’ya’yan gari kuma ya zama ɗa cikin iyalin mutumin da ya ɗauke shi a matsayin ɗansa.
Hakazalika, Jehobah ya canza yanayin wasu rukunin mutane ajizai ta wajen mayar da su ’ya’yansa. Manzo Bulus da ya kasance cikin wannan rukunin, ya rubuta wa ’yan’uwa masu bi: “Kuka karɓi ruhun ɗiyanci, inda muke kira, Abba, Uba. Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ’ya’yan Allah ne.” (Romawa 8:15, 16) Hakika, domin Allah ya mayar da su ’ya’yansa, waɗannan Kiristoci suka zama cikin iyalin Allah, ko kuma “’ya’yan Allah.”—1 Yohanna 3:1; 2 Korinthiyawa 6:18.
Hakika, ɗaukansu ’ya’ya da Allah ya yi bai canja yanayinsu ba, domin har ila su ajizai ne. (1 Yohanna 1:8) Bugu da ƙari, kamar yadda Bulus ya ci gaba da bayani, bayan da aka mai da su ’ya’ya, suka sami sabon matsayi. A wannan lokaci kuma, ruhun Allah ya kafa a cikin waɗannan ’ya’yan tabbacin cewa za su zauna tare da Kristi a samaniya. (1 Yohanna 3:2) Wannan tabbaci ta gaske da ruhu mai tsarki ya kafa a cikinsu ya sa rayuwarsu ta samu bambanci. (2 Korinthiyawa 1:21, 22) Hakika, sun sami sabon fari, maya haihuwa ke nan.
Littafi Mai Tsarki ya ce game da waɗanda Allah ya mai da ’ya’yansa: “Za su zama priests na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.” (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Tare da Kristi, waɗanda Allah ya mai da ’ya’yansa za su sami matsayin sarauta a Mulkin Allah, ko kuma gwamnati ta samaniya. Manzo Bitrus ya gaya wa ’yan’uwa masu bi game da wannan sarautar “gādo mara-ruɓewa, mara-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa” wanda aka “ajiyayye a sama dominku.” (1 Bitrus 1:3, 4) Hakika gado ne mai tamani!
Amma, wannan batun sarauta ya ta da wata tambaya. Idan waɗanda aka sake haifarsu za su yi sarauta a samaniya, bisa waye za su yi sarauta? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.
[Hotunan da ke shafi na 10]
Menene Bulus ya ce game da zama ɗa?