Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/15 pp. 9-13
  • Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YIN TSARO DON JA-GORA GAME DA INDA ZA A YI WA’AZI
  • KA NACE DA YIN ADDU’A
  • BA DA SHAIDA SOSAI DUK DA TANGARƊA
  • Ka Ƙudurta Ba Da Shaida Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Kasance a Faɗake Domin Yin Addu’a
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • An Koyar Da Su Domin Su Yi Wa’azi Da Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Yi Ƙarfin Zuciya, Jehobah Zai Taimake Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/15 pp. 9-13

Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu

“Ku yi tsaro tare da ni.”—MAT. 26:38.

1-3. Wane kuskure ne manzannin suka yi a daren ƙarshe na Yesu a duniya, kuma mene ne ya nuna cewa sun koyi darasi daga kuskurensu?

KA YI tunanin abin da ya faru a dare na ƙarshe na rayuwar Yesu a duniya. Yesu ya isa ɗaya cikin wurare masu kyau da yake son zuwa, wato, lambun Jathsaimani, a gabashin Urushalima. Ya zo nan tare da manzanninsa masu aminci. Da yake Yesu yana da abubuwa da yawa da zai yi tunani a kansu, saboda haka, yana bukatar ya nemi wurin da zai kasance shi kaɗai don ya yi addu’a.—Mat. 26:36; Yoh. 18:1, 2.

2 Manzo Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna sun bi Yesu zuwa ciki cikin lambun. Ya gaya musu: “Ku zauna daganan, ku yi tsaro tare da ni,” sai ya tafi ya yi addu’a. Sa’ad da ya dawo, ya sami abokansa suna barci. Sai ya ƙara gaya musu: “Ku yi tsaro.” Amma, ya same su sau biyu kuma suna barci! Bayan haka, a daren nan, dukan manzannin suka kasa yin tsaro a ruhaniya. Sun ma bar Yesu kuma suka gudu!—Mat. 26:38, 41, 56.

3 Babu shakka, manzannin sun yi nadama don sun kasa yin tsaro. Waɗannan maza masu aminci sun koyi darasi daga kuskurensu. Littafin Ayyukan Manzanni ya nuna cewa sun kafa misali mafi kyau na yin tsaro. Misalinsu ya taimaka wa ’yan’uwansu Kiristoci su yi hakan. Yanzu muna bukatar mu yi tsaro fiye da dā. (Mat. 24:42) Bari mu tattauna darussa uku game da yin tsaro da za mu iya koya daga littafin Ayyukan Manzanni.

YIN TSARO DON JA-GORA GAME DA INDA ZA A YI WA’AZI

4, 5. Ta yaya ruhu mai tsarki ya ja-goranci Bulus da abokan tafiyarsa?

4 Darasi na farko shi ne cewa manzannin sun yi tsaro don ja-gorar a kan inda za su yi wa’azi. A wani labari, mun koya yadda Yesu ya yi amfani da ruhu mai tsarki da Jehobah ya ba shi don ya ja-goranci manzo Bulus da abokansa a tafiye-tafiyensu. (A. M. 2:33) Bari mu karanta labarin tun daga somawarsa.—Karanta Ayyukan Manzanni 16:6-10.

5 Bulus da Sila da kuma Timotawus sun bar birnin Listra a kudancin Galatiya. Bayan ’yan kwanaki, suka isa babban hanyar Roma da za ta kai su zuwa yammancin wurin da mutanen suka fi yawa a gundumar Asiya. Suna son su bi wannan hanyar don su ziyarci birane inda mutane da yawa suke bukatar su ji game da Kristi. Amma wani abu ya hana su. Aya ta 6 ta ce: “Suka ratsa ƙasar Firijiya da ƙasar Galatiya, gama Ruhu Mai-tsarki ya hana su faɗin maganar cikin Asiya.” Littafi Mai Tsarki bai faɗa dalilin da ya sa hakan ya faru ba, amma a wata hanya, ruhu mai tsarki ya hana matafiyan yin wa’azi a yankin Asiya. Bulus da abokansa sun fahimci cewa wannan ja-gorar ruhu mai tsarki yana nufin cewa Yesu yana son su yi wa’azi a wani wuri.

6, 7. (a) Mene ne ya faru da Bulus da abokansa kusa da Bitiniya? (b) Wace shawara ce almajiran suka tsai da kuma da wane sakamako?

