-
Sakamakon Yin Wa’azi—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”Mulkin Allah Yana Sarauta!
-
-
1, 2. (a) Me ya sa almajiran Yesu suka rikice? (b) Wane irin girbi ne Yesu ya yi maganarsa?
YESU ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” Kalaman nan sun ɗan rikitar da almajiransa. Sun kalli filin da Yesu ya nuna musu, amma ba su ga gonar da ta isa girbi ba domin ba a daɗe da shuka sha’ir ba. Mai yiwuwa sun yi mamaki, ‘Wane girbi ke nan, tun da yake za a yi watanni kafin a soma girbin sha’ir?’—Yoh. 4:35.
2 Amma ba girbi na zahiri ne Yesu yake magana a kai ba. Maimakon haka, yana amfani da wannan damar ce don ya koya wa almajiransa muhimman darussa biyu game da girbi na alama, wato tattara mutane zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Waɗanne darussa ke nan? Domin mu sami amsar wannan tambayar, bari mu tattauna labarin dalla-dalla.
Gayyata don Aiki da Ke Sa Farin Ciki
3. (a) Mene ne wataƙila ya sa Yesu ya ce: “Gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi”? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) Ta yaya Yesu ya bayyana kalmominsa?
3 Yesu ya tattauna da almajiransa a ƙarshen shekara ta 30 a zamaninmu, a kusa da garin Samariyawa da ake kira Sukar. Sa’ad da almajiransa suka shiga cikin gari, Yesu ya zauna a bakin wata rijiya kuma ya yi ma wata mata wa’azi. Matar ta fahimci koyarwarsa nan da nan. Sa’ad da almajiran Yesu suka dawo, sai matar ta gaggauta zuwa garin Sukar don ta gaya wa maƙwabtanta abin al’ajabi da ta koya. A sakamakon haka, maƙwabtanta da yawa sun yi jerin gwano zuwa wurin Yesu. Wataƙila a lokacin ne Yesu ya kalli filin kuma ya hangi Samariyawa masu ɗimbin yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce: “Ku tā da idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.”a Sai ya bayyana cewa ba girbi na zahiri yake magana a kai ba, amma na alama ne. Yesu ya ce: “Mai-girbi . . . yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada.”—Yoh. 4:5-30, 36.
4. (a) Waɗanne darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika amsoshinsu?
4 Waɗanne muhimman darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? Na farko, aikin na gaggawa ne. Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun . . . yi fari, sun isa girbi,’ yana so almajiransa su ɗauki mataki. Domin Yesu ya nanata wa almajiransa gaggawar zancen, sai ya ce: “Mai girbi na samun lada.” Hakika, an riga an soma girbin kuma bai kamata a ɓata lokaci ba! Na biyu, masu girbin suna farin ciki. Yesu ya ce masu shuki da masu girbi za su “yi farin ciki tare.” (Yoh. 4:35b, 36, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda Yesu ya yi farin ciki sa’ad da ya lura cewa ‘Samariyawa da yawa sun ba da gaskiya gare shi,’ hakan ma almajiransa za su yi farin ciki yayin da suke yin girbi da zuciya ɗaya. (Yoh. 4:39-42) Wannan abin da ya faru a ƙarni na farko yana da muhimmanci sosai a yau. Me ya sa? Domin yana nuna abin da ke faruwa a yau, yayin da ake yin girbi mafi girma a tarihi. A yaushe ne aka soma wannan girbin? Su waye ne suke yin girbin? Kuma wane sakamako ake samu?
-
-
Sakamakon Yin Wa’azi—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”Mulkin Allah Yana Sarauta!
-
-
a Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun rigaya sun yi fari,’ wataƙila yana magana ne game da fararen tufafin da Samariyawan da suke zuwa wurinsa suka saka.
-