Bari Dukanmu Mu Yi Shelar Ɗaukakar Jehovah
“Ku bayar ga Ubangiji daraja da ƙarfi. Ku bayar ga Ubangiji daraja wadda ta kāmace sunansa.”—ZABURA 96:7, 8.
1, 2. Mecece take yabon Jehovah, kuma su waye aka aririce su ma su yi haka?
DAUDA ɗan Jesse, ya yi girma yana kiwon tumaki kusa da Bai’talahmi. Sau da yawa ƙila yana kallon taurari daddare sa’ad da yake lura da tumakin babansa a waɗannan wuraren kiwo da sun kaɗaita! Babu shakka, ya tuna da waɗannan abubuwa sa’ad da ruhu mai tsarki na Allah ya hure shi ya rubuta kuma rera kalmomi masu daɗi na Zabura ta 19: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa. Ɗamararsu ta fita har iyakar ƙasa, zantattukansu kuma har iyakacin duniya.”—Zabura 19:1, 4.
2 Sammai na ban al’ajabi da Jehovah ya halitta suna shelar ɗaukakarsa kowacce rana da kowane dare ba tare da magana ko kalma, ko wani amon da ake ji ba. Halitta ba ta daina shelar ɗaukakar Allah ba, abin da zai sa mutum sauƙin kai ne, yin tunanin tabbacin nan da ke a bayyane ga ‘dukan duniya’ don dukan mazaunanta su gani. Amma, tabbaci na halitta bai isa ba. An aririce ’yan Adam masu aminci su ma su yi shela. Wani mai zabura da ba a ambata sunansa ba ya gaya wa masu bauta da aminci waɗannan hurarrun kalmomi: “Ku bayar ga Ubangiji daraja da ƙarfi. Ku bayar ga Ubangiji daraja wadda ta kāmace sunansa.” (Zabura 96:7, 8) Waɗanda suke da nasaba ta kusa da Jehovah suna farin ciki su aikata wannan gargaɗi. Mecece ɗaukaka Allah ta ƙunsa?
3. Me ya sa mutane suke ɗaukaka Allah?
3 A ɗaukaka Allah yana bukatar fiye da a faɗa da baki kawai. Isra’ilawa na zamanin Ishaya sun ɗaukaka Allah da leɓunansu, amma yawancinsu ba daga zuciyarsu ba. Ta bakin Ishaya, Jehovah ya ce: “Wannan jama’a suna gusowa gareni, da bakinsu da leɓunansu suna girmama ni, amma sun nisantadda zuciyarsu daga gareni.” (Ishaya 29:13) Duk yabo da irin waɗannan mutane suka furta ba shi da ma’ana. Don ya kasance da ma’ana, yabo zai fito daga zuciya da ke cike da ƙaunar Jehovah da kuma amince da ɗaukakarsa da gaske. Jehovah ne kaɗai Mahalicci. Shi ne Maɗaukaki Duka, Wanda ya fi adalci, tushen ƙauna. Shi ne tushen cetonmu kuma Mamallaki da ya dace, da kowa da yake zama a sama da kuma ƙasa zai yi masa biyayya. (Ru’ya ta Yohanna 4:11; 19:1) Idan mun gaskata waɗannan abubuwa, bari mu ɗaukaka shi da dukan zuciyarmu.
4. Waɗanne umurni Yesu ya ba da game da yadda za mu ɗaukaka Allah, ta yaya za mu yi su?
4 Yesu Kristi ya gaya mana yadda za mu ɗaukaka Allah. Ya ce: “Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina.” (Yohanna 15:8) Ta yaya muke ba da ’ya’ya da yawa? Na farko, ta sa hannu a wa’azin “wannan bishara kuwa ta mulki” da dukan zuciyarmu, ta haka muna ‘faɗin’ “al’amura . . . da ba su ganuwa” na Allah tare da dukan halittu. (Matta 24:14; Romawa 1:20) Bugu da ƙari, a wannan hanya dukanmu za mu sa hannu—kai tsaye ko a kaikaice—a samun sababbin almajirai da suke rera yabo ga Jehovah Allah. Na biyu, za mu nuna halayen da muka samu daga ruhu mai tsarki kuma mu yi ƙoƙari mu yi koyi da halaye mafi girma na Jehovah Allah. (Galatiyawa 5:22, 23; Afisawa 5:1; Kolossiyawa 3:10) Ta haka, halinmu kowacce rana zai riƙa ɗaukaka Allah.
“Cikin Dukan Ƙasa”
5. Ka bayyana yadda Bulus ya nanata hakki da Kiristoci suke da shi su ɗaukaka Allah ta gaya wa wasu game da bangaskiyarsu.