6 Ina ne matafiyan suka je? Aya ta 7 ta bayyana: “Sa’anda suka zo kusa da Misiya, suka biɗi su tafi cikin Bitiniya; amma Ruhun Yesu ba ya yarda masu ba.” Da yake an hana su yin wa’azi a Asiya, Bulus da abokansa suka juya arewa, suna son su yi wa’azi a biranen Bitiniya. Amma, sa’ad da suka yi kusa da birnin Bitiniya, Yesu ya sake amfani da ruhu mai tsarki don ya hana su. Amma babu shakka, a lokacin mazan za su yi mamaki. Sun san jigon wa’azin da za su yi da kuma yadda za su yi wa’azin, amma ba su san inda za su yi wa’azin ba. Kamar dai sun ƙwanƙwasa ƙofar nahiyar Asiya, amma ba a buɗe ba. Sun kuma ƙwanƙwasa ƙofar Bitiniya, kuma ba a buɗe ba. Shin sun daina ƙwanƙwasawa ne? A’a, ba su daina ba!

7 A wannan lokacin, mutanen suka tsai da shawara mai ban mamaki. Aya ta 8 ta gaya mana: “Suka raɓi Misiya, kana suka zo Taruwasa.” Saboda haka, matafiyan suka bi ta yamma kuma suka yi tafiya na tsawon miloli 350, sun wuce birane da yawa har suka kai tashar jirgin ruwa na Taruwasa, hanyar zuwa Makidoniya. A wajen, a lokaci na uku, Bulus da abokansa suka ƙwanƙwasa wata ƙofa, amma a wannan lokacin, aka buɗe! Aya ta 9 ta faɗi abin da ya faru bayan haka: “Da dare ru’ya ta bayyana ga Bulus; ga wani mutumin Makidoniya yana tsaye, yana roƙonsa, yana cewa, ka ƙetaro zuwa Makidoniya, ka taimake mu.” A ƙarshe, Bulus ya san inda zai yi wa’azi. Nan da nan, mutanen suka shiga jirgin ruwa zuwa Makidoniya.

8, 9. Mene ne za mu iya koya daga tafiyar da Bulus ya yi?

8 Mene ne za mu iya koya daga wannan labarin? Ka lura cewa sai bayan da Bulus ya soma tafiya zuwa Asiya ne ruhun Allah ya soma yi masa ja-gora. Sai bayan da Bulus ya yi kusa da Bitiniya ne Yesu ya ba shi ƙarin ja-gora. A ƙarshe, sai bayan da Bulus ya isa Taruwasa ne Yesu ya ja-gorance shi zuwa Makidoniya. Yesu, a matsayinsa na Shugaban ikilisiya zai iya bi da mu hakan. (Kol. 1:18) Alal misali, wataƙila kana tunanin yin hidima a matsayin majagaba ko kuma zuwa inda ake bukatar masu shela sosai. Amma zai iya yiwuwa cewa sai bayan ka ɗauki matakin cim ma wannan maƙasudin ne Yesu ta wurin ruhun Allah zai ja-gorance ka. Alal misali, Sa’ad da mota take tafiya ne kaɗai direba zai iya juya motar ta hagu ko kuma dama. Hakazalika, sai sa’ad da muka ɗauki mataki ne kaɗai Yesu zai iya yi mana ja-gora don mu faɗaɗa hidimarmu, wato, idan muka sa ƙwazo don mu cim ma maƙasudinmu.

9 Idan ƙoƙarce-ƙoƙarcenka ba su sa ka cim ma maƙasudinka nan da nan ba fa? Ya kamata ka yi sanyin gwiwa ne, kana tunanin cewa ruhun Jehobah ba ya yi maka ja-gora? Ka tuna cewa Bulus ma ya fuskanci hakan. Duk da haka, ya ci gaba da nema da kuma ƙwanƙwasawa har lokacin da aka buɗe ƙofar. Hakazalika, idan ka nace wajen neman “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki,” kai ma za ka samu albarka.—1 Kor. 16:9.

