Yadda Yesu Ya Ɗaukaka Adalcin Allah
“Allah ya ayana [Kristi] abin fansa ne, ta wurin bangaskiya, bisa ga jininsa, domin a bayyana adalcinsa.”—ROM. 3:25.
1, 2. (a) Menene Littafi Mai Tsarki ya koya mana game da yanayin ’yan Adam? (b) Waɗanne tambayoyi ne wannan talifin zai bincika?
LABARIN tawaye a lambun Adnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki sananne ne sosai. Sakamakon zunubin Adamu yana shafan dukanmu kamar yadda aka bayyana a waɗannan kalaman: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Rom. 5:12) Duk da yadda muke ƙoƙari mu yi abin da yake da kyau, mukan yi kuskure, kuma don hakan muna bukatan gafarar Allah. Har ma manzo Bulus ya furta baƙin cikinsa: “Nagarta da na ke so in yi, ba na aikawa ba: amma mugunta da ba na so ba, ita na ke aikawa. Kaitona, ga ni mutum, abin tausai.”—Rom. 7:19, 24.
2 Tun da yake dukanmu masu zunubi ne, yana da kyau mu yi waɗannan tambayoyi masu muhimmanci: Yaya ya yiwu aka haifi Yesu Banazare ba tare da zunubi ba, kuma me ya sa aka yi masa baftisma? Ta yaya tafarkin rayuwar Yesu ya ɗaukaka adalcin Jehobah? Mafi muhimmanci, menene mutuwar Kristi ta cim ma?
An Ƙalubalanci Adalcin Allah?
3. Ta yaya Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u?
3 Iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u, da wawanci sun ƙi ikon mallakar Allah, domin sun fi son “tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan,” ya zama sarkinsu. (R. Yoh. 12:9) Ka yi la’akari da yadda hakan ya faru. Shaiɗan ya ƙalubalanci adalcin yadda Jehobah Allah yake sarauta. Ya yi hakan ta wajen tambayar Hauwa’u: “Ashe, ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” Hauwa’u ta maimaita umurnin Allah cewa ba za su taɓa wani itace ba, idan suka yi hakan za su mutu. Shaiɗan ya zargi Allah cewa yana ƙarya. “Ba lallai za ku mutu ba,” in ji Iblis. Ya ruɗi Hauwa’u ta gaskata cewa Allah yana hana su wani abu mai kyau ne kuma idan ta ci ’ya’yan itacen, za ta zama kamar Allah, za ta yi duk abin da take so.—Far. 3:1-5.
4. Yaya ’yan Adam suka shiga ƙarƙashin sarautar Shaiɗan?
4 Hakika, Shaiɗan yana nufin cewa ’yan Adam za su fi farin ciki idan suka samu ’yanci daga wurin Allah. Maimakon ya ɗaukaka adalcin ikon mallakar Allah, Adamu ya saurari matarsa kuma suka ci ’ya’yan itacen da aka hana su ci. Da hakan, Adamu ya yi rashin dangantakarsa da Jehobah kuma ya saka mu a ƙarƙashin wahalar zunubi da mutuwa. Hakazalika, ’yan Adam sun kasance a ƙarƙashin sarautar Shaiɗan, “allah na wannan zamani.”—2 Kor. 4:4; Rom. 7:14.
5. (a) Yaya Jehobah ya cika maganarsa? (b) Wane bege ne Allah ya ba zuriyar Adamu da Hauwa’u?
5 Kamar yadda ya faɗa, Jehobah ya yanke hukuncin mutuwa a kan Adamu da Hauwa’u. (Far. 3:16-19) Amma hakan ba ya nufin cewa nufin Allah ba zai cika ba. Akasin haka, sa’ad da yake yanke hukunci a kan Adamu da Hauwa’u, Jehobah ya ba zuriyarsu ta nan gaba dalilin kasancewa da bege. Ya yi hakan ta wajen sanar da nufinsa na ta da “zuriya” wanda Shaiɗan zai ƙuje duddugensa. Amma, wannan Zuriya da aka yi alkawarinsa zai warke daga wannan raunin kuma zai “ƙuje kan [Shaiɗan].” (Far. 3:15) Littafi Mai Tsarki ya bayyana wannan batun sosai ta wajen faɗin kalaman da ke gaba game da Yesu Kristi: “Dalilin bayyanuwar Ɗan Allah ke nan, ya halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yoh. 3:8) Amma yaya halin Yesu da mutuwarsa suka ɗaukaka adalcin Allah?
Ma’anar Baftismar Yesu
6. Yaya muka sani cewa Yesu bai gāji zunubi daga Adamu ba?
6 Sa’ad da ya zama mutum, Yesu zai yi daidai da Adamu sa’ad da yake kamiltacce. (Rom. 5:14; 1 Kor. 15:45) Hakan yana nufin cewa za a haifi Yesu kamiltacce. Yaya hakan zai yiwu? Mala’ika Jibra’ilu ya ba da wannan bayanin da ya fita sarai ga Maryamu, mahaifiyar Yesu: “Ruhu mai-tsarki za ya auko miki, ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantadda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.” (Luk 1:35) A farkon rayuwar Yesu, babu shakka, Maryamu ta gaya wa Yesu wasu abubuwa game da haihuwarsa. Saboda haka, a lokacin da Maryamu da uban Yesu na duniya, Yusufu, suka same Yesu a haikalin Allah, yaron ya tambaye su: “Ba ku san ba wajib ne a gareni in yi aikin sha’anin Ubana ba.” (Luk 2:49) Tun yana ƙarami, Yesu ya san cewa shi Ɗan Allah ne. Saboda haka, ɗaukaka adalcin Allah yana da muhimmanci sosai a gare shi.
7. Waɗanne abubuwa masu tamani ne Yesu yake da su?
7 Yesu ya nuna yana son abubuwa na ruhaniya sosai ta wajen halartar taro na bauta a kai a kai. Domin shi kamili ne, ya fahimci dukan abubuwan da ya ji kuma ya karanta a cikin Nassosin Ibrananci. (Luk 4:16) Yana da wani abu kuma mai tamani, wato, kamiltaccen jiki da za a iya ba da hadayarsa domin ’yan Adam. Sa’ad da aka yi masa baftisma, Yesu yana addu’a kuma wataƙila yana tunani game da kalaman annabci na Zabura 40:6-8.—Luka 3:21; karanta Ibraniyawa 10:5-10.a
8. Me ya sa Yohanna mai Baftisma ya yi ƙoƙarin ya hana Yesu yin baftisma?
8 A dā, Yohanna mai baftisma ya so ya hana Yesu yin baftisma. Me ya sa? Domin Yohanna yana yi wa Yahudawa baftisma don su nuna alamar tubansu daga zunubi bisa Dokar. A matsayin dangi na kusa, Yohanna ya san cewa Yesu adali ne saboda haka ba ya bukatan tuba. Yesu ya tabbatar wa Yohanna cewa ya dace ya yi baftisma. “Gama haka,” Yesu ya bayyana, “ya dace a garemu mu cika adalci duka.”—Mat. 3:15.
9. Baftismar Yesu alamar menene?
9 A matsayin kamiltacce, da Yesu ya kammala cewa kamar Adamu, yana iya zama uba ga kamiltattun mutane. Amma, Yesu bai taɓa sha’awar wannan ba domin hakan ba nufin Jehobah ba ne a gare shi. Allah ya aiko Yesu zuwa duniya don ya cika hakkin Zuriya da aka yi alkawarinsa, ko kuma Almasihu. Hakan ya ƙunshi Yesu ya yi hadaya da kamiltaccen ransa. (Karanta Ishaya 53:5, 6, 12.) Hakika, baftismar Yesu ba ɗaya ba ce da ta mu. Ba ta nufin keɓe kai ga Jehobah, domin Yesu ya riga yana cikin sashen keɓaɓɓiyar al’ummar Isra’ila ta Allah. Maimakon haka, baftismar Yesu alamar miƙa kansa ne ga yin nufin Allah kamar yadda aka annabta a cikin Nassosi game da Almasihu.
10. Menene yin nufin Allah a matsayin Almasihu ya ƙunsa, yaya Yesu ya ji game da hakan?
10 Nufin Jehobah ga Yesu ya ƙunshi yin wa’azin bisharar Mulkin Allah, almajirantarwa, da kuma shirya su don aikin almajirantarwa a nan gaba. Miƙa kai da Yesu ya yi ya kuma ƙunshi amincewa ya jimre tsanantawa da mutuwa ta zalunci don ya tallafa wa ikon mallaka na adalci na Jehobah Allah. Domin Yesu yana ƙaunar Ubansa na samaniya da gaske, ya yi farin cikin yin nufin Allah kuma ya samu gamsuwa sosai ya miƙa jikinsa don hadaya. (Yoh. 14:31) Yana kuma farin cikin sanin cewa za a iya miƙa amfanin kamiltaccen ransa ga Allah a matsayin fansa don a cece mu daga bauta ga zunubi da mutuwa. Allah ya amince da yadda Yesu ya miƙa kansa don ya ɗauki wannan hakki mai girma kuwa? Ƙwarai kuwa!
11. Yaya Jehobah ya nuna amincewarsa da Yesu a matsayin Almasihu ko Kristi da aka yi alkawarinsa?
11 Dukan marubutan Linjila huɗu sun ba da shaidar furcin amincewa na Jehobah Allah sa’ad da Yesu ya fito daga cikin ruwan Kogin Urdun. Yohanna mai Baftisma ya ba da shaida: “Na ga ruhu yana saukowa da kamar kurciya daga cikin sama, ya zauna a kansa [Yesu] . . . Ni ma na gani, na kuwa shaida, wannan Ɗan Allah ne.” (Yoh. 1:32-34) Bugu da ƙari, a wannan lokacin Jehobah ya sanar: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.”—Mat. 3:17; Mar. 1:11; Luk 3:22.
Ya Kasance da Aminci Har Mutuwa
12. Menene Yesu ya yi cikin shekara uku da rabi da yin baftismarsa?
12 A cikin shekara uku da rabi, Yesu ya ba da kansa wajen koya wa mutane game da Ubansa da kuma adalcin ikon mallakar Allah. Ko da yake yin tafiya a dukan Ƙasar Alkawari da ƙafa ya gajiyar da shi, amma babu abin da ya hana shi ba da shaida sosai game da gaskiya. (Yoh. 4:6, 34; 18:37) Yesu ya koya wa mutane game da Mulkin Allah. Ta wajen warkar da masu ciwo, ciyar da taron jama’a masu jin yunwa, da kuma ta da matattu ta hanyar mu’ujiza, ya nuna abin da Mulkin zai cim ma ga ’yan Adam.—Mat. 11:4, 5.
13. Menene Yesu ya koyar game da addu’a?
13 Maimakon ya karɓi yabon koyarwarsa da kuma ayyukan warkarwa, Yesu ya kafa misali na musamman ta wajen mai da dukan yabo ga Jehobah cikin tawali’u. (Yoh. 5:19; 11:41-44) Yesu ya kuma sanar da batutuwan da suka fi muhimmanci da ya kamata mu yi addu’a a kansu. Ya kamata addu’o’inmu su haɗa da roƙon cewa a “tsarkake” sunan Allah, Jehobah, kuma ikon mallaka na adalci na Allah ya sauya muguwar sarautar Shaiɗan domin “abin da [yake] so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Mat. 6:9, 10) Yesu ya kuma aririce mu mu yi abubuwa da suka jitu da irin waɗannan addu’o’in ta wajen ‘fara biɗan mulkin [Allah], da adalcinsa.’—Mat. 6:33.
14. Ko da yake Yesu kamili ne, me ya sa yake bukatan dagewa don ya cika hakkinsa a nufin Allah?
14 Yayin da lokacin mutuwarsa ta hadaya ta kusa, Yesu ya san cewa yana da hakki mai girma a kansa. Cika nufin Ubansa da kuma kāre sunansa ya dangana ne da jimre gwajin da bai dace ba da Yesu zai yi kuma ya yi mutuwa ta wulakanci. Kwana biyar kafin mutuwarsa, Yesu ya yi addu’a: “Yanzu raina yana wahala; me zan ce kuma? Ya Uba ka cece ni daga cikin lokacin nan? Amma saboda wannan na zo cikin lokacin nan.” Bayan ya furta yadda yake ji, ba tare da son kai ba Yesu ya mai da hankalinsa ga batun da ya fi muhimmanci kuma ya yi addu’a: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Jehobah ya amsa nan da nan: “Na rigaya na ɗaukaka shi, kuma ni sake ɗaukaka shi.” (Yoh. 12:27, 28) Hakika, Yesu yana shirye ya fuskanci gwaji mafi girma na aminci da babu ɗan Adam da ya taɓa fuskanta. Babu shakka jin waɗannan kalamai na Ubansa na samaniya ya ba Yesu tabbaci mai girma cewa zai yi nasara wajen ɗaukaka da ƙunita ikon mallakar Jehobah. Kuma ya yi nasara!