5 Bulus a wasiƙarsa zuwa ga Romawa ya nanata hakkin da Kiristoci suke da shi su ɗaukaka Allah ta wajen gaya wa wasu game da bangaskiyarsu. Saƙo na musamman na littafin Romawa shi ne cewa za a ceci waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu Kristi ne kaɗai. A sura ta 10 ta wasiƙarsa, Bulus ya nuna cewa Yahudawa na kwanansa har ila suna ƙoƙari su kasance da adalci ta bin Dokar Musa, ko da “Kristi matuƙar shari’a ne.” Shi ya sa, Bulus ya ce: “Gama idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma bada gaskiya cikin zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira.” Daga lokacin zuwa gaba, “ba maraba tsakanin Bayahudi da Baheleni: gama shi wannan ɗaya shi ne Ubangiji duka, yana kuwa da wadata zuwa ga dukan waɗanda ke kira bisa gareshi: gama, Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.”—Romawa 10:4, 9-13.
6. Ta yaya Bulus ya yi amfani da Zabura 19:4?
6 Sai Bulus ya yi tambaya: “Ƙaƙa fa za su kira bisa ga wanda ba su bada gaskiya gareshi ba? kuma ƙaƙa za su bada gaskiya ga wanda ba su ji ba? ƙaƙa za su ji kuwa in ba mai-yin wa’azi ba?” (Romawa 10:14) Bulus ya ce game da Isra’ila: “Ba dukansu suka lura da bishara ba.” Me ya sa Isra’ila ba ta yi biyayya ba? Rashin biyayyarsu domin rashin bangaskiya ne, ba domin ba su da zarafi ba. Bulus ya nuna wannan ta yin ƙaulin Zabura 19:4 kuma ya yi amfani da shi ga aikin wa’azi na Kirista maimakon shaida ta halitta. Ya ce: “I, hakika, muryarsu ta fita cikin dukan ƙasa, kalmominsu kuma har iyakan duniya.” (Romawa 10:16, 18) Hakika, har ma yadda halitta marasa rai take ɗaukaka Jehovah, Kiristoci na ƙarni na farko sun yi wa’azin bishara na ceto ko’ina, da haka sun yabi Allah a “dukan ƙasa.” A wasiƙarsa zuwa Kolossiyawa, Bulus ya kwatanta yadda bishara ta yaɗa a ko’ina. Ya ce an yi wa’azin bishara “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kolossiyawa 1:23.
Shaidu Masu Himma
7. In ji Yesu, wane hakki Kiristoci suke da shi?
7 Mai yiwuwa, Bulus ya rubuta wasiƙarsa zuwa ga Kolossiyawa misalin shekara 27 bayan mutuwar Yesu Kristi. Ta yaya aikin wa’azi a ɗan lokaci ya yaɗa har zuwa Kolossi haka? Ya kasance hakan domin Kiristoci na ƙarni na farko suna da himma, kuma Jehovah ya albarkaci himmarsu. Yesu ya annabta cewa mabiyansa za su zama masu wa’azi da ƙwazo sa’ad da ya ce: “Dole kuma sai an yi wa’azin bishara ga al’ummai duka tukuna.” (Markus 13:10) Yesu ya daɗa umurnin da aka rubuta cikin ayoyi na ƙarshe na Lingilar Matta ga wannan annabci: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Ba da daɗewa ba bayan Yesu ya hau sama, mabiyansa suka soma cika wannan umurni.
8, 9. Bisa ga Ayukan Manzanni, yaya Kiristoci suka aikata ga umurnin Yesu?
8 Bayan an zubo da ruhu mai tsarki a Fentakos ta 33 A.Z., wa’azi ne abu na farko da mabiyan Yesu masu aminci suka yi, suna gaya wa jama’a a Urushalima game da “ayyuka masu-girma na Allah.” Wa’azinsu ya fi ba da ’ya’ya, kuma aka yi wa “masu-rai wajen talata” baftisma. Almajiran suka ci gaba da yabon Allah a fili da himma, wannan ya ba da ’ya’ya masu kyau.—Ayukan Manzanni 2:4, 11, 41, 46, 47.
9 Ba da daɗewa ba shugabannin addini suka san game da ayyukan waɗancan Kiristoci. Da yake sun damu game da gaba gaɗin Bitrus da Yohanna, suka umurci manzanni biyun su daina wa’azi. Manzannin suka ce: “Ba shi yiwuwa a garemu mu rasa faɗin abin da muka ji muka gani.” Bayan da aka yi musu kashedi aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen ’yan’uwansu, kuma dukansu suka yi wa Jehovah addu’a. Da gaba gaɗi suka roƙi Jehovah: “Ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfinzuciya duka.”—Ayukan Manzanni 4:13, 20, 29.