KA NACE DA YIN ADDU’A

10. Me ya nuna cewa lura ƙwarai cikin addu’a zai sa mutum ya yi tsaro?

10 Bari mu tattauna darasi na biyu da za mu iya koya daga Kiristoci na ƙarni na farko game da yin tsaro, sun nace da yin addu’a. (1 Bit. 4:7) Nacewa wajen yin addu’a zai sa mu yi tsaro. Ku tuna cewa kafin a kama Yesu a lambun Jathsaimani, Yesu ya gaya wa manzanninsa uku: ‘Ku yi tsaro, ku yi addu’a.’—Mat. 26:41.

11, 12. Me ya sa Hiridus ya wulakanta Kiristoci da Bitrus kuma yaya ya yi hakan?

11 Bayan wannan aukuwar, Bitrus da yake wurin, ya shaida amfanin nacewa cikin addu’a. (Karanta Ayyukan Manzanni 12:1-6.) A farkon ayoyin wannan labarin, mun koya cewa Hiridus ya wulakanta Kiristoci don ya samu tagomashin Yahudawa. Wataƙila ya san cewa Yaƙub manzo ne kuma abokin Yesu ne sosai. Saboda haka, Hiridus ya sa aka kashe Yaƙub da “takobi.” (Aya ta 2) Ikilisiyar ta yi hasarar wannan manzo ƙaunatacce. Wannan gwaji ne sosai ga ’yan’uwan!

12 Mene ne Hiridus ya yi kuma? Aya ta 3 ta ce: “Sa’ad da ya ga wannan ya gami Yahudawa, ya koma ya dauƙe Bitrus.” Amma ba da daɗewa ba, an sako manzannin har da Bitrus ta mu’ujiza daga kurkuku. (A. M. 5:17-20) Wataƙila Hiridus ya san da hakan. Yana son ya tabbata cewa Bitrus ba zai gudu ba. Hiridus “ya bada shi ga hannun ’yan yaƙi guda goma sha shida, su tsare shi; yana da nufi ya fito da shi wurin jama’a bayan Faska.” (Aya ta 4) Abin mamaki! Hiridus ya saka Bitrus tsakanin masu gadi biyu a kurkuku, tare da masu gadi goma sha shida, suna yin tsaro dare da rana don su tabbata bai gudu ba. Manufar Hiridus ita ce ya sa jama’ar farin ciki ta wurin fito da Bitrus ga jama’a don ya kashe shi bayan Faska. A irin wannan yanayi mai wuya, mene ne ’yan’uwan Bitrus Kiristoci za su yi?

13, 14. (a) Yaya ikilisiyar ta aikata sa’ad da ta ji cewa an saka Bitrus a kurkuku? (b) Mene ne za mu iya koya daga misalin da ’yan’uwan Bitrus Kiristoci suka kafa game da batun addu’a?

13 Ikilisiyar ta san daidai abin da za ta yi. Aya ta 5 ta ce: “Bitrus fa yana tsare a cikin kurkuku: amma ikilisiya tana yin addu’a da himma ga Allah dominsa.” Hakika, sun yi addu’a da roƙo sosai a madadin ɗan’uwansu ƙaunatacce. Kuma, rasuwar Yaƙub bai sa su fid da rai ba ko kuma su yi tunani cewa addu’o’insu ba su cim ma kome ba. Akasin haka, sun san sarai cewa Jehobah yana jin addu’o’in ’yan’uwa masu aminci. Idan irin waɗannan addu’o’in sun jitu da nufinsa yana amsa su.—Ibran. 13:18, 19; Yaƙ. 5:16.

14 Mene ne za mu iya koya daga yadda ’yan’uwan Bitrus suka aikata? Yin tsaro ya haɗa da yin addu’a ba ga kanmu kaɗai ba amma har ga ’yan’uwanmu maza da mata. (Afis. 6:18) Ka san wasu ’yan’uwa masu bi da suke fuskantar gwaje-gwaje kuwa? Wasu suna fuskantar tsanani da hani daga gwamnati ko kuma tsarar bala’i. Zai dace ku saka waɗannan cikin addu’o’inku. Wataƙila kun san wasu da suke shan wahala da ba a ganewa da sauri. Wataƙila suna fama da matsalolin iyali da sanyin gwiwa ko kuma ciwo. Ya kamata ka ambata sunayen wasu ’yan’uwa da ka san su sa’ad da ka ke yin addu’a ga “mai-jin addu’a,” wato, Jehobah.—Zab. 65:2.

15, 16. (a) Ka kwatanta yadda mala’ikan Jehobah ya ceci Bitrus daga kurkuku. (Ka duba hoton da ke ƙasa.) (b) Me ya sa yake da ban ƙarfafa mu yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaki Bitrus?

15 Mene ne ya faru da Bitrus? Sa’ad da Bitrus yake barci tsakanin masu gadi biyu a kurkuku a dare na ƙarshe, wani abu mai ban mamaki ya faru da shi. (Karanta Ayyukan Manzanni 12:7-11.) Ka yi tunanin abin da ya faru, farat ɗaya, haske ya haskaka cikin kurkukun. Sai mala’ika ya tashe Bitrus da sauri, amma babu shakka, masu gadin ba su gan mala’ikan ba. Sai sarƙan da aka ɗaure hannunsa da shi suka zube! Sai mala’ikan ya fitar da Bitrus daga kurkukun, a gaban masu gadin da ke waje, kuma ta ƙyauren ƙarfen da ta buɗe musu da “kanta.” Da zara suka fita waje da fursunan sai mala’ikan ya ɓace. Bitrus kuma ya tsira!

16 Yana da ban ƙarfafa mu yi tunani a kan yadda Jehobah ya yi amfani da ikonsa wajen ceton bayinsa. Ko da yake ba ma tsammanin Jehobah ya cece mu ta mu’ujiza a wannan lokacin. Amma muna da tabbaci cewa yana amfani da ikonsa a madadin mutanensa a yau. (2 Laba. 16:9) Ta ikon ruhunsa mai tsarki, zai iya ƙarfafa mu don mu jimre wa kowanne gwaji da za mu iya fuskanta. (2 Kor. 4:7; 2 Bit. 2:9) Kuma ba da daɗewa ba, Jehobah zai ba Ɗansa iko don ya ’yantar da miliyoyin mutane daga mutuwa. (Yoh. 5:28, 29) Bangaskiyarmu ga alkawuran Allah zai ba mu gaba gaɗi sa’ad da muka fuskanci gwaje-gwaje a yau.

BA DA SHAIDA SOSAI DUK DA TANGARƊA

17. Ta yaya Bulus ya kafa misali mai kyau a yin wa’azi da ƙwazo da kuma gaggawa?

17 Ku yi la’akari da darasi na uku da za mu iya koya daga manzannin game da yin tsaro: Sun ci gaba da ba da shaida sosai duk da tangarɗa. Yin wa’azi da ƙwazo da kuma gaggawa yana da muhimmanci don yin tsaro. Manzo Bulus misali ne mai kyau a wannan batun. Ya sa ƙwazo sosai, yana tafiya mai nisa kuma yana kafa ikilisiyoyi da yawa. Ya jimre da mawuyacin yanayi, duk da haka bai yi sanyin gwiwa ba ko kuma ya daina kasancewa da azanci na gaggawa.—2 Kor. 11:23-29.

18. Ta yaya Bulus ya ci gaba da yin wa’azi sa’ad da aka tsare shi a ƙasar Roma?

18 Lokaci na ƙarshe da muka karanta game da Bulus shi ne a littafin Ayyukan Manzanni sura ta 28. Bulus ya isa ƙasar Roma, don ya bayyana a gaban Nero. An tsare shi, wataƙila an ɗaure shi a jikin sojan. Duk da haka, babu irin sarƙar da ta hana wannan manzon mai ƙwazo daga yin magana! Bulus ya ci gaba da neman hanyoyin yin wa’azi. (Karanta Ayyukan Manzanni 28:17, 23, 24.) Bayan ya yi kwanaki uku, Bulus ya kira manyan Yahudawa don ya yi musu wa’azi. A ranar da ya zaɓa, Bulus ya yi musu wa’azi sosai. Aya ta 23 ta ce: “Sa’ad da [Yahudawan wurin] suka sa masa rana, mutane dayawa suka zo wurinsa cikin masaukinsa; ya buɗe masu zance, yana shaida mulkin Allah, yana nema ya rinjaye su a kan zancen Yesu, daga cikin Attaurat ta Musa da annabawa kuma, tun safiya har maraice.”

19, 20. (a) Me ya sa Bulus ya samu sakamako mai kyau a wa’azinsa? (b) Yaya Bulus ya aikata sa’ad da wasu mutane ba su saurari saƙonsa ba?

19 Mene ne ya sa Bulus ya ƙware wajen yin wa’azi? Ku lura cewa aya ta 23 ta taƙaita dalilan. (1) Ya mai da hankalinsa ga Mulkin Allah da kuma Yesu Kristi. (2) Ya yi ƙoƙari ya taɓa zuciyar masu sauraronsa ta wajen yin amfani da ‘rinjaya.’ (3) Ya yi amfani da Nassosi. (4) Ya nuna halin sadaukarwa, ta wajen yin wa’azi “tun safiya har maraice.” Bulus ya yi wa’azi sosai, amma ba kowa ba ne ya yi na’am da abin da ya ce ba. Aya ta 24 ta ce: “Waɗansu suka gaskata abin da aka faɗi, waɗansu ba su gaskata ba.” Sai gardama ta tashi kuma mutanen suka watse.

20 Shin Bulus ya yi sanyin gwiwa domin ba kowa ba ne saurari bisharar? A’a! Ayyukan Manzanni 28:30, 31 sun ce: “Ya zauna a cikin gidan sufuri [haya] na kansa har ya cika shekara biyu, yana karɓan dukan waɗanda suka shigo wurinsa, yana wa’azin mulkin Allah, yana koyarwa da al’amura na wajen Ubangiji Yesu Kristi gaba gaɗi sarai ba mai-hana shi.” Da waɗannan kalamai masu ban ƙarfafa ne aka kammala littafin Ayyukan Manzanni.

21. Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Bulus sa’ad da aka tsare shi a cikin gida?

21 Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Bulus? Sa’ad da aka tsare shi a cikin gida, Bulus bai sami damar yin wa’azi daga gida zuwa gida ba. Duk da haka, ya kasance da ra’ayi mai kyau, ta wajen yi wa dukan waɗanda suka zo wurinsa wa’azi. Hakazalika, mutanen Jehobah da yawa a yau sun ci gaba da kasancewa da farin ciki kuma sun ci gaba da yin wa’azi duk da cewa an saka su a kurkuku domin imaninsu. Wasu ’yan’uwanmu maza da mata ba sa iya fita waje, wataƙila suna zama a gidan jinya saboda tsufa ko kuma rashin lafiya. Yayin da suka samu zarafi, suna yin wa’azi ga likitoci da baƙi da kuma wasu da suka shigo wurinsu. Muradinsu shi ne su yi wa’azi sosai game da Mulkin Allah. Muna godiya sosai domin misalan da suka kafa!

22. (a) Wane tanadi ne yake taimaka mana mu amfana daga littafin Ayyukan Manzanni? (Duba akwatin da ke sama) (b) Mene ne ka ƙudurta za ka yi yayin da kake jiran ƙarshen wannan zamanin?

22 Hakika, akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya daga tsaron da manzannin suka yi da wasu Kiristoci na ƙarni na farko a littafin Ayyukan Manzanni. Yayin da muke jiran ƙarshen wannan zamanin, bari mu ƙuduri aniya mu yi koyi da Kiristoci na ƙarni na farko wajen ba da shaida da gaba gaɗi da kuma ƙwazo. Babu gata da ya fi wanda muke da shi na ba da “shaida” game da Mulkin Allah!—A. M. 28:23.

MENE NE ZA KA IYA KOYA GAME DA:

․․․․․

Neman ja-gora a inda za ka yi wa’azi?

․․․․․

Nacewa da yin addu’a?

․․․․․

Ba da Shaida sosai duk da tangarɗa?

[Akwati da ke shafi na 13]

“BA ZAN ƊAUKI LITTAFIN AYYUKAN MANZANNI KAMAR YADDA NAKE ƊAUKANSA A DĀ KUMA BA”

Wani mai kula mai ziyara ya faɗa yadda yake ji bayan ya karanta littafin nan “Bearing Thorough Witness” About God’s Kingdom: “Ba zan ɗauki littafin Ayyukan Manzanni kamar yadda nake ɗaukansa a dā kuma ba. Na karanta littafin Ayyukan Manzanni sau da yawa, amma ban fahimci abin da na karanta ba, yanzu da na karanta wannan sabon littafin, ina jin zan ƙara amfana ta wurin karanta littafin Ayyukan Manzanni.”

[Hoton da ke shafi na 12]

Mala’ika ya ja-goranci Bitrus zuwa babban ƙyauren ƙarfe

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba