Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Janairu
    • 15, 16. (a) Ka kwatanta yadda mala’ikan Jehobah ya ceci Bitrus daga kurkuku. (Ka duba hoton da ke ƙasa.) (b) Me ya sa yake da ban ƙarfafa mu yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaki Bitrus?

      15 Mene ne ya faru da Bitrus? Sa’ad da Bitrus yake barci tsakanin masu gadi biyu a kurkuku a dare na ƙarshe, wani abu mai ban mamaki ya faru da shi. (Karanta Ayyukan Manzanni 12:7-11.) Ka yi tunanin abin da ya faru, farat ɗaya, haske ya haskaka cikin kurkukun. Sai mala’ika ya tashe Bitrus da sauri, amma babu shakka, masu gadin ba su gan mala’ikan ba. Sai sarƙan da aka ɗaure hannunsa da shi suka zube! Sai mala’ikan ya fitar da Bitrus daga kurkukun, a gaban masu gadin da ke waje, kuma ta ƙyauren ƙarfen da ta buɗe musu da “kanta.” Da zara suka fita waje da fursunan sai mala’ikan ya ɓace. Bitrus kuma ya tsira!

  • Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Janairu
    • BA DA SHAIDA SOSAI DUK DA TANGARƊA

      17. Ta yaya Bulus ya kafa misali mai kyau a yin wa’azi da ƙwazo da kuma gaggawa?

      17 Ku yi la’akari da darasi na uku da za mu iya koya daga manzannin game da yin tsaro: Sun ci gaba da ba da shaida sosai duk da tangarɗa. Yin wa’azi da ƙwazo da kuma gaggawa yana da muhimmanci don yin tsaro. Manzo Bulus misali ne mai kyau a wannan batun. Ya sa ƙwazo sosai, yana tafiya mai nisa kuma yana kafa ikilisiyoyi da yawa. Ya jimre da mawuyacin yanayi, duk da haka bai yi sanyin gwiwa ba ko kuma ya daina kasancewa da azanci na gaggawa.—2 Kor. 11:23-29.

Littattafan Hausa (1987-2025)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba