Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Addu’ar Yesu
“Ya Uba, . . . ka ɗaukaka Ɗanka, domin Ɗan shi ɗaukaka ka.”—YOH. 17:1.
1, 2. Mene ne Yesu ya yi wa manzanninsa masu aminci bayan sun yi Idin Ƙetarewa a shekara ta 33?
A CIKIN daren ranar 14 ga Nisan a shekara ta 33 a zamaninmu, Yesu da manzanninsa sun kammala yin Idin Ƙetarewa, wanda ke tunasar musu da yadda Allah ya ceci ubanninsu daga bauta a ƙasar Masar. Amma za a fanshi almajiransa masu aminci “har abada” a hanya mafi girma. Washegari, magabtan Ubangijinsu za su kashe shi. Amma wannan muguntar za ta zama albarka, domin hadayar da Yesu ya yi za ta ceci ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa.—Ibran. 9:12-14.
2 Domin ya tabbata cewa ba za a mance da wannan tanadin ba, Yesu ya soma wata sabuwar idin shekara-shekara da ta maye gurbin Idin Ƙetarewa da ake yi sau ɗaya a shekara. Ya yi hakan ta wajen karya gurasa marar yisti kuma ya miƙa wa kowanne cikin manzanninsa masu aminci guda sha ɗaya, ya ce: “Wannan jikina ne wanda an bayar domin ku: ku yi wannan abin domin tunawa da ni.” Hakazalika, ya ɗauki ƙoƙon ruwan inabi, ya ce musu: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.”—Luk 22:19, 20.
3. (a) Wace babbar canji ce ta auku bayan mutuwar Yesu? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka dace mu yi tunani a kai yayin da muke tattauna addu’ar Yesu da ke Yohanna sura 17?
3 An kusan daina amfani da Dokar Alkawari da Allah ya ba wa al’ummar Isra’ilawa. Domin Jehobah zai ƙafa sabon alkawari tsakaninsa da mabiyan Yesu shafaffu. Yesu ba ya so mabiyansa su zama kamar al’ummar Isra’ilawa. Domin al’ummar Isra’ilawa ba su bauta wa Allah tare ba, kuma sun ƙi girmama sunansa. (Yoh. 7:45-49; A. M. 23:6-9) Yesu yana so mabiyansa su kasance da hali iri ɗaya domin su yi aiki tare wajen girmama sunan Allah. To, mene ne Yesu ya yi? Ya yi wata addu’a mai ma’ana sosai da kowane ɗan Adam zai ɗauka a matsayin gata ya karanta. (Yoh. 17:1-26; duba hoto na farko.) Yayin da muke tattauna wannan addu’ar, zai dace mu yi tunani a kan wannan tambayoyin: “Shin Allah ya amsa addu’ar Yesu kuwa? Ina rayuwar da ta jitu da addu’ar kuwa?”
ABIN DA YESU YA FI ƊAUKA DA MUHIMMANCI
4, 5. (a) Mene ne muka koya daga sashen farko na addu’ar Yesu? (b) Ta yaya Jehobah ya amsa roƙon da Yesu ya yi game da kansa?
4 Yesu ya koya wa almajiransa abubuwa masu ban al’ajabi har tsakar dare. Sai ya kalli sama ya yi addu’a cewa: “Ya Uba, sa’a ta zo; ka ɗaukaka Ɗanka, domin Ɗan shi ɗaukaka ka; kamar yadda ka ba shi hukunci bisa dukan rai domin iyakar waɗanda ka ba shi, ya ba su rai na har abada. . . . Na ɗaukaka ka a duniya, yayinda na cika aikin da ka ba ni in yi. Yanzu, ya Uba, ka ɗaukaka ni da kanka da daraja wadda ni ke da ita tare da kai tun duniya ba ta zama ba.”—Yoh. 17:1-5.
5 Ku lura da abubuwan da Yesu ya ɗauka da muhimmanci a farkon addu’arsa. Abu mafi muhimmanci da ya ambata a addu’arsa shi ne a ɗaukaka Ubansa na sama, kuma hakan ya jitu da abin da ya soma ambatawa a addu’arsa na misali: “Ya Uba, A tsarkake sunanka.” (Luk 11:2) Sai ya ambata bukatun almajiransa, wato “ya ba su rai na har abada.” Bayan waɗannan abubuwan, sai Yesu ya ambata bukatunsa, ya ce: “Uba, ka ɗaukaka ni da kanka da daraja wadda ni ke da ita tare da kai tun duniya ba ta zama ba.” Jehobah ya albarkaci amintaccen ɗansa kuma ya yi masa fiye da abin da ya roƙa, wato ya ba shi suna da ke “da fifiko nesa kan” na mala’iku.—Ibran. 1:4.
SANIN ‘ALLAH MAƘAƊAICI MAI GASKIYA’
6. Mene ne ya kamata manzannin su yi don su sami rai na har abada, kuma ta yaya muka san cewa sun ci gaba da yin hakan?
6 Yesu ya kuma yi addu’a game da abin da ya wajaba mu yi don mu sami baiwar rai na har abada. (Karanta Yohanna 17:3.) Ya ce wajibi ne mu ci gaba da ‘sanin’ Allah da kuma Yesu. Ta yaya za mu iya yin haka? Hanya ɗaya ita ce, ta ƙoƙartawa don mu ƙara sani game da Jehobah da kuma Ɗansa. Wata hanya kuma mai muhimmanci na sanin Allah ita ce, ta yin amfani da abubuwan da muka koya a rayuwarmu. Manzannin sun riga sun yi waɗannan abubuwa biyu kamar yadda Yesu ya nuna a addu’arsa, domin ya ci gaba da cewa: “Gama zantattuka waɗanda ka ba ni, na ba su; suka karɓa.” (Yoh. 17:8) Amma, idan suna so su sami rai na har abada, suna bukata su ci gaba da yin bimbini a kan maganar Allah kuma su aikata ta a rayuwarsu ta yau da kullum. Shin manzannin sun ci gaba da yin hakan har ƙarshen rayuwarsu a duniya ne? E, sun yi hakan. Mun san hakan domin sunayen kowannensu yana rubuce a kan duwatsu goma sha biyu na Sabuwar Urushalima ta sama kuma ba za a iya soke sunayen ba.—R. Yoh. 21:14.
7. Mene ne ‘sanin’ Allah yake nufi, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
7 Idan muna so mu rayu har abada, wajibi ne mu ci gaba da ‘sanin’ Allah. Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin cewa mu ci gaba da daɗa koyo game da Allah, kuma hakan ba ya nufin sanin halayensa da nufe-nufensa kawai ba. Wajibi ne mu ƙaunace shi sosai kuma mu kasance da dangantaka ta kud da kud da shi. Kuma ya wajaba mu ƙaunaci ’yan’uwanmu maza da mata. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ba ya yin ƙauna ba, bai san Allah ba.” (1 Yoh. 4:8) Ƙari ga haka, sanin Allah ya ƙunshi yi masa biyayya. (Karanta 1 Yohanna 2:3-5.) Babu shakka, gata ce zama cikin waɗanda suka san Jehobah! Kamar Yahuda Iskariyoti, za a iya rasa wannan dangantaka mai tamani. Saboda haka, bari mu yi aiki tuƙuru don mu ƙarfafa abokantakarmu da Jehobah. Idan muka yi hakan, Jehobah zai ba mu baiwa mafi girma na rai har abada.—Mat. 24:13.
DON “SUNANKA”
8, 9. Mene ne ya fi muhimmanci ga Yesu sa’ad da yake duniya, kuma wace koyarwa ce ya ƙi?
8 Da yake mun karanta addu’ar Yesu a littafin Yohanna sura 17, babu shakka mun fahimci cewa Yesu yana ƙaunar manzanninsa na dā sosai kuma yana ƙaunar mu ma a yau. (Yoh. 17:20) Duk da haka, ya kamata mu fahimci cewa ba cetonmu ba ne ya fi muhimmanci ga Yesu. A lokacin da yake duniya, abin da ya fi masa muhimmanci shi ne ya ɗaukaka sunan Ubansa. Alal misali, sa’ad da Yesu ya bayyana dalilin da ya sa ya zo duniya, ya karanta naɗaɗɗen littafin Ishaya cewa: “Yahweh . . . ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta.” Babu shakka, Yesu ya furta sunan Allah sosai sa’ad da ya karanta wannan ayar.—Luk 4:16-21; Isha. 61:1.a
9 Wani tarihin al’adar Yahudawa ya nuna cewa tun kafin Yesu ya zo duniya, malaman addinai sun hana mutane yin amfani da sunan Allah. Babu shakka, za mu tabbata cewa Yesu ya ƙi irin wannan ra’ayin al’adar. Kuma ya faɗa wa magabtansa cewa: “Ni na zo cikin sunan Ubana, ba ku karɓe ni ba: Idan wani ya zo a cikin sunan kansa, wannan za ku karɓa.” (Yoh. 5:43) Ƙari ga haka, kwana kaɗan kafin mutuwarsa, Yesu ya kuma ambata abin daya fi muhimmanci a gare shi a addu’a cewa: “Uba, ka ɗaukaka sunanka.” (Yoh. 12:28) Kuma a addu’ar da muke tattaunawa, a bayyane yake cewa abin da ya fi muhimmanci a rayuwar Yesu shi ne ya ɗaukaka sunan Ubansa.
10, 11. (a) Ta yaya Yesu ya sa aka san sunan Ubansa? (b) Me ya sa almajiran Yesu suke sanar da sunan Jehobah?
10 Yesu ya yi addu’a cewa: “Na bayana sunanka ga mutane waɗanda ka ba ni daga cikin duniya; naka su ke, ka ba ni su; sun kuwa kiyaye maganarka. Ba ni cikin duniya kuma nan gaba, amma waɗannan suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa gare ka. Ya Uba mai-tsarki, ka kiyaye su a cikin sunanka wanda ka ba ni, domin su zama ɗaya kamar mu.”—Yoh. 17:6, 11.
11 Sa’ad da Yesu ya faɗa wa almajiransa sunan Ubansa, ba kiran sunan a baƙi kawai ya koya musu ba. Amma ya koya musu abin da sunan Allah ya ƙunsa, wato halayensa masu ban al’ajabi da kuma yadda yake sha’ani da mu. (Fit. 34:5-7) Yesu ne yanzu Sarki a sama, kuma ya ci gaba da taimaka wa almajiransa su sanar da sunan Jehobah a duniya baƙi ɗaya. Mene ne maƙasudin wannan aikin? Ana so a taimaki mutane da yawa su koya game da Jehobah kafin a halaka wannan mugun zamanin. A lokacin, Jehobah zai sa a san sunansa yayin da yake cetan shaidunsa masu aminci.—Ezek. 36:23.
“DOMIN DUNIYA TA GASKATA”
12. Waɗanne abubuwa uku ne ya wajaba mu yi don mu yi nasara a aikin ceton da muke yi?
12 Yesu ya yi aiki tuƙuru don ya taimaka wa almajiransa su shawo kan kasawarsu. Ya yi hakan ne don ya taimake su su iya kammala aikin da ya soma. Yesu ya yi addu’a cewa: “Kamar yadda ka aiko ni a cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya.” Amma Yesu ya san cewa suna bukatar taimako don su iya cim ma wannan aikin ceton rayuka, shi ya sa ya nanata abubuwa guda uku. Na farko, ya yi addu’a cewa kada almajiransa su kasance cikin wannan duniyar Shaiɗan. Na biyu, ya yi addu’a cewa a tsarkake su, ko kuma su kasance da tsarki, ta yin biyayya ga Kalmar Allah. Na uku, Yesu ya roƙa cewa almajiransa su kasance da hali ɗaya, kamar yadda shi da Ubansa suke. Ya kamata kowannenmu ya yi wa kansa wannan tambayar, ‘Shin ina yin abubuwa uku da Yesu ya ambata a addu’arsa kuwa?’ Yesu ya tabbata cewa idan almajiransa suka yi waɗannan abubuwan, mutane da yawa za su karɓi saƙonsa.—Karanta Yohanna 17:15-21.
13. Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Yesu a ƙarni na farko?
13 Sa’ad da muka yi nazarin littafin Ayyukan Manzanni, za mu ga cewa Jehobah ya amsa addu’ar Yesu. Akwai Yahudawa da ’yan Al’ummai, mawadata da talakawa, bayi da ubanningijinsu a ikilisiyoyi na ƙarni na farko. Ka yi tunanin irin tsatsaguwar da za ta iya tasowa tsakaninsu. Amma, sun kasance da haɗin kai har manzo Bulus ya kwatanta su da gaɓaɓuwan jikin mutum da kuma Yesu a matsayin kansu. (Afis. 4:15, 16) Wannan haɗin kai ya yiwu a wannan duniyar Shaiɗan don taimakon ruhu mai tsarki na Jehobah.—1 Kor. 3:5-7.
14. Ta yaya Jehobah yake amsa addu’ar Yesu a yau?
14 Abin baƙin ciki, abubuwa ba su ci gaba hakan ba bayan rasuwar manzannin Yesu. Maimakon haka, aka soma koyarwar ƙarya a cikin ikilisiya kuma hakan ya jawo tsatsaguwa. (A. M. 20:29, 30) Amma a shekara ta 1919, Yesu ya yantar da mabiyansa shafaffu daga bautar ƙarya kuma ya tattara su cikin “magamin kamalta.” (Kol. 3:14) Ta yaya wa’azin da suke yi ya shafi dukan duniya? Fiye da mutane miliyan bakwai daga “dukan kabilai da al’ummai da harsuna” sun soma bauta wa Jehobah tare da shafaffu. (Yoh. 10:16; R. Yoh. 7:9) Wannan amsa ce ta musamman ga addu’ar da Yesu ya yi ga Jehobah cewa “domin duniya ta sani ka [Jehobah] aiko ni, ka yi ƙaunarsu kuma kamar yadda ka ƙaunace ni”!—Yoh. 17:23.
KAMMALAWA MAI BAN SHA’AWA
15. Wane roƙo na musamman ne Yesu ya yi a madadin almajiransa shafaffu?
15 A yammar ranar 14 ga Nisan, Yesu ya ‘ɗaukaka’ manzanninsa ta wajen yi musu alkawari cewa za su yi sarauta tare a Mulkinsa. (Luk 22:28-30; Yoh. 17:22) Sai Yesu ya yi addu’a a madadin dukan shafaffu da za su zama mabiyansa. Ya ce: “Ya Uba, waɗanda ka ba ni, ina so su zauna wurin da na ke, tare da ni; domin su duba darajata, wadda ka ba ni: gama ka ƙaunace ni tun ba a kafa duniya ba.” (Yoh. 17:24) Waɗansu tumaki ba sa jin haushin shafaffun Kiristoci domin za su samu wannan ladar, amma suna murna. Hakan ya kuma nuna cewa Kiristoci na gaskiya a yau suna da haɗin kai.
16, 17. (a) Mene ne Yesu ya ce zai ci gaba da yi a kammalawar addu’arsa? (b) Me ya kamata mu ƙudura niyyar yi?
16 Mutane da yawa a duniya sun ƙi amince cewa Jehobah yana da bayi da suka san shi kuma suna da haɗin kai. Hakan yana yawan faruwa domin limamai sun koya musu ƙarya. Hakan ma ya faru a zamanin Yesu. Shi ya sa ya kammala addu’arsa da waɗannan kalmomin: “Uba mai-adilci, duniya ba ta san ka ba, amma ni na san ka; waɗannan kuma sun sani ka aiko ni. Na kuma sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi; domin wannan ƙauna wadda ka ƙaunace ni da ita ta zauna cikinsu, ni kuma a cikinsu.”—Yoh. 17:25, 26.
17 Babu shakka, Yesu ya sanar da sunan Ubansa. Kuma a matsayinsa na Shugaban ikilisiya a yau, ya ci gaba da taimaka mana mu sanar da sunan Ubansa da kuma nufinsa. Bari dukanmu mu yi biyayya ga shugabancin Yesu, ta wajen yin wa’azi da kuma almajirtar da mutane da ƙwazo. (Mat. 28:19, 20; A. M. 10:42) Bari mu kuma yi aiki tuƙuru don mu kasance da haɗin kai. Idan mun yi hakan, za mu yi rayuwar da ta jitu da addu’ar Yesu, za mu ɗaukaka sunan Jehobah kuma za mu yi farin ciki na dindindin.