10. Wace hamayya suka soma fuskanta, kuma menene Kiristoci na gaskiya suka yi?
10 Wannan addu’a ta yi daidai da nufin Jehovah, yadda ya kasance a bayyane ba da daɗewa ba bayan haka. Aka kama manzannin kuma mala’ika ya sake su ta hanyar mu’ujiza. Mala’ikan ya gaya musu: “Ku tafi, ku tsaya cikin haikali, ku faɗa ma jama’a dukan maganar wannan Rai.” (Ayukan Manzanni 5:18-20) Domin manzannin sun yi biyayya, Jehovah ya ci gaba da yi musu albarka. Saboda haka, “kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fasa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” (Ayukan Manzanni 5:42) Babu shakka, hamayya mai tsanani ba ta iya sa mabiyan Yesu su daina ɗaukaka Allah a fili ba.
11. Menene halin Kiristoci na farko game da aikin wa’azi?
11 Ba da daɗewa ba aka kama Istifanas kuma aka jejjefe shi har ya mutu. Mutuwarsa ta ta da tsanantawa a Urushalima, kuma aka tilasta wa dukan almajiran su watse ban da manzannin. Tsanantawar ta sa su sanyin gwiwa ne? Ko kaɗan. Mun karanta: “Su fa da suka watse suka yi tafiya ko’ina, suna wa’azin kalmar.” (Ayukan Manzanni 8:1, 4) An ga himmarsu wajen shelar ɗaukakar Allah a kai a kai. A Ayukan Manzanni sura ta 9, mun karanta cewa Shawulu Bafarisi na Tarsus, sa’ad da yake tafiya zuwa Dimashƙu don ya soma tsananta wa almajiran Yesu a wajen, ya ga wahayin Yesu kuma aka sa ya makance. A Dimashƙu, Hananiya ya warƙar da Shawulu makaho ta mu’ujiza. Menene abu na farko da Shawulu—wanda daga baya aka san shi da manzo Bulus ya yi? Labarin ya ce: ‘Nan da nan kuwa ya yi ta wa’azin Yesu cikin majami’u, shi Ɗan Allah ne.’—Ayukan Manzanni 9:20.
Duka Sun Yi Aikin Wa’azi
12, 13. (a) In ji ’yan tarihi, menene aka lura game da ikilisiyar Kirista ta farko? (b) Ta yaya littafin Ayukan Manzanni da kalmomin Bulus suka yarda da furcin ’yan tarihi?
12 A ko’ina an san cewa duka a cikin ikilisiyar Kirista ta farko sun yi aikin wa’azi. Game da Kiristoci na waɗancan zamani, Philip Schaff ya rubuta: “Kowacce ikilisiya tana da nufin hidima, kuma kowane Kirista mai bi mai wa’azi ne.” History of the Christian Church (Tarihin Cocin Kirista) W. S. Williams ya ce: “Galibin tabbacin shi ne cewa dukan Kiristoci na Coci na farko, musamman waɗanda suke da kyautar ruhu, sun yi wa’azin bisharar.” Daga littafin nan The Glorious Ministry of the Laity, (Hidimar Limamai na Ɗaukaka) Ya kuma ce: “Yesu Kristi ba ya nufin wa’azi ya zama gatar wasu kalilan kawai ba.” Har ma Celsus, abokin gaban Kiristanci na dā ya rubuta, “Maɗinkan ulu, masu yin takalma, majema, jahilai da talakawa, masu wa’azin lingila ne da himma.”
13 An san cewa waɗannan furci gaskiya ne a rubutaccen tarihi na Ayukan Manzanni. A Fentakos ta shekara na 33 A.Z., bayan an zubo da ruhu mai tsarki, dukan almajiran, maza da mata, a fili suka sanar da ayyuka masu girma na Allah. Bayan tsanantawa da aka kashe Istifanas, dukan Kiristoci da suka watse suka yaɗa bishara sosai. Misalin shekara 28 bayan haka, Bulus ya rubuta wa dukan Kiristoci na Ibraniyawa, ba kawai ga ƙaramin aji na limamai ba, sa’ad da ya ce: “Ta wurinsa fa bari mu miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.” (Ibraniyawa 13:15) Da yake kwatanta nasa ra’ayin game da aikin wa’azi, Bulus ya ce: “Idan ina wa’azin bishara, ba ni da abin fahariya; gama ya zama mini dole; kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.” (1 Korinthiyawa 9:16) A bayyane yake cewa duka Kiristoci masu aminci a ƙarni na farko sun yarda da haka.
14. Wace nasaba ta kasance tsakanin bangaskiya da wa’azi?
14 Hakika, Kirista na gaske ya kamata ya yi aikin wa’azi domin yana da nasaba sosai da bangaskiya. Bulus ya ce: “Da zuciya mutum ya ke bada gaskiya zuwa adalci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto.” (Romawa 10:10) Rukuni kalilan ne kawai cikin ikilisiya—kamar ajin limami—za su ba da gaskiya kuma ta haka su kasance da hakkin wa’azi? A’a! Dukan Kiristoci suna gina bangaskiya sosai cikin Ubangiji Yesu Kristi kuma su motsa su gaya wa wasu wannan imani. Idan ba haka ba, bangaskiyarsu matacciya ce. (James 2:26) Domin dukan Kiristoci masu aminci a ƙarni na farko na Zamaninmu sun nuna bangaskiyarsu ta haka, an yabi sunan Jehovah sosai.
15, 16. Ka ba da misalai da suka nuna cewa an ci gaba da aikin wa’azi duk da matsala.
15 A ƙarni na farko, Jehovah ya albarkaci mutanensa da ƙari duk da matsaloli da ke ciki da kuma waje da ikilisiya. Alal misali, Ayukan Manzanni sura ta 6 ta ruwaita jayayya tsakanin Ibraniyawa da Helenawa da suka tuba. Manzannin ne suka magance matsalar. Saboda haka, muka karanta: “Maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai; babban taro kuma na malamai suka yi biyayya ga imanin.”—Ayukan Manzanni 6:7.
16 Bayan haka, jayayya ta siyasa ta taso tsakanin Sarki Hirudus Agaribas na Yahudiya, da mutanen Taya da Sida. Mazaunan waɗannan birane suka shafa masa mai a leɓa a roƙon salama, domin wannan Hirudus ya yi wa jama’ar magana. Taron suka soma kururuwa: “Muryar wani allah ke nan, ba ta mutum ba ce.” Nan da nan, mala’ikan Jehovah ya bugi Hirudus Agaribas, kuma ya mutu “domin ba ya bada girma ga Allah ba.” (Ayukan Manzanni 12:20-23) Abin baƙin ciki ne ga waɗanda suka sa begensu ga sarakuna ’yan Adam! (Zabura 146:3, 4) Amma, Kiristocin suka ci gaba da ɗaukaka Jehovah. Saboda haka, “maganar Allah tana daɗuwa, tana riɓanɓanya” duk da irin wannan zirga-zirga ta siyasa.—Ayukan Manzanni 12:24.
Yanayi na Lokacin da Kuma na Yanzu
17. A ƙarni na farko, menene mutane da yawa suka yi?
17 Hakika, masu yabon Jehovah Allah, masu himma da ƙwazo sune ke cikin ikilisiyar Kirista na dukan duniya a ƙarni na farko. Dukan Kiristoci masu aminci sun yaɗa bisharar. Wasu sun sadu da waɗanda suka saurara, kuma yadda Yesu ya faɗa, suka koya musu su yi biyayya da dukan abubuwa da ya umurta. (Matta 28:19, 20) Sakamakon shi ne ikilisiyar ta ƙaru, kuma ƙarin mutane suka bi Sarki Dauda na dā a yabon Jehovah. Duka sun maimaita hurarrun kalmomin nan: “Ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata zan yabe ka; in darajanta sunanka kuma har abada. Gama jinƙanka mai-girma ne wajena.”—Zabura 86:12, 13.
18. (a) Menene bambanci da yake tsakanin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko da Kiristendam a yau? (b) Menene za a bincika a talifi na gaba?
18 Game da wannan, kalmomin farfesar tauhidi Allison A. Trites masu sa tunani ne. Da take gwada Kiristendam na zamani da Kiristanci na ƙarni na farko, ya ce: “Coci na yau tana samun ƙaruwa ta wurin haihuwa (sa’ad da yara da suke cikin iyali na cocin suka ba da gaskiya) ko kuma ta wurin canji (daga wani coci zuwa wani). Amma, a Ayukan Manzanni ana zancen ƙaruwa ta wurin samun sababbi zuwa ikilisiyar, domin bai daɗe ba da aka soma ikilisiyar.” Wannan yana nufin cewa Kiristanci na gaskiya ba ta ƙaruwa a hanyar da Yesu ya ce zai yi? A’a. Kiristoci na gaskiya a yau suna da himma a yabon Allah a fili kamar Kiristoci na ƙarni na farko. Za mu ga wannan a talifi na gaba.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• A waɗanne hanyoyi ne muke ɗaukaka Allah?
• Ta yaya Bulus ya yi amfani da Zabura 19:4?
• Wace nasaba take tsakanin bangaskiya da wa’azi?
• Menene ya kamata a lura da shi game da ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko?
[Hoto a shafi nas 18, 19]
Sammai sau da yawa suna shaida ɗaukakar Jehovah
[Inda aka Dauko]
Anglo-Australian Observatory ne suka bayar, hoton da David Malin ya ɗauka
[Hotuna a shafi na 20]
Aikin wa’azi da addu’a suna da nasaba ta kusa