Abin da Mutuwar Yesu ta Cim Ma
15. Kafin ya mutu, me ya sa Yesu ya ce: “An gama”?
15 Yayin da Yesu yake kan gungumen azaba kuma zai ja numfashinsa na ƙarshe, ya ce: “An gama!” (Yoh. 19:30) Waɗannan abubuwa masu girma ne Yesu ya cim ma da taimakon Allah a cikin shekaru uku da rabi tun daga baftismarsa har mutuwarsa! Sa’ad da Yesu ya mutu, an yi mugun girgizar ƙasa, hakan ya motsa jarumin Roma da ya kula da kisan ya ce: “Hakika wannan Ɗan Allah ne.” (Mat 27:54) Wataƙila wannan jarumin ya ga yadda aka yi wa Yesu ba’a don yana da’awar shi Ɗan Allah ne. Duk da wahalar da ya sha, Yesu ya kasance da aminci kuma ya nuna cewa Shaiɗan mugun maƙaryaci ne. Game da dukan waɗanda suka goyi bayan ikon mallakar Allah, Shaiɗan ya ce: “Dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayu. 2:4) Ta wurin amincinsa, Yesu ya nuna cewa Adamu da Hauwa’u za su iya kasancewa da aminci a gwaji mafi sauƙi da suka fuskanta. Mafi muhimmanci, rayuwar Yesu da mutuwarsa sun ɗaukaka da kuma girmama adalcin ikon mallakar Jehobah. (Karanta Misalai 27:11.) Mutuwar Yesu ta cim ma wani abu kuma? Ƙwarai kuwa!
16, 17. (a) Me ya sa ya yiwu shaidun Jehobah kafin lokacin Kiristanci suka kasance da matsayi na adalci a gabansa? (b) Yaya Jehobah ya saka wa Ɗansa don amincinsa, kuma menene Ubangiji Yesu Kristi ya ci gaba da yi?
16 Bayin Jehobah da yawa sun rayu kafin Yesu ya zo duniya. Sun more matsayi na adalci a gaban Allah kuma an ba su begen tashin matattu. (Isha. 25:8; Dan. 12:13) Amma bisa menene Allah mai tsarki Jehobah, zai albarkaci ’yan Adam masu zunubi a wannan hanya mai ban al’ajabi? Littafi Mai Tsarki ya bayyana: “Allah ya ayyana [Yesu Kristi] abin fansa ne, ta wurin bangaskiya, bisa ga jininsa, domin a bayyana adalcinsa, inda ya bar lura da zunubai marigaya cikin jimrewar Allah; domin bayyanuwar adalcinsa a cikin zamani na yanzu: domin shi da kansa shi barata, ya kuma baratar da wanda yake da bangaskiya cikin Yesu.”—Rom. 3:25, 26.b
17 Jehobah ya saka wa Yesu da tashin matattu zuwa ga matsayin da ya fi wanda yake da shi kafin ya zo duniya. Yanzu Yesu yana more rayuwa da ba a mutuwa a matsayin halittar ruhu mai ɗaukaka. (Ibran. 1:3) A matsayin Babban Firist da Sarki, Ubangiji Yesu Kristi yana ci gaba da taimaka wa mabiyansa su ɗaukaka adalcin Allah. Kuma muna godiya cewa Ubanmu na samaniya, Jehobah, Mai sakayya ne ga dukan waɗanda suka yi hakan kuma suke bauta masa da aminci ta wajen yin koyi da Ɗansa!—Karanta Zabura 34:3; Ibraniyawa 11:6.
18. Za a mai da hankali a kan menene a talifi na gaba?
18 Mutane masu aminci tun daga lokacin Habila sun more dangantaka na kud da kud da Jehobah domin sun ba da gaskiya kuma suna da tabbaci a Zuriya da aka yi alkawarinsa. Jehobah ya san cewa Ɗansa zai kasance da aminci kuma mutuwarsa za ta ɗauke “zunubin duniya.” (Yoh. 1:29) Mutuwar Yesu ta kuma amfane mutanen da suke rayuwa a yau. (Rom. 3:26) Saboda haka, wane albarka ne fansa na Kristi zai kawo maka? Wannan shi ne batun da za mu tattauna a talifi na gaba.
[Hasiya]
a A nan manzo Bulus ya yi ƙaulin Zabura 40:6-8 bisa fassarar Septuagint na Helenanci, wanda ya ƙunshi kalaman nan “ka shirya mani jiki.” Wannan furcin ba ya cikin rubuce-rubucen Nassosin Ibrananci na dā.
b Ka duba “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a shafuffuka na 6 da 7.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya aka ƙalubanci adalcin Allah?
• Baftismar Yesu tana nuna alamar menene?
• Menene mutuwar Yesu ta cim ma?
[Hoton da ke shafi na 9]
Ka san abin da baftismar Yesu take nuna alamarsa?