Bari Ikilisiya Ta Ingantu
“Ikilisiya fa ta sami salama, tana ginuwa.”—AYUKAN MANZANNI 9:31.
1. Waɗanne tambayoyi ne za a iya yi game da “ikilisiya ta Allah”?
A RANAR Fentakos ta shekara ta 33 A.Z., Jehobah ya karɓi rukunin mabiyan Kristi a matsayin sabuwar al’umma, wato “isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Waɗannan Kiristoci da aka shafa da ruhu sun zama abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “ikilisiya ta Allah.” (1 Korinthiyawa 11:22) Menene wannan ya ƙunsa? Ta yaya ne za a tsara “ikilisiya ta Allah”? Ta yaya ne za ta yi aiki a duniya a duk inda waɗanda ke cikinta suke da zama? Kuma ta yaya ne hakan ya shafi rayuwarmu da kuma farin cikinmu?
2, 3. Ta yaya ne Yesu ya nuna cewa ikilisiya za ta kasance da tsari?
2 Kamar yadda muka tattauna a talifi na baya, Yesu ya annabta wanzuwar wannan ikilisiyar ta shafaffun mabiyansa, sa’ad da ya gaya wa Bitrus: “A kan wannan dutse [Yesu Kristi] kuma zan gina ikilisiyata; ƙyamaren Hades kuma ba za su rinjaye ta ba.” (Matta 16:18) Bugu da ƙari, sa’ad da Yesu yake tare da manzanninsa, ya ba su umurni game da yadda abubuwa za su kasance da yadda za a tsara ikilisiyar da za a kafa nan ba da daɗewa ba.
3 Yesu ya koyar ta kalami da kuma ayyuka cewa wasu za su yi ja-gora a cikin ikilisiya. Za su yi haka ne ta wajen yin hidima ga waɗanda suke rukuninsu. Kristi ya ce: “Kun sani su waɗanda an sanya su su mallaki Al’ummai su kan nuna masu sarauta; manyansu kuma suna gwada masu iko. Amma ba haka ya ke a cikinku ba: amma dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, baranku za ya zama: kuma wanda ya ke so shi zama nafari a cikinku, bawan duka za ya zama.” (Markus 10:42-44) Babu shakka, “ikilisiya ta Allah” ba za ta zama mutane ɗaɗɗaya da suka watsu a ko’ina ba, wanda hakan zai iya jawo ikilisiya marar tsari. Maimakon haka, za a kasance da tsari, inda mutane za su dinga aiki da tattaunawa tare a cikin ikilisiya.
4, 5. Ta yaya ne muka sani cewa ikilisiya za ta bukaci umurni na ruhaniya?
4 Wanda shi ne zai kasance Shugaban wannan “ikilisiya ta Allah” ya nuna cewa manzanninsa da kuma wasu da suka yi koyi a wurinsa za su kasance da hakki a ikilisiya. Menene za su yi? Aiki mafi muhimmanci da za su yi shi ne su ba da umurni na ruhaniya ga waɗanda suke cikin ikilisiya. Ka tuna cewa Yesu da aka ta da daga matattu, a gaban wasu manzanni ya gaya wa Bitrus: “Siman, ɗan Yohanna, ka fi waɗannan ƙamnata?” Bitrus ya ce: “I, Ubangiji; ka sani ina sonka.” Yesu ya ce masa: “Ka yi kiwon ’ya’yan tumakina. . . . Ka zama makiyayin tumakina. . . . Ka yi kiwon ’yan tumakina.” (Yohanna 21:15-17) Wannan aiki ne mai muhimmanci sosai!
5 Daga kalaman da Yesu ya yi, mun ga cewa an kwatanta waɗanda aka tattara zuwa cikin ikilisiya da tumakin da ke cikin garke. Waɗannan tumakin, Kiristoci maza da mata da yara ƙanana, suna bukatar a ciyar da su a ruhaniyance kuma a kula da su sosai. Bugu da ƙari, tun da Yesu ya umurce duka mabiyansa su koyar da wasu kuma su almajirtar, duka mutanen da suke son su zama tumakinsa suna bukatar a koyar da su game da yadda za su tafiyar da wannan hurarren aiki.—Matta 28:19, 20.
6. Waɗanne tsare-tsare ne aka yi a sabuwar “ikilisiya ta Allah” da aka kafa?
6 Sa’ad da aka kafa “ikilisiya ta Allah,” waɗanda suke cikinta suna taruwa a kai a kai domin su yi koyi kuma su ƙarfafa juna: “Suka lizima a cikin koyarwar manzanni da zumunta da kakkaryawar gurasa da addu’o’i.” (Ayukan Manzanni 2:42, 46, 47) Wani batu kuma da Littafi Mai Tsarki ya nuna shi ne, an zaɓi wasu maza da suka ƙware su taimaka wajen kula da wasu batutuwa. Ba wai an zaɓe su ba ne domin yawan iliminsu, ko kuwa domin ƙwarewarsu a wasu ayyuka ba. Waɗannan maza ne “cike da Ruhu Mai-tsarki da hikima.” Ɗaya daga cikinsu shi ne Istifanus, kuma labarin ya nanata cewa shi “mutum [ne] cike da bangaskiya da Ruhu Mai-tsarki.” Wani sakamako na wannan tsari da aka kafa a cikin ikilisiya shi ne “maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai.”—Ayukan Manzanni 6:1-7.
Maza da Allah Ya Yi Amfani da Su
7, 8. (a) Menene matsayin manzanni da dattawa da ke Urushalima a tsakanin Kiristoci na farko? (b) Wane sakamako ne aka samu sa’ad da aka ba ikilisiyoyi umurni?
7 Babu shakka, manzannin ne suka yi ja-gora a tsarin ikilisiya na farko, amma ba su kaɗai ba ne ke ɗauke da wannan hakkin ba. Akwai lokacin da Bulus da abokansa suka koma Suriya ta Antakiya. Ayukan Manzanni 14:27 ta ce: “Sa’anda suka zo, har suka tattara ikilisiya wuri ɗaya, suka rattaba dukan abin da Allah ya yi a wurinsu.” Sa’ad da suke tare da wannan ikilisiyar, wata tambaya ta taso ko ya kamata ’yan Al’ummai da suka zama masu bi su yi kaciya. Don a magance wannan batun, an aika Bulus da Barnaba zuwa “Urushalima wurin manzanni da dattiɓai,” waɗanda su ne hukumar mulki.—Ayukan Manzanni 15:1-3.
8 Yakubu wanda Kirista ne dattijo, ɗan uban Yesu amma ba manzo ba ne, shi ne ya ja-goranci taron sa’ad da “manzanni da dattiɓai suka tattaru garin su duba wannan al’amari.” (Ayukan Manzanni 15:6) Bayan sun yi mahawara kuma da taimakon ruhu mai tsarki, sun yanke shawarar da ta jitu da Nassosi. Sai suka aika shawarar ta wasiƙa ga duka ikilisiyoyin. (Ayukan Manzanni 15:22-32) Waɗanda suka sami wannan bayanin sun yi na’am da ita kuma sun bi abin da aka ce. Menene sakamakon? An inganta ’yan’uwan kuma an ƙarfafa su. Littafi Mai Tsarki ya ba da rahoto cewa: “Ikilisiyai fa suka ƙarfafa cikin imani, yawansu yana ƙaruwa kowace rana.”—Ayukan Manzanni 16:5.
9. Waɗanne hakkoki ne Littafi Mai Tsarki ya tsara wa maza Kiristoci da suka ƙware?
9 Amma ta yaya ne za a tafiyar da ikilisiyoyin a kowane lokaci? Bari mu yi la’akari da misalin ikilisiyoyin da ke tsibirin Karita. Ko da yake yawancin mutanen da ke zaune a wurin ba su da hali mai kyau, waɗansu a cikinsu sun yi canji kuma sun zama Kiristoci na gaskiya. (Titus 1:10-12; 2:2, 3) Suna zaune ne a birane dabam dabam, kuma inda suke yana da nisa daga inda hukumar mulki take a Urushalima. Amma, wannan ba babbar matsala ba ce, domin an naɗa “dattiɓai” na ruhaniya a duka ikilisiyoyin da ke Karita, kamar yadda aka yi a sauran wurare. Waɗannan maza sun cika ƙwarewar da ake bukata da ke cikin Littafi Mai Tsarki. An naɗa su su zama dattawa, ko masu kula waɗanda za su iya “yin gargaɗi da sahihiyar koyarwa, [su] kuwa rinjayi masu-jayayya.” (Titus 1:5-9; 1 Timothawus 3:1-7) Wasu mazan na ruhaniya sun ƙware su taimaka wa ikilisiyoyi a matsayin bayi masu hidima.—1 Timothawus 3:8-10, 12, 13.
10. In ji Matta 18:15-17, ta yaya ne za a magance manyan matsaloli?
10 Yesu ya nuna cewa za a yi irin wannan tsarin. Ka tuna labarin da ke Matta 18:15-17, inda Yesu ya faɗi cewa a wasu lokatai rashin fahimta na iya faruwa tsakanin bayi biyu na Allah, sa’ad da ɗaya ya yi wa ɗayan laifi. Wanda aka yi wa laifin zai je ya sami wanda ya yi masa laifi ya “nuna masa laifinsa,” tsakanin su biyu kawai. Idan hakan bai magance matsalar ba, ana iya kiran mutum ɗaya ko biyu da suka san batun sosai su taimaka. Idan aka kasa magance matsalar fa? Yesu ya ce: ‘Idan kuwa ya ƙi jin waɗannan, ka faɗa ma ikilisiya: idan ya ƙi jin ikilisiya kuma, shi zama maka kamar Ba’al’ummi ko mai-karɓan haraji.’ A lokacin da Yesu ya yi wannan kalamin, Yahudawa ne “ikilisiya ta Allah,” saboda haka, kalamansa na nuni ne ga Yahudawa na lokacin.a Amma, sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, za a yi amfani ne da abin da Yesu ya ce a cikinta. Wannan wata alama ce da ta nuna cewa mutanen Allah za su kasance da tsari na ikilisiya don ƙarfafa da kuma yin ja-gora ga kowane Kirista.
11. Wane hakki ne dattawa suke cikawa wajen magance matsaloli?
11 Dattawa ko masu kula ne za su wakilci ikilisiya wajen magance matsaloli ko batutuwa na zunubi. Wannan ya jitu da ƙwarewar dattawa da aka ambata a Titus 1:9. Babu shakka, dattawan ajizai ne kamar Titus, wanda Bulus ya aika ga ikilisiyoyi domin ya “daidaita al’amuran da suka tauye.” (Titus 1:4, 5) A yau, waɗanda aka gabatar don su zama dattawa suna bukatar su bayyana bangaskiyarsu da ba da kai na wani ɗan lokaci kafin a naɗa su. Waɗanda suke cikin ikilisiya suna bukatar su amince da ja-gora da kuma shugabancin da aka yi tanadinsa ta wannan tsarin.
12. Wane hakki ne dattawa suke da shi a ikilisiya?
12 Ga dattawan da ke ikilisiyar Afisa, Bulus ya ce: “Ku tsare kanku, da dukan garke kuma, wanda Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki, garin ku yi kiwon ikilisiyar Allah, wadda ya sayi da jinin kansa.” (Ayukan Manzanni 20:28) Hakika, a yau ma ana naɗa masu kula da ke cikin ikilisiya su “yi kiwon ikilisiyar Allah.” Za su yi haka ne cikin ƙauna, ba wai su nuna sarauta bisa tumakin ba. (1 Bitrus 5:2, 3) Masu kula za su yi iya ƙoƙarinsu su ƙarfafa da kuma taimaka wa “dukan garke.”
Manne wa Ikilisiya
13. A wasu lokatai, menene zai iya faruwa a cikin ikilisiya, kuma me ya sa?
13 Dattawa da duka waɗanda suke cikin ikilisiya ajizai ne, saboda haka, a lokaci lokaci, rashin fahimta ko matsaloli za su faru, kamar yadda ya faru a ƙarni na farko sa’ad da wasu a cikin manzannin suke raye. (Filibbiyawa 4:2, 3) Mai kula ko wani mutum na iya faɗin wani abu da ba shi da daɗin ji, ko ya yi baƙar magana, ko ya faɗi abin da ba cikakkiyar gaskiya ba ce. Ko kuwa muna iya tunanin cewa wani abu da ba bisa nassi ba yana faruwa, kuma kamar dai dattawa sun san da batun, amma sun ƙi su magance matsalar. Amma, wataƙila an magance matsalar ko kuwa ana cikin magance ta bisa ga Nassosi wanda ƙila ba mu san da haka ba. Ko da yanayin ya faru kamar yadda muke tunani, ka yi la’akari da wannan: An yi wani mugun zunubi a cikin ikilisiyar Koranti na wani ɗan lokaci, kuma wannan ikilisiya ce da Jehobah yake kula da ita. Bayan wani lokaci, Jehobah ya sa an magance zunubin yadda ya kamata. (1 Korinthiyawa 5:1, 5, 9-11) Muna iya tambayar kanmu, ‘Da ina zaune a Koranti a wannan lokacin, wane irin mataki ne zan ɗauka?’
14, 15. Me ya sa wasu suka daina bin Yesu, kuma wane darassi ne wannan ya koya mana?
14 Ka yi la’akari da wani abu kuma da zai iya faruwa a cikin ikilisiya. A ce ya yi wa wani wuya ya fahimci kuma ya yi na’am da koyarwa na Nassi. Wataƙila ya yi bincike a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ya samu ta hanyar ikilisiya, kuma ya nemi taimako daga Kiristocin da suka ƙware, har da dattawa. Duk da haka, ya yi masa wuya ya fahimci ko ya karɓi bayanin. Menene zai iya yi? Wani abu makamancin wannan ya faru kusan shekara ɗaya kafin Yesu ya mutu. Ya ce shi ne “gurasa ta rai” kuma idan mutum yana son ya sami rai ta har abada, yana bukatar ya ‘ci namansa, ya sha jininsa.’ Hakan ya ba wasu daga cikin almajiransa haushi. Maimakon su nemi ma’anar ko kuma su jira cikin bangaskiya, yawancin almajiran “ba su ƙara tafiya tare da [Yesu] ba.” (Yohanna 6:35, 41-66) Da a ce muna wurin, da menene za mu yi?
15 A zamaninmu, wasu sun daina tarayya da ikilisiya, suna ganin cewa za su iya bauta wa Allah su kaɗai kawai. Suna iya cewa sun yi haka ne domin an yi musu laifi, ko ba a magance wani laifi da aka yi ba, ko kuwa sun kasa yin na’am da wasu koyarwa. Wannan tafarkin ya yi daidai? Ko da yake ya dace kowane Kirista ya kasance da dangantaka mai kyau da Allah, ba za mu iya ƙaryata cewa Allah yana amfani da duka ikilisiyoyin da ke duniya ba, kamar yadda ya yi a zamanin manzanni. Bugu da ƙari, Jehobah ya yi amfani kuma ya albarkaci ikilisiyoyi a ƙarni na farko, kuma ya yi tanadin dattawa da bayi masu hidima da suka ƙware su amfane ikilisiyoyin. Haka yake a yau.
16. Idan mutum yana son ya bar ikilisiya, menene ya kamata ya yi tunani a kai?
16 Idan Kirista ya ji cewa yana iya dogara da dangantakarsa da Allah ba tare da yin tarayya da ikilisiya ba, yana bijirewa ne daga tsarin Allah, wato duka ikilisiyoyi na duniya na mutanen Allah. Mutumin yana iya soma bauta wa Allah shi kaɗai ko kuwa ya ɗan taru da wasu ’yan ƙalilan, to idan haka ne, menene amfanin tanadin da aka yi na dattawa da bayi masu hidima na ikilisiya? Sa’ad da Bulus ya yi wa ikilisiyar da ke Kolosi wasiƙa kuma ya ba da umurni cewa a karanta ta a Lawudikiya, ya faɗi cewa su “dasassu, ginannu kuma cikin [Kristi ne].” Waɗanda suke cikin ikilisiyoyi, ba waɗanda suka ware kansu daga cikinta ba ne za su amfana daga wannan.—Kolossiyawa 2:6, 7; 4:16.
Jigon Gaskiya da Ƙarfinta
17. Menene 1 Timothawus 3:15 ta koya mana game da ikilisiya?
17 A wasiƙarsa ta farko ga Timoti wanda dattijo ne na Kirista, manzo Bulus ya bayyana abubuwan da ake bukata daga dattawa da kuma bayi masu hidima a ikilisiyoyi. Bayan haka, Bulus ya ambata “ikilisiyar Allah mai-rai,” yana cewa ita ce “jigon gaskiya da ƙarfinta.” (1 Timothawus 3:15) Duka ikilisiyoyin shafaffun Kiristoci na ƙarni na farko sun tabbatar da cewa su jigon gaskiya ne. Kuma babu shakka cewa kowane Kirista zai iya samun irin wannan gaskiya ne kawai ta hanyar ikilisiya. Domin a nan ne kawai za su iya jin koyarwar gaskiya, su kuma samu ƙarfafa.
18. Me ya sa taron ikilisiya yake da muhimmanci?
18 Hakazalika, duka ikilisiyar Kirista na duniya gidan Allah ne, “jigon gaskiya da ƙarfinta.” Idan muna halartar taro a ikilisiya a kowane lokaci kuma muna yin kalami, hakan zai sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah, mu kuma yi shirin yin nufinsa. Sa’ad da ya yi wa ikilisiyar da take Koranti wasiƙa, Bulus ya mai da hankali ne a kan abin da ake cewa a irin wannan taron. Ya rubuta cewa yana son mutane su fahimci sosai abin da ake faɗi a taronsu saboda waɗanda suka halarta su “ginu.” (1 Korinthiyawa 14:12, 17-19) Mu ma a yau za mu iya samun ƙarfafa idan muka fahimci cewa Jehobah Allah ne ya ba da umurnin tsara ikilisiyoyi kuma yana tallafa mata.
19. Me ya sa ka ji cewa kana bukatar ka nuna godiya ga ikilisiyarka?
19 Hakika, idan muna son mu sami ƙarfafa a matsayin Kirista, dole ne mu kasance a cikin ikilisiya. Ta daɗe tana kāre mu daga koyarwar ƙarya, kuma Allah yana amfani da ita ya sanar da bisharar Mulkin Almasihu a dukan duniya. Babu shakka, Allah ya cim ma abubuwa masu yawa ta hanyar ikilisiyar Kirista.—Afisawa 3:9, 10.
[Hasiya]
a Manazarcin Littafi Mai Tsarki Albert Barnes ya fahimci cewa umurnin da Yesu ya bayar na “faɗa ma ikilisiya” na iya nufin “waɗanda aka ba umurnin bincika irin wannan batun, wato, wakilan coci. A cikin majami’ar Yahudawa akwai dattawan da su ne alƙalai, waɗanda ake kawo irin wannan ƙarar a gabansu.”
Za Ka Iya Tunawa?
• Me ya sa ya kamata mu yi tunanin cewa Allah zai dinga amfani da ikilisiyoyi a duniya?
• Menene dattawa ajizai suke yi wa ikilisiya?
• Ta yaya kake samun ƙarfafa ta ikilisiya?
[Hoto a shafi na 12]
Manzanni da dattawa a Urushalima ne hukumar mulki
[Hoto a shafi na 14]
Dattawa da bayi masu hidima suna samun umurni don su cika hakkinsu na ikilisiya