Jehovah, Allah Na Gaskiya
“Ka fanshe ni, ya Ubangiji, ya Allah na gaskiya.”—ZABURA 31:5.
1. Waɗanne yanayi yake sama da kuma duniya lokacin da babu rashin gaskiya?
DA AKWAI lokaci da babu rashin gaskiya. Kamilan halittu na ruhu ne mazaunan sammai marar ganuwa, suna bauta wa Mahaliccinsu, “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5) Babu ƙarya, babu ruɗu. Jehovah yana gaya wa ’ya’yansa na ruhu abin da ke gaskiya. Yana yin haka ne domin yana ƙaunarsu kuma domin ya damu game da lafiyarsu. Yanayi ɗaya ne ma a duniya. Jehovah ya halicci namiji da tamace na farko, kuma ta hanyar sadarwarsa, yana magana da su, kai tsaye, kuma gaskiya yake gaya musu. Babu shakka wannan abar ban sha’awa ce!
2. Wanene ya gabatar da rashin gaskiya, kuma me ya sa?
2 Amma, da sannu sannu, sai wani ɗan ruhu na Allah da taurin kai ya ta da kansa ya zama allah, yana adawa da Jehovah. Wannan halittar ruhu, da ya zama Shaiɗan Iblis ya so wasu su bauta masa. Domin ya cim ma burinsa, ya gabatar da rashin gaskiya, ya zama hanyar da zai mallake wasu. A yin haka nan, ya zama “maƙaryaci . . . , da uban ƙarya kuma.”—Yohanna 8:44.
3. Yaya Adamu da Hauwa’u suka aikata a batun ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan, kuma menene sakamakon?
3 Ta wurin maciji, Shaiɗan ya gaya wa mace na farko, Hauwa’u, cewa idan ta yi watsi da dokar Allah kuma ci daga ’ya’yan itace da aka haramta, ba za ta mutu ba. Ƙarya ce wannan. Ya sake gaya mata cewa idan ta ci za ta zama kamar Allah, da sanin nagarta da mugunta. Wannan ma, ƙarya ce. Ko da yake ba a taɓa yi wa Hauwa’u ƙarya ba, lallai ta sani cewa abin da ta ji daga bakin macijin bai yi daidai da abin da Allah ya gaya wa mijinta, Adamu ba. Duk da haka, ta zaɓi ta gaskata da Shaiɗan, ba Jehovah ba. Domin an ruɗe ta ƙwarai, ta tsinki ’ya’yan itacen ta ci. Adamu ya zo daga baya kuma shi ma ya ci ’ya’yan itacen. (Farawa 3:1-6) Adamu shi ma bai taɓa jin ƙarya ba kamar Hauwa’u, amma ba a ruɗe shi ba. (1 Timothawus 2:14) Abin da ya yi, ya nuna cewa ya ƙi Mahaliccinsa. Sakamakon wannan ga mutane ya zama bala’i. Domin rashin biyayyar Adamu, zunubi da mutuwa—tare da lalata da masifu da yawa—sun yaɗa ga dukan ’ya’yansa.—Romawa 5:12.
4. (a) Waɗanne irin ƙaryace-ƙaryace ne aka yi a Adnin? (b) Menene dole mu yi don kada Shaiɗan ya ruɗe mu?
4 Rashin gaskiya ma ya yaɗu. Dole ne mu fahimci cewa ƙaryace-ƙaryace da aka yi a gonar Adnin farmaki ne a kan gaskiya har ga Jehovah ma. Shaiɗan ya ce wa Allah yana ruɗin ma’aurata na farko don ya hana su wani abu mai kyau. Amma, ba haka ba ne. Adamu da Hauwa’u ba su amfana ba daga rashin biyayyarsu. Sun mutu, yadda Jehovah ya ce zai faru da su. Duk da haka, mugun farmaki na Shaiɗan gāba da Jehovah ya ci gaba, har ya sa aka hure manzo Yohanna ƙarnuka daga baya ya rubuta cewa Shaiɗan “mai-ruɗin dukan duniya” ne. (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Domin kada Shaiɗan Iblis ya ruɗe mu, dole ne mu kasance da cikakkiyar dogara ga gaskiyar Jehovah da Kalmarsa. Ta yaya za ka gina kuma ƙarfafa dogararka ga Jehovah kuma ƙarfafa kanka game da ruɗi da ƙaryace-ƙaryacen da Magabcinsa ke gabatarwa?
Jehovah Ya San Gaskiya
5, 6. (a) Wane sani Jehovah yake da shi? (b) Yaya za a iya gwada ilimin mutane da na Jehovah?
5 Sau da sau Littafi Mai Tsarki yana kiran Jehovah cewa shi ne “ya halitta abu duka.” (Afisawa 3:9) Shi ne “wanda [y]a yi sama da ƙasa da teku, da abin da ke cikinsu duka.” (Ayukan Manzanni 4:24) Tun da yake Jehovah shi ne Mahalicci, ya san gaskiya game da kome. Ga misali: Wani mutum ya zana kuma gina gidansa, yana yin jinka yana kafa ƙusoshi a kan dukan katakai da kansa. Zai san gidan ciki da waje kuma zai zama ya san gidan fiye da kowa. Mutane suna sanin abin da suka zana kuma yi. Haka nan ma, Mahalicci ya san kome game da abin da ya halitta.
6 Annabi Ishaya ya furta da kyau yawan yadda sanin Jehovah yake. Mu karanta: “Wanene ya auna ruwaye a cikin tāfin hannunsa, ya gwada sama kuma da taƙi? ya tara turɓayar duniya kuma cikin mudu, ya auna duwatsu cikin mizani, tuddai kuma cikin ma’auni? Wanene ya gwada ruhun Ubangiji, wanene kuwa ya zama mai-ba shi shawara har ya koya masa? A wurin wa ya yi shawara, wanene kuwa ya sanashe shi, ya koya masa cikin hanyar shari’a kuwa, ya koya masa sani, ya nuna masa hanyar fahimi?” (Ishaya 40:12-14) Hakika, Jehovah “Allah mai-sani ne” kuma “kamili ga ilimi.” (1 Samu’ila 2:3; Ayuba 36:4; 37:16) Ba mu ma yi rabin kusa da saninsa ba! Duk da yawan ilimi da mutane suke tattarawa, fahiminmu na halitta ba ta kai ma “gefen al’amuran ikon [Allah]” ba. Kamar “raɗar” ne kawai idan aka gwada da “tsawar ikonsa.”—Ayuba 26:14.
7. Menene Dauda ya fahimta game da sanin Jehovah, saboda haka, menene dole mu fahimta?
7 Tun da Jehovah ne ya halicce mu, daidai ne a ce ya san mu sosai. Sarki Dauda ya yarda da wannan. Ya rubuta: “Ya Ubangiji, kā bincike ni, kā kuwa san ni. Zamana da tashina ka sani, kā fahimci tunanina tun daga nesa. Kā bincike tafarkina da kwanciyata, kā san dukan al’amurana. Gama babu wata magana da ke bakina, sai dai, ka san ta duk, ya Ubangiji.” (Zabura 139:1-4) Dauda ya sani cewa mutane suna da ’yancin zaɓe—Allah ya ba mu iyawar da za mu yi masa biyayya ko kuma mu ƙi yi masa biyayya. (Kubawar Shari’a 30:19, 20; Joshua 24:15) Ban da haka ma, Jehovah ya san mu fiye da yadda muka san kanmu. Yana son abin da ya fi mana kyau, kuma yana matsayin da zai jagabanci hanyoyinmu. (Irmiya 10:23) Hakika, babu wani malami, gwani, mashawarci da aka koyar domin ya koyar mana da gaskiya kuma ya sa mu hikima da farin ciki ba.
Jehovah Yana da Gaskiya
8. Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana gaskiya?
8 Abu ɗaya ne a san gaskiya, wani abu ne kuma a dinga faɗan gaskiya. Alal misali, Iblis ya zaɓi ya ƙi ‘tsayawa a kan gaskiya.’ (Yohanna 8:44) Akasin haka, Jehovah “mai-yalwar . . . gaskiya” ne. (Fitowa 34:6) A kowane wuri Nassosi na tabbatar da gaskiyar Jehovah. Manzo Bulus ya ce “ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya,” kuma cewa Allah ba “shi iya yin ƙarya.” (Ibraniyawa 6:18; Titus 1:2) Kasance da gaskiya halin Allah ne na musamman. Za mu iya dangana kuma dogara ga Jehovah domin yana gaskiya; ba ya taɓa ruɗin waɗanda suke nasa masu aminci.
9. Ta yaya sunan Jehovah yake haɗe da gaskiya?
9 Sunan Jehovah ya tabbatar da gaskiyarsa. Sunan Allah yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Wannan yana nuna cewa Jehovah Mai Cikar dukan alkawuransa ne a kai a kai. Babu wani da yake wannan matsayin. Domin Jehovah ne Mafifici, babu wanda zai iya hana cikar ƙudurinsa. Ba kawai ne Jehovah yana gaskiya ba amma yana da iko da kuma hikima ya sa duk abin da ya ce su cika.
10. (a) Ta yaya ne Joshua ya shaida gaskiyar Jehovah? (b) Waɗanne alkawuran Jehovah ne ka gani suke cika?
10 Joshua ɗaya ne cikin waɗanda suka shaida aukuwa na musamman da ke tabbatar da gaskiyar Jehovah. Joshua yana Masar lokacin da Jehovah ya kawo annoba goma a kan al’ummar, yana annabta zuwan kowannen da daɗewa. Ban da waɗannan, Joshua kuma ya shaida cikar alkawuran Jehovah a cetar da Isra’ilawa daga Masar kuma ya kai su cikin Ƙasar Alkawari, yana mallakar rundunar Kan’ana da suke adawa da su. Kusa da ƙarshen rayuwarsa, Joshua ya gaya wa tsofaffi na al’ummar Isra’ila: “Kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” (Joshua 23:14) Ko da yake ba ka taɓa shaida mu’ujizai da Joshua ya gani ba, ka taɓa shaida gaskiyar alkawuran Allah a rayuwarka?
Jehovah Yana Bayyana Gaskiya
11. Menene ya nuna cewa Jehovah yana son ya yi wa mutane gaskiya?
11 Ka yi tunanin wani mahaifi da yake da ilimi mai yawa amma da ƙyar ya yi magana da yaransa. Ba ka godiya ne da cewa Jehovah ba ya haka? Cikin ƙauna Jehovah yana magana da ’yan Adam, kuma yana haka da zuciya ɗaya. Nassosi ya ƙira shi ‘Mai-koyarwa [Mai Girma].’ (Ishaya 30:20) A cikin alherinsa, yana kai wa wajen waɗanda ba sa son su saurare shi. Alal misali, an ce Ezekiel ya yi wa waɗanda Jehovah ya san ba za su saurara ba wa’azi. Jehovah ya ce: “Ɗan mutum, je ka, ka tafi wurin gidan Isra’ila, ka yi zance da su, kana faɗa musu maganata.” Sai kuma ya faɗakar: “Ba za su kasa kunne gareni ba: gama dukan gidan Isra’ila masu-taurin kai ne, masu-ƙarfin zuciya ne.” Aiki ne mai wuya, amma Ezekiel ya yi shi cikin aminci, a yin haka kuwa yana nuna tausayin Jehovah. Idan ka iske kanka cikin aikin wa’azi mai wuya haka, kuma ka dogara ga Allah, za ka tabbata da cewa zai ƙarfafa ka yadda ya yi da annabinsa Ezekiel.—Ezekiel 3:4, 7-9.
12, 13. A waɗanne hanyoyi ne Allah ya yi magana da mutane?
12 Jehovah yana son “dukan [ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Ya yi magana ta wurin annabawa, ta wurin mala’iku, har kuma ta wurin Ɗansa ƙaunatacce, Yesu Kristi. (Ibraniyawa 1:1, 2; 2:2) Yesu ya ce wa Bilatus: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya. Kowanene da ke na gaskiya ya kan ji muryata.” Bilatus yana da zarafi mafi kyau ya koyi gaskiya game da tanadin Jehovah domin ceto daga wurin Ɗan Allah kansa. Amma, Bilatus ba ya gefen gaskiya, saboda haka bai so ya koya daga wurin Yesu ba. Maimakon haka, cikin rashin gaskatawa Bilatus ya ce: “Menene gaskiya?” (Yohanna 18:37, 38) Abin baƙin ciki kuwa! Mutane da yawa sun saurari gaskiya da Yesu ya yi shelarta. Ya ce wa almajiransa: “Idanunku masu-albarka ne, gama suna gani; kunnuwanku kuma, gama suna ji.”—Matta 13:16.
13 Jehovah ya adana gaskiya ta wurin Littafi Mai Tsarki kuma ya sa mutane a ko’ina su same shi. Littafi Mai Tsarki ya bayyana gaskiyar abubuwa. Ya kwatanta halayen Allah, ƙudurinsa, da kuma dokokinsa, har kuma da yanayin harkokin mutane. Yesu ya faɗa cikin addu’a ga Jehovah: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki littafi ne na musamman. Shi ne kaɗai aka rubuta ta wurin hurewar Allah da ya san kome. (2 Timothawus 3:16) Kyauta ce mai tamani ga mutane, wanda bayin Allah suke ɗauka da tamani. Hikima ce mu karanta shi kowacce rana.
Ka Riƙe Gaskiya Sosai
14. Waɗanne ne wasu abubuwan da Jehovah ya ce zai yi, kuma me ya sa za mu gaskata da shi?
14 Ya kamata mu ɗauki abin da Jehovah ya gaya mana cikin Kalmarsa da muhimmanci. Shi yana tabbata abin da ya faɗa, kuma zai yi abin da ya ce zai yi. Muna da kyakkyawan dalili na dogara da Allah. Za mu iya gaskata da cewa Jehovah zai kawo “ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tassalunikawa 1:8) Za mu kuma iya gaskata da Jehovah sa’ad da ya ce yana ƙaunar waɗanda suke biɗan adalci, sa’ad da ya ce zai ba da rai na har abada ga waɗanda suke ba da gaskiya, kuma da ya ce zai kawar da azaba, da kuka, har ma da mutuwa. Jehovah ya tabbatar da gaskiyar wannan alkawari na ƙarshe ta wurin ba da umurnin nan ga manzo Yohanna: “Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5; Misalai 15:9; Yohanna 3:36.
15. Waɗanne ƙaryace-ƙaryace ne Shaiɗan yake gabatarwa?
15 Shaiɗan dabam yake sarai da Jehovah. Maimakon ya wayar da mutane, ruɗinsu yake yi. Don ya cim ma burinsa na juyar da mutane daga bauta mai tsarki, Shaiɗan yana gabatar da ƙaryace-ƙaryace masu yawa. Alal misali, Shaiɗan yana son mu gaskata da cewa Allah ba ya ganin bukatar ya matso kusa da mu kuma ba ya damuwa da wahalar da ke duniya. Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah yana kula da halittunsa kuma ba ya son mugunta da kuma wahala. (Ayukan Manzanni 17:24-30) Shaiɗan kuma yana son mutane su gaskata da cewa biɗan abubuwa na ruhaniya ɓata lokaci ne. Akasin haka, Nassosi sun tabbatar da mu cewa “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” Bugu da ƙari, ya bayyana sarai cewa “shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.—Ibraniyawa 6:10; 11:6.
16. Me ya sa dole ne Kiristoci su kasance a faɗake kuma su riƙe gaskiya sosai?
16 Game da Shaiɗan, manzo Bulus ya rubuta: “Allah na wannan zamani ya makantarda hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda shi ke surar Allah, ya waye musu.” (2 Korinthiyawa 4:4) Kamar Hauwa’u, Shaiɗan Iblis yana ruɗin wasu ƙwarai. Wasu suna bin tafarkin Adamu da ba a ruɗe shi ba amma da son ransa ya zaɓi tafarkin rashin biyayya. (Yahuda 5, 11) Saboda haka, muhimmin abu ne Kiristoci su kasance a faɗake kuma su riƙe gaskiya sosai.
Jehovah Yana Bukatar “Bangaskiya Marar-Riya”
17. Menene dole mu yi don mu sami tagomashin Jehovah?
17 Domin yana da gaskiya a dukan hanyoyinsa, Jehovah yana bukatar dukan waɗanda suke bauta masa su kasance da gaskiya su ma. Mai Zabura ya rubuta: “Ya Ubangiji, wa za ya sauka cikin [tanti] naka? Wanene za ya zauna cikin tudunka mai-tsarki? Shi wanda ke tafiya sosai, yana aika adalci, yana kuwa faɗin gaskiya cikin zuciyarsa.” (Zabura 15:1, 2) Ambata tudu mai tsarki na Jehovah babu shakka ya tunasar da Yahudawa da suka rera kalmomin nan, Dutsen Sihiyona, inda Sarki Dauda ya kawo sunduƙin alkawari zuwa mazauni da ya gina a wurin. (2 Samu’ila 6:12, 17) Dutsen da tanti suna sa a tuna da waje na alama da Jehovah yake zama. A wurin mutane suna iya zuwan wurin Allah domin su roƙi tagomashinsa.
18. (a) Menene abota da Allah yake bukata? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
18 Duk wanda yake son abotar Jehovah dole ya faɗi gaskiya “daga zuciya,” ba bisa leɓa kawai ba. Abokan gaske na Allah dole su yi gaskiya daga zuci kuma su tabbatar “bangaskiya marar-riya” ce, domin ayyukan gaskiya daga zuciya ce. (1 Timothawus 1:5; Matta 12:34, 35) Abokin Allah ba ya zamba ko kuma ruɗu ba, domin “Ubangiji yana ƙyamar mutum . . . mai-algus.” (Zabura 5:6) A dukan duniya, Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su yi gaskiya a yin koyi da Allahnsu. Talifi na gaba zai bincika wannan batun.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa Jehovah ya san gaskiya game da kome?
• Me ya nuna cewa Jehovah yana gaskiya?
• Ta yaya ne Jehovah ya bayyana gaskiya?
• Game da batun gaskiya, me ake bukata a gare mu?
[Hotuna a shafi na 20]
Allah na gaskiya ya san kome game da abin da ya halitta
[Hotuna a shafi na 22, 23]
Alkawuran Jehovah za su cika