-
Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dallaMulkin Allah Yana Sarauta!
-
-
3, 4. (a) Ta yaya Yesu ya ci gaba da koyar da mutane masu aminci game da Mulkin Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan babin?
3 Yesu ya yi wannan furucin da aka rubuta a Yohanna 16:12 a dare na ƙarshe kafin ya mutu. Bayan mutuwarsa, ta yaya zai ci gaba da koyar da mutanensa masu aminci game da Mulkin Allah? Ya gaya wa manzanninsa cewa: “Ruhu na gaskiya . . . zai bishe ku cikin dukan gaskiya.”a (Yoh. 16:13) Ruhu mai tsarki yana kama ne da mai ja-gora mai haƙuri. Yesu yana amfani da ruhu mai tsarki ne wajen koya wa mabiyansa dukan abubuwan da ya kamata su sani game da Mulkin Allah, kuma yana yin hakan a lokacin da ya dace.
-
-
Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dallaMulkin Allah Yana Sarauta!
-
-
a Wani binciken da aka yi ya nuna cewa kalmar nan “bishe” a Helenanci yana nufin “nuna hanya.”
-