Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Maya Haihuwa—Yaya Muhimmancinsa?
    Hasumiyar Tsaro—2009 | 1 Afrilu
    • A ƙarshe, don ya kawar da shakka game da batun, Yesu ya ce: “Dole a sāke haifarku.” (Yohanna 3:7) A bayyane yake, in ji Yesu, sake haifar mutum wajibi ne, tilas ne, domin mutum ya “shiga Mulkin Allah.”—Yohanna 3:5.

  • Maya Haihuwa—Shawara Ce da Mutum Zai Yanke da Kansa?
    Hasumiyar Tsaro—2009 | 1 Afrilu
    • Maya Haihuwa—Shawara Ce da Mutum Zai Yanke da Kansa?

      WAYE yake sa a maya haihuwa? Sa’ad da suke ƙarfafa masu sauraronsu su zama Kiristoci da aka sake haifansu, wasu masu wa’azi suna yin ƙaulin kalmomin da Yesu ya furta: “Dole a sake haifarku.” (Yohanna 3:7) Irin waɗannan masu wa’azi suna yin amfani da waɗannan kalamai ne suna ba da doka, cewa, “Je ka a sake haifarka!” Saboda haka, suna wa’azi ne cewa ya dangana ne a kan kowane mutum mai bi ya yi wa Yesu biyayya kuma ya ɗauki matakai domin ya samu a maya haifarsa. Bisa ga irin wannan ra’ayi, sake haihuwa abu ne da mutum yana iya zaɓa wa kansa ko kuma ya ƙi. Amma wannan ra’ayi ya jitu da abin da Yesu ya gaya wa Nikodimu ne?

      Karanta kalmomin Yesu cikin natsuwa ya nuna cewa Yesu bai koyar da cewa mutum ne zai zaɓi ko yana son a maya haifarsa ko kuma a’a ba. Me ya sa muka faɗi haka? Kalmar Hellenanci da aka fassara “sake haihuwa” za a iya kuma fassara ta “sake haifansa daga sama.”a Saboda haka, bisa ga wannan fassarar, maya haihuwa tana faruwa ne “daga samaniya” ko kuma “daga wurin Uba.” (Yohanna 19:11; Yaƙub 1:17) Hakika, Allah ne yake sa ta faru.—1 Yohanna 3:9.

      Idan mun tuna cewa ainihin wannan furcin yana nufin “daga sama,” ba zai yi wuya mu fahimci abin da ya sa mutum ba zai iya saka a sake haifarsa ba. Ka yi tunanin yadda aka haife ka a zahiri. Kai ka zaɓi a haife ka? A’a! An haife ka ne domin babanka ne ya yi sanadin haihuwarka. Hakazalika, za a sake haifanmu ne idan Allah, Ubanmu na samaniya, ya sa aka sake haifanmu. (Yohanna 1:13) Saboda haka, manzo Bitrus ya ce yadda ya dace: “Godiya ta tabbata gare shi, shi wanda ke Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifarmu”—1 Bit. 1:3; LMT.

      Doka Ce?

      Amma wasu za su yi mamaki, ‘idan gaskiya ne cewa babu wanda zai zaɓi a sake haifansa, me ya sa Yesu ya ba da umurnin nan: “Dole a sake haifarku.”?’ Wannan tambaya ce mai kyau. Ban da haka ma, idan kalmomin Yesu hakika umurni ne, to ya umurce mu ne mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ke nan. Hakan kuma ba zai kasance abin da ya dace ba. To, ta yaya ya kamata a fahimci wannan kalaman dole a “sake haifarku”?

      Bincika wannan furci a harshensa na hasali ya nuna cewa ba umurni ba ne, ko doka. Maimakon haka, furcin lafazi ne kawai. Wato sa’ad da Yesu ya ce dole a “sake haifarku,” gaskiya kawai ya faɗa ba umurni ya bayar ba. Ya ce: “Wajibi ne a sake haifarku daga samaniya.”—Yohanna 3:7, Modern Young’s Literal Translation.

      Don a kwatanta bambancin wannan batu na umurni da kuma lafazi, ka yi la’akari da wannan kwatanci. Ka yi tunanin wani birni da yake da makarantu da yawa. Aka keɓe ɗaya daga cikinsu ta zama makaranta domin yaran garin ko kuma ’yan asalin garin da suke zuwa makaranta daga wurare da ke da nesa da birnin. Wata rana, wani saurayi da baya wannan makarantar ya gaya wa shugaban makarantar, “Ina so in shiga makarantarka.” Shugaban ya gaya masa, “Dominka shiga wannan makarantar, dole ne sai ka kasance ɗan asalin garin nan.” Hakika, kalamin shugaban makarantar ba umurni ba ne. Ba ya umurci ɗalibin ba ne, “Ya zama ɗan asalin gari!” Shugaban makarantar yana faɗin gaskiya ne kawai, abin da ake bukata domin a shiga makarantar. Hakazalika, sa’ad da Yesu ya ce “dole a sake haifarku,” yana faɗi ne kawai abin da ake bukata domin “shiga Mulkin Allah.”

Littattafan Hausa (1987-2025)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba