Za Ka Iya ‘Bambance Nagarta Da Mugunta’?
“Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—AFISAWA 5:10.
1. A wace hanya ce rayuwa a yau za ta kasance da wuya, kuma me ya sa?
“YA UBANGIJI, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irmiya 10:23) Wannan muhimmiyar gaskiya da Irmiya ya lura tana da ƙarin ma’ana a gare mu a yau. Me ya sa? Domin muna zama cikin “miyagun zamanu,” yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta. (2 Timothawus 3:1) Kowacce rana, muna fuskantar yanayi masu wuya da ke bukatar mu tsai da shawarwari. Manya ko yara, waɗannan shawarwari za su iya tasiri sosai bisa zaman lafiyarmu—a jiki, a tunani, da ruhaniya.
2. Waɗanne zaɓe ne za a iya ɗauka ba su da muhimmanci, duk da haka yaya Kiristoci da suka keɓe kansu suke ɗaukar irin wannan?
2 Zaɓe da yawa da muke yi a rayuwarmu na yau da kullum ana iya ɗaukansu abin da ake yi koyaushe ko kuma da babu muhimmanci. Alal misali, kowacce rana, muna zaɓan tufafi da za mu saka, abinci da za mu ci, mutane da za mu gani, da sauransu. Muna yin waɗannan zaɓe kusan haka kawai, da kyar ma mu kula. Amma da gaske ne irin waɗannan al’amura ba su da muhimmanci? Wajen Kiristoci da suka keɓe kansu, muna damuwa sosai cewa zaɓe da muke yi wajen ado da yadda muke, a abinci da muke ci da abin da muke sha, a furcinmu da hali koyaushe na nuna cewa mu bayi ne na Maɗaukaki Duka, Jehovah Allah. An tunasar mana da kalmomin manzo Bulus: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.”—1 Korinthiyawa 10:31; Kolossiyawa 4:6; 1 Timothawus 2:9, 10.
3. Waɗanne zaɓe ne suke da muhimmanci sosai?
3 Da akwai zaɓe da suka fi muhimmanci. Alal misali, zaɓan yin aure ko babu aure yana iya shafar mutum ƙwarai. Gaskiya, zaɓan wadda ta dace da za ka aura, ta zama abokiya na dukan rayuwa, ba ƙaramin abu ba ne.a (Misalai 18:22) Ƙari ga haka, zaɓan abokai da waɗanda za mu yi tarayya da su a makaranta, wajen aiki, wajen nishaɗi yana da tasiri, har da na tsai da shawara ma a ruhaniyarmu—a madawwamin rayuwarmu.—Romawa 13:13, 14; Afisawa 5:3, 4.
4. (a) Wace iyawa ce za ta fi kyau? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata a bincika?
4 Da yake duka waɗannan na gabanmu, yana da kyau mu iya rarrabe tsakanin abin da ke nagarta da abin da ke mugunta ko kuma tsakanin abin da kamar daidai ne da abin da da gaske daidai ne. Littafi Mai Tsarki ya yi kashedi: “Akwai hanya wadda ta ke sosai bisa a ganin mutum, amma matuƙarta tafarkun mutuwa ne.” (Misalai 14:12) Da haka za mu iya tambaya: Yaya za mu gina iyawa ta rarrabe tsakanin nagarta da mugunta? Ina za mu samu ja-gorar da muke bukata don yin zaɓe? Menene mutane, a dā da kuma a yanzu suka yi game da wannan, menene sakamakon?’
‘Falsafa da Ruɗin Banza’ na Duniya
5. Wace irin duniya ce Kiristoci na farko suka rayu ciki?
5 Kiristoci na ƙarni na farko sun rayu ne a duniya da ƙa’ida da ra’ayoyin Hellas da Roma ke rinjaya. A gefe ɗaya kuma, da akwai holewa ta hanyar rayuwar mutanen Roma, da mutane da yawa suke gani abin da za a yi koyi da shi ne. A wata sassa, rukunin haziƙai na zamanin suna murna ba kawai don ra’ayoyin falsafa ba na Plato da Aristotle amma kuma na sababbin makarantu, irinsu Abikuriyawa da Sitokiyawa. Lokacin da manzo Bulus ya zo Atina a tsarin tafiye-tafiyensa na biyu, ya fuskanci ’yan falsafan Abikuriya da Sitokiya waɗanda suke ji sun fi “wannan mai-surutu,” watau Bulus.—Ayukan Manzanni 17:18.
6. (a) Menene aka jarabci wasu Kiristoci na farko su yi? (b) Wane kashedi Bulus ya bayar?
6 Saboda haka, ba shi da wuya a gane abin da ya sa wasu cikin Kiristoci na farko suka janye zuwa hanyoyi masu girma na yayin rayuwar mutane da suke kewaye da su. (2 Timothawus 4:10) Waɗanda suke cikin tsarin musamman kamar suna moran fa’idodi da yawa, kuma zaɓe da suke yi kamar yana da kyau. Duniya kamar tana da aba mai kyau da za ta bayar wadda hanyar rayuwa ta Kirista da ke a keɓe ba ta da ita. Amma, manzo Bulus ya yi kashedi: ‘Ku yi hankali kada kowa shi same ku ta wurin falsafa da ruɗin banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga ruknai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.’ (Kolossiyawa 2:8) Me ya sa Bulus ya faɗi haka?
7. Menene ainihin amfanin hikima ta duniya?
7 Bulus ya ba da wannan kashedi domin ya ga haɗari yana jiran waɗanda suke sha’awar duniya. Amfani da ya yi da furcin nan ‘falsafa da ruɗin banza’ yana da muhimmanci. Kalmar nan ‘falsafa’ a zahiri na nufin “son hikima da kuma biɗan hikima.” Wannan wataƙila yana da amfani. Hakika, Littafi Mai Tsarki, musamman littafin Misalai, ya ƙarfafa biɗan irin ilimi da hikima da ke daidai. (Misalai 1:1-7; 3:13-18) Amma Bulus ya haɗa ‘falsafa’ da ‘ruɗin banza.’ A wasu kalmomi, Bulus yana ɗaukan hikima da duniyar take bayarwa cewa ruɗu ne na banza. Kamar balambalau da aka hura, a ganin ido yana da ƙarfi amma babu kome ciki. Babu shakka zai zama wofi, har ma bala’i, mutum ya zaɓi nagarta da mugunta bisa wani abu da ba shi da tushe, ‘falsafa da ruɗin banza’ na duniya.
Waɗanda ke Ce da “Mugunta Nagarta; Nagarta Kuma Mugunta”
8. (a) Ga wanene mutane suke juyawa don shawara? (b) Wace irin shawara ce ake bayarwa?
8 Abubuwa ba su bambanta ba a yau. A kowanne fanni na rayuwar ’yan Adam, akwai masana da yawa. Masu ba da shawara a kan aure da iyali, marubutan littattafai, waɗanda suka mai da kansu gwanaye, masana taurari, masu duba, da wasu suna shirye su ba da shawara—kyauta. Amma wane irin shawara ake bayarwa? Sau da yawa, ana tura mizanan Littafi Mai Tsarki game da tarbiyya a gefe ɗaya saboda abin da wai sabuwar tarbiyya ce. Alal misali, wajen magana game da “auren jinsi ɗaya” da gwamnati ta ƙi rajista, wani labari cikin jaridar Canada The Globe and Mail ya ce: “A shekara ta 2000, ba shi da kyau mutane biyu da suke ƙaunar juna kuma suka yi alkawari, a hana su abin da suke so domin sun kasance jinsi ɗaya.” Ra’ayin yau, ka yarda da kome kawai kada ka sūki ra’ayi. Ana ɗaukan kome daidai; ba wani abin da yanzu ya kasance cikakken nagarta ko mugunta.—Zabura 10:3, 4.
9. Menene mutane da ake daraja su a jam’iyya sau da yawa suke yi?
9 Wasu suna dangana ga masu kuɗi cikin jam’iyya—masu arziki da mashahurai—misalansu wajen yin zaɓe. Ko da ana daraja masu arziki da mashahurai a jam’iyyar yau, sau da yawa suna magana ne kawai game da ɗabi’u kamarsu yin gaskiya da riƙe amana. A wajen biɗan iko da kuma samun riba, mutane da yawa suna jin ba damuwa game da yin banza da dokoki da kuma taka ƙa’idodin ɗabi’a. Don su yi suna kuma a san su, wasu ba sa damuwa da mizanai da aka kafa sun fi son hali da ba shi da kyau na ban mamaki. Sakamakon shi ne, jam’iyya mai son riba, da ƙa’idar da take ja-gorarsu ita ce, “Kome daidai.” Abin mamaki ne da mutane suka rikice kuma suka ɓatā yayin da ya zo ga batun nagarta da mugunta?—Luka 6:39.
10. Yaya kalmomin Ishaya game da nagarta da mugunta suka zama gaskiya?
10 Mummunan sakamakon zaɓe da aka yi bisa ja-gora da ba daidai ba suka kewaye mu—aure da kuma iyalai da suke rabuwa, yin maye da miyagun ƙwayoyi da kuma giya, matasa ’yan iska masu mugunta, lalata, cututtuka da ake samu ta wurin jima’i, da sauransu. Hakika, yaya za mu zata abubuwa su kasance dabam yayin da mutane suka yi banza da dukan mizanai ko kuma abu da zai taimaka musu su gane wani yanayi yayin da ya zo ga nagarta da mugunta? (Romawa 1:28-32) Daidai yake kamar yadda annabi Ishaya ya sanar: “Kaiton waɗannan da ke ce da mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta su ke ce da ita; waɗanda su kan sa duhu maimakon haske, haske kuma maimakon duhu: su sa ɗaci madadin zaƙi, zaƙi kuma madadin ɗaci! Kaiton waɗanda ke maida kansu masu-hikima, suna ganin kansu masu-hankali!”—Ishaya 5:20, 21.
11. Me ya sa ba shi da kyau mutum ya dogara da kansa yayin da yake tsai da nagarta da mugunta?
11 Gaskiyar cewa Allah bai ƙyale waɗancan Yahudawa na dā da suka ga “kansu masu-hikima ne” ya sa shi ƙara zama da muhimmanci mu guji dogara ga kanmu wajen zancen nagarta da mugunta. Mutane da yawa a yau sun yarda da ra’ayin “ka saurara ga abin da zuciyarka ta faɗa,” ko kuma “ka yi abin da kake jin ya yi daidai.” Hakanan yana da kyau ne? Ba dai kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce ba, wanda ya ce: “Zuciya ta fi kome rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?” (Irmiya 17:9) Za ka dogara ga mutum mai rikici da ciwuta ya ja-gorance ka a yin zaɓe? Da kyar. Hakika, wataƙila za ka yi akasin abin da wannan mutumin ya gaya maka. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya tunasar mana: “Wanda ya dogara ga zuciyar kansa wawa ne: amma wanda ya taka a hankali, za a cece shi.”—Misalai 3:5-7; 28:26.
Koyon Abin da Allah Ya Amince da Shi
12. Me ya sa muke bukatar mu tabbatar wa kanmu “nufin nan na Allah”?
12 Tun da yake ba za mu dogara ga hikima ta duniya ba ko kuma kanmu in ya zo ga nagarta da mugunta, menene ya kamata mu yi? Ka lura da wannan gargaɗin daga manzo Bulus da ke a bayyane: “Kada ku kamantu bisa ga kamar wannan zamani kuma: amma ku juyu bisa ga sabontar azancinku, da za ku gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (Romawa 12:2) Me ya sa muke bukatar mu tabbatar wa kanmu nufin Allah? A cikin Littafi Mai tsarki, Jehovah ya ba da dalili kai tsaye kuma mai ƙarfi, yana cewa: “Kamar yadda sammai suna da nisa da duniya, hakanan kuma al’amurana sun fi naku tsawo, tunanina kuma sun fi naku.” (Ishaya 55:9) Da haka, maimakon dogara a kan namu fahimi ko kuma abin da muke ganin daidai ne, an yi mana gargaɗi: “Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afisawa 5:10.
13. Ta yaya kalmomin Yesu da ke rubuce a Yohanna 17:3 ya nanata bukatar mu san abin da Allah ya yarda da su?
13 Yesu Kristi ya nanata wannan bukata yayin da ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Furcin nan “su san ka” na da ma’ana mai zurfi fiye da “sani” kawai. In ji Vine’s Expository Dictionary, ya “nuna dangantaka tsakanin mutumin da ya sani da abin da aka sani; domin wannan, abin da aka sani yana da amfani ko kuma muhimmanci ga wanda ya sani, saboda haka dangantaka da aka kafa na da amfani da kuma muhimmanci.” A kasance da dangantaka da mutum yana nufi fiye da kawai sanin mutumin ko kuma sunansa. Ya haɗa da sanin abin da yake so da abin da ba ya so, sanin abubuwa da yake daraja, mizanansa—kuma yake ɗaukaka su.—1 Yohanna 2:3; 4:8.
Koyar da Hankalinmu
14. Menene Bulus ya ce shi ne bambanci na musamman tsakanin jarirai na ruhaniya da isassun mutane?
14 To, yaya za mu iya rarrabe tsakanin nagarta da mugunta? Kalmomin Bulus ga Kiristoci Ibraniyawa na ƙarni na farko sun ba da amsar. Ya rubuta: “Kowanne mai-shan madara mara-sanin maganar adalci ne; gama jariri ne shi. Amma abinci mai-ƙarfi domin isassun mutane ne, watau waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” A nan Bulus ya gwada “madara,” wadda ya kwatanta cikin ayar da ta gabata da “tussa na farkon zantattukan Allah,” da “abinci mai ƙarfi,” wanda ke na “isassun mutane,” waɗanda “suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—Ibraniyawa 5:12-14.
15. Me ya sa ake bukatar aiki tuƙuru don a samu cikakken sanin Allah?
15 Wannan yana nufin cewa, da farko, tilas ne mu yi aiki tuƙuru mu samu cikakken fahimta na mizanan Allah yadda yake cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ba ma neman zumamin dokoki da zai gaya mana abin da za mu yi ko abin da ba za mu yi ba. Littafi Mai Tsarki ba irin wannan littafi ba ne. Maimako, Bulus ya bayyana: “Kowanne nassi hurare daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowanne managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Don mu amfana daga wannan koyarwar, tsautawa, da horo, dole ne mu soma amfani da zuciyarmu da hankalinmu. Wannan yana bukatar ƙoƙari, amma sakamakon—zai zama “kamili, shiryayye sarai domin kowanne managarcin aiki”—kwalliyar ta biya kuɗin sabulu.—Misalai 2:3-6.
16. Menene yake nufi mutum ya koyar da hankalinsa?
16 Kamar yadda Bulus ya nuna, isassun mutane suna da “hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” A nan mun zo ga tushen wannan batun. Furcin nan “hankulansu wasassu” a zahiri na nufin a koyar da gaɓoɓin ji (kamar mai wasan gina jiki).” (Kingdom Interlinear Translation) Mai wasan gina jiki da ya gwaninta a wani wasa, da zai iya yin abubuwa da sauri yana kuɓuce wa ƙarfin maganaɗiso ko kuma wasu dokokin halitta. Yana sarrafa gaɓoɓin jikinsa kowanne lokaci, yana lura da kusan kowanne abu da yake yi don ya gama wasan cikin nasara. Dukan wannan don ya ba da kansa ne ga koyo sosai da gwadawa a kai a kai.
17. A wane azanci ne ya kamata mu zama kamar masu wasan gina jiki?
17 Mu ma dole ne a koyar da mu kamar mai wasan gina jiki a zancen ruhaniya, idan muna so mu tabbata cewa shawarwari da zaɓe da muke yi koyaushe daidai ne. Dole ne kowanne lokaci mu kasance da iko bisa azancinmu da gaɓoɓin jikinmu. (Matta 5:29, 30; Kolossiyawa 3:5-10) Alal misali, kana horar da kanka kada ka kalli abubuwa na lalata ko kuma kada kunnenka ya saurari kaɗe-kaɗe na ƙazanta ko kuma furci? Gaskiya ne cewa irin waɗannan munanan abubuwa sun kewaye mu. Duk da haka, har ila zaɓen namu ne ko za mu bari ya kasance a zuciyarmu da azanci. Za mu iya yin koyi da mai Zabura da ya ce: “Ba zan sa wani mummunan al’amari a gaban idanuna ba: aikin masu-ratsewa na ƙi: ba kuwa za ya kama ni ba. . . . Mai-yin ƙarya ba za ya tabbata a gabana ba.”—Zabura 101:3, 7.
Ka Koyar da Hankalinka ta Wurin Amfani da Shi
18. Menene ake nufi da furcin ‘aikata’ a bayanin da Bulus ya yi game da mutum ya koyar da hankalinsa?
18 Ka tuna cewa ta wurin ‘amfani da shi’ ne za mu iya koyar da hankalinmu mu bambance nagarta daga mugunta. A wasu kalmomi, kowanne lokaci da muke so mu tsai da shawara, ya kamata mu koyi mu yi amfani da hankalinmu mu rabe ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da ya ƙunshi yadda za a yi amfani da su. Ko gina halin yin bincike a littattafai na Littafi Mai Tsarki da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadinsu. (Matta 24:45) Hakika, za mu iya mu nemi taimakon Kiristoci da sun manyanta. Duk da haka, ƙoƙari da muke sakawa a nazarin Kalmar Allah, haɗe da addu’a ga Jehovah don ja-gorarsa da ruhu, zai kawo albarka mai yawa daga baya.—Afisawa 3:14-19.
19. Wace albarka ce za ta zama tamu idan mun ci gaba da koyar da hankalinmu?
19 Yayin da muke ci gaba a koyar da hankalinmu, manufar shi ne “kada nan gaba mu zama yara, waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowacce iskan sanarwa, ta wurin wawa-idon mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.” (Afisawa 4:14) Maimako, bisa ga abin da muka sani da fahiminmu na abin da Allah ya yarda da shi, za mu iya tsai da shawarwari masu kyau, manya da yara, da za su amfane mu, suna gina ’yan’uwanmu masu bi, fiye da kome suna faranta wa Ubanmu na sama rai. (Misalai 27:11) Albarka da kuma kāriya ce a waɗannan miyagun zamanu!
[Hasiya]
a A zumami sama da 40 na wahala a rayuwar mutane, da Likitoci Thomas Holmes da Richard Rahel suka rubuta, mutuwar abokin aure, kashe aure, da rabuwa ne aka jera su da farko. Aure ya zo na bakwai.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wace iyawa ake bukata don a yi zaɓe mai kyau?
• Me ya sa ba shi da kyau a dangana da mashahuran mutane ko kuma dogara da kanmu yayin da muke bambance nagarta da mugunta?
• Me ya sa za mu tabbata da abin da Allah ya yarda yayin da muke tsai da shawarwari, kuma yaya za mu yi haka?
• Menene ake nufi ‘a koyar da hankalinmu’?
[Hoto a shafi na 21]
Dangana ga mawadata da mashahurai don ja-gora, wofi ne
[Hoto a shafi na 22]
Kamar mai wasan gina jiki, dole ne mu sarrafa azancinmu da gaɓoɓin jikinmu sosai