Ka Sa Hannu Sosai A Yin Babban Girbi Na Ruhaniya
“Ku yawaita cikin aikin Ubangiji.”—1 KOR. 15:58.
1. Wace gayyata ce Yesu ya yi wa almajiransa?
SA’AD da yake tafiya a yankin Samariya a ƙarshen shekara ta 30 A.Z., Yesu ya tsaya ya huta a bakin wata rijiya da ke kusa da garin Sukar. A wajen ya gaya wa almajiransa: “Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” (Yoh. 4:35) Yesu ba ya maganar girbi na zahiri, amma yana magana ne game da tattara mutane masu zuciyar kirki a ruhaniyance, waɗanda za su zama mabiyansa. A gaskiya, yana gaya wa almajiransa ne su sa hannu a wannan aikin na girbi. Da akwai aiki da yawa da za su yi kuma ɗan lokaci ne kawai suke da shi na cim ma hakan!
2, 3. (a) Menene ya nuna cewa muna rayuwa a lokacin kaka? (b) Menene wannan talifin zai tattauna?
2 Kalaman Yesu game da girbi suna da ma’ana na musamman a zamaninmu. Muna rayuwa a lokacin da filin duniya na ’yan adam ‘ya rigaya ya yi fari, ya isa girbi.’ A kowace shekara, miliyoyin mutane suna samun gayyatar koyon gaskiya mai ba da rai, kuma sababbin almajirai dubbai suna yin baftisma. Muna da gatar sa hannu a wannan girbi mafi girma a tarihi, a ƙarƙashin ja-gorancin Ubangijin girbi, Jehobah Allah. Kana “yawaita” saka hannu a wannan aikin girbin?—1 Kor. 15:58.
3 A lokacin hidimarsa na shekara uku da rabi a duniya, Yesu ya shirya almajiransa don gurbin da za su cika na masu girbi. Wannan talifin zai tattauna uku daga cikin darussa da yawa masu muhimmanci da Yesu ya koya wa almajiransa. Kowane darassi ya nanata halin da yake da amfani sosai a gare mu yayin da muke yin iya ƙoƙarinmu wajen tattara almajirai a zamani. Bari mu bincika waɗannan halaye ɗaya bayan ɗaya.
Tawali’u Yana da Muhimmanci
4. Yaya Yesu ya kwatanta muhimmancin tawali’u?
4 Ka yi tunanin wannan yanayin: Bai daɗe ba da almajiran suka yi musu game da wanda ya fi girma. Rashin jituwa da ƙiyayya ya bayyana a fuskarsu. Sai Yesu ya kira yaro ƙarami ya tsaya a tsakiyarsu. Ya mai da hankali ga ƙaramin yaron, ya ce: “Dukan wanda za ya ƙasƙantarda kansa fa kamar yaron nan, wannan shi ne mafi girma cikin mulkin sama.” (Karanta Matta 18:1-4.) Maimakon su yi tunani kamar mutanen duniya da suke kallon mutum bisa ikonsa, arzikinsa, da matsayinsa, almajiran suna bukatan su fahimta cewa girmansu ya dangana ne ga ‘ƙasƙantar da kansu’ a gaban mutane. Jehobah zai albarkace su kuma zai yi amfani da su idan suka kasance da tawali’u na gaske.
5, 6. Me ya sa kake bukatan ka zama mai tawali’u domin ka yi aikin girbi sosai? Ka ba da misali.
5 Har zuwa yau, mutane da yawa a duniya sun ba da kansu ga biɗar iko, arziki, da matsayi. Saboda haka, ba su da lokacin batutuwa na ruhaniya. (Mat. 13:22) Akasin haka, mutanen Jehobah suna farin ciki su ‘ƙasƙantar da kansu’ a gaban wasu domin su samu albarka da kuma amincewar Ubangijin girbi.—Mat. 6:24; 2 Kor. 11:7; Filib. 3:8.
6 Ka yi la’akari da misalin Francisco, wanda yake hidimar dattijo a Amirka ta Kudu. Sa’ad da yake matashi, ya daina makarantar jami’a don ya zama majagaba. “Sa’ad da nake son na yi aure,” in ji shi, “Ina da zarafin samun aikin da zai sa ni da matata mu yi kuɗi sosai. Maimakon haka, mun tsai da shawarar sauƙaƙa rayuwarmu kuma muka ci gaba a cikin hidima na cikakken lokaci. Daga baya muka samu yara, kuma ƙalubalen ya ƙaru. Amma Jehobah ya taimaka mana mu manne wa shawararmu na yin rayuwa mai sauƙi.” Francisco ya kammala: “Fiye da shekara talatin, na more gatar yin hidima a matsayin dattijo, ƙari ga ayyuka da yawa na musamman da nake yi. Ba mu taɓa yin da na sanin yin rayuwa mai sauƙi ba.”
7. Ka taɓa ƙoƙarin yin amfani da shawarar da ke Romawa 12:16? Menene sakamakon?
7 Idan ka ƙi “maɗaukakan al’amura” na wannan duniya kuma ka ƙyale ‘ƙanƙananan’ al’amura su yi maka ja-gora, kai ma za ka more ƙarin albarka da gata a aikin girbi.—Rom. 12:16; Mat. 4:19, 20; Luk 18:28-30.
Ƙwazo Yana Kawo Albarka
8, 9. (a) Ka taƙaita kwatancin Yesu na talanti. (b) Su waye musamman za su samu ƙarfafa daga wannan kwatancin?
8 Wani halin da muke bukata domin mu yi aikin girbi sosai shi ne ƙwazo. Yesu ya kwatanta wannan a cikin almarar talanti.a Kwatancin na wani mutumi ne wanda kafin ya yi tafiya zuwa ƙasar waje, ya ɗanka wa bayinsa guda uku dukiyarsa. Bawa na farko ya samu talanti biyar, na biyu ya samu talanti biyu; kuma na uku talanti guda. Bayan da ubangijinsu ya tafi, bawa na ɗaya da na biyu suka nuna ƙwazo kuma nan da nan suka “yi ciniki” da talantinsu. Amma bawa na uku “mai-ƙiwuya” ne. Ya binne talantinsa a cikin ƙasa. Da mutumin ya dawo, ya ba bawa na ɗaya da na biyu lādā ta wajen sanya su bisa aiki “mai-yawa.” Ya ƙwace talanti da ya ba bawa na uku kuma ya kore shi daga gidansa.—Mat. 25:14-30.
9 Babu shakka, kana son ka yi koyi da waɗannan bayin masu ƙwazo da ke cikin almarar Yesu kuma ka saka hannu sosai a aikin almajirantarwa. Amma idan yanayinka ya rage abin da kake yi fa? Wataƙila mugun yanayi na tattalin arziki ya tilasta maka yin aiki na dogon lokaci don ka biya bukatun iyalinka. Ko kuma tsufa ya sa ba ka da ƙarfi da koshin lafiya. Idan haka ne, almarar talanti tana ɗauke da saƙo mai ban ƙarfafa a gare ka.
10. Ta yaya ubangijin da ke cikin almarar talanti ya nuna sanin ya kamata, kuma me ya sa ka samu wannan da ban ƙarfafa?
10 Idan ka lura, za ka ga cewa ubangiji da ke cikin almarar ya san cewa kowanne cikin bayinsa yana da nasa iyawa. Ya nuna hakan sa’ad da ya ba da talanti “kowa . . . gwargwadon iyawatasa.” (Mat. 25:15) Kamar yadda za mu yi zato, bawa na farko ya yi ciniki fiye da bawa na biyu. Amma, ubangijin ya nuna amincewarsa ga ƙwazon da waɗannan bayin suka nuna ta wajen kiransu bayi ‘masu kirki masu aminci’ kuma ya ba su lada iri ɗaya. (Mat. 25:21, 23) Hakazalika, Ubangijin girbi, Jehobah Allah, ya san cewa yanayinka zai shafi abin da za ka iya yi a hidimarsa. Ba zai taɓa kawar da idanunsa daga ƙoƙarce-ƙoƙarcen da kake yi da dukan zuciyarka ba don ka bauta masa kuma zai ba ka lada yadda ya kamata.—Mar. 14:3-9; karanta Luka 21:1-4.
11. Ka ba da misalin yadda nuna ƙwazo a yanayi mai wuya zai iya kawo albarka mai yawa.
11 Misalin Selmira, wata ’yar’uwa Kirista da take da zama a Brazil, ya nuna cewa yin ƙwazo a hidimar Allah bai dangana ga kasancewa da yanayi mai kyau a rayuwa ba. Shekara ashirin da ta shige, ’yan fashi da makami sun kashe mijin Selmira, aka bar ta da kula da yara uku. Aikinta na ’yar aikin gida ya ƙunshi yin aiki na sa’o’i masu yawa da kuma yin tafiya mai gajiyarwa a motar haya da ke cike da mutane. Duk da waɗannan matsaloli, ta tsara ayyukanta domin ta yi hidima na majagaba na kullum. Biyu daga cikin yaranta uku su ma suka soma hidimar majagaba. “A cikin waɗannan shekarun, na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane fiye da ashirin kuma sun zama ‘iyalita,’” in ji ta. “Har yau, ina jin daɗin ƙauna da kuma abotarsu. Hakan wani abu ne mai tamani da kuɗi ba zai iya saya ba.” Babu shakka Ubangijin girbi ya albarkaci ƙwazon Selmira!
12. Ta yaya za mu nuna ƙwazo a aikin wa’azi?
12 Idan yanayinka yanzu a rayuwa ya rage lokacin da kake ba da wa a hidima, kana iya yin ƙoƙari ka ƙara sa hannu a aikin girbi ta wajen sa hidimarka ta ƙara ba da ’ya’ya. Sa’ad da ka yi amfani da shawarwari masu ban taimako da ake gabatarwa kowane mako a Taron Hidima, za ka kyautata yadda kake wa’azi kuma ka gwada sababbin hanyoyi na yin wa’azi. (2 Tim. 2:15) Kuma idan zai yiwu, kana iya daina ayyukan da ba su da muhimmanci ko kuma ka yi su a wani lokaci don ka riƙa tallafa wa shirin hidimar fage na ikilisiya a kai a kai.—Kol. 4:5.
13. Wane abu mai muhimmanci ne zai taimaka mana mu gina kuma mu kasance da ƙwazo?
13 Ka tuna cewa muna nuna ƙwazo ne domin ƙaunarmu da kuma godiya ga Allah. (Zab. 40:8) Bawa na uku da aka ambata a almarar Yesu yana jin tsoron ubangijinsa, kuma ya ɗauke shi a matsayin mutumin da ba za a iya gamsar da shi ba wanda bai da sanin ya kamata. Saboda haka, mutumin ya binne talantinsa maimakon ya yi amfani da shi ya ƙara dukiyar ubangijinsa. Don mu guji irin wannan sakacin, muna bukatan mu gina kuma mu kasance da dangantaka na kud da kud da Ubangijin girbi, Jehobah. Ka keɓe lokaci don ka yi nazari da bimbini game da halayensa masu kyau, kamar su ƙaunarsa, haƙuri, da jin ƙai. Ta hakan, zuciyarka za ta motsa ka ka yi iya ƙoƙarinka a hidimarsa.—Luk 6:45; Filib. 1:9-11.
“Ku Zama Masu Tsarki”
14. Wane bukata mai muhimmanci ne dole waɗanda suke son su zama masu aikin girbi za su cika?
14 Da yake ƙaulin Nassosin Ibrananci, manzo Bitrus ya faɗi nufin Allah ga bayinsa a duniya, yana cewa: “Yadda shi wanda ya kira ku mai-tsarki ne, ku kuma ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi; domin an rubuta, Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” (1 Bit. 1:15, 16; Lev. 19:2; K. Sha 18:13) Wannan furcin ya nanata cewa masu aikin girbi suna bukatan su kasance da tsabta na ɗabi’a da na ruhaniya. Muna iya cika wannan bukata mai muhimmanci ta wajen ɗaukan matakin tsabtace mu a alamance. Yaya za a yi hakan? Da taimakon kalmar gaskiya ta Allah.
15. Gaskiyar kalmar Allah tana da ikon yin menene a madadinmu?
15 An kamanta kalmar gaskiya ta Allah da ruwa da ke tsabtacewa. Alal misali, manzo Bulus ya rubuta cewa ikilisiyar shafaffun Kiristoci suna da tsabta a gaban Allah, kamar amarya mai tsarki na Kristi, wanda ya tsabtace ta da “wankin ruwa ta wurin kalman . . . ta zama mai-tsarki marar-aibi.” (Afis. 5:25-27) A dā, Yesu ya yi maganar ikon tsabtacewa ta kalmar Allah, wadda ya sanar. Da yake magana ga almajiransa, Yesu ya ce: “Yanzu ku tsarkakakku ne saboda magana da na faɗa muku.” (Yoh. 15:3) Saboda haka, gaskiyar kalmar Allah tana da ikon tsabtaccewa na ɗabi’a da na ruhaniya. Idan muka ƙyale gaskiyar Allah ta tsabtace mu a wannan hanyar ce kaɗai zai amince da bautarmu.
16. Ta yaya za mu kasance da tsabta a ruhaniya da kuma ɗabi’a?
16 Saboda haka, don mu zama masu aiki a girbin Allah, da farko za mu kawar da dukan ayyukan ƙazanta na ɗabi’a da na ruhaniya daga rayuwarmu. Hakika, domin mu cancanci ci gaba da samun gatan zama masu aikin girbi, dole ne mu ci gaba da ɗaukaka mizanan Jehobah na ɗabi’a da na ruhaniya. (Karanta 1 Bitrus 1:14-16.) Kamar yadda muke mai da hankali a koyaushe ga tsabtar jikinmu, dole ne mu miƙa kanmu ga tsabtacewa ta kalmar gaskiya na Allah. Hakan ya ƙunshi karanta Littafi Mai Tsarki da halartan taron Kirista. Yana kuma nufin yin iya ƙoƙarinmu mu yi amfani da tunasarwar da muke samu daga Allah a rayuwarmu. Yin hakan zai taimaka mana mu yaƙi halayenmu na son yin zunubi kuma mu tsayayya wa muguwar rinjaya ta wannan duniyar. (Zab. 119:9; Yaƙ. 1:21-25) Hakika yana da ban ƙarfafa mu san cewa da taimakon kalmar gaskiya ta Allah, za a iya “wanke” mu daga zunubi mai tsanani!—1 Kor. 6:9-11.
17. Domin mu kasance da tsabta, wane gargaɗi na Littafi Mai Tsarki ne ya kamata mu bi?
17 Kana amincewa da tsabtacewa na kalmar gaskiya ta Allah a rayuwarka? Alal misali, menene kake yi sa’ad da aka faɗakar da kai game da haɗarurrukan da ke tattare da lalatattun nishaɗi na wannan duniyar? (Zab. 101:3) Kana guje wa yin cuɗanya da bai dace ba da abokan makaranta da kuma abokan aiki da ba sa bin imaninka? (1 Kor. 15:33) Kana iya ƙoƙarinka don ka sha kan kasawarka da za ta iya sa ka kasance marar tsarki a gaban Jehobah? (Kol. 3:5) Kana ware kanka daga hargitsin siyasa na wannan duniya da halin kishin ƙasa da yake shafan wasanni na gasa masu yawa?—Yaƙ. 4:4.
18. Ta yaya kasancewa da tsabta a ɗabi’a da kuma ruhaniya yake taimaka mana mu zama masu girbi da ke ba da amfani?
18 Yin biyayya da aminci a waɗannan batutuwa zai kawo albarka masu yawa. Sa’ad da yake kwatanta almajiransa da rassan kuringar anab, Yesu ya ce: ‘Kowane reshe a cikina wanda bai bada ’ya’ya ba, [Ubana] yakan kawashe shi: kowane reshe kuma da ya bada ’ya’ya, yakan tsarkake shi domin ya daɗa bayasda ’ya’ya.’ (Yoh. 15:2) Yayin da kake ba da kanka ga ruwan tsabtacewa na gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, za ka ƙara ba da ’ya’ya.
Albarka a Yanzu da Kuma Nan Gaba
19. Yaya almajiran Yesu suka sami albarka a ƙoƙarinsu a matsayin masu aikin girbi?
19 An ƙarfafa almajiran Yesu masu aminci da suka yi na’am da koyarwarsa da ruhu mai tsarki a ranar Fentakos na shekara ta 33 A. Z., su zama shaidu har zuwa “iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Sun ci gaba da hidima a matsayin waɗanda suke cikin hukumar mulki, masu-wa’azi a ƙasashen waje, da kuma dattawa masu ziyara, kuma sun cika gurbi na musamman a wa’azin bishara a “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Sun sami albarka mai yawa, kuma sun sa mutane farin ciki!
20. (a) Wace albarka ce ka samu ta wurin yin girbi na ruhaniya da ƙwazo? (b) Menene ƙudurinka?
20 Hakika, ta wurin nuna tawali’u, ƙwazo, da kuma ɗaukaka mizanai masu girma na Kalmar Allah, za mu ci gaba da moran cikakken aikin girbi mai girma da ake yi a yanzu da kuma yin rayuwa mai ma’ana. Yayin da mutane da yawa suke fuskantar azaba da baƙin ciki da ke tattare da salon rayuwa na neman abin duniya da yawan biɗar nishaɗi, muna samun farin ciki na gaske da gamsuwa. (Zab. 126:6) Mafi muhimmanci shi ne, “wahalar[mu] ba banza ta ke ba cikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Ubangijin girbin, Jehobah Allah, zai albarkace mu har abada don ‘aikinmu da ƙauna wadda muka nuna ga sunansa.’—Ibran. 6:10-12.
[Hasiya]
a Almarar ta talanti ainihi tana nuni ne ga yadda Yesu ya bi da almajiransa shafaffu, amma tana ɗauke da ƙa’idodin da suka shafi dukan Kiristoci.
Ka Tuna?
Yayin da kake ƙoƙarin ka yi aikin girbi sosai . . .
• me ya sa yake da muhimmanci ka nuna tawali’u?
• ta yaya za ka gina kuma ka ci gaba da nuna ƙwazo?
• me ya sa yake da muhimmanci a kasance da tsabta a ɗabi’a da kuma ruhaniya?
[Hoton da ke shafi na 17]
Tawali’u zai taimaka mana mu yi rayuwa mai sauƙi da ta mai da hankali ga al’amuran Mulkin